WATA FUSKA

Chapter 1-2

by @momislam11

✨✨✨✨✨✨
*WATA FUSKA*
✨✨✨✨✨✨

     _Mom Islam_


Page 1-2
Ƙauyen Kwaso dake wajen birnin Tamale a arewacin ƙasar Gana.
Ƙauyen ya haɗa da addinai daban-daban, addinin Musulunci da addinin Kirista, Akwai wani babban gida wanda ya kasance kaf ƙauyen babu kamarsa, Gidan David kenan, ya kasance ba musulmi ba, matarsa sunanta Deborah, ƴarsu ɗaya Mary, suna raguwa ne irin na mazauna ƙauyen, sannan sun yiwa addininsu kyayyawan ruƙo, duk da cewa su ɗin ba musulmai bane, amma lokacin zuwa yin bautarsu yana yi duk wani abu da sukeyi, suna barinsa su tafi gurin bauta, David dattijo ne sosai, zai kai shekaru sittin a duniya, m matarsa Deborah itama dattijuwa ce, dan zatakai shekaru arba'in da biyar, sai ƴarsu Mary wacce ita kaɗai Allah ya basu, tanada shekaru Ashirin da biyu, Mary ba fara bace, zamu iya kiranta da chocolate color, sai dai Allah yayi mata kyau sosai, wanda kaf faɗin kauyen idan ka zagaya zai yi wuya ka samu yarinya mai kyau irina Mary, sai dai abin mamaki, duk tarin samarin da suke cikin wannan ƙauyen Mary bata da saurayi ko guda ɗaya.
Ƙarfe 12:pm na rana, Mary ta fito daga ɗakinta, tana sanye da baƙar t-shart da zanin atamfa, sai ɗankwalin atamfar da ta ɗaura a kanta, Tulu ta ɗauka, har ta fara tafiya, daga cikin ɗakin Mahaifinta David ya ƙwala mata kira, Deborah mahaifiyarta ta fito daga ɗakin da suke ita da baban Mary tace "Mary sau nawa zan gaya miki ki daina fita a tsakiyar rana hakan ba abu ne me kyau ba, amma kinƙi dainawa, babanki dai yace karki fita"!.
Mary ta marairaice murya tace "Mama kiyi haƙuri ruwa zan ɗibo kuma bazan daɗe ba" Maman tace "ba nice na baki umarni ba, babanki ne yace karki fita", Mary ta fashe da kuka, kafin ta sake cewa "haba mama, ruwa fa zan ɗibo" Baban ya fito daga ɗaki, yana sa riga yace "ni nace ban amince ba, ki bari rana tayi sanyi, saboda na gaji da kwashe-kwashen da kike yimin a cikin tsakiyar rana, idan banda abinki duk ruwan da yake gidannan be isheki kiyi amfani dashi ba har sai kinje rafi ɗibowa?" Mary ta durƙusa a gaban mahaifinta, cikin Muryar kuka tace "baba nayi maka alƙawarin yau babu abinda zan kawo maka ka yarda dani baba, ruwan wanka zan ɗibo, na cikin randa yayi zafi saboda zafin da ake yi" Mama ta girgiza kai, tana mamakin Mary, Baban yace "tashi kije kuma karki daɗe" sannan na gargaɗeki..." Mary ta fice hannunta na riƙe da tulun ɗibo ruwa" sannu a hankali take takawa tana tafe tana rera waƙa har ta iso bakin rafi, kamar kullum da ko yaushe idan tazo a irin wannan lokacin bata samun masu ɗibar ruwa ko masu wanki a bakin rafin, Ta durƙusa tare da sanya tulu a cikin ruwan ta ɗibo ruwan, sannan ta miƙe tsaye, ko taku ɗaya bata ƙara ba, ruwan rafin yayi wani irin murɗewa sosai, lokaci ɗaya ruwan ya buɗe, cikin firgici Mary ta ke kallon ruwan, da tulun ruwa a kanta, wani kyakkyawan matashi ingarman namiji ruwa ya kaɗo ya taho bakin rafin, a haka kamar babu numfashi a tare dashi, Mary ta dafe ƙirji cike da fargabar gargaɗin da mahaifinta yayi mata, tsabar rikicewa bata san lokacin da hawaye ya fara sintiri a saman kumatunta ba, ta