DUHU BAYAN MURMUSHI

9

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 9.

Sarac Stars R Pen...✍️

Safiyya ta samu mama babba tana zaune a tabarma suna hira da mama ƙarama da take yanka alayyahun da za a saka cikin abinci, Safiyya ta fashe da gigitaccen kuka ta faɗa cinyar mama. 

Ke lafiya zaki tashi hankalinmu da kuka irin wannan, meya faru.? 

Cewar mama babba tana ɗago Safiyya wacce fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye, cikin kukan tace. 

Mama Jabir ne zai yi aure nan da sati uku. 

To shi ne me.? Ai kaɗan kenan daga halin wasu mazan, kuma idan bai yi haka ba ai bai nuna miki shi ya haifu ba, dan haka sai ki cire shi a ranki gabaɗaya domin ba bu alamar ma zai zo ayi sulhu, ke ce kawai kika kwazzabi kanki da damuwa akansa. 

Ta ƙare maganar tana share mata hawaye, mama ƙarama taja dogon tsaki. 

To dama ai dole zai samu wata tunda ke ya gama kashe taki rayuwar, wlh Safiyya ki shiga hankalinki ki yakice shi a ranki, in da yana sonki wlh da yanzu ya zo biko akan ki koma, ai abun da mamaki ace mahaifiyarsa bata zo ba balle ta kira, dama sun gaji da ke kece baki sani ba. 

Safiyya ta kuma rushewa da kuka wanda yake fita tun daga allon zuciyarta. Sai da tayi mai isanta kafin tayi shuru dan kanta tana sauke ajiyar zuciya, mama babba da mama ƙarama suka cigaba da bata maganganu na rarrashi tare da hasko mata Jabir ba shi ne kaɗai namiji ba, idan baya sonta akwai da yawa da zasu so ta suyi zaman aure da ita har ta haihu ba tare da ƙorafi ba, sannan a wannan gaɓar addu'a zata cigaba dayi domin babu abunda yafi karfin Allah, duk abunda ke faruwa da saninsa kuma idan ta jure zata samu mafita cikin ruwan sanyi, wannan maganganun sune suka sanyaya mata zuciya ta daina kukan sai dai idaununta sunyi ja sun ƙanƙance, tabbas itama a yanzu tana jin koda son Jabir zai kashe ta ne to ta haƙura da aurensa, sai tayi kwofa tana cewa. 

Wai kun san ce min yayi idan na amince zan cigaba da bin tsarinsa to zai zo ya mayar da aurena mu koma. 

Iye.! lallai bai shirya ki koma ba, amma yaron nan asalin mara kunya ne, duk wannan abun da aka yi masa akan ya gyara kuskurensa ne amma babu alamar zai gyara, shiyasa ya shirya yin aure domin ya tabbatar miki da ba kya gabansa. Wlh Safiyya ki dawo cikin hayyacinki Jabir baya sonki tunda baya son ƙaruwa da ke, ai idan namiji yana son mace duk lalurarta zai ɗauka ya jure ya taya ta niman magani, dan haka Allah ya haɗa kowa da rabonsa amma fa idan kin so kenan. 

Cewar mama ƙarama cikin damuwa, mama babba tayi kwafa. 

Ai idan tayi wa kanta faɗa zata kwantar da hankali ne ta mayar da jikinta, kuma miji goma ba uba goma bane, abincin wani gubar wani kina nan zaune zaki ga na kwarai ya fito. Bari ma Baffa ya dawo yasa Gadanga ya fara niman miki aiki, kina fita idda ki fara zuwa, ai Jabiru ba autan maza bane da ba zaki barshi ba.

