BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 17

by @maidambu41


"Da wani yana da iko to da ya kalubalanci ƙaddara, amma da yake sha'anin na Allah ne ba wanda ya isa cewa bai iya ba, da kake mishi gori da ƙaddaransa kasan karshenka? Eh ita karshen nan dai mutuwa ce bayan ita sai me zaka ce ko? To tsakiyar ka sani ne? Shi yasa wasu suke cewa idan ka san farkonka to baka san tsakiyarka ba domin bai zama dole ya kai farkon domin ƙarshen ai mutuwa ce, kada ka kara kallonshi da rayuwarshi ta baya, ko ba a gaya maka ba ka kalle shi da kyau kasan bai kama da wanda ya faɗa tarkon shaidan ba, ita kanta rayuwar da yake abin ace Alhamdulillahi ne tunda har yau ba a ga yayi hauka ba kashe kashe, Alhamdulillahi ina da yakinin wata rana sai labari. Sannan Hajjama Rukayyah ta shirya gobe ta koma ɗakinta, tunda har ya fara wanke kafarshi ya biyo Matarshi ina da tabbacin wata rana zai zo ya dauke ta ba ruwansa. Kuma yana da ikon yin haka tunda Matarshi ce."


     "Nima haka na gani, ita tana taya ɗanta kishi ne don an ka sa su da kasa amma maganar gaskiya Yaron nan babu wata manufa ko matsala a maganar da yayi matuƙar yadda ya fada cewa ba zai katse mata karatunta da rayuwarta ba, ina ga ya kamata Rukayyah ki yi hakuri ki barwa Allah ikonsa, kada ki zurma dayawa ki ji kunya." Inji Hajjama,

     Cike da takaici kamar tayi kuka ta ce musu. "Wallahi itama bata son auren nan, kuma ga can ku tambaye ta bata sonshi." Inji Maamah, kafin wani ya bata amsa ta kara da cewa. "Ina da tabbacin wallahi ko kai ta aka yi ba zata taɓa samun nutsuwa ba, Allah ya gani bana goyon bayan auren nan kuma nasan Hajiya ba zata barta haka  ba balle yayanta da jikokinta." Murmushi Hajjama tayi tana fadin."tow ba sai ki kyale su da ita ba, ki ga idan Mijinta bai tsaya mata ba sai ki tsaya mata, amma yanzu kika sake bayan auren wani abu ya faru wallahi za a ce kece dama bakya son zaman aurensu, muna nan dake za'a yi ta yawo dake kin kashe auren Yarki don wata manufa naki, amma idan kika yi hakuri wani abu ya faru ko  idan zaman bai yi dadi ba. Ni da Yayanki zamu shiga mu fita a kashe auren ba tare da an kai ruwa rana ba ko ba haka ba?"

         Sanin cewa haka zai iya faruwa, aka zuciyarta bai yarda zasu aikata haka ba, amma ganin yadda Hajjama take rarrashinta, yasa ta saka a ranta zata hakura su koma gidan. Amma batun ta bawa Adam damar ɗaukar mata Y'a wannan zancen ake so, ita ai bata da maƙiya a duniya sama da Hajiya da bangarenshi. 

***

     Tuka motarshi ya cigaba da yi, yana goge bakinsa da Mahmoud ya zabga mishi naushi har ya fashe, tsotse jinin yayi yana kallon hanya, murmushi yayi ya cigaba da tafiya har ya isa gida, ko bangaren Hajiya bai leka ba domin yasan itama wata kayan damuwa ce yana shiga zata kara mishi wani damuwar ne, domin maganar gaskiya yadda ya ga idanunta nan yasan tana jin jiki, ya shiga bangarenshi wiwinsa ya nima ya fara bankawa cikinsa, yana fitar da iska baki da hanci, lumshe idanunsa yayi yana jin kanshi yana ɗaukar chaji, yadda ya ga ta kara dunƙulen a cikin bargon ya bashi dariya, cizon bakinsa yayi yana mai zukar wiwi din sai da ya zuketa tas ya fesar da hayakin hanci da bakinsa ya yana d'ago kai, ya bude rinnanun idanunsa, yana kara hango lokacin da Mahmoud ya zubga mishi naushi, ta bude idanunta da suke cike da kwalla. Tana gudunsa amma bata kaunar wani abu ya sameshi,  me ya kawo haka? Zukar wiwi din yayi sannan ya zauna yana kallon sararin samaniya a cikin daren nan.  Shafa kanshi yayi yana tuna yadda Mahmoud ya zubga mishi naushi, jin wurin yayi yana mishi tsami. Zai rama kota tsiya ko ta arziki shi ba'a cin bashinsa a zauna lafiya.  Banda a gaban Hajjama yake ai Mahmoud yaci uwar karya ya kwana da yunwa ya naushe shi a zauna lafiya? Haba karya kenan. Shi fa yafi kurma naci, shi yasa fadarshi baya karewa ta dadi kuma duk wanda ya fara fada da shi dole yake guduwa ya bar fadar domin shi a wurinsa ba karamin jarumta ba ce ka tsaya ka nunawa Duniya waye kai. Amma dan iskan gaye nan ya naushe shi, murmushi yayi yana shafa wurin, tabbas yayi kuskure ta yadda zai ganar da shi kuskurenshi. Zai rama wallahi.

