SAFIYYA

SAFIYYA PAGE 3

by @smauta

Page 3

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

BAYAN SHEKARA BIYAR

Rabi ce na hango da wani tartsetsen ciki,tana surfa ma malam bala'i tana cemashi talasurun banza wanda bai iya cida gidan shi yana zaune kofar daki ya kasa cewa komi,tace kuma naje asibiti daga wannan haihuwar bazan kara haihuwa ba saboda yara ma baka iya rikon su rikon kirki ƙiri ƙiri inaji ina gani na hakura naba adama yayata lauratu ta tafi da ita lagos wurin neman kudin da takeyi ɗiyar tawa ta biyu saidai inna tace itama ta daukeman ita ina nan ka kawomu wannan mugun ƙauyen da bamusan kowa ba ka baro mu da garin mu na kwankwaso saboda shegen ciye ciyen bashin ka aka kusa hallaka mana rayuwa,muda kauyen kwankwaso yanzu saidai waya muddin mutane sukasan muna nan ƙauyen roni kashin ka ya bushe,malam dai uffan bai ce ba yana zaune ya zubama sarautar Allah ido,rabi tace hamza magana nike maka hwaa yace na'am rabi tace wai dazu nayi waya da inna ta naji yan ƙauye kwankwaso suna cema Habiba mata SANGARTATTA malam ya murmusa yace ai inna na kula da habiba sai abinda takeso shi takeyi su kuma kinsan yan ƙauye dasa ido shiyasa nasan suke ce mata SANGARTATTA😄tace ummm, Assalamu Alaikum wata yar black beauty yarinya da bazata wuce shekara biyar ba ta shigo da uniform din primary tashigo,tana shigowa inna rabi tace ke zonan sahiya kike ko safiyya wadda cikin ki daba na alheri bane munafuntata akayi saidai kawai naga uwarki da ciki wai malam ka zagaye kayima zuwaira ciki to dayake Allah ba azzalumin kowa bane cikin sai yazo mata da magangamin ajali ai yanzu zuwaira lokaci kawai take jira,ciwon ƙoda kuwa ai yariga da ya cinye zuwaira lokaci kawai take jira,malam yacema safiyya ke wuce ki bani wurin kikaiman tsaye saman kai sai kin shanye mana jini simi simi safiyya ta wuce dakin su tashiga ta hango ummanta kwance abunka da yaro ta ruga da gudu ta fada ta hayetaaaaa umma tace washhh safiyya bakisan banida lafiya ba?tace umma to ai na taso daga bokon
Umma ta lumfasa tace safiyyan ummanta yan boko Allah ya bada saa kinji ko yar albarka ga abincin ki can kije ki dauka kici sai ki cire uniform dinki anjima ki tafi islamiyya banda wasa duk wani namiji idan ya kiraki karkije kinji ko safiyya tace eh umma,umma tace Allah ka bayyana man mamata dada kafin wannan ciwon yayi ajalina in gano mamata kona samu wanda zai rikaman diyata safiyya,haka rayuwa ke tafiya yau da daɗi gobe babu mama kullum ciwo kara rufeta yake malam kuma bai canza hali na sai abinda rabi tace a gidan nan to tabbas da shi za'ayi girma nata zuwar ma safiyya mama kuma rauni yana kara rufeta a yanzu safiyya ta fuskanci rayuwar gidansu duka yasan wahalar da suke sha ita da umman ta,inna rabi kuwa tunda ta haihu safiyya ke rainon salisu autanta injita ta goyashi tai mashi wanka duk wata bautar salisu kan safiyya amma haka inna rabi zata saka bulala taima safiyya ɗan bura'uban bugu idan taji salisu na kuka sai tace tsunkulin shi takeyi😄 makarantar bokon ma tayi tayi malam ya hana safiyya ita kuma yarinya Allah yasamata son karatu malam nasa kafa ya fice safiyya zata dauki uniform dinta ta fice da gudu watarana ma cikin ajinsu takesa uniform saidai in ta dawo gida a kasheta da bugu saboda tayi alkawarin ita sai tazama likita,ta inganta rayuwar mama ta samamata lafiya shiyasa take shanye duk wani bugun da akeyi mata a gidansu akan bokon nan