Haka suka cigaba da mitar maganar har su Salim da sauran yaran gidan suka dawo, suma da suka samu labari ƙara ƙarfafa wa Safiyya guiwa suka yi akan ta haƙura da Jabir ta cigaba da rayuwarta. Kuma koda Baffa ya dawo ya samu labari shima ƙara rarrashin ta yayi tare da nasiha akan yarda da ƙaddara, Safiyya ta samu sukuni a zuciyarta ta kuma gamsu Jabir ba zai sauya ba dan haka ta haƙura da shi itama yaje yayi aurensa itama ta kama rayuwarta. Dama maza da dama sukan yi amfani da raunin mace ne suna juya akalarta da shi su ci gaba da gallaza wa rayuwarta, idan namiji ya fahimci zaki jure wulaƙanci saboda tsoron saki, ko tsaron barin yaranki akan wani hali zaki barsu, ko kuma kina yi masa mugun so da zaki jure komai matsawar zai zauna dake, ko kuma kina son zama dashi dan kuɗinsa duk wahala da wulaƙanci zaki jure muddun ba zai matse miki zif ɗin aljihunsa ba, to tabbas kina ruwa.! Idan kika bari yasan raunin ki to zai cigaba da janki ne a ƙasa saboda ya gane lagonki na tsoron rabuwa da shi, mata da dama suna fuskanta ƙalubale ne a gidan aurensu da jurewa wahala saboda wani tsoro da suke yiwa gobensu, amma shi namiji babu ruwansa zai cigaba da amfani da wannan damar da kika buɗe masa ƙofar yana azabtar dake yana kashe miki rayuwa, kuma wani lokacin rabuwar aure maslahce a rayuwarki, idan 'ya'yane kike tsoron karsu tagayyara sai kiga a dalilin matsawarki hankalin uban ya dawo kansu Allah ya saka masa son su da tausayinsu, idan kuma tsoron saki ne da tunanin faɗan iyaye sai kiga da zarar kin fita sai Allah ya duba lamarinki ya baki wani mijin cikin ƙanƙanin lokaci kiyi aure. Haƙiƙa idan har ba kece kika cutar da mijin ba In Sha Allah sai kiga kin rabauta bayan fitowarki, sai Allah ya dube ki ya baki mafita. Shi yasa Jabir yayi amfani da raunin Safiyya yake juya rayuwarta ba tare da ta fahimci kasheta yake yi a tsaye ba, kuma har yanzu irin wannan tunanin yake da shi akan Safiyya na cewar ba zata taɓa iya rayuwa da wani namijin ba sai shi, domin shi kaɗai yasan irin abubuwan da ya yi mata a cikin zamansu ta shanye ta jure zama da shi duk dan tana sonsa, yanzu ma yana ganin zugin 'yan uwanta ne yasa har aka samu galaba akan son da take yi masa ta nima su rabu, yana ganin zata basu kunya, zata dawo masa ya cigaba da gasa mata aya a hannu wanda a ganinsa shi ne iya soyayyar da zai nuna mata, domin a kullun tunaninsa yana ƙoƙarin gina musu rayuwa mai daɗi ne a nan gaba da yaran da zasu haifa. Safiyya ta nisa tare da cewa cikin rauni. 

In sha Allah Baffa na haƙura kuma har yanzu ban sauya daga niyyar ƙin koma wa aurensa ba, na bar shi kamar yadda shima ba zai sauya daga nashi ƙudurin ba. 

Allah yayi miki albarka Safiyya ya zaɓa miki abunda yafi alkhairi a rayuwarki. Idan kina buƙatar cigaba da karatunki In Sha Allah da zarar kin gama Idda zan saka Gadanga ya shige miki gaba. 

Cewar Baffa da murmushi a fuskarsa, Mama babba tace. 

Wani karatu kuma Baffa ai wanda tayi ya isa, kawai yanzu a samar mata aiki ne, dama nace in ka dawo sai muyi maganar, idan kuma miji ya fito da aikin ta ya ganta sai ayi yarjejeniya. 

Hakane amma abunda take so shi zanyi mata ko Safiyya. 

Baffa ya ƙare maganar ga Safiyya cikin murmushi, itama murmushi tayi tana gyaɗa kai kafin ta miƙe ta yi masa sai da safe ta wuce ɗaki tana mai sauke ajiyar zuciya mai nauyi, haƙiƙa mara mata bayan da iyayenta suka yi da bata ƙarfin guiwa yasa ta samu wani natsuwa a zuciyarta, kuma In Sha Allah zata yi amfani da damar ta wajen cin ribar rayuwa. Da ace haka iyaye suke shiga cikin matsalar gidan auren 'ya'yansu da tabbas matsaloli sun ragu sosai kuma maza zasu daraja matansu, abunda iyayen Safiyya suka yi tabbas sun samar mata 'yanci ne, sai dai kuma suma basu samu damar haka ba sai da goyon bayanta saboda wasu matan ga shi dai suna cikin matsala amma fa sai suƙi yarda iyayen su shiga ciki balle a samo bakin zaren matsalar a gyara, saboda tsoro ko son mijin ya rufe musu ido. 