          Har dare ya raba yana wurin, komawa cikin parlourn yayi ya dauki wata jacket dinsa baki, ya saka hula a kai ya fito. Da kafa ya isa La Coffee shop, sai da ya isa can kasa bar yayi duk abinda za ayi ya amshi abinda zai amsa. Sannan ya fito kusan karfe biyu da rabi na dare duk da watan Ramadan ce kana iya hango mutane ɗai-ɗai suna yawo a cikin garin duk da ba wani cunkoson mutane amma idan ka isa zaka samu. Shi da ya dace ya wuce gida Amarewat a'a sai ya tsinci kanshi na nufar Azin, unguwarsu Maamah.  Tun zuwanshi dazun ya auna kome na gidan, yana isa bai yi wata wata ba ya haura katangar cikin gidan. Ya dirka a hankali,  a hankali yake takawa kamar yana cikin gidan Hajiya Innah. 

      Bai tsaya ko ina ba sai bayan window dakin, glass din window idan wanda zaa tura ne. A hankali ya bude ya hangota tana gefe Faɗime tana gefenta. A hankali ya ture window sosai, sannan ya shiga dakin yana karkaɗe jikinsa, nufar inda take yayi ya zauna a gefenta. Cire safar hannunshi yayi tare da saka hannunsa a gaban goshinta, yaji dumi ba wani can ba. Hannun ya kai wuyarta ya ji daidai da goshin ne. A hankali ya mike tare da ja mata bargo sannan ya juya yana me barin ɗakin ta window kamar barawo. Yana gyara window ta bude idanunta. A hankali barci yayi gaba da ita amma ita dai ta ga kamar mutum ya fita ta window har ta ji motsin window. 


     Da ya fita kai tsaye ya haura katangar ya bar gidan, sai da ya dauki hanyar gida ne ma ya tsaya tambayar kanshi me ya kai shi gidan? Ba mamaki ko don bai gamsu da rashin bashi amsar da bata yi ba ne, amma abin kamar asiri ya rasa gane kanshi ba dai kalaman likitan ne suke tasiri kanshi ba ai haba shi ko iya haka ya tabbatar mishi da ya dauki fansa akan kowa tunda ya shiga tsakanin masu hana shi mu'amala da Naanah Asma'u yanzu ya musu iyaka da ita. Haka zai ajiye ta yadda suma zasu ji bakin cikin da suka yi ta kuntatta mishi lokacin suna yara. Haka ya cigaba da tafiya har ya isa gida. Da asuba Mairoh ta kaiwa Hajiya abin sahur amma don masifa Hajiya ta fara masifa. Ita kuwa ta ce mata. "Kin ga idan ba zaki ci ba,  me na ihu kamar wacce aka yanki namar jikinki!" Ta juya zata bar dakin, ganinshi tsaye a bakin kofar yasa ta haɗe rai amma a zuciyarta ba karamin razana tayi ba, ta ajiye tare da  fita daga dakin bai kulata ba, ya bata hanya ta wuce nufar dakin yayi ya samu Hajiya Atikah ta fito daga bakin daki. "Amma yarinyar nan anyi yar iska!" Hajiya kamar zata yi kuka ta ce mishi. "Uban kowa kana ganin abinda tayi min?" Kamar bai gani ba ya ce mata. "Hm me ya faru?" Ya zauna yana ɗaukar kular abincin. "Cewa nayi a kawo mana abincin sahur ba dumame ba shine yarinyar nan ta kawo mana dumame?" Shiru yayi yana kallon abincin lafiya lau,  cokali ya dauka ya ɗibi abincin ya kai  bakinsa  yana me cin a hankali bai ji kome ba a cikin abincin, ban da zuga irin na mutanen banza meye illar abincin nan? Hajiya bata da matsala yaran Hajiya sune matsalarta. "Meye matsalar wannan abincin?" Ya tambaye ta "Tow ai dumame ne kuma Atikah ya gundure ta." "Akan me ba zata shiga tayi girkin ba?Nan fa ba gidanta ba ne, gidanki ne Hajiya ke ce kika haife su ba sune suka haife ki ba, Akan me zasu na juya min ke?" Ya kuma jefawa Hajiya tambayar, yana kallon kanwar mahaifinsa da ta kura mishi idanu tana mamakin yadda Yaron ya kasance mara kunya na fitar hankali baya kunyar kowa baya shayin kowa. Duk cikin Yara maza na familynsu babu mara kunya irinsa."Ya kake kallona? Ai Hajiya ce ta ce idan ina son abu na fada idan a gidana."