Safiyya kuwa ta ƙeƙeshe rashin kunya sai wacce ba'ayi saboda tana laku lakun amma inaaaa kullum cikin jibgarta ake shiyasa yanzu ta tsefare bataji bata gani gatseni kuwa har yazamar mata jiki idan ta fita waje kuwa sai Sam barka amma tana shigowa soron gidansu zata yafa rigar rashin mutuncin ta itama ana cemata kulle sai tace casss abu daya take tsoro idan abbanta ya shigo yana bala'in nan yace zai koresuto shine kadai yakesa watarana saita russuna badan tana tsoro ba,a yanzu kuwa data girma itace wahala da umma sbd idan ciwon umma ya taso bata iya komai safiyy ita zatayi girki wasu yan iskan awakai da inna rabi ta kwashi adashe ta siyo an ƙaƙabamata ita ke kula dasu yanzu kuwa salisu ya girma ya raina safiyya in tayi shara sai ya bata gidan idan ta ɗebo ruwa saiya zudda ruwan itakuma safiyya muddin salisu yayimata haka fa ranar idonta idon shi saita cimashi uwa tasss😅dan mutunniyar rawa bata barin kota kwana,watarana ma da inna rabi da zaneta akan ɗebo ruwa bari tayi saida inna rabi ta ɗora girki ta kusa gamawa shinkafa saura kaɗan ta tsane ta dauke tukunyar tsaf tabar gidan da ita😅ta tara almajirai ta rabasu shinkafar ta aiko yaro da tukunyar tace acema mama rabi ita tayi sama🤣ranar fa an daki garwar bala'i a gidan dan ranar ba umma zuwaira ba hatta malam saida aka sauke mashi kwandon bala'i,aka kuma nemi safiyya ƙaura wambai a ƙauyen roni yarinya ta ɓoye,umma tun yana daukar abin wasa har dare ba safiyya ba labarin ta, hankalin ta tashi karfe goman dare ta fita neman safiyya duk inda tasan tana zuwa zaace batazo ba,tun tanada karfin tafiya har ƙarfin ta ya kare ta dawo gida can tsakar dare umma taji an hauro katanga jiff an duro gabanta ya fadi tace ɓarayi a gidan nan me muke dashi da za'a dauka bata gama mgnr a ranta ba taji alamun mutum yashigo ta haska torchlight dinta taga safiyya tsaye kafar ƙututu😅umma ta mike zaune tace ke daga ina tace umma wata ruga naje na boyema inna rabi tana rufe baki umma ta dauketa da mari tace safiyya ni zakijama sharri ina zamana lafiya sata kika koya?ina kika koyi sata safiyya?ina hakura dacin abinci in baki dan kici shine zaki daukema rabi tukunyar abinci kije waje ki cinye ehhh,safiyya tace wlh ko lashe banci abincinta ba sadaka nayi mata almajirai na rabawaaaa

Fauuuuuuu kakeji kan fuskar safiyya data dimau ce da wani gigitaccen mari safiyya ta fashe da kuka tace wayyo Allah umma aiko ina malam ne da rabi suka rutsa safiyya suke bugu kamar zasu kasheta ashe tun durowar ta a bango suka ganta,bugu suke kamar suna bugun ƙato umma tana basu hakuri amma ina tace zata fizge ɗiyar malam ya haɗa da ita ya dinga lafta mata bulalar nan a gadon baya,haba kafin kace me umma kingin ciwo ta sume malam naganin haka yace rabi kardai ace na kashe zuwaira😳😳rabi tace inma ka kasheta ka kashe banza an rage mugun iri ba wanda yaga ka kasheta sai wannan shegiyar itama kuma mu kasheta kawai…..wani irin tari ne ya tsarke mama da safiyya tayi sauri ta debo ruwa tazo ta shafama umma ta bata tasha tace umma ki yafeman ninaja maki wannan bugun umma na rokeki karki mutu umma,umma nice safiyyan ki umma idan kika mutu bansan inda zan saka raina ba,umaa tace safiyya ban mutu ba kuma na yafe maki kinji suka rike juna sai kukaaaaaaaaaaaaaaaaaa.