fara matsowa inda saurayin yake, fari ne sosai, yanada dogon hanci kamar balarabe, yanada faffaɗan ƙirji sannan kuma yanada kwantaccen gashi mai sheƙi, bugu da ƙari laɓɓansa pink ne, jikinsa wani irin kaya ne, mai kama da na sarauta kamar kuma na wata ƙasar, jikin Mary a sanyaye ta ajiye tulun ruwan, ta isa gurinsa ta durƙusa, matashin bazai wuce shekaru 35yrs ba, ta ɗora tafin hannunta a saman ƙirjinsa, babu numfashi a tare dashi ko kaɗan, cikin kiɗimewa ta tafi gidansu da gudu, dan ta mugun tsorata da ganin yanayinsa, dan harda yankan wuƙa a gefen wuyansa, tana isa gidansu, cikin ɗaga murya ta fara ƙwalawa mahaifinta kira tana cewa "baaabaaa....!! Ba ba..." Mahaifin nata ya amsa lokacin da ya fito daga wanka hannunsa riƙe da bokiti da kwandon soson wanka, bai amsa mata ba, ya dai tsaya yana kallonta, dan tuni jikinsa ya gama bashi abinda take gani ta jajiɓo masa yau ma shi ta jajiɓo, Baba Ina ta kiranka baka ce min komai ba, baba wlhi wani mutumi ne a gefen rafi ga dukkan alamu baya numfashi ammafa ba ɗan wannan ƙauyen bane" baba yace "hmm" Mary abinda nake gudu kenan shi yasa kikaji nace karki fita, yanzu dai ina ruwanki dashi kawai kiyi abinda yake gabanki" Mama ta fito daga ɗaki saboda ta saurari maganar tasu tace "kayi haƙuri kaje ka dubashi tunda dai kasan ko ba komai sarki ya naɗaka a matsayin mai kula da komai na wannan ƙauye, Baba yace "Mary ta jira shi, kaya kawai ya saka ya fito yasa takalmi suka kama hanyar zuwa bakin rafi, suna isa suka samu matashin ya mirgina ɓangaren dama, alamun yana da rai kenan, Mary ce ta taimakawa babanta suka kawo shi gidansu, Mama ta shimfiɗa tabarma da bargo mai taushi, aka kwantar dashi, baba ya sa masa pillow a gurin kansa, yace "Mary taje tukunyar magani ta ɗibo masa magani a ƙwarya, bayan Mary ta ɗibo maganin ta dawo jikinta yana ɓari, ta miƙawa mahaifin nata ya karɓa, "ki durƙusa anan ki hura bakinsa sosai har sai ya fara motsi" Mary ta zare idanu tana kallon Mama, Mama itama Mary take kallon, cikin daka tsawa tace "bazakiyi bane, waye mai yi idan ba keba, tunda kika nemo ai kema bazaki zauna haka ba" Mary ta marairaice idanu tare da juyar da kallonta ga baba da ita yake jira, shima daka mata tsawar yayi yace "Noor ke nake jira, ki gaggauta saboda ceto ransa" Mary ta durƙusar da guwaiwoyinta a ƙasa, tasa tafin hannunta a ƙasa, sannan ta sunkuyo da kanta, suna iya jiyo numfashin juna sai dai baya motsawa, tun bayan motsin da yayi ɗazu, wani irin ni'imtaccen ƙamshi ne ya kaiwa hancinta ziyara, wanda yasa taji ƙamshin kamar ya gauraye garin duka, ta sanya bakinta ana matashin saurayin ya hura sosai, iya ƙarfinta, can sai ya fara motsa yatsun hannunsa, kafin ya fara ƙoƙarin buɗe idanu a hankali, sai kuma ya buɗesu gaba ki ɗaya, fararen ƙwayar idanunsa ne suka sauka akan kyakkyawar fuskar Mary, ya zuba mata idanu babu ko ƙiftawa, baba yace ta tashi ta bashi guri sai in ya nemeta sai ta dawo" Mary ta miƙe tabar gurin. Baba ya karɓi ƙwarya a hannun Mama ya fara yayyafawa matashin saurayin har sai da ya shafa masa duka a jikinsa kafin yace "sannu, zaka samu lafiya yaro..."

Mom Islam