" A gidanki ma bakya samun damar dumame, ban ki ruwan zafi ba, ba fa addini ba ne ka shiga rayuwar mutane kayi kane-kane kana yadda ka so, Hajiya ina son ki yi nisan kwana domin ki ga yadda Allah zai albarkaci rayuwata, Hajiya idan kika sake Yaran nan suka fara miki addu'ar mutuwa lamarin ba zai miki kyau ba, ki daina biyewa waɗannan da ba kaunarki suke don Allah ba." 

 "Kai Adamu ka fita idanuna na ga rashin kunyar da kake ji dashi ya fara yawa!"  Cikin fada da hayagag ya mike tare da cewa. "Karya nayi? Karya nayi? Nan ba gidanki ba ne, tsakaninki da gidan nan gaisuwa da sauransu bayan nan iko da isa ba naki bane, Hajiya ita ce kusan Uwata ba zan zuba idanun kuna juya min lissafinta ba, idan kuma kashe aurenki kika yi bismillah? Matata da surukata zasu dawo gidan nan gobe wallahi wani ya shiga lamarinta zai ga iskanci da renin hankali." Yayi kwallo da kayan gabanshi, tare da barin ɗakin yana jin yadda Hajiya take kiranshi amma fir yaki dawowa. 


           Kallon Hajiya Innah Atika take tana mamaki, kafin ta ce mata. " Hajiya shi kenan kin rasa Uban kowa." "Kai ban rasa shi ba, kawai rikici ne irin nasa."

***

Azin

Wurin karfe goma na safe, Maamah ta gama shiryawa, ita da Faɗime da Naanah Asma'u wacce aka cire ƙarin ruwan da yake hannunta. Tana can jikin kujerar parlourn a zaune, Hajjama sai nasiha take mata akan aure da ita kanta rayuwar aure. Yadda take share hawayen da yake zuba mata zaka tabbatar abin ya fi karfinta ne. "Ki kwantar da hankalinki, yaushe zaki koma makaranta?" Faɗime ta cewa Hajjama. "Sallah da sati daya zasu koma!" "Shi kenan, idan bai kawo ki ba ni zan zo da kaina ma na kawo miki abinda kike bukata kin ji ko!" Gyada kai tayi tana share hawayen da ya zubo mata. "Rukayyah ki ji tsoron Allah, kada ki raba musu aure, Rukayyah ki barwa Allah ikonsa da zaɓinsa, don Allah kada ki yi abinda zai taɓa mutuncin gidan nan, bana fata ko mugun nufi akan auren nan akwai alkhairin da jikina yake bani, ki taya mijinki ya rabu da Mahaifiyarshi lafiya wannan shine adalcin da zaki mishi, nasan Asma'u bata kyautawa amma ki yi hakuri, matukar kika ga baki yi dariya ba wallahi haka Allah ya nufa amma matuƙar kin bi Allah kin bi Dinnah ma'aikin Allah wallahi babu wanda ya isa ya hana ki ganin dai-dai. Rukayyah nawa duniyar take? Ina ga ai yanzu kin girmi yaji da tashin hankali, ki yi hakuri kamar yadda Mijinki ya bukaci a baki hakuri in sha Allah sanadin auren nan sai kin ce Alhamdulillahi. Ubangiji yasa gwagwarmayar da kika yi bata tashi a banza ba. In sha Allah Allah zai tsaya miki."

