FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Salis Adam (S-Reza) Marubucin littattafan Hausa, sannan kuma ɗalibin ilimi. Alhamdu lillah! I Love All fans with one Hart🥰
Sample · Chapter 1
MIJIN AMAL chapter 1Bayan ta idar da Sallah kenan ta ɗaga hannu a fili ta fara addu'o'i kaman yadda ta saba. "Ya Allah ka buɗawa mijina duk wasu ƙofofin alkairanka. Allah ka haɗa shi da alkairi maras yankewa duniya da lahira. Allah ka bashi arziki mai albarka, ka yaye masa duk wata damuwar da take damunsa. Ubangiji kasa yafi ƙarfin duk wasu buƙatunsa, alfarmar Annabi Muhammad s a w". Ta na idarwa ta shafe jikinta. Ta na cikin naɗe sallayar ya turo ƙofar ya shigo da sallama. Ta amsa tana sakar masa murmushin da bata rabo da shi muddin yana kusa da ita. Ya ce "Allah ya amshi addu'o'in nan Hafiza, Ina tsaye a ƙofa ina sauraron ki, shi yasa ma na bari har sai kin gama kar na katse wasu". Tayi dariya tana faɗin "Idan ban maka addu'a ba wa zan yiwa Mijina?". Hafiz ya ce "Kinga idan nayi kuɗi ko hamm! Zan gina miki gida mai hawa bakwai ke ɗaya ba wanda zai zauna a ciki". Ya faɗa ya na dari...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.