*****

Mujaheed. 

Da rana wajen ƙarfe biyu inna tana ɗaki ta idar da sallah saboda tayi bacci sosai bata daɗe ta farkawa ba, Aina'u ce ta kawo mata abinci a wani plate an rufe da murfi sai ta fita ba jimawa ta dawo da ruwan pure wata a hannu guda ɗaya ta ɗaura a saman plate ɗin, sai ta fita zuwa tsakar gida dan amsar kuɗin cefane da zata fita kasuwa tayi wanda mama zata yi mata bayanin abunda zata siyo. Daga ɗaki kuma Inna da sauri ta shafa addu'a ta buɗe plate ɗin saboda tana jin yunwa sosai dan karin safen nan bai yi mata ba haƙuri kawai tayi, a hankali ta jawo plate ɗin gabanta sosai, taga abincin dake ciki babu yawa sosai kuma an zabga masa yaji a sama an yaɗa mai, sarai Uwale tasan inna bata son yaji shiyasa ko zata ci shinkafa da wake tafi gane a bata yaji ta zuba da kanta yadda ba zai cutar da ita ba, haka tajuya abincin da tunanin ƙila yajin bai da zafi sosai shiyasa ta zuba mata haka, sai dai sai'lin data kai abincin bakinta nan take harshen ta ya ɗau zafi kau kamar ana tsaga mata shi dan azaba, da sauri ta haɗiye ba dan ta shirya ba sai dan ta samu sassauci, ta ture plate ɗin ta fasa pure water ta soma sha sai da ta sanye kafin ta samu sauƙi, sai ta miƙe cikin sauri ta ɗauki plate ɗin abincin kafin ta fito tsakar gida ta samu mama tana yiwa Aina'u lissafi, Inna ta dire mata plate ɗin a gabanta. 

Yanzu Fisabilillahi Uwale sau nawa nake faɗa miki bana son yaji da yawa a abinci nafi gane a bani na saka da kaina, loma ɗaya nayi amma da kyar ya wuce maƙoshina, gaskiya in da wani ki sauya min da shi bazan iya cin wannan ba. 

Aiko inna sai dai kiyi haƙuri mu gama tuwon dare dan abincin daya rage na yara 'yan makaranta ne kuma duk na zuba yaji a ciki, ni na sha'afa bakya son yaji wlh. 

Aina'u kasuwa zaki je ne.?

Cewar inna dan bata bi takan zancen inna ba saboda tasan karya take yi kawai kora da hali take yi mata duk dan kar ta zauna a gidan ɗanta, Aina'u tace mata eh sai ta kunce haɓar zaninta ta ciro kuɗi ɗari biyar data ɗaure tun ɗazu data tsinta a cikin kayanta. 

Ungo ki siyo min fura da nono na sha kin ji, a saka miki sugar a ciki. 

To Inna amma zaki rage min ko dan ina son nono. 

Idan naƙoshi ba. 