      Wannan nasiha da Hajjama tayiwa Maamah shi ya kashe mata duk wata buri da take da shi, sannan ta riko hannun Faɗime suka yiwa Hajjama sallama. Mahmoud ya shigo ya dauki kayan da Yan uwan Maamah suka hada mata.  Kallon Naanah Asma'u yayi ya ce mata. "Da fatan babu inda yake miki ciwo!"

    Gyada mishi kai tayi idanunta cike da kwalla, haka suka shiga baya ita da Maamah, Faɗime ta shiga gaba. Haka ya ja motar yana tafiya yana kallon Naanah ta cikin madubin motar. Share hawayen da yake zubo mata take. "To kukan dai bai isa haka ba ne? Fisabiilillahi tuntuni sai kuka kike idan kika janyo ciwonki ya tashi ba ruwa haka zan tattara ki na tura mishi ke ya je can ya karasa ki!" Haɗiye kukan tayi tana fadin."" Na daina Maamah" a yanzu Naanah da kace mata zaka tura ta wurin Uban kowa gara ka mata kome. Zata ɗauka. 


     Har suka isa gidan tana share hawayen da yake zuba. Haka suka fito ta nufi cikin gidan. Khamilah ce a tsakar gidan tana wanke tsakar gidan. "Maamah, Didih! " Wucewa dakinsu tayi.." Khamilah ya gida, ya aiki? " " Alhamdulillahi Maamah ya Ibada? Me ya samu Didih?" Tabe baki Maamah tayi tana fadin. "Har akwai wani abu da za a kara mata ne bayan wanda aka mata? Ita ta sani." Suka wuce cikin parlourn lokacin Mahmoud ya shigo da kaya. Nan ma ta gaishe shi sannan suka shiga cikin. Sun taɓa hira kafin ya musu sallama suka y wuce aikinsa. Har zuwa yanzu baya jin ya amshi rasa Naanah Asma'u, sai dai yadda yake shakkar mahaifinsa yasa shi rufe  abun a ransa domin mahaifinsa kaifi daya ne. 


         Wurin karfe daya na rana, Abba babba ya shigo gidan da cefane. Kallon Maamah da take wani dauke kai yayi sau daya sannan ya ajiye kayan cefanen ya wuce ɗakinsa. Mairoh ta nufi kayan ta fara budewa kasancewar bata azumi ɗaukar danyen shinkafa tayi ta watsa a bakinta.  " Yau tuwo miyar ganye Abba yake so?" Sallama da aka yi yasa ta juya, "Zak da Abram, suka shigo dauke da kaya niki-niki. Bayansu Uban gayyan ne dauke da wasu kaya a manyan ledojin. Ya dire a tsakar gidan. Dukkansu suka zube a gaban Maamah suna gaishe ta. Duk da fuskarta a daure yake amma kuma ta amsa. "Ya mai jiki?" "Da sauki!"  Shiru suka yi kafin ya mike zai fita Abba babba ya ce mishi." Adamu wannan kayan fa?"  Sosa kai yayi kawai, Zak da Abram suka fita ya rage shi daya sai su Maamah. "Tow amma wa matarka ka kawowa ko?" Ma bai ce kala ba yana sosa kanshi. "To Allah ya zaunar daku lafiya!" A can kasan ransa ya ce  *to me zance ma* shi fa irin wannan sabgar basawa yayi da su ba. "Ka kwashe kayanka bama buƙata!" Inji Maamah, "Mairoh Khamilah ku shiga da shi ciki!" Inji Abba babba, sannan ya kalli Uban kowa ya ce mishi. "Ka shiga ciki tana daki. Idan ma ba zaka shiga ba, zata zo yanzu nan." Ai da kunya ya shiga don haka ya girgiza kai yana faɗin. "Aa a barta dai!"  Ya juya ya fita daga cikin dakin. "Ke Mairoh ki d'ago ta, ta je ta gaida Hajiya sannan ta wuce ɓangaren Mijinta!" Mikewa Maamah tayi tsaye. "Ba inda zata ya kashe min ita."

