21-22
Watanni uku sun shuɗe tun daga ranar da mutuwar Jameelu da haihuwar jaririyar Aisha me suna amna, suka sauya rayuwar Aisha gaba ɗaya, kuma a hankali, ƙarƙashin kulawar Moneer da kuma yawan kulawar da yake tabbatar mata ana ba ta, jikinta ya dawo da ƙarfi, ciwon da ta sha ya ragu, ta fara cin abinci yadda ya kamata, ta fara samun barci mai kyau, har ita da jaririyarta suka ƙara kyau sosai, abin da ya sa duk wanda ya gan su a yanzu ba zai yi tunanin irin mawuyacin halin da suka fito daga ciki ba.
Aisha kuwa, duk da cewa ba ta manta da Jameelu ba, ta fara koyon yadda za ta rayu da rashin sa, musamman saboda jaririyar da take ɗauke da wani ɓangare na kamannin mahaifinta, amma a cikin zuciyarta akwai abu guda da bai taɓa gushewa ba, wato sha’awar komawa Sudan domin kasancewa tare da ’yan uwanta, saboda duk lokacin da take waya da su sai su tambaye ta yaushe za ta dawo, ita kuma ta kan ba su amsa cewa da zarar jikinta ya ƙara ƙarfi, Moneer zai kai ta.
Ranar da suka cika watanni uku, Moneer ya kira Baba Ladi, matar da aka ɗora wa alhakin kula da Aisha da jaririyar tun lokacin da suka dawo gida, ya ba ta haƙƙinta tare da yi mata kyakkyawar sallama, yana mai godiya da irin aikin da ta yi musu.
“Baba Ladi, kin yi aiki mai kyau sosai kuma mungode Allah ya biyaki,” Moneer ya ce yayin da yake ba ta abin da ya shirya mata. “Allah Ya saka miki da alheri, daga yau Aisha ta samu sauƙi sosai, kuma ina ganin ba za ta ƙara buƙatar taimakonki kamar da ba dan haka zaki iya tafiya .”
Baba Ladi ta yi godiya sosai, ta yi wa Aisha da jaririya Amna addu’a, sannan ta tafi.
Aisha kuwa ba ta ji daɗin rabuwar ba, domin Baba Ladi ta zama kamar wata uwa a gare ta a cikin watannin da ta shafe tana jinya, amma abin da ya fi damunta shi ne cewa daga ranar da aka sallami Baba Ladi, Moneer ya fara rage yawan shigowa sashenta.
Yau da yamma, bayan Moneer ya dawo daga aiki, ya shiga ɗakin Aisha domin duba lafiyarta, sai ya same ta zaune a bakin gado tana sauya wa Amna kaya, yayin da jaririyar ke motsa ƙafafunta cikin fara’a kamar yadda yara sukeyi.
Da Aisha ta gan shi, ta gyara zamanta tayi sannan ta ce cikin girmamawa, “Sannu da dawowa, Moneer.”
“Yauwa,” ya amsa, yana kallon jaririyar kafin ya tambaya, “Yaya jikinku? Kuna buƙatar wani abune?”ya faɗi yana kallon agogon hannunsa.
Aisha ta girgiza kai.Tace
“A’a, komai muna da shi.”
Moneer ya gyada kai,yace"to Allah tashemu lafiya" sannan ya juya kamar zai fita, amma kafin ya kai ƙofa sai muryar Aisha ta dakatar da shi.
“Moneer…”ta kira sunanshi
Ya tsaya, amma bai juyo ba.
“Yaushe ne za ka kai ni Sudan?”ta jeho masa tambayar.
ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce cikin sanyin murya, “Da na shirya tafiyar, zan sanar da ke.”
Bai jira amsarta ba, ya buɗe ƙofar ya fita.
Aisha ta zauna tana kallon ƙofar bayan ya rufe ta, zuciyarta cike da tambayoyi.
Tun daga wannan rana, Moneer ya fara guje wa haɗuwa da ita kamar yana tsoron wani abu, domin idan yana son aymata da wani abun amfaninta sai ya aika megadi, idan akwai maganar abinci ko wani abu na gida, sai a kawo mata ba tare da shi ya shigo ba, idan kuma ya dawo daga aiki, sai ya wuce kai tsaye ɓangarensa, abin da ya sa Aisha ta fara jin cewa ko dai akwai wani abu da yake ɓoye mata, ko kuma ya sauya ra’ayinsa game da ɗaukar nauyin tafiyarta ta.
Duk da haka ba ta daina kiran ’yan uwanta ba.Tana basu haƙuri da tabbacin zata zo
“Ku yi haƙuri,Ina ganin ba da jimawa ba zan dawo.Insha Allahu”
“Kin tabbata?” ɗaya daga cikinsu kan tambaye ta.
“Eh, jikina ya yi kyau sosai yanzu, kuma Moneer ya ce da zarar na warke zai kawo ni.”
Saboda haka a Sudan suka fara shirya mata inda zata zauna bayan dawowarta, suna ɗokin ganin ita da jaririyar, musamman saboda tun kan rasuwar Jameelu rabonsu da ita shiyasa,sun yi kewarta sosai.