Chapter 1
by @reza12
MIJIN AMAL
chapter 1
Bayan ta idar da Sallah kenan ta ɗaga hannu a fili ta fara addu'o'i kaman yadda ta saba. "Ya Allah ka buɗawa mijina duk wasu ƙofofin alkairanka. Allah ka haɗa shi da alkairi maras yankewa duniya da lahira. Allah ka bashi arziki mai albarka, ka yaye masa duk wata damuwar da take damunsa. Ubangiji kasa yafi ƙarfin duk wasu buƙatunsa, alfarmar Annabi Muhammad s a w". Ta na idarwa ta shafe jikinta. Ta na cikin naɗe sallayar ya turo ƙofar ya shigo da sallama. Ta amsa tana sakar masa murmushin da bata rabo da shi muddin yana kusa da ita. Ya ce "Allah ya amshi addu'o'in nan Hafiza, Ina tsaye a ƙofa ina sauraron ki, shi yasa ma na bari har sai kin gama kar na katse wasu". Tayi dariya tana faɗin "Idan ban maka addu'a ba wa zan yiwa Mijina?". Hafiz ya ce "Kinga idan nayi kuɗi ko hamm! Zan gina miki gida mai hawa bakwai ke ɗaya ba wanda zai zauna a ciki". Ya faɗa ya na dariya domin ya saba faɗa mata hakan. "Hahaha ni ɗaya kuma, to duk girman gidan da zaka gina mini idan babu kai a ciki ai shirme ne. Ni dai fatana ka zauna dani ni ɗaya dan Allah". Ta faɗa tana rungume shi. "Daga ke ba ƙari ke ɗaice wacce rai ke buri". Ya faɗa da sigar waƙa yana matseta a jikinsa. Gaba ɗaya suka yi dariya. Suna cikin haka suka ji ana sallama a palo. Koda ta fito taga ƙawarta ce Hadiza kamar an korota. Ta ce "Mugudu ko mu tsaya? Lafiya dai?" "Ke samu guri ki zauna, wannan abun ba na wasa bane, amma kafin nan Mijinki na gida ne?" "Eh yana gida mai ya faru?" Hadiza ta ce "Wani abu zan nuna miki, kuma bana so ya ji ko ya gani ne". "Hafiza ta ce "Wani abu kuma? yayi wani abu ne?" Ta ce "Ni dai kawai idan ya fita ki kira ni bani da lokaci". Ta na faɗa tayi waje ta bar Hafiza da mamaki da kuma fargaba. Sai zuciyar ta ta shiga wasuwasi da saƙe-saƙe. Ita dai ta yarda da mijinta bata zargin sa da komai. Haka ta koma ɗaki ta samu har ya fara karatun Alqur'ani na safe kaman yadda ya saba kafin ya fita. Ta kafe shi da ido ko zata tsinkayayo rashin gaskiya a fuskar sa. Amma ina koda yaushe fuskarsa fess take kamar zuciyarsa. Take ta kawar da wannan tunanin tayi murmushi ta rufe masa ƙofar. Hafiz bai bar gidan ba sai da ya karanta uzufi uku kaman yadda ya saba, sannan ya fita izuwa neman aikin da yake ta fama a cikin wannan satin. Ai kuwa yana fita ta kira Hadiza. Itama Kamar mai zama jira ta ƙaraso gidan a sukwane. Bayan sun zauna ta ce "Ina jinki? Mai ya faru?" Hadiza ta fito da waya. Ta ce "Buɗe datar ki". "Data kuma?" "Ke dai ki buɗe mana dan Allah?" Hafiza ta buɗe tana dai mamaki. Ta na budewa kuwa sai ga abu ya faɗo ta number Hadiza ɗin. Da sauri ta shiga chatting ɗin nasu. Sai taga decommt ne. Tai mata kallon ƙarin bayani. Ta ce "Sunan wannan littafi ne Mijin Amal, ɗazu na fara karanta shi, kuma ban ƙarasa ba, abun da na gani a cikin sa ne yasa na kasa natsuwa nace