Chapter 18
by @maidambu41
Da gaske ya saka kai zai fita, Hajiya ta ce mishi. "Da gaske tafiya zaka yi ba zaka rarrashini ba? Da gaske biya mata ka yi Innalillahi wainnalihir rajoun, wallahi asiri suka maka na rantse da Allah." Ta fashe da wani irin kuka, har jikinta yana rawa. Abinda take tsoro kenan kada daya cikinsu ya auri yaran Rakiya gashi tana ji tana gani, ya tsallake ta ya bar parlourn. Tun daga kofar ya shaki kamshin turaren wutan, lokaci guda yaji wasu irin gajiya sun sauko mishi. Cikin wata irin sassarfa da gajiya ya isa parlourn ya tura labulen, hangota yayi a can karshen kujerar parlourn. Ga kayan abincin yadda suka jera. Ita kuma tana zaune akan kujerar kamar wata mara gaskiya. Da wata karamar sallama ya shiga wanda iya bakinsa ya motsa, bai kalli inda take ba tun kallo ɗaya da ya mata, ya ga yadda ta cusa kanta cikin cinyoyinta. Ya wuce ɗakinsa ya shiga ya jima a wajen take jin karar ruwan da yake zuba a can ban ɗakin. Can kuwa ya fito sanye da jallabiya milk colour, ya fito ya zauna a kasa gaban kayan abincin.
Bankaɗo labulen aka yi, "Zo ki fita munafika abinda Uwarki tayi ta takaita min ɗa shine aka haɗa ki shi domin ki ga bayanshi. " Jikinta yana rawa ta mike dama zaman kamar akan wuta take, yasan ta gabanshi zata wuce, don haka tana takowa zuwa inda yake ta raɓa, zata wuce hannunsa ya saka ya fisgota bakiɗaya ta fada kanshi ya kuwa mata masauki a gefenshi, a razane ta kuma yunkurin zata mike ya cabke hannunta ya mata wani mugun riko da yasa ta hakura da tashi tare da fashewa da kuka. D'ago kai yayi ya kalli Hajiya fuskarshi a wani irin hade babu annuri ya ce mata. "Kin ga ni azumi nake, ki je idan na sha ruwa zan zo!"
Ya cigaba da zuba abinda zai zuba da hannu daya, daya hannun yana riƙe da ita. Haka ya cigaba da abinda yaƙe. Ai kuwa cikin fushi Hajiya ta kai hannu zata mare ta, yayi kasa da kanta ai kuwa ta sami gefen goshinsa. Bai d'ago ba ya ce mata." Na ce ki tafi Hajiya idan kuma anan zaki sha ruwa ga wuri nan zauna."
A fusace ta bar parlourn, yana ganin ta bar parlourn ya tureta yana hade rai. "Bar nan!" Ba musu ta mike zata fita ya ce mata. "Na sallame ki ne?" Komawa tayi kujeran ta zauna tare da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Har ya gama ya tafi masallaci. Itama ma tashi tayi ta bar bangaren, a hanyar da zai kaita bangarensu ta gamu da Hajiya Atikah. Raɓewa tayi a bango. Ai kuwa ta janyota zata rufe ta da duka. Yadda ta rike kanta da hannu bibbiyu yasa ta fasa tana faɗin. "Ki shirya ganin bakin cikin da zai kai ki mutuwa, wallahi wannan auren a gantale zai kare domin kuwa sai na mai dake abin tausayi." Har ta gama ta wuce bata fahimci laifinta a wannan lamarin ba. Tana shiga bangarensu ta ga haske a kofar Tente Hasiya, da sauri ta wuce kofar domin tsoron yadda Matar ta mata wancan karo bata manta ba.
Lokacin da ta shiga ta samu Khamiee da Faɗime suna sallah, Mairoh kuwa tana cin abincin, da mamaki Mairoh ta kalleta sai kuma ta share, jin muryan Hajiya a tsakar gidan yasa ta shigewa daki da sauri. Yadda Hajiya take fada da masifa babu wanda ya kulata sai Hasiyah. Har da cewa su gayawa Malaminsu aikinsu da saura babu wacce zata kwace mata jikanta. Kamar yadda aka ɗauki hankalin ɗanta. "Kiyi hakuri Innah in sha Allah, Allah ba zai bari ayi nasara akanki ba. Ai zalunci ne ma bayan abinda aka yi sannan ace kuma an mallake maka jika."
