MATAR GIDA PAGE 45
MATAR GIDA 045
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P45
Safiyar talata karfe tara dai dai Jamila da Jaleela suna kitchen suna haɗa abin kare Unaisa kuma na can waje wajen masu decoration da Hajiya Zulfa'u ta tura su,tun karfe bakwai Hajiya Zulfa'u ta kira Unaisa ta sanar da ita masu decoration na hanya,tun karfe tara suka fara decoration ba su suka gama ba sai karfe biyu na rana,sosai decoration ɗin ya yiwa Unaisa kyau dake lokacin bikinta da Ɗalha bata yi wasu program ba iya walima kaɗai ta yi shima kuma ba a yi wani decoration mai tsada ba,Jamila ne tare da Jaleela tsaye wajen saif dake ɗakin Unaisa,Unaisa na daga gefe tana kallon ikon Allah ''a gaskiya bana son less na fi son abaya'' Jamila ta faɗa tana fidda kaya daga saif ɗin Unaisa wani tsadadden abaya ta dauko tare da mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''na dauki wannan'' a sanyaye Unaisa ta ce ''to'' duk tsiwa da rashin kunyar Unaisa ta ƙasa hana Jamila da Jaleela abinda suke tun shigar su ɗakin Jaleela ke lura da yanayin Unaisa ta fahimci Unaisa bata ji daɗin kwashe mata sutura da suka yi ba ita ko Jamila ba ta ma san Unaisa na yi ba kawai zaɓar kaya take, numfasawa Jaleela ta yi tare da faɗin ''Unaisa ke yi hakuri ba da shiri muka zo ba kuma ƙinga yau za a yi taro kowacce zata ƙore a daƙa kin ga kuwa muma ya kamata mu fita tsaf kar mu fita daban cikin mutane'' Unaisa ta ƙakalo dariya da bai kai ciki ba ta ce ''haka ne na fahimta bara na je na yi wanka in kun gama ku rufe min saif'' ta faɗa tana barin wajen ta nufi hanyar bathroom dake ɗakin,Jaleela ta ce ''oky babu damuwa'' tsadaddun dogayen rigunan Jamila da Jaleela suka dauko daga saif ɗin Unaisa ko sau ɗaya Unaisa bata taɓa sa su ba bayan sun gama zaɓarwa kansu kaya kowacce ta dauki atamfuna kala bibbiyu Unaisa ta danna zuciya bata ce masu komai ba,in Unaisa ta tuna da an gama taro za su bar mata gida sai ta samu sauki cikin zuciyarta,bayan fitar Unaisa daga bathroom shirya kanta ta yi cikin wani less blue da aka yiwa ado da fulawa ja sosai less ɗin ya yi mata kyau,karfe huɗu dai dai matan gida sun halarci gidan Unaisa cikin shiga ta kamala kowacce sanye take da atamfa da a ƙalla kuɗinsa zai yi dubu tamanin zuwa ɗari sun baza gwala gwalai suna zuba ƙhamshi kallo ɗaya za ka yi masu ka fahimci mata ne isassu masu ji da kansu wanda sun tara kuɗi,Hajiya Bilƙisu da Hajiya Zulfa'u idanunsu sanye da ɓakin madubi,suna tafiya cike da gadara da ƙasaita,kusan duk matan ƙungiyar suna da ƙiba,da yawan su farare ne harda wasu daga cikinsu suna shafa mai, masu shafa mai cikin su mai me shegin tsada suke shafawa wannan dalilin yasa in ba faɗa suka yi ba babu wanda zai gane hasken mai ne,yanda wasu sun zauna yadda Allah ya halicce su suna dai shafa mai me kyau amma ba me sa haske ba,tarɓa mai kyau Unaisa tare da su Jaleela suka yi masu,duk sun yaba da kyau da kuma tsarin bangaren Unaisa,karfe huɗu da rabi dai dai tawagar matan gida ne zaune kan kujeru compund ɗin gidan Ɗalhab kowace an ajiye mata ruwa da lemo a teburin gabanta,sai wani cika suke suna batsewa kamar sun sha yest,Hajiya Zulfa'u ta buɗe taro da addu'a kafin ta koma ta zauna