sai na kawo miki shi ko idan kin karanta zaki dawo hankalinki. Wallahi labarin wannan mutanen dake cikin littafin nan sak da rayuwar ki. Dan Allah ki karanta shi zaki bani labari". Ta na faɗa ta sake tashi tayi waje tana cewa "Zaki ga wacce ta dama ki son miji da masa addu'ar yayi kuɗi, daga baya kuma kiga abun da ya faru". Hafiza ta zubawa littafin ido cike da mamaki. Gashi kuwa sunansa Mijin Amal Kaman yadda tace. Sai kawai tayi dariyar fatar baki tana jin anya kuwa za'a samu macen da ta fita son miji. Bama wannan ba, taji kamar tace tana masa addu'ar yayi kuɗi kuma bayan yayi wani abu ya faru, to menene?". A fili ta ce "Idan ba rashin hankali ba, kawai dan kin karanta abu a littafi sai ya zama a gaske ma haka. Ita dai wallahi Hafizunta ba kamar na kowa bane. Kaman ba zata buɗe ba kuwa sai dai ta danna kansa har ya buɗe. Zata fara karantawa kenan aka kirata a waya. Ganin number Hafiz ɗin yasa a fili ta ce "Ɗan halak". "Albishirinki?" Ya faɗa ceke da fara'a?" "Goro" Ta bada amsa tana tashi tsaye ba tare da ta sani ba. "Alhamdu lillah, Hafiza yanzu aka turo min message ta email address na, sun bani aikin". Ya faɗa kamar zai fasa wayar dan murna. Ta ce "Alhamdu lillah! Yanzu kayi Sujjadar godiya ga Allah nima yanzu zanyi! Dan Allah ka tabbatar kayi, kuma duk inda kake ka dawo gida muyi alaula mu godewa". "Zan fara biyawa ta gida gurin Hajiya na faɗa mata. Bayan sun gama wayar ta sake godiya ga Allah. Har ta manta da wani littafi, sai dai kuma zata ajiye wayar kenan sai ta ganta a farkon labarin da ya ɗauki hankalinta saboda wani abu da aka fara sawa a farko.
Tana buɗewa ta fara cikin karo da gabatarwa kaman hakan.
"Ni Amal bari na fara faɗa muku waye mijina a gurina kafin mu shiga cikin wannan labarin mai kama da almara. Mijin ɗan aljanna ne a karon farko, mijina shine rayuwata, mijina shine komai nawa. Duk wani abu da Mace take buƙata a gidan aure, to tabbas na same shi. Farinciki, jin dad'i, soyayya, kulawa, mutuntawa, ciyarwa da shayarwa. Tabbas mijina ɗan aljanna ne sahun farko, aljannar ma irin wacce Manzon Allah s a w ya umarcemu da mu roƙa wato Aljanna Furdausi. Wannan shine halin mijina a tashin farko na auran mu. Amma daga baya mijina ya zama Tsinnanne, shege, ɗan matsiyata, azzalumi mara tsoron Allah ɗan wuta. Tabbas mijina ɗan wuta ne wallahi tallahi ba zanyi kaffara ba, mijina azzalumi ne, maha'inci ne. Nayi nadama nayi kuka na suma na shiga daga uku har zuwa tara akan mijina. Ina da tabbacin mijina ɗan wuta ne, wutar ma babbar wacce Manzon Allah s a w ya faɗa mana cewar a cikinta za'ayi wa munafukai azaba. Wato Hawiya".
Hafiza na zuwa nan da karatu ta gyra zama tana mamaki wannan matar kamar wata mahaukaciya ko aniya. Wani irin abu yayi mata haka da zata masa fatan shiga Hawiya. Ta buɗe shafi na gaba domin shiga cikin asalin labarin da har ta ƙagu taji.
