RIKICIN DUNIYA

Chapter 10

by @meenatyandoma

CHAPTER 10
..."Malam! Malam me nake ji nake gani haka.?" Haɗe tsohuwar fuskarsa da ta yamutse yayi.
"Me kika ji ta fada? Ke Nadiya maimaita mata abinda kika ji na fada"
Da sauri Nadiya ta fara magana
"Kai nake so, kai zan aura a daina yi mini maganar Kasim na tsanesa"
Ta karasa maganar idanuwanta cikin na Malam Bawa.
Zabura tayi ta miƙe.
"Na shiga uku! Me nake gani haka? Shin gaske ne ko kuma mafarki. Baka ji abinda na ce kayi mana bane"
Murmushin mugunta ya yi. "Na ji mana sannan abin da idanuwanki suka nuna miki haka take. Ki bini a sannu saboda control din diyarku ya dawo hannuna, sai yadda nayi da ita"
Zaman yan bori Inna ta yi tare da rushewa da kuka.

"Kai da muka zo ka share mana kuka kai zaka yi mana irin wannan cin amanar. tsofai-tsofai dakai ko ni dana haifi Nadiya ka girme mini bare Nadiya ina zata kai ka. Don girman Allah kada ka karasa lalata rayuwar yarinyar nan na yafe na fasa son aiki ka sallame mu kawai..."
Tsawar daya daka mata ce ta sakata hadiye sauran maganar dake bakinta.
"Ku je ku kawo mini ita a matsayin mata ko kuma ta kawo kanta ba tare da barin gidan nan ba"
Ya karasa maganar ya na kallon Nadiya.
A firgice Inna ta miƙe.
"Allah ya tsine Maka albarka la'anannen ɗan tsubbu. Wallahi ko zata mutu ba zata aureka ba mayaudari maha'inci"
Ta karasa maganar tana fizgar hannun Nadiya.
Ƙin tashi tayi ta fara tirjewa.
"Ki sake ni ki rabu da Ni"
Cewar Nadiya tana mai kwace hannunta.
"Tunda kince bakya ji kin dauki lamarin nan wasa. Bari In nuna miki wanene Malam Bawa. Ke Nadiya miƙe tsaye"
Kafin ya rufe baki ta miƙe tana muzurai.
"Koma ki zauna" 
Shi ma da sauri ta zauna.
Baki buɗe Inna ta yi tsabar tashin hankali kukan da take yi ma ya tsaya.
"Ba sai nayi miki dogon bayani yanzu ke ganau ce ba jiyau ba. Don haka zaɓi ya rage ga mai shiga rijiya. Ko ku kawota matsayin matar aure ko kuma ita ta kawo kanta. Ke Nadiya kama hannun mahaifiyarki ku tafi gida.