Bayan guduwar malam daga garin kwankwaso saboda bashin da sukayi mashi yawa tafiyar su jim kaɗan da watanni Dada ta kasa hakurin batajin labarin diyarta zuwaira ba saboda lokacin da aka kawota batazo ba ita uwace tadai san tabbas hamza ɗan garin kwankwaso ne watarana kuwa daga kano ta shiryo tazo da driver ta har garin kwankwaso neman malam hamza amma kash da zuwansu ake shaida mata malam hamza yaci kudin mutane ya kasa biya ya gudu ba'asan inda yake ba,ana kuma ake cemata matar shi zuwaira ta haihu tana fama da matsanancin ciwon ƙoda a yadda kuma labarai suka bazu a garin ance bayan tafiyarsu zuwaira rai yayi halin da, Dada gabanta ya fadi tace zuwaira ɗiyar ɗan uwanta daya tilo da kuma ita ta shayar da ita ta rasu,haka umma ta dawo gida kano gwuiwa sage har hawan jininta saida ya tashi kusan watan ta ɗaya asibiti mijinta da jikokin ta nata ɗawainiya da ita suna kwantar mata da hankalin idan da rai da rabo watarana Allah zai bayyana mata hamza sai taji labarin komai ya faru dasu🥹wayyo Dada🥹💔

WANNAN KENAN BACK TO STORY….


Yanzu ma aka fara nice taku har kullum mai son farin cikin ku SM AUTA ina maku fatan alheri✊👏🙏💃FREE BOOK NE BAN YARDA WANI KO WATA BA SU SAUYAMAN LITTAFI TA KOWANE SIGA BA IDAN KUMA MUTUM YAYI HAKAN NA BARSHI DA ALLAH…….. LITTAFINA NA SAFIYYA MALLAKIN SM AUTA KYAUTA NE💪💪💪💪 LET'S GO MY PEOPLE I LOVE YOU ALL❤️💃💃💃💃


Kullum safiyya cikin bauta take a gidan mahaifinta,inna rabi maidata boyi boyi,ita kuma safiyya ta dage akan rashin lafiyar mahaifiyar ta wanda yanzu ciwon ya tsananta ba ruwan abbansu da ummanta sai wata kawar safiyya da take shigowa ta taimaka ma safiyya wurin tsaftace umma ta kuma kawo masu abinci anan gaɓar da ake ciki safiyya ta ƙara zaburewa rashin kunya acikin gidansu hatta abban idan taga yayima mamanta ba dai-dai ba to fa bazata yarda ba,shiyasa yanzu inna rabi ta fita harkar ta kwata kwata saidai kullum da sabon tuggun da zata hadoma safiyya da umma da ke kwance dan kuwa yanzu inna rabi rabi tabi ƙauyen nan da suka tadawo na roni tace umma mayya ce ta gidi abinda yasama kenan ƙauyensu aka koro su shiyasa gatanan tanata ciwo mutanen dataci acan garin nasu ne suke tambayar umma,itama safiyya yanzu umma ta bata maitar shiyasa gaba daya babu mai rabar safiyya bata zuwa ko ina kullum tana gida jinyar umman ta sai in ta fita rijiya ɗibar ruwa kuwa tana zuwa kowa zai watse ace ga mayya nan karta kama mutum,safiyya tazama depressed shiyasa tana fita kullum cikin faɗa take da mutane in banda gidansu kawar ta babu mai saurarar su,damuwa ta taru tayima safiyya yawa ga baƙin talauci suna fama dashi kudin da zata samu ma takai umma asibiti batada su ga jikin umma saidai muce ALHAMDULILLAH dan kullum ciwon nata ba sauki,tun safiyya na kuka har zuciyar ta ta ƙeƙeshe burinta daya ne yanzu ta koma makarantar boko wanda har an cinye first term ita bataje ba burinta na biyu kuma Allah yaba ummanta lafiya🥹watarana tana zaune sai ga malaman NGO's an aiko su garinsu akan ilimin yara mata haka sukayi tsinke gidan mai gari anabi lungu da sako ana shela safiyya tana kwance kusada ummanta da bacci ya dauketa taji ana shelar aje kofar gidan mai gari ga malaman makaranta nan sunzo akan ilimin yara mata gaba tsulum ta mike ta zari wata koɗaddar hijabinta blue tayi kofar gidan mai gari….