Labarin mijin Amal labari ne mai cike da ruɗani da kuma soyayya mai tafiya da imanin mai karatu, soyayya kala uku ce, a kwai soyayya kafin aure, akwai soyayya bayan aure, sannan kuma a kwai asalin soyayya bayan dai auran. To ni gaba ɗaya mijina ya bani su. Ku da kanku zakuyi mamakin wannan lamarin kaman yadda nima nayi. Mijina mutum ne mai son rayuwar hutawa da holewa da kuma jin dad'i. Mijina mutum ne Kamar kowa sai dai Allah ya ba shi wata zuciya mai kyau wacce ba kowa Allah yake bawa ba. Mijina baya shaye-shaye, baya bin Mata. Kai a duniya samun miji irin nawa tabbas sai an tsallaka wata duniyar domin dai a wannan duniyar babu. Mijina ba mai kuɗi bane, haka zaluka ba kuma za'a ce masa ma mai rufin asiri ba, kawai dai yana da wadatar zuci, domin sau da yawa sai ya fita ya ke samo abun da zamu ci a ranar. Mun fahimci juna da shi tamkar ciki ɗaya muka fito. Yana da son wasa, hakan yasa gaba ɗaya hankalinsa ya tafi ga harkar wasanni. Misali. Mijina yana kallon Ball, wanda a gida muke kallo tare. Club ɗin da yake so sune Chelsea na ƙasar Ingila. Wanda yanzu haka tsaf zan iya lissafo muku yan wasan club ɗin gaba ɗaya saboda yadda nima yasa dole na san su. Haka zaluka yana kallon resslin, ɗan wasan da yafi so a gurin shine AJ style. Duk wasan sa baya wuce mu. Haka a finafinan indiya suma yana kallo sosai, babban jaruman sa shine Alu Arjun. A mata kuma Puja. Tabbas yana sonsu wanda hakan yasa nima nake mugun yinsu. Haka a nan gida Nigeria yan wasan Hausa yana son jarumai biyu. Wato Aminu Sharif Momo da kuma mai sunana wato Amal Umar. Tabbas Film Indai nasu ne ba'a barinmu a baya. Sannan a bangaren waƙoƙin Hausa yana son Umar M Sharif sosai. A Nigeria Film kuma yana son Soniya Uche. Wannan kaɗai zai tabbatar muku da cewar mijina ɗan wasa ne. Duk da haka fa baya wasa da addini, ranar juma'a tun sha ɗaya zai tafi masallaci, haka zaluka azkar na safe da na yammaci baya wuce mu. Sannan idan zamu kwanta dole ne sai mun haɗa baki a fili mun karanta addu'ar kwanciya barci. Duk wannan abubuwan da na lissafo tare muke yi, wani lokaci muna girki muna kallo ana dariya. Komai tare muke yi da mijina, mutum ne shi mai sauƙin kai da fahimta. Mukan hakura da wani abun akan dai samun abun da yake so na wasa. Sannan mijina yana da kishi, bana taɓa fita sai da nikaf, kuma ko ina shi yake kaini a mashin ɗin sa. Amma daga karshe mijina ɗan wuta ne in sha Allah. Nasan zaku min tambayar yanzu da nake baku wannan labarin shin muna tare ne ko mun rabu?" To ku biyo ni a cikin lamarin zaku fahimci komai kaman yadda aka saba".
Hafiza ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Amma wannan Amal ɗin bata da hankali ko, harda wani addu'a wai in sha Allah. To wai mai ya faru, ace ki samu miji irin wannan amma har ki tsaya ya kufuce miki. Tana faɗa ta sake buɗe shafin gaba domin shiga asalin gundarin labarin kaman yadda taga an rubuta.
*LABARI*
Fitowar ta daga ɗaki kenan ta hango shi zaune a palo. Ta ƙaraso da sauri tana mamakin ganin nasa. Ta ce "Au wai dama baka fita ba?" Ya juyo ya kalleta ya ce "Na tafi, amma na dawo". Ta ƙaraso ta zauna kusa da shi tana dariyar jin irin amsar da ya bayar. "Tom ina jinka mai ya dawo da kai?" Ta faɗa tana mamakin dawowar tasa, domin dai yanzu fa suka gama karyawa yace abokinsa Ali ne yake nemansa. Ya buɗe baki zai bata amsa kenan nefa suka ɗauke wuta. Ta kalleshi ya kalle ta. Sai kawai ta fashe da dariya domin dai tana da tabbacin dalilin ganin wannan wutan ne yasa zai tsaya yayi kallo. Ai kuwa ya kai mata kamu ta ta shi a guje. Ya bita tana dariya yana son kama ta. Har sai da ta faɗi kafin ya iya kama ta yana faɗin "Ai tambayar da kika min ce tasa aka ɗauke wuta, dan haka maza kisa su dawo min da ita kafin a fara dan Allah". Ya faɗa yana ɗaga ta. "Ai dama na sani, yanzu dai kaje ka dawo dan Allah". "Ok korata ma kikeyi kenan ko?" "No wane ni na kori rayuwata, kawai dai bana so ne ka rasa abu mai muhimmanci akan abun da nasan watarana muna zaune zasu kara sawa. Ko baka gida idan suka sa zan kiraka in sha Allah". Ya ce "Kinyi alƙawari?" "Eh nayi". Ya sake faɗa. "Tom bani abu mai dad'i kafin na tafi?" "Mai kake so yanzu a baka Yallaɓai?" "Ya nuna wani sashe daga jikita, sai tayi murmushi ta ce "Kai da kaya duk mallakar mai shi ne". Ya kama hannunta suka sa labule. Minti sha biyar ya sake wanka, ya sauya kaya ya suka fito.