Inna ta faɗa tana gutun murmushi wanda ya ɗan kawar da ɓacin ran da take ciki, sai ta koma ciki ta samu waje ta zauna tana tunanin mugun halin Uwale, banda rahin arziki taya ma zata saka mata wannan dan abincin da ba zai ishe ta ba, ƙiri-ƙiri ita da gidan ɗanta amma zama yana niman gagararta, to duk in tazo dan ta zauna ta kwana biyu amma Uwale sai tayi mata abunda taji zaman ya ishe ta ta koma ba shiri, ita kuma ba irin tsofaffin nan bane masu takurawa Surikarsu ko kuma ta riƙa kai ƙararta wajen baba wanda bata fatan ace sadaninta suna samun saɓani, musamman data lura baba yana mugun son Uwale shiyasa ta zaɓi yin shuru tare da nuna dattako, ta tabbatar watarana zai zama labari komai zai wuce, sannan tasan itama Uwalen uwar maza ne watarana zata zama surukar wasu, idan har alkhairi tayi mata zata cimma haka a gaba imma akasinsa ne duk zata ga sakamako. Haka ta kai kusan uku da mintuna bata ci abincin rana ba har wani dishi-dishi ta fara gani dan sam bata da jumurin yunwa, bata da ci sosai amma bata wasa da ci uku a rana da zarar lokaci yayi zata nima taci, a lokacin Aina'u ta kawo mata furan ta haɗo da kofi ta juye mata daga ledan ta miƙa mata, Inna ta amsa ta kafa kai bata sauke kofin ba sai da ta yi rabi kafin ta fidda numfashi ta kuma kafa kai, shaf ta manta da Aina'u tace zata sha sai da ta shanye tas ta aje kofin kafin gyatsa ya biyo baya, tayi hamdala da addu'ar Allah ya buɗa wa kowa. Sai ta miƙe ta fito da kofin ta samu mama ta soma goge kuɓewa, inna ta shanye fushin ta ta zauna suka cigaba da hira, tunda take bata taɓa nunawa Uwale tana fahimtar abunda take yi mata ba balle tagane fushinta, shiyasa ita kuma bata fasa ba dan ta tabbatar abunda take yi wa inna dole zai ɓata mata rai tunda gashi duk zuwa in tayi bata jimawa take tafiya.

Da daddare bayan sun gama cin tuwon dare suna ɗaki, wannan karan saboda akwai wutar nepa suna kallo a TV. Inna taci tuwo ta ƙoshi ba ƙorafi, dan Mama ta iya allonta tunda tasan dole ta bata abincin da zai isheta saboda kar baba ya dawo ya tambayeta ta bata mata wasan. Aina'u da ta ke waya a tsakar gida bayan ta gama ta shigo tana murmushi ta samu guri ta zauna tace wa mama. 

Wai kin ji yaya Idris yace nan da kwana biyu zasu zo a tsayar da magana, yace in faɗa amma Kawu ma zai kira babanmu. 

Kai Masha Allah Allah ya kaimu, kice muna da manyan baƙi, to da Idi za a zo.?

A'a yace sai an kwana biyu zai zo. 

Aina'u ta bata amsa tana sunne kai cikin jin kunya, inna ta murmusa tace. 

Ja'ira ji yadda take sunne kai wai ita kunya, yarinya aure ba abun wasa bane in zaki ware yafi miki. Wai ko Uwale kina ƙoƙarin koya mata abubuwa musamman kula da miji da sauran ayyukan gida, kinsan uwa ita ce makarantar farko ga yara, haka ma kuma in maganar aure yazo uwa ce ke fayyacewa yarinya rayuwar auren da komai da yake cikinsa dan kar ta tafi kai a duhu. 

Ina iya ƙoƙarina inna, sai dai zan ƙara zage damtse tunda abu yazo. 

Cewar mama cike da farin ciki, tana matuƙar son auren saboda zumuncin da zai ƙara ƙulluwa a tsakaninta da ɗan uwanta. A lokacin aka ɗauke nepa sai Aina'u ta kunna wayarta mai Torchlight haske ya bayyana, mama ta miƙe ta ɗauko hasken ɗakin ta kunna sai suka tattara suka koma tsakar gida kan tabarma suka cigaba da hira. Ko da baba ya shigo a lokacin yayi matuƙar farin cikin ganin inna idonta biyu gashi suna ta hira gwanin burgewa, yana son yadda Uwale take hulɗa da mahaifiyarta dan inna bata taɓa kawo masa ƙorafinta ba, sai dai kullun faɗanta ya kyautatawa iyalinsa. Baba ya ƙaraso da sallama ya zauna a kusa da inna yana gaisheta, ta amsa fuska sake tare da yi masa sannu da zuwa, mama itama tayi masa sannu ya amsa kafin ta miƙe ta kawo masa abinci, haka suka cigaba da hira har wajen goma na dare kafin inna ta yi musu sai da safe ta koma ɗakinsu Aina'u ta yi shimfida ta kwanta, a lokacin baba ya samu damar shiga ciki danya yi wanka. 

Rahma ce.