Miƙewa tayi ta damƙi hannun Inna suka fice.
Bata zame ko ina ba sai tsakar gidansu ta sakarwa Inna hannu. Kuka ta sake fashewa da shi tare da faduwa kasa.
"Na shiga uku" 
Ta karasa maganar tana billayi cikin ƙasa.
Jamila da ke suyar qwara a kofar gida a gigice ta shigo gidan hankali tashe tana tambayar baasi.
"Jamila mun shiga uku, mun kai kanmu ga halaka. Malam Bawa ya cucemu"
"Inna ki Sanar da ni abin da ke faruwa kun tayar min da hankali yadda naga kun shigo gidan nan"
Sallamar Malam Amadu ce ta tsayar da Inna daga maganar da take yi.
"Yawwa Malam asirinmu ya tono muna cikin masifa"
Ta karasa maganar tana dafe kirji.
"Subhanallahi! Ke Jamila me ya faru"
Malam Amadu ya fada cikin tashin hankali.
"Wallahi Baba nima ban sani ba, ina kofar gida ina suya naga sun wuceni a cikin wani irin yanayi daya sakani dole na biyosu."
"Ke Nadiya ƙila za ki iya fada mini abin da ya faru tunda tare kuka je ke da mahaifiyarki. Shin ina kuka je?"
Kafeta da ido ya yi yana jiran amsa.
"Gidan Malam Bawa muka je"
Nadiya ta fada tana sosa ƙeya
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Gidan Malam bawa kuma?"
Wani sabon kukan ne ya kwacewa Inna ta fizgi hannun Nadiya alamar  tayi shuru. Sai dai a banza saboda ƙaimi ta kara wurin fara bayani.
"Dama.. dama... Baba dama kai nake jira so nake In Sanar maka ina kaunar Malam Bawa ka ceci rayuwata ku aura mini Shi wallahi idan na rasa shi mutuwa zanyi na roke ka dan girman Allah Baba"
Ta karasa maganar murya na kyarma ta zube bisa guiwowinta tana mai rike kafar mahaifinta.
Malam Amadu mutuwar tsaye ya yi Jamila kuwa tsabar mamaki ta kasa kwakwkwaran motsi.
Sun dauki ya kai mintuna biyu kafin ya samu ya fizgo maganar dake bakinsa.
"Asibi!"
Yanayin daya kira sunanta sai da ya haifar mata da mummunar faduwar gaba.
"Me ye gaskiyar abinda yarinyar nan ke fada. Da gaske daga gidan Malam bawa kuke, tsohon ɗan tsubbu dana sani?"
"Tabbas munje amma bazan taba bari Nadiya ta auri wancan tsohon banzar ba. Wallahi Malam yaudarar mu yayi?"
Murmushin takaici yayi 
"Asibi kenan. Wato kaf abubuwan da ake fada mini a kanki kin aikata ko? Wato kaikayi ne ya koma kan mashekiya?"
"Tuggu ne da mugunta kawai ake hada mana a wurinka. Amma abin da ya kai mu wurin Malam bawa neman taimako ne akan cutar da Kawar Nadiya Wasila ta yi mana, Malam Wasila ta kwace Kasim shi ne muke yaki bakin kokarinmu ganin mun kwatosa. Munje wurin Malam bawa da zummar neman taimako shi ne ya ha'incemu ya yaudarar mana diya yanzu dai ya asirce ta sai abinda ya ce shi take yi"
Zafi da ƙunar da zuciyar Malam Bawa keyi masa ji yake kamar zata faso ƙirjinsa ta faɗo.
"Na fada kuma zan sake nanatawa. Ni ban rena matsayin da Allah ya ajiyeni ba, don haka shi ya sa kuka ganni cikin rufin ashirin Allah. Ku fada mini yau mugun halinki a ina ya kai ku In banda fadawa ga halaka. Muguntar da kuka so yi gata nan ta kare a kan diyarki. Ke da kika kasance uwa mai bada tarbiyyar, yau kece ke jan hannun diyarki ku je har wurin boka. Wannan wace irin rayuwa ce.
Abu na karshe da nake so in fada mini, na rantse miki da Allah yadda kika yi sanadin fadawarta gidan Malam Bawa banga abinda zai haka In aura masa ita ba."
"Wallahi Malam baka isa ba. Ko Ni dana ga jiya naga yau me zanyi da Malam bawa bare kuma Nadiyata, wallahi ko zanyi yawo tsira bazan taba bari ta zauna ba."
Nadiya dake riƙe da kafar mahaifinta jin furucib Inna ya sakata miƙewa a rikice ta tsayar da kukan.
"Guduwa zanyi in bar gidan nan muddun aka ce ba za a aura miki shi ba sai na shiga duniya."
Nadiya ta ƙarasa maganar tana cizgar kuka.
"Wallahi ko za ki mutu ba bazan bari ki auri Malam Bawa ba."
Cewar Inna 
"Kinyi ƙarya Asibi. Yadda kuka je kuka ɗebo ruwan dafa kanku bazan bari ku wulakantani a cikin al'umma ba gobe zan daura mata aure da wanda take so."
"Amadu ka kasheni. Ka rasa sakayyar da zaka yi muni sai ta aura mata wancan tsoho. Indai ina numfashi ba zata aureshi ba"
Inna ta karasa maganar tana fizgar hannun Nadiya. Sai dai a banza domin kamar dutse take ja.
"Baba zaka aura mini shi KO in kwashe kayana In koma gidansa?"
Duk da ɗacin da maganar tayi masa da sauri ya ɗaga mata kai alamar e.
A cikin daren ba karamin artabu aka yi ba tsakanin Nadiya da Inna Asibi sai da Jamila ta fara tofa mata addu'a sannan aka samu bacci ya dauketa.
Cikin daren Malam Amadu ya taka kafa da kafa har gidan Malam Bawa. Sun tsayar da magana bayan sallar asuba za a daura auren Nadiya da Malam bawa hatta kudin sadaki ya tanada.

Bayan an gama sallar Asuba ba tare da sanin Inna Asibi ba Malam Amadu ya bada auren Nadiya.
Ita dai ta ga ya shigo gida hannunsa dauke da goro, abinda ya fada mata ihu ta kwala ta yanke jiki ta fadi...

Meenat A. Yandoma
***