Hannunsu cikin na juna har gurin da yake ajiye mashin ɗin sa. Ya ce "Amal ki cigaba da addu'ar Allah ya kawo mana wata yar dama mu saka sola a gidan nan mu huce takaicin yan nefa". Tayi murmushi domin tasan mijinta yana da wannan burin a ransa sosai, kasancewar sau da yawa ƴan nefa suna katse masa hanzari a lamurran sa. "Amin Angon Amal, ai kar ka damu muddin addu'ar mata nada tasiri a gurin Ubangiji, to Tabbas mijina zai tasirantu a rayuwarsa, zaiyi arzikin da babu talauci". Ya ce "Shi yasa nake sonki matar Yasir, Allah ya cigaba da buɗa min, zamu bawa mara ɗa kunya". Ya faɗa daidai yana tada mashin ɗin. Ta ce "Allah ya tsare min kai mijina, ya haɗa ka da dukkanin alkairin dake cikin wannan safiyar, ya baka abun da ka fita nema ya dawo min da kai lafiya. Sannan zan ajiye maka abun da ka fiso". Ya amsa da amin da kuma dariya domin ya gane abun da take nufi. Har ya fara tafiya ya ce "Kar ki manta fa kisa laptop din nan a chaji da kuma Pawapag idan sun kawo wuta, anjima muna da wasa". Yana faɗa ya ƙara gaba. Ta bishi da kallon so da ƙauna har ya ɓacewa ganinta. A ranta tana jin yanzu da ba shi ta aura ba kamar yadda mahaifiyarta ta dage da ba zata samu irin wannan farin cikin ba.
Ta dawo gida ta ɗauko ƴanfin (Radio) ta kamo waƙar Umar M Sharif ta kunna ta ƙure kara ita ɗaya a cikin gidan. Tana aiki tana bin waƙar kamar ita da shi suka rera ta. Bayan ta gama ta koma daki ta gyara gadon da suka hargitsa. Tana cikin gyaran suka kawo wuta. Tazo da sauri tasa komai a chaji. Ta kashe waƙar ta kunna kallo. Bata zauna ba, saboda ba Film ɗin da take so aka saka ba. Kiching ɗin ta shiga Allah yasa suna da taliya har guda uku. Ga kuma wake da ya kawo jiya. Sannan a kwai komai na hadi. Hakan yasa ta yanke shawarar kawai ta yi girki sai ta juye a kula, daga nan sai tayi duk shiriritar da zatayi. Haka kuwa cikin ƙasa da awa ɗaya ta gama abincin da ba kifi ba nama. Ta juye shi a Kula. Sannan ta dawo palo ta zauna. Tana zama kamar haɗin baki sai kuwa taga an saka wannan Film ɗin da tai masa alkawarin idan an sa zata kira shi. Dama part 1 ne da 2. To yanzu sun saka 2 ɗin. Ai kuwa ta rarimo waya ta latsa masa kira. Sai dai har ta katse bai daga ba, sai hakan ya bata mamaki. Ta sake gwadawa stli dai bai daga ba. Ta sake kallon number da kyau ta sake kira a karo na uku. Sai da ta kusa aka ɗaga. "Hi baby ina kan hanya ne idan na sauƙa zan kira ki". Ya faɗa da sauri. Ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To ka kula da hanya dan Allah, sai ka dawo, ina sonka". Ya amsa da amin yana mata kiss ta cikin wayar.