Isar ta keda wuya an fara wayar da kan mata iyaye akan yadda zasu bar yaransu su shiga makarantar boko wani kyakkyawan saurayi ke bayanin wanda safiyya ta tsire shi da ido tana kallon shi ko kyaftawa batayi ita har ga Allah wani tunanin take daban bashi take kallo ba😅can taji kawar ta tana taɓo ta tace suna tambayar wanda bashida littafin makaranta da uniform su daga hannu aiko safiyya ta daga hannu wannan kyakkyawan saurayi yana binsu yana tambaya ajinka nawa har akazo kan safiyya,yana zuwa gabanta ya tsaya yace hey ajinki nawa, safiyya taji lokaci daya zuciyarta ta tsinke muryarta na kyarma kamar mai tunanin wani abu tace js 1 zanshiga ya kalleta da kyau yace zaki shiga?tace eh ya kara matsowa kusa da ita yace meyasa baki koma makaranta ba tace bamuda kudi,nan take yaji ƙirjin shi ya ansa yadda tai mashi maganar da sigar shagwaba yace kun tabbata idan na taimaka maki zakiyi karatun bazakiyi ƙalular makaranta ba tace wallahi zanyi karatu sosaiiiiiiiiiiiiiiiiiii in zama likita inyima ummata magani🥹matashin nan yayi shuru yace ya sunanki???tace MY NAME IS SAFIYYA HAMZA KABIR KWANKWASO arrr safiyya turawan roni😅samarin nan yace good👍ina babanki safiyya tayi shuru kawai sai yaga ta juya tabar wurin da gudu sai yaji gaba daya baiji dadin tambayar da yayi mata ba,amma ya dauki alwashin gobe yana tashi daga wurin aiki garin roni yayo wurin safiyya😅😅 
                    Fans mezan gani haka safiyya aljanna mai masoyawa dayawa ko safiyya zata cika burinta na zama likitar nan kuwa???To mu nutsa cikin rubutun muga yadda zata kasance💃💃🔥NICE TAKU HAR KULLUM MAISON FARIN CIKIN KU SM AUTA INA MAKU FATAN ALKHAIRI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃🔥

Washe gari kamal tundaga garin kano ya tuko motar shi Honda Accord 2015 har garin roni isowar shi keda wuya ya sauka gidan mai gari yayi mashi bayanin abinda ya dawo dashi,mai gari yayi na'am yasa aka nemo malam hamza yazo koda malam hamza yazo akai masa bayani firr yace bai yarda ba dama ko primary da tayi uwarta ce ta daure mata gindin yinta yanzu kuwa ta girma ba wata bokon yahudu da nasara da za'a saka mashi diya a koya mata karuwanciiiiiiiii shi safiyya aure zai mata,wannan kalmar aure ta soki kamal sosai ya girgiza kai yace ahh abba inason magana dakai baba ya dauke kai yace inajin ka,kunne keji ba ido ba🙄kamal yace haba abba bakasan ilimin ya'ya mata yanada amfani ba idan kabari safiyya tayi karatun nan kai kanka sai kafi kowa alfari da ita mace ita ke taimakon gida mudda ta samu,sannan mace itace makarantar farko ta yaranta da zata haifa yanzu baba kanada tabbacin idan kayi mata auren safiyya da take da burin tayi karatu zata zauna?sannan baba idan safiyya taji labarin auren nan ta gudu fa?kasan wane hali zata fada?kamar yadda taceman jiya tanaso tayi karatu dan ta nemama mamanta lafiya?Abba yai shuru kamal yace baba kungiyar mu ta NGOs bamu fara aikin nan da ba saida muka nemi na sani na malaman addini dana boko,amma tunda kace safiyya aure zakayi mata waye mijin baba??? Abba yai shuru mai gari yace hamza magana ake maka fa🙄abba yace ummm ranka ya dade ba mijin yanzu yarinyar batada mashinshini amma ina nan ina bincikawa zan samomata amma maganar bokon nan abarta akwai yayyenta biyu duk basuyi bokon nan ba kuma hankali kwance yanzu haka salisu kanenta na nan shima baiyi bokon ba mai gari sai itaceman zatayi boko,Abba ya juya wurin kamal yace kai yaro safiyya diyata ce kuma bazan yarda tayi boko baaaaa dan bafin sauran yarana zanen takashi tayi ba eheeeeee,