" Kin ga Rukayyah ina ganin girmanki da mutuncinki, na san ban kyauta miki ba kuma anyi miki laifi, Rukayyah kada ki fusata ni wallahi na gaya miki zan aikata kome domin Naanah Asma'u ta zauna a gidanta lafiya." Yadda ya fadi maganar da karfi tare da bude muryanshi yasa bakiɗaya wani irin tsoro da shakkar shi ya cika Maamah hatta Yaran suma tsoro ya basu.. shiga dakin Khamilah tayi ta mikawa Naanah Asma'u Hijab. "Tashi maza ki je ki gaida Hajiya sannan ki wuce bangarenshi ku gaisa!" Jikinta ne ya dauki rawa, kamar wacce aka jonawa wuta. 

                  "Khamiee!" Ta kira sunanta zata yi kuka,  katse ta Khamilah tayi tana fadin "Don Allah zo muje kada ki yi sanadin da zamu fara jin haushinki!" Saka hijab din tayi jikinta yana wani irin rawa. Riko hannunta tayi har zuwa lungun Hajiya suka ka nufa ta kaita bangaren Hajiya. "Abba babba ya ce akan aurenki zai aikata kome don Allah ki daina wannan tsoron kada mu rasa Mahaifiyarmu saboda aurenki!" Ta fada tana kuka itama, share hawayenta ta fara ta wuce ɓangaren Hajiya jikinta na rawa. Da sallama ta shiga ta samu suna parlourn.  Daga bakin kofar ta durkusa tare da gaishe su. Mufidah da Hamidah ne, sai Humairah da take ta jijjiga babynta.  Duk ta gaishe su. Amma suka ki amsawa.  "Munafuka an je an baki sihiri da asiri da zaki shafa ko ki manna yadda zai bijirewa umarnin Hajiya ko?" Ita dai kanta a sunkuye bata iya d'ago kai ba, sai zaginta suke suna aibantata amma bata ce musu komai ba. Kamar wanda aka turo shi amma bai shiga ba yana jin yadda suke zaginta, tare da kiranta da suna kala kala,  shiga parlourn yayi duk suka yi shiru. Saka hannu yayi ya d'ago ta. Wani irin zabura tayi tare da sake wani irin marayan kuka. " Ki min shiru;" ya daka mata tsawa. Haɗiye kukan tayi tana me sunkuyar da kainta kasa jikinta yana wani irin rawa. A hankali ua janyota jikinshi ya ce musu. "Matata kuke zagi da cin zarafinta?" Shiru suka yi suna kallon juna. Wani irin ashar din da ya maka musu yasa duk suka razana. Ko azumin da yake tuna ba, ya danna danna musu zagin da sai da suka ji wani irin kunya ta rufe su. Ya isa gaban Hajiya ya ajiye mata takardan Umra ya juya tare da riko hannunta suka fito , sake mata hannu yayi ya ga ta nufi lungu da zai kaita bangarensu.

                Sai da ta share hawayen da yake zuba mata, ta shiga cikin gidan. A Parlourn ta samu su Khamilah suna buɗe kayan da ya kawo mata, kayan sallah kala biyar, takalmi da jaka. Sai mayafai da dogayen riguna kala biyar biyar. Sai irin haɗin ramadan basket din nan, da kudi kusan bunch na kuɗinsa na nijar. Sai kayan ciye-ciye da kwai caret biyu kai ya kashe kuɗi sosai. Ban da sabuwar waya sumgsun da ya saya mata sabuwa dal da layin airtel network.  Wuce su tayi ta koma daki ta kwanta. 


         A kayan da Maamah take tara musu na aure musamman ita, ta ciro wani kyakkyawan da basket, da jug da duk wani abin bukata. Ta shiga ajiyewa Khamilah da Mairoh. "Idan kun saka na Abbanku da Hajiya ku saka na mijinta a nan, ita zata kai mishi!" Daga haka ta koma daki, ta same ta kamar yadda take kullum ta haɗe kai da kafa tana kuka. "Bana ce ya isa ba?"  Share hawayen da yake zuba mata tayi. "Nace ya isa ko an gaya miki bana jin zafin abinda ya faru ne? Kada ki manta nima ina da hakkin akanki ko?" Gyada kai tayi, "Ni nace miki ki yi hakuri ko ban isa nace ki yi hakuri ba ne?" "Kin isa!" Murmushi tayi sannan ta ce mata. "Masha Allah, ki yi hakuri idan ya miki abunda ba zaki iya jurewa ba ki dawo gida kin ji? Idan kuma zaki iya hakuri to ki yi hakuri. Nima ina jin zafin wannan abin balle ke, don Allah ki daina kukan kin ji. Ban san me yake nufi ba amma zan tambayi Abbanku na ji za ayi bikin tarewanki idan ya ce za a yi sai mu shiga kasuwa mu sayi kayan da babu ko?"

