ZALLAR SHA'AWA...

27-28

by @zahrasurbajo

Amma ganin ba shi da lafiya, kuma tun safe bai ci abinci ba, bai sha magani bane, sai ta kawar da duk wani tunani da zai hana ta zuwa, ta ɗauki Amna ta goya a bayanta, sannan ta fita daga ɗakinta ta nufi part ɗin nashi
Wannan shi ne karo na farko da Aisha ta nufi ɓangaren Moneer da kanta tun bayan da suka koma gidan, kuma yayin da take tafiya a cikin gidan da dare ya riga ya yi, ta kasa hana kanta jin wani irin sabon yanayi a zuciyarta, domin ko da yake ta saba da ganin Moneer a matsayin mutumin da yake taimaka mata, wannan karon tana shiga sashensa ne ba tare da wani mutum tare da ita ba,
tana shiga falon,ta tsaya ba tare da ta shirya ba.Sabida Falonsa ya yi matuƙar kyau, kayan ɗakin an zaɓa su cikin tsari mai kayatarwa, kujerun sun kasance masu kyau da tsada, hasken fitilu da ƙamshin turarene ya ba wajen wani irin nutsuwa, sannan komai yana nan cikin tsafta da tsari wanda ya sa Aisha ta manta dalilin da ya kawo ta wajen, domin idanuwanta sun shagala gun bin kowane ɓangare na falon da kallo cike da mamaki, tana kallon yadda aka haɗa kayan cikin salo mai kyau..

Ta tsaya tana kallon wata babbar show glass da aka jera komai na cikinta da kyau, sannan ta kalli wasu kayan ado da ke gefe, kafin ta girgiza kai da kanta ta ce a zuciyarta, “Aisha, me kike yi? Mutum na rashin lafiya, ke kina tsaye kina kallon kayan falonsa?.”
Da sauri ta ɗauke idonta akan falon Ta ɗauki wayarta ta sake kiran lambar Moneer, domin har yanzu ba ta san ainihin inda yake ba.
Bayan ya ɗaga wayar ta ce, “Ina kake?”
“Ina sama.”
“Wane ɗaki?”
“Ki hau sama, za ki gan ni.”
Aisha ta ɗan kalli matakalar da ke gabanta, sannan ta fara hawa a hankali, tana riƙe da Amna sosai a jikinta, har ta kai saman ta fara kallon ɗakunan da ke can, amma kafin ta yi nisa sai ta ji ya kirata da murya mai rauni daga wani ɓangare.

“Aisha.”ya kirata ahankali

Ta bi hanyar da  muryar ke fitowa, har ta isa bakin ɗakin.

Koda ta leƙa ciki sai ta ga Moneer kwance a ƙasa,, fuskarsa cike da alamun gajiya, hannunsa ɗaya yana riƙe da cikinsa, yayin da numfashinsa yake fitowa a hankali kamar wanda ya kwashe lokaci yana fama da ciwo.

“Astaghfirullah!” Aisha ta furta cikin firgici, ta shigo ɗakin da sauri, “Moneer, me ya same ka haka?”
Ya ɗaga kansa a hankali ya kalle ta, sannan ya ce, “Ciki na ne.”
Ta zauna kusa da shi cikin tausayi, “Tun yaushe yake maka ciwo haka?”
“Tun ɗazu.”
“Ka sha magani?”
Ya girgiza kai.
“Me ya sa?”
“Ban samu damar yin hakanba.”

Aisha ta kalle shi da mamaki, “Kai fa likita ne, Moneer, yaya za ka bar ciwo ya kai ka wannan hali kuma ka ce ba ka samu damar shan  magani ba?”
Bai amsa ba, sai dai ya rufe idanunsa na ɗan lokaci kamar wanda ko magana ma ta fara zama masa wahala.
Aisha ta ji tausayinsa ya ƙara shiga zuciyarta, sannan ta ce, “To bari in kira wani ya zo ya duba ka.”
Nan take ya buɗe idanunsa ya kalle ta.Yace

“A’a.karki kiramin kowa"

“Me ya sa?”

“Ba sai kin kira kowa ba.”

“Amma kana kwance a ƙasa kana jin ciwo, Moneer nide tsoro nakeji ka bari ataimaka maka.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, “Abin da nake buƙata yanzu shi ne in yi wanka.”
Aisha ta kalle shi cikin mamaki,tace “Wanka?”
“Eh.”ya bata amsa

“Yaya za ka iya yin wanka a wannan halin?”

“Ki taimaka min ki haɗa min ruwan wanka kawai.”ya bata amsa

Ba msu Ta miƙe da sauri, tana shirin shiga ɗakin wankan da Amna har yanzu a bayanta, amma kafin ta kai ga ƙofar sai Moneer ya kira ta.

“Aisha.”
Ta juya, “Na’am?”

“Ki kwantar da Amna mana.”

Ta kalli jaririyar da ke bayanta, sannan ta kalle shi.Tace"naga bacci takene shine yasa

“Za ki shiga toilet da ita da daren nan kanta ko hula babu?” ya tambaya cikin wata murya mai sauƙi, kamar yana faɗa mata abin da ya kamata  ta fahimta.
Aisha ba ta kawo wata komai a ranta ba, domin hankalinta gaba ɗaya yana kan rashin lafiyar da Moneer yake ciki, don haka ta dawo ta cire Amna daga bayanta, ta kwantar da ita a kan gadon da ke kusa dashi,sannan ta juya ta nufi ɗakin wankan.
Ko kaɗan Ba ta yi tunanin dalilin da ya sa Moneer ya dage da cewa ta kwantar da Amna ba, ba ta kuma yi tunanin yadda wannan dare zai iya canza abubuwa da yawa arayuwarta ba; abin da ta sani kawai shi ne mutumin da ke gabanta yana fama da ciwo, kuma ta ji ya kamata ta taimaka masa kamar yadda shi ma ya taɓa taimaka mata a lokacin da rayuwarta ta yi mata tsanani.