SOYAYYAR ZUCI

Chapter 41&42

by @deeyamerh10

💖💖 SOYAYYAR ZUCI 💖💖
(Love and Romantic story)
                Written
                       By
                Deeyamerh
0707064236
Page 41&42
Ba wanda ya runtsa a wannan gidan domin kowa jiran safiya yake, zuciyarsu cike da zullumin jin halin da Ammey ta tsinci kanta a JEMETA domin Ko kusa ba su da haddi da Yola, amma ace an same ta a nan? Wannan shi ne abin da ya fi daure musu kai.

Kiran Sallar farko ya fara ratsawa cikin kunnuwansu.

“Allahu Akbar… Allahu Akbar…”

Nan take mazan suka fara shirin zuwa masallaci,domin duk idan su biyu kowa da irin tunanin da yake,yayin da mata suka fara suna shin Sallah a cikin dakin da suke.

Lokacin da hajjiya tajin SH ya dauki suhaima ba irin fada da batai ba akan danme zai dauke ta shi bashi da kawaici ne haka dai taita fada shi kuwa yana can ya samu suhaiam kamar zai cinye kayarsa,Da Yan dabaru tayi masa tafi masallaci amma da cewa yayi shi a dakin zai yi.

Sai da yayi wani wankanka kafin ya fito ya tarar da su Abba zasu wuce,cikin girma mamawa ya gaiashi su kafin su dunguma zuwa masallacin unguwar.

Cikin sauri har tana haɗawa da gudu tai part din Hajjiya,Allah ya tai maketa ba kowa a parlon kai tsaye dakin da aka basu ita da Fatima tashige domin bazata iya hada ido da Ammey ba a wanna yayin domin gane take kamar za'agane abinda yayi mata jiya.

Sosai tasha dariya gun fatima,dan wlh ba karamin Dariya suhaiam ta bata dan tunda tadawo takima yadda su hada ido da fatimar ina kuma ga hajjiyar mahaifiyar SH din.

Sai da Haske ya fara futuwa Sannan suka dawo,inda sukai wata da Baffa yake shaidawa musuwya shigo driver SH ne yaje taho da su.

Yan matan kaff din sune yau masu Aikin gidan Domin Hajjiya tace su zasuyi girkin tarar baki,hak suka hadu har suhaiam da ta kasa sakin jiki da su,dai sai da aka kai ruwa rana kafin Fatima tasa ta agaba domin gaidasu Hajiya da Ammey da Mama,duk sun san  me takewa wanna boyewar Amma sai suka nuna mata kamar basu fahimta ba.

Kafin wani lokaci sun gama komai na abincin da za'aci,sosai kannan SH suka ji dadin kasance da Suhaima domin ana aiki suna hira sai dai su hajjiya suji dariyarsu.

Karfe 7:00am dai dai motocin yan Abuja suka sauka.A hankali kifar ko wacce mota take bude,baki nasaki domin wasu zaratan maza nagani guda biyu wanda kana ganinsu kaga Suhaima dan sosai suke kama da junah.Juyuwar da zanyi sai ga Baffa ya fito shi ma.

Fuskarsa cike da  annuri domin kamar ya bude idanuwansa ya ganshi gaban kanwarsa,SH ne yayi musu jagorancin shiga ciki.

Cikin takun nutsuwa suka mara masa baya har cikin Parlon da su Ammey suke zaune Domin An fada masu isowar su Baffa.

Sallama dauke a bakunansu suka shiga cikin parlon tundaga kan Baffa har Abdul tsayawa kallon Ammey suke,duk da tayi rashin lfy Amma bazakace tayi ba domin tana samun kulawa shiyasa tayi fresh da ita.

Kallon kallo ake tsakanin Ammey Da Baffa gefe guda kuma Zaratan samarinta ke kallonta cike da kewa irin ta Da da Uwa,Cikin sauri ta meke take ta rungume Baffa kafin kuka ya kwace mata.

“Baffa ta furta cikin kuka

Na'am Autanah

“Kun iso lafiya?”

Alhmdullah Auta Ya nasameki tsayin Shikaru Alhmdullah da kasace sanyawa a tsakanin da Ganawa Alhmdullah ya Allah.

Hajjiya ta bude baki za tayi magana, amma kafin ta yi magana sai idonta ya sauka akan  Suhaima ta taje ta rungume su Abdul sai shafa kanta suke suma suna kuka kamar ba maza ba.

Sosai zuciyar SH ya buga shifa bayaso yaga tana rabar wani Indai bashi ba,duk da yasan Yan uwanta ne Amma yaji badadi haka ya kauda kai

Suhaima ta tsaya a gansu suka kallon Ammey da suka kasa rabuwa da juna  kallon inda SH Batai ba duk da tana jin Kallonsa a cikin jikinta Amma bazata iya ba duba da wanda suke tare da ita a parlon, SH  kuwa yana kallonta cikin wani irin nutsuwa da ke nuna cewa ya damu da ita.