    Gyada kai tayi tana kuka ta ce mata." Maamah tsoronshi nake ji, idan na ganshi kamar zan mutu. Don Allah Maamah ki ce a fasa auren nan kin ji ko, idan ma kuna so ku haɗa ni da kowa ma na yarda don Allah!"

     Rike hannunta tayi tana fadin. "Ki nutsu zaki daina jin tsoronshi. Shi ba dodo ba ne. Kin ji a hankali zaki saba dashi. Sannan a kashe auren kin san me yake saka a kashe auren mace? Kin taɓa yarda da wani namijin ne?" Yadda Maamah tayi mata tambayar yazo mata wani irin bazata. Dafe kirjinta tayi tana zare ido hawaye na zuba da gudu wannan na koran wannan. "Allah ya nuna min ranar mutuwata da wannan zunubin. " Murmushi Maamah tayi ta ce mata. "A cikin al'ummarku wannan yana cikin dalilan da zai saka a kashe auren, idan kuma baki taɓa ba shi idan yayi ra'ayin rabuwa dake ba tow babu dalilin kashe auren kin ji." Duk yadda uwa zata so yarta Maamah ta so Naanah Asma'u, kuma tayi ta rarrashinta tare da nuna mata tana tare da ita. 


    Sai dai tsoron Adam wani abu ne da Naanah Asma'u ta rayu a kai, zai matuƙar wahala ta daina tsoronshi cikin sauƙi tunda ai ba abu ne da ya gini dare daya ba, abu ne da ya ginu tsawon shekaru masu yawan gaske. 

      Wurin karfe shida saura Maamah ta saka ta gaba tayi wanka ta dauko wata farar atamfa ta ajiye mata, sai pant da bra. Da humra tare da body milk, da ita Naanah Asma'u ta kawo mata, ta shirya yarta cikin kammala da nutsuwa. Fitowa tayi ta saka Khamilah da Mairoh suka kwashe abincin da suka jera aka kai bangaren Hajiya da bangarenshi. Sannan ta saka Khamilah ta rakata har bangarenshi. 


     Ba kowa sai kamshin turaren wuta da suka saka lokacin da suka kawo abincin. Rike hannun Khamilah tayi tana girgiza mata kai.. "Ke ni sake ni don Allah!" Haka ta kwace hannunta tare da barin Naanha Asma'un ita ɗaya. Ana kiran sallah Magariba, bangaren Hajiya ya nufa ta zuba masa ido. "Kai kace su turo maka ita?" "Eh ni na gayawa Abba Babba zan bata sakonta ne tunda tare zamu tafi Umara da ita wani abu ne?" Kafe shi da ido Hajiya Innah tayi wani irin tsoro yana taɓa zuciyarta. 


 Anya bata yi kuskure ba kuwa? "Kasan me kace?" "Eh na sani mana Hajiya yarinyar can tare da ita na biya umara!" "To ni na fasa zuwa sai ka kaiwa Uwarta da Kakarta su tafi!" "Alhamdulillahi kin kyauta kuwa dama ai ita Maamah aikin Hajji na biya mata tunda ita ce Allah bai kira ba ta ba, kin ga yanzu sai ta tafi tunda ta samu ta sanadin Yarta." Ya fada yana mikewa. Shi kai tsaye yake abinsa sai dai ka mutu amma idan ya yi niyya ba wanda ya isa. 


  Shi fa auren nan ma dalilai uku suka amsa ka shi auren nan, na farko ya nunawa Mustapha da Mahmoud bai kaishi kome ba da suka shiga tsakaninsu na tsawon rayuwa, na biyu jinyarta da yake da yakinin ga sanadin ɗinsa ciwon nan ya same ta. Musamman da likita ya tabbatar mishi ciwon ya jima a jikinta. Ba a haife ta da shi ba amma kuma ya jima yana cin jikinta....