Kamal yace baba ina binka ta lalama ne kafin in fito maka da karfin ikon kungiyar mu,amma yanzu ina neman alfarma daya daga wajenka abba yace inaji,kamal ya gyara zama yace baba ina neman alfarma kabani auren yarka safiyyya,baba ya kwalalo ido yace yaro aure kace fa kamal yace eh baba ai aure zakayi mata kuma bakada wanda zakaba aurenta ni ina rokon alfarma daka auraman safiyya baba,mai gari yayi gyaran murya yace to ALHAMDULILLAHI hamza tunda dama yarinyar nan aure zakayi mata kuma gashi an samu mai sonta kabashi auren ta kawai, Abba yace hakane mai gari amma saina koma gida nayi shawara da iyalaina sannan,mai gari yace to kai kaji,kamal yace eh naji nakuma yarda da hakan Allah yasaka da alkhairi nizan wuce gaba gobe In Shaa Allahu zan dawo, Abba yace Allah ya kaimu lafiya sukayima mai gari bankwana kowa ya tashi,kamal yace baba idan ba damuwa ka shigo in rage maka hanya,baba bai musa ba yashiga motar nan yanata sake sake a ranshi kamal kuwa ya galgalama baba AC ana zuwa daidai gidanshi yace nan yayi saiga safiyya ta fito da wani katon bokiti zata tafi rijiya da sauri kamal ya fito yace mata safiyya,ko a mafarki bazata manta muryar dan gayun nan ba na jiya,Abba kawai ya raɓata ya shige gida🤣💔 kamal ya matso kusada safiyya yace ina zakije tace rijiya zanje debo ruwa,kamal yace babu masu saida ruwa a garin nan ne?tace akwai kamal yace meyasa baku saya ba saike zaki tafi cikin maza ɗibar ruwa safiyya ya karashe maganar da da alamar tambaya,safiyya tayi shuru ta sadda kai kasa tana cewa cikin ranta shikuma wannan ina ruwan shi dani kuma naga fa abba kamar daga cikin motar nan tashi ya fito,ya kira sunanta SAFIYYA tai firgigi ta farka daga dogon tunanin da take tace umm yace ina mamaki, safiyya tace umma na cikin gida batada lafiya kamaleyace Allah ya bata lafiya safiyya tace amin 🥹 💔 kamal yace wannan ne babanki safiyya?tace eh Abba nane ya hana in cigaba da makaranta ko?kamal ya sadda kanshi ƙasa yace eh safiyya wai aure za'ayi maki kinada wanda kikeso?tace Aure ni safiyya abba zayayima aure ta fashe da kuka tace nashiga ukku,kamal yace shiiiiii stop crying safiyya nacema Abba idan har aure zaiyi maki toni yabani auren ki amma yaceman sai yayi shawara mamanki zata yadda a banike aure?safiyya tace ni babu wani aure da zanyi kuma bazan aure ka ba,kamal yace safiyya aurena idan kikayi ceton ki zanyi zan aureki ne in kaiki gidanmu kano sai kicigaba da karatun idan kin gama karatun naki kin zama likita idan kin yarda sai in sakeki ki auri wanda kikeso ya haɗa hannun shi wuri ɗaya yace safiyya kiyiman wannan alfarmar kodan mahaifiyar ki ta samu lafiya kema kin inganta da karatun boko,habaa inaaa a lokacin safiyya tayi nisa cikin kuka tace umma zata yarda in aureki amma inna rabi ba lalle tabar abbana ya aura maka ni ba,kamal yace wacace kuma inna rabi?safiyya tace abokiyar zaman umma nace,kamal ya nisa yace safiyya marece zaimun a hanya gobe zan dawo idan nazo kuma zamuyi magana amma karki fadama umman ki maganar abbanki yace aure zayayi maki bazaki cigaba da makaranta ba tace to nagode har zata tafi yace safiyya ta juyo tace na'am yace baki tambayeni sunana ba tayi murmushi yace sunana kamal kuma a kano nake zo nan yayi mata alama da hannu ta matso ya zaro bandir din yan ɗari biyu guda daya ya bata yace ki aje hannunki ki sai maku ruwa yau karkije rijiya,tayi shuru tana kallon kudin tace wannan kuɗin idan na anshesu ummana zatayi fushi dani yaya kamal kawai ka koma da kudin zanje in debo ruwan ai na saba,kamal ya daure fuska yace idan babba yaba yaro kudi baya musu dashi ki amshi kudin nan kuma bance ki nunama umman ba gobe idan nazo dakaina zan fadamata na baki kudi kinji ko tace to tasa hannu biyu ta anshi kuɗin nan karaf kan idon rabi da tunda malam yazo ya fara fesa mata bayani tazo ta laɓe tana lekensu🤣🤣