Ba wanda ya tanka musu, waye ma yake da lokacinsu da zai kula su. Haka ta gama masifar ta sannan ta bar gidan. Lokacin da ta shiga bangarenta, ta same shi zaune yana kallon yadda take haki. Ta zata zai rarrashe ta ne sai ta ga akasin haka domin ko cikan, abinda xai yi amfani da shi ya shiga ya dauka a kitchen ya wuce abinsa. Haka kawai ba zata ɗaga mishi hankali kuma ta kwana lafiya ba.
Lokacin da ya isa dakin ya samu bata nan, bai yi mamakin rashin samunta ba. Zama yayi ya kwashi gara, ya gama ya shiga ban daki ya dauko wiwinsa ya shiga bankawa cikinsa har yayi ya nutsu. Sannan ya fito ya shirya zuwa sallah Isha, bayan an idar har da sallah tarawee, daga nan ya wuce yawonsa. Tunda ya fita bai dawo ba sai karfe biyu na dare, lokacin da ya dawo bai shiga bangarensu ba, can bangarensu Abba babba ya wuce ya je bayan window, ya leka ta window tana barci yau haska flashlight na wayarshi yayi ya ga tana ta barci, motsi tayi ya kashe flashlight din, ya bar wurin. Bude idanunta tayi ta shiga leka window amma bata ga kome ba. Komawa tayi ta kwanta..
Bayan sallah asuba ko wurin Hajiya bai nufa ba, ya wuce bangarenshi, daukar takardar umara yayi ya fito, bangarensu Abba babba ya nufa yayi mishi sallama, ya fito gaishe da Abba Babba yayi ya durkusa kasa. "Dama wannan na kawowa Maamah ne ko zata shirya su tafi umara sai ta bani karamin hotonta." Amsa yayi ya ce mishi. "Ikon Allah tow bari na mata magana!" Haka ya shiga yana kiranta, "lafiya?" Ta fito sanye da hijab dinta. "Adamu ne ya biya miki umara!" Abin yazo mata bazata, hade fuska tayi ta amshi takardan tare da fitowa ta ce mishi. "Ungo!" Ta mika mishi takardar, "Na gode sosai, bana bukata." Abin ya zo mata bazata amma bata jin zata ci koda kwayar shinkafa ne da ya fito daga hannun Adamun, musamman a yanzu da yake auren Naanah Asma'u. "Na gode sosai, Allah ya baka lafiya amma kada ka kara kawo min wani abu da ya shafe ka, yata ba sayar maka da ita nayi ba, tunda ka ji ka gani kada ka kara kawo min duk wani abu da ya shafe ka. Ita da ta zama dolenka sai ku kara ta can!" Daga haka ya sake takardar ta koma cikin. "Amma Maaamh ai da niyyar alkhairi yayi kyauta... " Tass ta wanke Khamiee da mari da yasa ta yin shiru, " kina nan kakarshi tazo tana ihu za'a mallake mata jika, idan har ni na haifi Naanah Asma'u wallahi ko me zai bata matuƙar xai fito daga hannunsa na haramta mata shi."
"Nan kuma kika yi karya wallahi domin matarshi ce, tunda ba zaki ba shi kenan batun ƙananan magana ba zan dauka ba." Inji Abba babba, haka yasa Maamah jan bakinta.
"Allah ya baka ladan niyya!" Rashin amincewar Maamah shi ya kashe tashin hankalin da Hajiya take, amma tunawa da Naanah Asma'u abin ya kara bakanta mata rai, don haka ta shiga kiran Yaranta, wanda take da yakinin zasu dakatar da shi, sai dai duk cikinsu babu wanda uban kowa yake jin maganarshi, domin su kansu sun san Uban kowa yana da kuɗin da har mamaki suke idan aka ce musu yana da kudi na shi na kasan, yana da wani gida da ake yawan bada labarin amma basu yarda ba tunda babu wanda ya taɓa zuwa gidan ya gani, mutum ne mai matukar kiyayye sirrinsa da zurfin ciki.
