23-24
Haka wata guda ta sake wucewa ba tare da Aisha da Moneer sun yi wata tattaunawa mai ma’ana game da tafiyar ba.Hakanne yasa Aisha ta fara gajiya.
Wata Ranar Asabar dare ya yi sosai, gidan ya yi shiru,Aisha na zaune a ɗakinta tana jiran dawowar Moneer, jaririyar kuma tana kwance kusa da ita bayan ta gama shayar da ita.
Ta duba agogo.Ta sake dubawa.Sai daga baya ta ji karar motar Moneer ta shigo harabar gidan.Zuciyartace ta ɗan buga da ƙarfi.
“Yau sai na sake yin magana da shi,” ta faɗa a zuciyarta.Dan ta lashi takobin tafiya sudan akowanne hali
Miƙewa tayi Ta ɗauki jaririyar ta ɗora ta a bayanta, ta gyara ɗan mayafinta, sannan ta fito daga ɗakinta.
Ta tsaya a nesa tana kallon Moneer yayin da ya sauka daga motarsa, ya miƙa ma megadi wasu abubuwa, sannan ya nufi sashensa.
Sai Da taga ya shiga, Aisha ta jira ƴan daƙiƙu, sannan ta bi bayansa.
“Yau dole ne ya saurare ni,” ta faɗa a ranta, tana ƙara sauri.
Ta isa bakin ƙofar ɓangarensa ta tsaya, ta ɗaga hannu ta buga ƙofar sau biyu.
Babu amsa.Ta sake bugawa.
“Moneer”ta kira sunanshi
Shiru.Be amsaba be fitobaTa ƙara bugawa, wannan karon da ƙarfi kaɗan.
“Moneer, ni ce Aisha.”ta faɗi cikin ɗaga murya
A wannan lokacin Daga ciki sai ta ji motsin ƙafarsa.Yana zuwa
Ƙofarce taga an buɗe.Moneer ya tsaya a gabanta, sanye da kayan gida, fuskarsa cike da alamun gajiya, amma da ya ga Aisha tsaye a gabansa goye da jaririyar, wani ɗan canji ya bayyana a idanunsa kafin ya ɓoye shi da sauri.Yace
“Me ya faru?” ya tambaya.
Aisha ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, “Ina son mu yi magana ne.”
“Game da me?”ya buƙata
“Game da tafiyata Sudan.”ta bashi amsa tana kallonshi.
Moneer ya sauke idanunsa zuwa kan jaririyar da ke bayanta, sannan ya sake kallon Aisha.Yace
“Na gaya miki, idan lokacin tafiyar ya yi zan sanar da ke.”
“Amma to yaushe ne lokacin zai yi?” Aisha ta tambaya, wannan karon muryarta tana nuna alamun ƙosawa.
“kusan Watanni huɗu kenan ina nan, jikina ya warke, na gama jinya, ’yan uwana suna can suna jiran dawowata, kuma duk lokacin da suka kira ni sai na ce musu zan dawo nan ba da jimawa ba. Me ya sa kake ci gaba da jinkirta tafiyar?”cewar aisha tana kallonshi.
Moneer bai amsa ba.Aisha ta ci gaba da kallonsa.Tace
“Idan akwai wani dalili, ka faɗa min, Moneer. Kada ka riƙa gaya min ‘zan sanar da ke’ alhali wata guda kenan ya wuce ban ji komai ba.Daga gareka”
Moneer ya ɗaga idanunsa ya kalle ta sosai.Sannan yace
“Aisha, ki koma ɗakinki yanzu darene bacci nakeji.”
Ta girgiza kai.“A’a.Moneer inason sanine a fasa kainin ne kamar yadda kai alƙawari ko yaya? ”
Moneer ya ɗan daure fuska.Yace“Na ce ki koma ɗakinki.”
“Ba zan koma ba har sai ka gaya min gaskiyar abin da yake hana ka kai ni gidan bayan kaine ka hana a tafi dani.”
Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci,sannan ya sauke numfashi a hankali.Yace
“Ba yanzu zamuyi maganarba.”
“sai Yaushe?”cewar aisha
“Gobe.”ya bata amsa.
“Ka taɓa ce min haka.Amma gashi wata guda kenan shuru”
“Aisha…”ya dakatar dabita
“Na gaji da jira gaskiya.”ra bashi amsa
Moneer ya kalleta, sannan idanunsa suka koma kan jaririyar da take bayanta.Da yake yawaita ayyana abubuwa akanta a zuciyarshi dan yana ganin kamar zata kawo masa cikas a rayuwarsa.
A wannan lokacin ne Aisha ta lura ckallon da Moneer yake yi wa yarinyar ya ɗauki wani irin salo na daban, wanda ya sa zuciyarta ta ɗan yi mata wani irin nauyi ba tare da ta san dalili ba.
Moneer ya ce a hankali, “Ki koma ɗakinki ki kwanta. Za mu yi magana nace.”
“Yaushe?”ta tambaya
Ya yi shiru na ɗan lokaci,sannan yace
“Gobe,” ya amsa yana mata wani shuumin kallo.
Aisha ta kalle shi na wasu daƙiƙu, sannan ba tare da ta ƙara magana ba ta juya ta koma sashenta, amma wannan karon zuciyarta ba ta cika da kwarin gwiwar da ta fito da shi ba.
Domin a karon farko, ta fara jin cewa matsalar bata tafiyar ba ce kawai.Akwai wani abu da Moneer yake ƙoƙarin hana ta sani.Wanda taji zuciyarta na bata shawarar tayi ƙoƙarin son sanin meye shi wannan abun ɗin.