Bayan Hajiya Zulfa'u ta zauna Hajiya Bilkisu ta miƙe tsaye ta fara magana kamar haka ''Assalamu alaikum matan wannan kungiya mai albarka da fatan kuna lafiya kamar dai yadda muka saba yau zamu yiwa daya daga cikinmu rijistan shiga kungiya harda ba yau ta shiga kungiyar ba,amma kamar yadda kuka sani duk wacce ta zo garemu ta ce tana son shiga kungiya muna karɓar ta hannu bibbiyu walau budurwa matar aure ko bazawara sai dai duk budurwa da ta shiga cikin mu da sunan tana cikinmu ne kawai,duk wasu dokoki da sharaɗan kungiya baza su hau kanta ba sai ranar da ta yi aure haka zalika bazawara sai dai ita bazawara za a faɗa mata dokokin kungiya da sharuɗa amma ba su wajaba gareta ba sai bayan ta samu wani mijin ta yi aure saɓanin budurwa'' Hajiya Bilƙisu ta tsagaita na wasu ƴan sakanni tare da sauki hankichef ta share zufa tana mayar da madubi a idonta gyara tsayuwa ta yi tana mayar da dubanta ga Unaisa tare da faɗin ''Unaisa yau kin tabbata ƴar kungiyarmu,muna da wasu dokoki da sharaɗi sharaɗin kwara ɗaya ne tal,sharaɗin shine duk wacce ta shiga wannan kungiya baza ta fita ba har gaban abada in kuwa kin ce za ki fita to tabbas za ki yi nadama,dokokin kuma sune kamar haka na farko cikin watanni uku zuwa huɗu na shiharki kungiya dole ne ki siya mota kamar yadda kin gani kusan dukkan mu muna da mota zaurawan cikin mu ne kaɗai basu da mota abu na biyu shine cikin wannan shekara ko shekara me zuwa dole ne ki je Hajji sannan abu na uku kowanne karshen wata muna haɗa taru gidan ɗaya daga cikin mu kowacce za ta bada Naira dubu talatin,misali wannan wata za a haɗu a gidana kowacce zata bani naira dubu talatin wata me zuwa sai a haɗu a gidan ki a haɗa maki dubu talatin talatin zuwa taro gidan juna wannan dole ne babu ɗaga kafa duk wacce bata halarci taro ba kungiya zata cita taran naira dubu arba'in abu na huɗu shine duk bayan shekara muna canza furniture ɗin mu da kuma mota,sannan maganar siya mota da zuwa Hajji duk wata hanya da za ki bi ki samu dole ki bi ki samu kuɗade ki siya mota ki kuma je Hajji mu bamu san babu ba''shiru Hajiya Bilƙisu ta yi idonta kan Unaisa kafin ta daura da ''waɗan nan sune dokokin kungiya da fatan kin fahimta'' gyaɗa kai kawai Unaisa ta yi,ina zata samu kuɗi ta siya mota ta kuma je Hajji sanin kanta ne bata da wadannan kuɗaden kuma har ga Allah ba za ta iya fita daga kungiyar ba ko da Hajiya Bilƙisu bata ce ba a fita ba,ita bata da niyya fita
Unaisa na cikin wannan tunani ta jiyu muryar Hajiya Bilƙisu ta ce ''amarya tashi ki gabatar da kan ki'' numfasawa Unaisa ta yi kafin ta miƙe tsaye ta fara magana a natse ta gabatar da kanta kamar yadda Hajiya Bilƙisu faɗa mata bayan Unaisa ta gama gabatar da kanta ne sauran ƴan kungiya sun shiga gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya wanda da yawa sai yau Unaisa fara ganinsu amma kullum suna chat a group ɗinsu,bayan sun gama gabatar da kansu ne Hajiya Zulfa'u ta umurce mutanen da ta yi order abinci a wajen su da su sawa kowa abinda yake son ci,basu bar gidan Unaisa ba sai da ana daf da kira sallah magrib bayan an tashi taro wasu daga cikin ƴan kungiya sun koma ciki bangaren Unaisa inda sun ɗiɓa kayan abinci iya son ransu,kaji bakwai Ɗalha ya zubawa Unaisa cikin firiji amma kaf sun kwashe haka ma kifi, nama kowa basu bar mata ko kaɗan ba gaba daya sun kwashe katan ɗin taliya da macaroni da sauransu duk sun kwashe,buhun shinkafa ƴar gwamnati da Ɗalha ya siya mata raba shi gida uku suka yi inda sun dau kashi biyu sun bar mata ɗaya,Unaisa na compund tana sallamar baƙi bayan tafiyar bakin ne ta koma cikin gida lokacin su Jaleela da Jamila sun tafi,bayan shigar ta