Sakin Ammey Baffa yayi inda su Abdul suma sukazo suka rungume,anan dai kowa ya samu gurin ya zauna.kafin a shiga abinda ya tarasu.

Su Fatima ne masu Serving Inda suhaima tana bangaran da SH yake haka tagama zubawa yan uwanta kafin tazo kansa tana cikin zuba masa kunun gyada yayi saurin rike mata Hannu"barshi haka ngd"kowa ya ga abinda ya faru Amma shi ko a jikinsa.

Fatima da yaya Abdul suka kalli juna ta kashe masa ido daya irin ya kagani,Murmushi yayi kafin yayi mata magana da ido shima,ai baki sake suke kallonsu domin yaran sun gama kwance musu zani a kasuwa wato wani lamarin sai yan zamani.

Sai da kowa ya koshi Sannan aka kuma parlon inda ka fara bada labarin yadda Aka rasa Ammey da kuma Yadda aka sameta a JEMETA.

Cikin sanyi jiki Ammey ta fara bada labarin yadda abin ya kasane"Suhaima batayi 1 month da fara zuwa University ba wata ranaTun kafin Abba ya fita wasu abubuwa sun fara canzawa a jikina, Wani lokaci ina  fama da ciwon kai mai tsanani, wani lokaci jikina yana yin nauyi, ina kasa cin abinci, kuma sai na kasa bacci,haka kawai zanji kamar ana kirana a waje,tun abun bayamun tasiri har yazama nadaina samun nutuwa jiki da ruhi,haka zanji kamar ana huramun wuta a cikin jikina a ranar bayan kafita abin ya tsananta haka kawai naji Kamar a fizgata idan ban bar gidan ba bazan sami nutsuwa,tunda na fita bansan ko ina a cikin Garin Kano ba Amma naji garin gaba daya yayi mun zafi,tun daga wanan lokacin ban sake sanin komai ba,na manta da komai .

Innalillahi wa'inna'ilaihi Raju'un
Innalillahi wa'inna'ilaihi Raju'un
Innalillahi wa'inna'ilaihi Raju'un

Baffa yake mai maitawa domin kana jin wannan labari kasan da akwai Sihiri a cikin abin Amma abin tambayar shin waye?me kuma tayi musu?

Hajjiya ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta kalli Baffa tace"tabbas Asiri kaiwa Ammey Domin Anan ka karya asirin

Kowa da ke parlon shiru yayi,domin biri yayi kama da mutum,cikin tashin hankali Abba yace"Asiri?"Abba ya dafe kansa jin kansa na juyawa to shidai ba iya saninsa babu wanda Ammey ta taba yin fada dashi dan ko Mommy bata shiga harkarta tunuwa da Mommy da yayi yass ya dago da kansa cikin fargaba da tashin hankalin abinda kunuwansa zasu ji masa.

cikin  kwalla Ammey tace "Ban sani ba a lokacin,Na ɗauka rashin lafiya ce kawai".

Cikin Sauri Abba yace"kenan tun daga Kano kika zuwa JEMETA a kafa"?

Wallhi bansan ya kaina zonan ba kawo Ni kai da kafata nazow Allah mashini.

Sai a lokacin SH yayi magana yace"tabbas a ranar da Ammey tashigo JEMETA na ganta Ni ne na same ta

Kowa ya juya yana kallesa dan jin yadda abin yake,SHya sauke ajiyar zuciya yace"tabbas naga Ammey a Ranar ina dawowa daga wani wuri  a Lokacin duhun magariba ya gaba to,Ina kan hanya ta dawowa gida domin nayi mantuwa kuma ina so na daga nan na wuce Asibity.

Ya yi shiru na ɗan lokaci"Na ga wata mata tana tafiya ita kaɗai a bakin hanya wanda hanyar yana da hatsari sosai domin  manya manya motocine suke yawo su bugeka suyi tafiyarsu,gashi idan ta shiga tsakiyar titi sai ta koma gefe kuma,har na hira ta da motata sai nadawo baya domin a yadda take bazaka ce bata da lfy domin da hijjab a jikinta sabanin masu irin matsalarta da zakaga suna wayo cikin moni abin ba kyau.kallon farko da nayi mata nagane bata da lafiya ba,da farko ban sani ba. Amma yadda take tafiya ya sa na tsaya.

Na sauka daga motata naje gareta domin na tambaye ta ko lfy take hawa tsakiyar titi,ko da na tambayata kai tsaye tace mun"Ba na tuna komai sosai daga wannan lokacin,duk tambayar da nayi mata bata fadamun komai ba,nayi juyin duniya Amma taja bakinta tayi shiru.

Suhaima ta share hawaye abun gwanin tausayi.