Kamal yana nan tsaye jikin mota yana kallon safiyya harta shige gida,sannan yashiga motar shi ya tada sai kanooooo,safiyya na shigowa taga Abba da inna rabi tsaye kofar daki inna rabi tace to karuwan gari zonan ke daga zuwa har ya baki kudi ki ansa kina washe baki kamar ƙadangarwa,safiyya ta gyara tsayuwar ta tace wlh ba rokon shi kudi nayi ba shine fa ya bani yace kar inje rijiya dibar ruwan a siya ruwan kuma yanzu zanje bakin tasha taro mai ruwan bokitin kawai zan ajiye in tafi,inna rabi tace iyyi ke ƙundun ubanki nace uwariyonki tayo kan safiyya a gigice ta hau mazgarta tana danna mata ashar kala kala umma na kwance saboda tun shigowar malam taji komai yanzu haka ma da ake bugun safiyya taji,kawai umma a ranta tace kowaye wannan mai son safiyya nayi na'am dashi Allah ga amanar diyata nan naba wannan yaro Allah ka kulaman da safiyya, Allah yasa safiyya zatayi rayuwar ƴanci kamar yadda kowace ƴa mace keda ƴanci,inna rabi kuwa wurin bugun safiyya saida ta kwalkwale wannan kuɗi tass sannan tace maza ta dauki boki taje rijiya yau saita cika gidan nan da ruwa,haka safiyya ta dauki bokiti ta fita tana gunguni inna rabi zaki dawo ki sameni ni nike magana kike gunguni,tana juyowa taga abba yayi kasaƙeeeee alamar tausayin safiyya a ranshi ta buga tsoka tace malam bani hanya nan zan shiga daki kai tsaye anata kiran sallah bata tafi masallaci ba, Abba sumsum ya fice rabi ta kama ƙugu tace gaskiya nayi sake da har na lura da fuskar hamza ya farajin tausan safiyya dole yanzu in shirya kuwa komin dare sai naje wurin malam na kangeeeeeeeeeeee.

               Fans yaya labarin safiyya yana bada citta???
To mu hadu a comment section a kafta 🔥💃