Yasir na fita sai da ya fara biyawa ta shagon sa na kayan sawa da yake sayarwa. Ya buɗe ya jira har yaron da yake zama masa a gurin ya zo. Kasancewar bayan wannan shagon yana ƴan buge-buge haka na rayuwa. Ya tada mashin ya nufi gurin Ali da yake ta kiransa, wanda yana da tabbacin ba wani abun kirki bane duba da yasan halin abokin nasa, sam ba mutumin kirki bane. Yana kan hanya sai kiransa yake, hakan yasa lokacin da Amal ta kira yayi tunanin shine yasa bai ɗaga a lokacin ba. Ya na zuwa Ali ya ce "Alhamdu lillah, kai wallahi Yasir kai ɗan iska ne wani lokacin, sai alkairi ya wuce ka ma a wannan iskancin naka". Ya faka mashin ɗin sa ya ce "Irin wannan kiran da kake ta min ko bashin ka dai na ci iyaka kenan, haba, kai baka taɓa kira sau ɗaya zuwa biyu uku ka hakura ne. To yanzu dai gani, Allah yasa dai samu ne?". Ya ƙarasa da tambaya yana shiga cikin shagon. Ali ya ce "Kai harka ce ta faɗo dan ubanka mai gwaɓin gaske, duk da nasan halinka, nasan da kana son kuɗi amma ba lailai ka yarda ba, sai dai kuma barin wannan damar daidai take da a baka kyautar GLK kace baka so". Yasir ya ce "Bani na sha, har kasa na fara hango Amal a cikin GLK wallahi, faɗa min yanzu muddin ba irin harkar ka bace?" Ali ya harare shi ya ce "Wata mata ce suka samu akasi da mijin ta har yayi mata saki uku cikin fushi, to kuma basa son rabuwa, sai dai kaga tunda saki uku ya shiga ai dole su hakura, amma kuma basa son hakan ya kasance".
Yasir yayi masa wani kallo ya ce "To meye nawa a ciki, maganar banza, baya son rabuwa da ita ɗin ne har ya sake ta dan uwarsa, sakin ma har uku, dan Allah bar wannan maganar wallahi har rai na ya ɓaci". Ali ya ce "Ba zaka taɓa cin ribar zance ba wallahi, ai sai ka tsaya naje end kaji ko". "To naji ma maganar ne kamar a kwai rainin hankali a ciki ne". Ya ce "Bari na fito maka da batum a faifai kaiwa. Wannan mijin da matar suna neman wanda zai auri matar nan ya sake ta a cikin sati ɗaya tal irgen yara. Zasu bashi zunzurutun kuɗaɗe har miliyan uku a farko, idan kuma kayi sakin a ƙara masa biyu, wato miliyan biyar kenan. Na nuna musu hoton ka sun yarda, idan ka amince yanzu zan faɗa musu, za'a ɗaura duk ranar da ka shirya. Dan girman Allah Yasir ka duba wanann abun, kuma auran sirri za'ayi ta bangaren ka, iya ta bangaren su ne za'a baiyana domin asan tayi aure". Ali ya ƙarasa yana kafe Yasir da ido.
Yasir yayi shiru yana kallon Ali. Yasan waye shi, kawali ne mai haɗa maza da mata a biya shi, kuma yana haɗa maza da maza da mata da mata, amma ko kaɗan bai taɓa yin sha'awar irin harkar ba duk da kuwa irin kuɗin da Alin yake samu. A cikin dai wannan harkar ya samu wannan shagon nasa, ga mota da gida mai kyau harda mata da yara biyu. Ali da Yasir gaba ɗaya suna son kuɗi tun tasowarsu, Ali ya faɗa harkokin neman kuɗi ko ta yaya ne, yayin da Yasir yake ƙoƙarin gujewa haram, gashi kuma Allah ya haɗa shi da mata mai fahimta da tunani irin nasa. Yasir ya ce "Kuma duk yan iskan mutanen ka sai ka rasa wa zaka kira sai ni ko Ali, wallahi ka raina min hankali ma, ko ka manta ina da mata ne, kuma dai auran kisan wuta kasan babu kyau a musulunci ko? To daga kai har su ɗin Allah ya shirye ku". Ya faɗa yana tashi zai bar gurin. "Kai matsala ta da kai rashin tsayawa ka fahimci abu wallahi, Yasir miliyan biyar fa, kuma babu wanda zai san kayi wannan auran har ita matar taka, ko ba komai zaka ƙara jari, dan Allah Yasir ka tsaya kayi tunani". Yasir ya hau mashin ɗin sa yayi masa ki ya ce "Bana so, kuma dan Allah kar ka sake kira na akan wannan maganar ku samu wani". Yana faɗa yayi gaba...📝
Mijin Amal