gidan ne ta ji ƙishi na niman hallakata duk wasu abubuwan ciye ciye da aka ci wajen taron ƙasa ci ta yi saboda gaba ɗaya bata cikin nitsuwa tunani kawai take inda zata samu ƙudin siyan mota,nan cikin kitchen ta tsaya ta sha ruwa bayan ta dauka daga firiji bayan ta gama shan ruwa ne hankalinta ya kai pantry inda aka tanadar domin tara kayan abinci,nan ta ga aika aika da matan gida suka yi mata,nan ta shiga bin pantry ɗin da kallo a hankali ta sulale jiki ta zauna nan ƙasa tare da daura hannu a ka murya can ƙasa ta ce ''na shiga uku ni kam harda ɓarayi ne cikin kungiyar?" ganin babu mai bata amsa yasa ta tashi ta wuce ɗaki ta dauki wayarta ta yiwa pantry ɗin vidoe tare da voice over tana kai ƙara ga shuwagabannin ƙungiya kan a bi mata hakki aiy wannan rainin hankali ne,ina dalili ta siya masu abinci sama da dubu ɗari shidda amma a ce su shiga mata kitchen su ɗiba mata ɗanyar abinci wallahi sai an biyata bata da matsala da Ɗalha in ya dawo da ya mata magana zata rufesa da masifa ta sani babu abinda zai iya yi iyaka ya kalleta kawai,Unaisa ta ƙasa zaune ta ƙasa tsaye sai kaiwa da komuwa take cikin parlour har an idar da sallah magrib Unaisa na nan cikin parlour tana jiran reply can ta ji motsin shigar saƙo da sauri ta buɗe waya ta shiga group ɗin matan gida cike da mamaki Unaisa ke kallon rubutun da aka tura tare da emoji na dariya wata ce ta yi mata reply inda ta ce ''amarya Unaisa mun je gidan ki kin bamu abinci amma ba ki bamu abun tsaraba ba,tsaraba suka yi da shi haka ta rubuta da emoji ɗin dariya cike da mamaki Unaisa ke bin saƙon can wata ta rubuta duk sanda mun ziyarci gidan ɗaya daga cikinmu to duk abinda mun gani a gidan in har ya yi mana dauka muke ba tare da tambaya ba sobada haka amarya Unaisa barka da zuwa kungiya,gaba ɗaya kanta ya gama kullewa wai wasu irin mutane ne haka wa ya kaita shiga cikin su gaba ɗaya kanta ya yi zafi ta dade zaune parlour tana tunani kafin daga bisani ta tashi jiki babu kwari ta wuce ɗaki ta dauro alwalah,karfe goma na dare dai dai Amirah ce kwance kan gado cikin ɗakinta tana mayar numfashi fitowarta kenan daga bathroom tun dawowarsu daga asibiti ita da Ammi ta ƙasa zama,Ammi bata faɗa mata inda zata kaita ba kawai ce mata ta yi tazo ta yi mata rakiya,bayan isowarsu asibiti Amirah bata kawo komai cikin zuciyarta ba a tunanin ta dubiya suka zo sai da ta ji wata nurse na tambayar Ammi ko Amirah ta taɓa haihuwa Ammi ta ce eh yaranta bakwai nan nurse ta mayar da dubanta ga Amirah sai a sannan suka gaisa,tun shigarsu entrance ɗin asibitin gaba ɗaya nurses ɗin hankalinsu na kan Ammi bayan Amirah ta gama gaisawa da nurse ɗin ne ta ce mata ta taso su tafi ita dai Amirah bata fahimci komai ba kawai ta tashi ta bi bayan nurse ɗin ganin ɗakin da ta shiga da ita yasa Amirah tambayar nurse ɗin ta ce mata lafiya me za ta yi mata,sai a sannan ne nurse ta yi mata bayanin cewar tun kwanaki uku da suka wuce Ammi ta zo asibiti ta biya ƙudi cewar tana son a yiwa ƴarta ɗinki ciki da waje sosai Amirah ta tsorata jin nurse ta kira mata ɗinki kamar baza ta yi magana ba sai kuma ta ce ''ba haihuwa na yi ba ɗinki me za a min? hasali ma ba a taɓa yi min ba duk haihuwata ba a taɓa kara ni ba'' nan dai nurse ta shiga kwantarwa Amirah hankali da kyar da ta samu Amirah ta amince nan ma sai da ta ce mata zata yi mata allurar kashe zafi,tun da aka yi mata ɗinki zafi da azaba sun hanata sakat
SHUUKRAN