MATAR GIDA PAGE 46
MATAR GIDA 046
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P46
Rintsa idanuwanta ta yi tana jin yadda wajen ke mata zafi a wannan dare bacci ɓarawo ne ya dauki Amirah,abu ɗaya ke sa ta samu sauƙin zafi da azaba,in ta shiga ruwan ɗumi sai ta ji sakat da ta fita bayan wasu ƴan mintina zafin zai dawo washe gari da ƙyar Amirah ta samu ta lallaɓa ta tashi ta yi wanka ta gyara jikinta,tana shirin fita daga ɗaki Ammi ta shigo hannunta riƙe da tray ta daura wani kwanon tangaran mai zurfi (bowl) farfesun kayan ciki ne cike cikin kwanon yana fitar da tururi da alama ba a dade da sauke shi daga wuta ba,cike da girmama Amirah ta gaida Ammi,Ammi ta amsa mata tare da daura tray ɗin kan bed side drower,kallon tray ɗin Amirah ta yi ko ba a faɗa mata ta gane da akwai maganin mata cikin farfesun,muryar Ammi ta ji hakan yasa ta mayar da dubanta ga Ammi ''ki daure ki ci naman gaba ɗaya har ruwan duk ki shanye bara na je wajen yaran nan'' gyaɗa kai kawai Amirah ta yi ta bi bayan Ammi da ido,ba dan ranta ya so ba ta dauki kwanon daga tray ta fara ci,har cikin zuciyarta bata son yin wani gyara ba wai dan tana jin haushin Ɗalha ba kawai gyaran baya gabanta,tun da can bata cika damuwa da shaye shaye magungunan mata ba,kamar wasa ta cinye kayan cikin tas sosai ya yi mata dadi ita kanta sai da ta yi mamakin kanta kamar normal farfesun kayan ciki haka ta ji ɗanɗanon sa,bayan ta gama ci ta share baki tana shirin fita daga ɗakin Ammi ta shigo hannunta riƙe da wani kwanon tangaran cike da wani musulmin fruit salad amma an zuba wa fruit salad ɗin magani da zuma har ya canza kala maimakon ya yi fari kalar madara sai ya yi kore kore,ba tare da kallon fuskar Amirah Ammi ta miƙo mata kwanon tare da ɗaukar na kayan ciki ta ce ''maza ƙarɓi ki shanye'' daga haka ta fita daga ɗakin ba tare da kallon inda Amirah ke zaune ba ita dai Amirah ta bita da ido,mayar da dubanta ta yi ga kwanon ta dauki a ƙallah mintina uku tana ƙarewa fruit salad ɗin kallo kafin daga bisani ta kai hannu ta dauka har cikin zuciyarta bata son shan abubuwan nan dan Ammi kawai za ta sha,a hankali ta fara sha har ta gama ta ajiye kwanon,a hankali Amirah ta shiga sauki numfashi ji ta yi gaba ɗaya ta koshi,Ammi ta sake shiga ɗakin a karo na uku hannuta riƙe da wani kofin plastic kallo ɗaya Amirah ta yi mata ta runtsa ido ba za ta iya shan wani abu ba yanzu a hankali ta buɗe baki ta ce ''Ammi na ƙoshi bazan iya sha komai ba a halin yanzu'' taɓe baki Ammi ta yi kafin ta ce ''to aiy shikenan zan ajiye maki da anjima sai ki sha'' a hankali Amirah ta ce ''to'' daga haka Ammi ta fita daga ɗakin,bayan fitar Ammi Amirah ta dauki kofin tana kallon abinda ke ciki tsumin itatuwa ne cike cikin kofin,taɓe baki ta yi murya can ƙasa ta ce ''na shiga uku da Ammi''
Karfe tara dai dai na safiyar Laraba Unaisa ce kwance kan bed kamar marar lafiya ta yi nisa cikin tunani,tunani take kan dokokin ƙungiya da kuma yadda zata samu kuɗi ta yi abubuwan da ake buƙatar ta yi,daga gefe ɗaya kuma tana tunanin yadda zata gyara gida, bayan watse taro babu wacce ta yi tunanin ta taimakawa Unaisa da gyaran gida ko da sharar compund ɗin da aka yi taro ne,duk sun watse parlournta da sauran ɗakuna duk suna buƙatar shara da morping har da basu yi wani datti sosai ba,Unaisa na nan