ZALLAR SHA'AWA...

25-26

by @zahrasurbajo

Tun bayan ranar da Moneer ya gaya wa Aisha cewa za su yi magana washegari game da batun tafiyarta zuwa Sudan, Aisha ta ci gaba da jiran ranar ta zo da fatan zai tuna da maganarsu, amma kwana ya wuce, dare ya sake sauka, har lokacin da ta saba ganin dawowarsa daga aiki ya yi, duk da haka Moneer bai nemeta ba, bai aiko mata da saƙo ba, bai kuma aika wani daga cikin ma’aikatansa ya sanar da ita komai ba, abin da ya sa zuciyar Aisha ta fara cika da tunani iri-iri, domin a ganinta idan da gaske yana shirin kai ta Sudan, da tuni ya kira ta ya sanar da ita lokacin da za su tafi ko kuma ya gaya mata dalilin da ya sa har yanzu bai shirya tafiyar ba.
Da dare ya yi sosai, Aisha ta zauna a ɗakinta tana kallon Amna wadda take kwance cikin kwanciyar hankali, tana wasa da yatsunta dan ba ta san irin damuwar da ke cikin zuciyar mahaifiyarta ba, yayin da Aisha take ta tunanin abin da Moneer yake yi da kuma dalilin da ya sa ya yi shiru tun bayan wannan maganar tasu, domin duk lokacin da ta tuna da alkawarin da ya yi mata na cewa zai kai ta Sudan da zarar jikinta ya warke, sai ta ji wani irin kewar gida ya taso mata, musamman saboda duk wanda take da shi maana ƴan uwanta suna can suna jiran dawowarta, ita kuma tana jin kamar zaman da take yi a nan yana ƙara tsawaita fiye da yadda ta tsara.

A ƙarshe, ganin dare ya yi kuma har yanzu bai nemeta ba ya sa ta kasa jurewa, sai ta ɗauki wayarta ta kira shi, tana tsammanin watakila yana cikin sashensa ne ko kuma yana aiki akan wani abu da ya hana shi tunawa da ita, amma da wayar ta fara ringing, zuciyarta sai  ta ƙara bugawa saboda ba ta san irin amsar da za ta samu ba.
Bayan ɗan lokaci sai aka ɗaga wayar.
“Hello?” muryar Moneer ta fito, amma Aisha tana ji muryarsa sai hankalinta ya tashi, domin muryar ba ta da ƙarfi kamar yadda ta saba ji daga gare shi, kuma akwai wani irin yanayi a cikinta da ya nuna mata cewa akwai abin da ke damunsa.
“Moneer?” ta kira sunansa cikin fargaba, “lafiya kuwa? Me yake faruwa da kai? Muryarka kamar baka da lafiya.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya amsa cikin kasala, “Ba ni da lafiya ne.”
Aisha ta mike daga inda take zaune kamar wacce aka tsikara, “Ba ka da lafiya? Me ya same ka? Ka kira likita ne? Kana ina?”sune jerin gwanon tambayoyin na aisha hankalinta atashe.
 ya amsa,mata  amma muryarsa na ci gaba da nuna baya jin daɗi “ciki na ne yake min ciwo.”

“Ciki?” Aisha ta maimaita cikin damuwa, “Tun yaushe? Ka sha magani kuwa?”

“Ban sha ba.”

“Me ya sa ba ka sha ba? Ai kai likita ne, ya kamata ka san abin da za ka yi idan wani abu ya same ka.”cewar aisha

Moneer bai yi saurin amsawa ba, sannan ya ce, “Yau ban samu damar cin abinci ba ma.Taya zan sha magani”

Aisha ta zaro ido, “Har yanzu ba ka ci abinci ba?”
“Tun safe.Ba abinda naci”ya bata amsa.
Maganar ta ƙara tayar mata da hankali, domin duk da abubuwan da suka faru a tsakaninsu a baya, Moneer shi ne mutumin da ya kasance yana kula da ita da Amna tun bayan mutuwar Jameelu, don haka ba za ta iya jin yana fama da rashin lafiya ta zauna kawai tana kallonsa daga nesa ba.

“Ko tea baka shaba?"cewar aisha
“Ban jin ƙarfin jikina bazan iya yin komaiba.”cewar moneer

Aisha ta lumshe idanuwanta, tana jin wani irin tausayi na mamaye zuciyarta, sannan ta ce, “To, me yasa ba ka kira wani ya taimaka maka ba?”
Sai Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce cikin wata murya mai rauni, “Shi ya sa na ce miki ban da lafiya.”

Aisha ta yi tunani na ɗan lokaci, sannan ta ce, “To ka kwanta ka huta, zan—”

Kafin ta ƙarasa, Moneer ya katse ta da cewa, “Aisha.”
“Na’am?”ta amsa
“pls Ki zo.”cewar moneer
Ta tsaya  tai shiru.Sannan tace
“in zo ina?” ta tambaya cikin rashin fahimta.

“Ki zo ɓangarena,” ya amsa, “ina bukatar taimako.”

Maganar ta sa zuciyarta ta ɗan buga, domin duk tsawon lokacin da ta zauna a gidansa, ba ta taɓa shiga ɓangaren da yake zama ba,sabia  ita tana sashenta tare da Amna, shi kuma a nasa, kuma ko da yake ba wani sabon abu ba ne mutum ya je ya taimaka wa wanda ba shi da lafiya, har yanzu zuciyarta ta ji kamar wannan karon akwai wani abu daban gameda kiran da yay matan.