Duk yadda zaka yi da shi ba zai ce maka yana shi ba, sai dai a aikace-aikacen shi zaka gane kyauta da kashe kudi ba wani abu bane a wurinsa. Shi kansan yasan yadda ya tara kuɗi ko shekaru goma zai yi ba zai iya kashe kuɗin nan a wannan shekarar ba. Tun ranar da ta je bangarenshi bata kara zuwa ba, asalima kunshe kanta take a daki, to ba kome take ba. Sai yawan shiga damuwa da kuka tare da nimawa kanta mafita. Ga fitinar Hajiya. Ana kwana biyu Hajiya zata tafi umara, mahaifinsa ya kira shi, bayan Isha ya shiga bangaren Maamah ya gaishe suna tsakar gida anan suka sha ruwa. Sanye yake da farar shadda wanda ko a cikin duhu zaka hango yadda hasken shaddar yake kara haska shi. Yana durkushe hannunsa daya yana kasa ya cewa Maamah. "Na zo ne ko zaki bani aronta muje ta gaida Abba karami!" Yadda yayi maganar cikin girmamawa yasa Maamah jin wani irin girmama kanta ya shige ta. "Faɗime ki ce ta shirya yana jiranta!" "A'a Maamah bari na shiga na tayata shiryawa." Inji Khamilah, wacce lokaci guda ta dawo tana bin bayansa. Ta shiga ta same tana kallon abincin da aka saka mata. "Tashi Didih!" Ta nufi wardrobe ɗinsu, wani farin abaya ta dauko mata, ta mika mata tana faɗin. "Ya Adam yana jiranki!" A firgice take kallonta jikinta yana wani irin rawa. "Ki nutsu ba cinye ki zai yi ba." "Khamiee!" Ta fada muryanta yana rawa. "Ya Allah! Ba fa kashe ki zai yi ba fa." Haka ta fada mata tana taimaka mata har ta shirya, wani bakin hula ta dauko mata tana saka gashinta a ciki sannan ta dauko mayafin ta nade mata a kai, kafin ta kwaso turare ta shafa mata. Wasu a jiki wasu kuma a cikin musamman humra da body milk.
Sai fuskarta da ta gyara mata, sannan ta dauko wata flat shoe da wata jakar Mairoh, suka fito tana rike da hannunta, baya tsakar gidan. "Ki dai kama kanki, ki gane inda kike ba inda kika saba ba ne." Haka Maamah ta gaya mata, har kofar gida suka rakota. Kin fita tayi tana kallonsu kamar xata yi kuka." Khamiee tsoro nake ji!" "Haba Didih cinye ki zai yi ne? Wacce irin tsoron masifa ce haka kike ji haka ne?" Inji Khamilah tare da juyawa ta barta a wurin, ta kai kusan minti goma a tsaye kafin ta fita, yana cikin motar ya hango yadda take tafiya kamar zata kifa. Da yake bata san motar da yake gabanta yake danna mata horn yayi ta dan razana, tare da juyawa inda motar take ta bude ta shiga a hankali, domin ta fara buɗe bayan motar sai ta ga yaki budewa, shine ta shiga gaba. Tana shiga ta zauna kamar irin yaro yayi laifi ana mishi fada haka ta zauna tare da cusa hannunta a cikin cinyoyinta. Kanta a sunkuye kamar me rokon gafara. Dariya ta bashi musamman yadda ta cusa hannunta a cikin cinyoyinta. Tafiya suke yana kallon hanya, amma jikinta rawa yake. "Kin sha magani?"ya furta a hankali, yana tuki gyada kai tayi tana hannunta. Har suka isa sabon gari babu wanda ya kara magana sai da suka isa kofar gidan zai yi parking ya ce mata. "Kin ci abinci?" Anan ne ta girgiza kai tana kallon hannunta. "Kina jin yunwa?" Abinda ta fahimta a dan zaman na yanzu duk abinda zai fada kalmar bata wuce uku, tayi nisa sosai ya kara ta kai huɗu.
"Ki kula sosai!" Bata fahimci abinda yake nufi ba, fita yayi daga motar itama ta fito, jiranta yayi ta zo gefenshi suka jera a tare. Yadda suke tafiya zaka fahimci yadda suka dace da juna, har cikin parlourn mahaifinsa suka shiga, a hankali ya kai hannunsa ya riko hannunta, da sauri ta kalle shi, wani irin cika mata ido yayi da sauri ta janye idanunta daga kanshi tana jin zuciyarta kamar zata fasa waje, ga jikinta da ya dauki rawa. Janyota jikinshi yayi yar tana shaƙar kamshin turarenshi me suna Sadauki, bata iya kallonshi ba a wannan karon domin ya cika mata idanu da kwarjini me yawan gaske. "Kada ki ci kome?" Yayi shiru tare da kai kansa wuyarta. "Idan ba ni na ce ba!" Yadda yayi maganar har tana jin dumin numfashinsa a wuyarta. Wani irin tsoro ne ya kamata bata san lokacin da ta fara motsi ya ce mata. "Shiiii!" Kamshin mouth fresh strawberry hade da wiwi ya daki hancinta, da sauri tayi kasa da kai. Jikinta yana rawa.