kwance tana mamakin wanda zai zo gidan a wannan lokaci jin ana bugun kofa tana nan kwance ta ji motsi kamar an buɗe gate,da wani irin sauri ta tashi daga kwanciya tare da zura hijab ɗin da ta yi sallah,tana shirin barin ɗakin Ɗalha ya turo kofar ɗakinta bakinsa dauke da sallama baki sake Unaisa ke kallonsa bata yi tunanin da wuri zai dawo ba a tunanin sai can yamma ko dare,a hankali Ɗalha ya tako har cikin ɗakin fuskarsa dauke da murmushi,jakar kayansa rataye a kafaɗarsa idonsa kanta ya ce ''babu sannu da zuwa?" numfasawa Unaisa ta yi kafin ta ce ''ban yi tunanin da wuri za ka dawo ba na yi tunanin sai dare'' a hankali Ɗalha ya tako har inda take jakar kayansa ya ajiye ƙasan ɗakin tare da kai hannu ya riƙe hannayenta duka biyu,a hankali ya janyota jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce ''sai kuma na dawo yanzu'' shiru Unaisa ta yi ta yi lamo jikinsa rabon da ya haɗa jiki da ita tun kafin ta fara wannan ciwon kaikayin,rungumeta ya yi yana sauki ajiyar zuciya murya can ƙasa ya ce ''ina ki ka baro wayar ki na yi ta kiran ki ba ki ɗaga ba'' shiru Unaisa ta yi tana son yin magana amma bata son ya ji warin bakinta harda jiya ta yi brush dalilin taro, ba dan taron ba ita da brush sai ranar juma'a a hankali ta raba jikinta da nasa tsaye Ɗalha ya yi yana kallonta hanyar bathroom ta nufa tana faɗin ''ina zuwa'' da ido Ɗalha ya bi bayanta har ta shiga cikin bathroom, bayan shigarta cikin bathroom Ɗalha ya ja ƙafarsa zuwa bed kwanciya ya yi tare da ciro waya daga aljihun wandonsa ya kira layin Amirah bugu ɗaya Amirah dake kwance tana fama da azabar ɗinki ta amsa kiran, cikin sassanyar muryarta ta yi masa sallama sai da ya gyara kwanciya kafin ya amsa sallamar fuskarsa dauki da murmushi ''ya na ji muryar ki haka ba ki da lafiya ne'' a natse Amirah ta ce ''eh kai na ke ciwo'' runtse idanunsa ya yi kafin ya ce ''kin sha magani? ko asibiti ki ke son zuwa?'' Amirah ta wani ƙara narkar da murya kafin ta ce ''a'a ba sai na je asibiti ba na sha magani'' Ɗalha ya ce ''oky ina yaran?" a takaice Amirah ta basa amsa ta ce ''ɓangaren Ammi'' dan jim Ɗalha ya yi kafin ya ce ''kun koma site ɗinki ne?" ''eh jiya'' cewar Amirah shiru Ɗalha ya yi yana tunani kafin can ya ce ''kenan da gangan Ammi ta riƙe ku bangarenta?" sarai Amirah ta fahimce abinda yake nufi amma sai ta ce ''kamar ya ya ta riƙe mu?" gashi nan daga bari na garin kun koma bangarenku'' ya faɗa yana gyara kwanciya dai dai lokacin da Unaisa ta fito daga bathroom kallo ɗaya ta yi masa ta taɓe baki, maganarsa ta karshe ya sa ta fahimci da Amirah yake waya,miƙa mata hannu ya yi alamar ta zo,da fari ta yi kamar bata fahimci abinda yake nufi ba sai kuma ta daura hannuta cikin nasa, kwantar da ita ya yi gefinsa tare da cire hular da ke kanta ya shiga wasa da sumarta
Cike da hikima Amirah ta canza zancen,sun dauki a ƙallah mintina ashirin suna waya,babu wani abinda Unaisa ta ji me kama da kishi hasali ma yunwa take ji kasancewar daren juya bata ci abinci ba muryar Ɗalha ne ya katse mata tunani inda ya ce ''an watse taro lafiya?" gyara kwanciya Unaisa ta yi tare da shigewa jikinsa ta ce ''lafiya ƙalau alhamdulillah'' shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''ba su gyara maki gida ba,bayan kun gama taron na ga compund gaba ɗaya sai a hankali