“Na tambaye ta inda take zama. Ta kasa amsawa. Sai kawai ta riƙe kanta tana cewa, ‘Ina so in koma gida… ina so in koma gida.’”
Sosai abin ya dameni take nayi waya asibityna a taho da Ambulance da mata guda biyar domin daukarta dan ban san matsalarta ba,ko da kazo daukatar da kyar kai nasarar sata a mota.

Ko da akai ga nan nasa DR Maryam ta duba ta ta wanke mata gashiduk wani abu da ake wa mara lfy akai mata nan da nan dawo cikin nutuwarta ta jiki Amma banda Na kwakwalwana,nasa DR ta sake dubamkn  lfyar jikinta,take aka gano tana fama da zazzabin nan fa natashi a hankalin kowa ka mata Test aka sa mata ruwa da allurai na bacci.

A lokacin abubuwan sun mun yawa shiysa na dura hakkin kulawa da ita karka shin. likitoci suka yi mata gwaje-gwaje.

Jini.

BP.

Sugar.

Scan.

Komai aka yi mata amma abin mamaki shi ne,ba a gano wata cuta mai tsanani a tare da ita ba, sosai likitocin sukai mun bayani game da ita bai nuna wata babbar matsala ba.

Abinda suka fara ganowa shin Har yanzu tana fama da ciwon kai, rashin barci da rikicewar tunani,sosai abin yake damuna domin haka kawai naji ina so na taimaka mata,ganin kullum kulawa ake da ita amma ba sauki kawai naje na samu wani Babban malami nake fada masa wanna abubuwan da suke faruwa ana yake yake fada mun tabba Anyi mata Asireni domin tabar gidanta da garin da take.domin kurciya akai mata wacce bazata taba daina yawo bahar sai kurciyarnan tasamie inda zata tsaya to itama anan zata tsaya da tafiya,Sosai na tsora ta irin wanna shirkar dan wani abu da bai kai ya kawo ba ace zaka iya salwantar da rayuwar sa.

Sosai parlon kowa ya shiga tashin hankalin jin irin abubuwan da suka faro da Ammey dan ma wasu abun ba cikin hankali bare ace ta sansu.haka ya jima yana basu labarin har yadda ashirin ya karya,da yadda ya gane Ammey mahaifiyar suhaima ce.

Sosai kayi addu'ar neman tsari ga dukkan abun ki,tare da fadar da su akan mahimmacin addu'ar a jiki da na dukkan al'amuran rayuwa.

Shiru kowa yayi kowa da irin abinda yake sakawa a zuciyar Baffane yayi gyran murya inda ya hau bayani cewa"Amm Auta da akwai wani abu da muka kulla tsanin mu,wanda mukace bazamu fada ba sai ranar tazo to Alhmdullah kuma gata,bayan Bacewarki Ni da Lamido da Dady Mun kwalu Aure tsakanin Sha'ayan da Suhaima sai kuma Fatima da Abdul,abinda yasa muka boye musu munyi Alkawarin har sai ranar da muka sameki Sannan zamu fada musu,to yau Allah yayi ikonsa gaki gamu gasu.

Sosai Ammey taji dadi inda bata boye ba tace"Alhmdullah Baffa Ni kagama min komai Domin Ko da suhaima tana soyayya da wani tofa bata da miji face sha'anyan domin yayi namijin kokari wajan kula dani dashi da family sa,Abdul kuwa wanna naka ne ko kare kai da shi ta fada tana dariya.

Dariya duk akayi inda Fatima tace yana da magana,sosai suka mai da hankali kanta domin jin abinda zatace"Dady Abba Baffa ita fa suhaima da akwai wanda take so Dan ya dade yana sonta Amma har yanzu bai Bayyana mata kansa ba,

Ai a 360 SH ya dawo yana watsawa Fatima wani kallo,gwalo tayi masa ta dauke kai,dan tayi alkawari sai ackin mutane zata sa ya tuna kansa.

Baffane ya kalli suhaima yace"Autar Ammey abinda Fatima tace haka ne?cikin kunya ta daga kai alamun eh hakane.

Murmushi Baffa yayi da cewa"To malam Sha'ayan kaji duk abindasuka fada ko"?

Da sauri yaya Abdul yace"dan Allah baffa abar maganar dan wanda take magana dai shine SH din ba SECRET LOVER ba to ga dai Shi a gabanki magana ta kare"

Sosai Suhaima ta kideme Daman duk shine Amma yake mata yawo da tunani.ai bata bari an karshe labarin ba tayi daki da gudu,Fatima ta rufa mata baya inda sister SH suma suka bita dan wllh yanzu zasuyi shirin bikin nagani na fada.

Barinau Parlon anan Baffa da Abba suka tsayar da lokacin biki 24 September 2026 idan Allah ya kai mu.