"Nutsu!" Haɗiye yawun bakinta tayi, suka shiga parlourn. D'ago kai yayi yana kallonsu. Wani irin tsinkewa zuciyarshi tayi. Dole hankalin Hajiya ya tashi domin babu wanda zai so ya wannan haɗin kai ina shima yana tare da Hajiya. Wani irin kallo yake aikatawa Uban kowa, shima da yake namijin duniya ne kusan kallon renin da yake mishi kenan, zama yayi a kujerar da yake parlourn ita kuma ta zauna a kasa tana gaida Abba karami. "Lafiya!" Daga haka tayi shiru. "Iya dan aike na tura ya ɗan aike zai hado da kaya." Wani lokaci idan har irin wannan maganar ce to yana jin kamar kada ya zauna da kowa ne ma. "Sakon shan ruwa aka tura min." Ya fada yana kallon inda aka jera abincin. Kiran Matarshi yayi tare da cewa. "Ga surukarki nan! Ki shiga da ita kafin mu ci abinci."
"Ba inda zata ta." Ya fada yana sosa giransa na dama. "Shi kenan! Ke je ki!" Juyawa tayi tare da barin wurin, kallon shi yayi ya ce mishi. "Hajiya ta kawo min ƙararka!" Take jikin Naanha Asma'u ya ɗauki rawa. Hannunsa ya kai tare da riko hannunta. Yana murzawa, "Kawo karata dai?" "Eh tace tunda kayi aure baka jin maganarta. Kuma ai gaskiya ne yaushe aka yi auren da har zaka fara wasa da dukiyarka, kada ka manta muna da haƙƙin akan dukiyar da kake tarawa." Bude baki da idanu yayi yana kallon yadda Abba karami yake bayani. "Eh mana duk abinda ka tara na mune, kuma mu ke da iko da alhakin kula da shi!"
"Yaushe kuka shirya min barin duniyar?" Shima da mamaki yake kallon Uban kowa. "Eh yaushe kuka shirya min barin duniyar nan? Kudina mallakar matata da ɗan cikinta ne." A wani zabure Alhaji Haris ya ce mishi. "Dan cikinta?" Ita kanta sai da ta d'ago da sauri ta kalle shi, shafa fuskarta yayi yana faɗin."Eh kai, ko baki shirya haihuwa da ni ba ne? Ki sani ko yau na mutu daga Abbana har Hajiya babu me gadona, ke ni rayuwata a shirye take kome na a lissafi yake. " Ya kalli Mahaifinsa." Kayanka basu shigo ba ne?" Yadda yayi maganar yana mikewa, yasa shima mahaifin mikewa suka nufi wurin cin abincin. "Ban gane bane?"
"Na me fa?"
" Ka kara aure?" Yadda ya riko hannunta suka zauna a kujerar,. Ya ciro plat tare da cokali ya ajiye mata, kiran Maman Fuad Alhaji Haris yayi ta zo ta zauna tare da Asma'u. Ta shiga zuba musu abincin. "Ka kara aure?" Inji Abba karami. " Amma wasa kake ko?" Ya fada yana zuba mata abincin. "Nayi maka kama da abokin wasanka?" " Eh to kusan dai haka!"
"Adam!"
"Na'am!"
"Aure zaka yi?"
" Babu me saka ni a aure ban shirya ba! "
" Adam! "
" Abba! " Ya amsa mishi." Kayi aure!" " Ba xan yi ba!" Ya furta kai tsaye, ya jima da zargin mahaifinsa amma a yanayin auren nan yake jin a ransa shi kamar karen farautarsa ne. "Ban amince da auren yar Muhammad don ina son haka ba, idan har ni na haife ka, ka. Kara aure saboda kai mahaifiyata take cikin wani hali. "
"Ni ba zan kara aure ba, da kana son nayi maka biyayya da tun farko baka. Watsar da rayuwata haka ba, da kana son nayi maka biyayya da baka shata wata ƙatuwar katanga a tsakaninmu ba. Wai so kake ka gaya min yadda zan yi da rayuwata? Ni nasan rigar da na saka kai wacce ka saka ai bata maka ba, ke tashi muje." Ya ajiye cokalin yana me mikewa zai fita. "Kada ka sake ka bar gidan nan, sai ka gaya min wacce rigar na saka!" Kallonshi yayi ya juya ya riko hannunta yana me janta suka bar gidan. "Ka sani kome zaka yi ba zai saka na amince har na saka maka albarka ba, idan baka son rayuwarka ta lalace ka dawo ka gaya min wacce rigar na saka?