ya yi datti and parlourn ki da ɗaki duk suna buƙatar gyara'' shiru Unaisa ta yi zuciyarta na mata zafi kwanaki biyu da Ɗalha ya yi bai kulata ba sanda suke Kano sosai ta ji daɗin kwanakin ko kaɗan bata son ya mata maganar gyara,lokaci guda walwalar fuskarta ta dauke,Ɗalha ya lura da hakan kawai sai ya ce ''zan kira almajirai gobe za su share mana compound,sai ki gyara ciki'' a dakeli Unaisa ta ce ''to'' ta faɗa tare da tashi daga jikinsa, tana shirin barin ɗakin Ɗalha ya jefo mata tambaya inda ya ce ''ina kuma za ki?" har sannan fuskarta babu fara'a ta ce ''kitchen zan je yunwa nake ji' yunƙurawa Ɗalha ya yi tare da miƙe tsaye yana faɗin ''muje na raka ki'' da sauri Unaisa ta ce ''a'a ka yi zaman ka kawai zan iya indomie zan dafa'' Ɗalha bai ce komai ba ya ja hannuta zuwa kitchen bayan shigarsu kitchen hankalin Ɗalha bai kai wajen kayan abinci ba pot ya dauka ya tara ruwa a ciki daga haka ya daura pot ɗin kan gas,Unaisa na tsaye kofar pantry Ɗalha ya mayar da dubansa gareta kafin ya ce ''kawo indomie mu sa ni ma yunwa nake ji'' Unaisa ta kafesa da ido Ɗalha na shirin magana idonsa ya sauka kan buhun shinkafa ganin shinkafar dake cikin buhu bai fi kwano shidda zuwa bakwai ba, da wani irin sauri ya ƙarasa ya shiga pantry ɗin nan ya shiga bin kayan abinci da ido cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa ya mayar da ga Unaisa da kyar ya iya furta ''what is this?" ya faɗa yana nuna inda ya shirya mata kayan abinci kafin ya bar gari cike da kwarin gwaiwa Unaisa ta ce ''me fa?" ta faɗa tana kallonsa a daƙeli Ɗalha ya ce ''ina ki ka kai kayan abinci da na siya two days ago?" gyara tsayuwa Unaisa ta yi kafin ta ce ''ohh oky kana nufin foodstuff? jiya bayan an tashi taro wasu daga cikin ƙawayena sun roƙi ni,ni kuma na basu shi ne kawai abinda ya fari'' ta faɗa tare da daukan indomie daga kwali,tun da ya aure ta bata taɓa ɓata masa rai irin yau ba wani irin zafi zuciyarsa ke masa ba dan ta bawa ƙawayenta abinci yasa ransa ya ɓaci ba a'a,a ganin sa rashin wayu da rashin sanin ya kamata ya sa ta bawa ƙawayenta foodstuff,da ɗiba masu ta yi dai dai misali hakan ba zai damesa ba amma ta kwashe komai ta basu,hannuta ya riƙe ya ja ta har parlour tana tambayarsa ko lafiya amma sai ya yi mata banza har cikin parlour ya zaunar da ita kan kujera one seater yana daga tsaya ya fara magana tun da take da Ɗalha bata taɓa ganinsa cikin wannan yanayi ba sosai ta tsorata amma sai ta danne zuciyarta magana yake cikin wata iriyar murya da ko ba a faɗa ba tabbas ransa a ɓace yake amma bai ɗaga murya ba ya fara magana inda ya ce ''daga ranar da na auro ki zuwa yau kin yi min abubuwa da yawa na ɓacin rai amma na danna zuciyata na yi hakuri..amma kin ga wannan abinda da ki ka yi yau Unaisa''...shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya daura da ''wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da za ki kwashe kayan abinci ba tare da sani na ba ki baiwa wani ko wata in ba haka ba za ki ga ɓacin raina..zan ba ki mamaki Unaisa zan maki abinda ba ki yi zato ba'' yana gama faɗin haka ya bar wajen taɓe baki Unaisa ta yi tare da faɗin ''abinci dai ba komai bane,abinda kashin sa za a yi,to me zai sa mutum ya riƙa ɗaga jijiyan wuya a kai'' sarai Ɗalha ya jita amma ya yi mata shiru bai ce komai ba
SHUUKRAN