10
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 10.
Sarac Stars R Pen...✍️
Mujaheed acikin duhun daren yake tafiya cikin sauri danya isa gida, sai dai a raɓe yake tafiyan ta gefen hanta saboda tsoro, sai dai ihun wasu karnuka daya ji shi ne ya tsinka masa tunanin da ya saki fitsari a wando saboda tsananin tsoron daya ji, sai ya ruga a guje, biyu daga karnukan suka bi shi, Mujaheed ya ƙara ƙaimin gudun ceton rai yana yi yana waigensu, a dalilin haka ne ya faɗa kwalbati kansa ya ɗaki wani dutse, sai ya suma. Bai sake sanin halin da yake ciki ba sai da garin Allah ya waye hayaniyar mutane ya dawo dashi hayyacinsa, gabaɗaya jikinsa ya ɓaci da ruwan kwata ga ciwon daya ji a goshinsa har jinin ya bushe, mutane sunata bayanin farfaɗiya ne ya bigeshi ya faɗa kwata, kuma aka rasa wanda zai ciro shi sai surutun banza suke yi, ana cikin haka sai ga Baba ya ƙaraso wajen saboda wani yaro ne ya je gidan ya sanar dasu halin da ake ciki, hawaye ya cika idon baba sai ya shanye su ya tsuguna gefen kwantan ya miƙa masa hannu, babu musu Mujaheed ya miƙo nashi hannun ya kama na baba sai ya yunƙura ya tashi zaune, baba ya jawo hannunsa ya miƙe tsaye ya taimaka masa ya fito daga kwatan ya tsaya akan ƙafafunsa, a lokacin mutanen da suka zagaye su suka ja da baya, wasu suna toshe hanci saboda warin zawon da Mujaheed yayi a jikinsa na wahala, baba ya ja shi suka fara tafiya, wasu yara suka fara waƙar sha tara malam Lawal maƙocinsu baba ya koresu ya shiga cewa baba.
Malam Musa wannan yaro ya dace ku dage wajen nima masa magani saboda abun nasa ƙara gaba yake yi.
In Sha Allah zamu dage.
To Allah ya bashi lafiya.
Ameen baba ya ce yana jin zuciyarsa tana yi masa nauyi saboda tausayi halin da Mujaheed yake ciki. A haka suka isa gida suka samu hankalinsu mama a tashe, Inna ta saka salati.
Meya same shi ne Babangida na ganshi haka.
Faɗuwa yayi a kwata.
Baba ya faɗa yana basu labarin yadda mutane suka sanar da shi, mama ta shiga salati sai ta wuce kitchen ta juye ruwan flakes a bokiti ta sirka ta kai bayi, baba ya ƙarasa da Mujaheed wajen bayin ya fara taya shi rage kayan jikinsa kafin ya tura shi cikin bayin ya taimaka masa yayi wanka, sai da mama ta kawo musu ruwa sau buyu dan ba ƙaramin wanka baba yayi masa ba, da suka fito ya shiga ɗankinsa ya saka wasu kayan suma masu datti ne, ya kwanta a katifarsa jiki babu kwari dan sosai yake jin kansa wani iri, a haka bacci ya ɗauke shi baba yace a rabu dashi ya huta zuwa anjima sai a bashi abinci ya ci, haka ya fice kasuwa yana tunanin Mujaheed da yadda zai nima masa magani, gashi dai suna ta ƙoƙari amma babu sauyi abun nasa sai ƙara gaba yake yi.
Inna kuwa ta saka Aina'u ta samo mata garwashi a maƙota sai tasa masa turaren magani, ta aje a ɗakin, shi dai baccinsa yake yi amma ko kaɗan bai farka ba duk da hayaƙi ya gauraye ɗakin. Mama ta dubi inna data yi shuru tana tunani tace.
Inna karfa ki saka damuwar Mujaheed a ranki dan wlh mu mun saba da wannan, bari ki gani anjima zai fito kamar ba shi ba kuma ba zai fasa fita yawon ba, baya jin magana yana da taurin kai wlh.
To ai ba yin kansa bane amma da ƙalau yake ba zai zama haka ba, Allah ya bashi lafiya, ni na fara tunanin ko na wuce da shi Daura ne Malam Babba ya ganshi, ƙila a gano matsalarsa.
To Allah yasa kar ya jawo miki magana, dan Mujaheed tantirin kansa ne.
Cewar mama tana taɓe baki, Inna ta dube ta cikin damuwa.
Haba Uwale a matsayinki na Uwa bai dace ki riƙa faɗar ko wace irin magana akansa ba, ai magana mai daɗi sadaka ce. Kuma furucin Uwa yana tasiri akan yaranta.
To Inna idan kika tafi da shi kauye ke da kanki zaki ji ya gundureki dan Mujaheed bai da hali, in ya ƙuntuka miki wani shirman sai kinji kamar ki yi ta zaginsa ko zaki huce.
To Allah ya kyauta.
Inna ta faɗa dan ta fahimci mama ba zata taɓa sauyawa ba, abunda ranta yaso shi take yi.
Mujaheed kuwa koda ya farka yaji kansa da nauyi sai ya kasa fitowa ya cigaba da zama a ɗaki, sai da inna ta leƙashi ganin rana ta yi bai ci komai ba ga shi ya farka, sai ta koma ta kira Aina'u ta saka masa abinci ta kawo masa yaci, tare da maganin da inna ta kawo masa, Mujaheed ya kali Aina'u yace mata.
Kaina yayi min nauyi ki bani magani.
To yaya bari na amso maka paracetamol.
Cewar Aina'u kafin ta fito ta amso maganin ta kawo masa yasha ya ƙara kwanciya, a haka ya yini a ɗaki sai wajen yamma ya fito ya sake ficewa daga gidan cikin sauri babu wanda ya ganshi.
*****
Jabir.
Murmushi yayi a lokacin da Safiyya ta kashe masa waya, yasan zata sauko ne dan yana ji a jikinsa ya samu hanyar dawowarta cikin rayuwarsa, ba zai bari ta ɓata masa shiri ba dan haka ko zai dawo da ita sai bayan anyi aurensa yaci amarci cikin natsuwa, ya tabbatar a lokacin ta gama tagayyara da ƙuncin zaman gidansu da kuma damuwar yana tare da wata mace ba ita ba, sai ya daki table ɗinsa da ƙarfi yana dariya.
Dole zaki dawo wlh, an gaya miki zan zauna damuwar tafiyarki ya wahalar dani ne, ai sai yanzu naga fa'idar yin wannan auren, ashe Ummi gata tayi mini, gwara na nuna miki ba ke kaɗai bace mace ina da damar inyi uku bayan ke. Nifa Duniya sabuwa.! ga Zaliha ɗanyen jini ga Safiyya tsohuwar zuma na tabbatar zan sha tarairaya idan na haɗasu.
Ya ƙare maganar yana murmushi jin daɗi saboda haƙƙarsa ya cimma ruwa kamar yadda yake fata, Safiyya tashi ce shi kaɗai ya tabbatar a yanzu ta gane muhimmancinsa tunda gashi kuka wiwi take yi akan aurensa, ai soyayyarsa ma ba zai barta ta samu sukuni ba, shi kaɗai yasan irin gubar soyayyar da yake shayar da ita a duk ranar da zasu raya dare wanda ba duk namiji ba, shi Allah ya yi shi da cikakken lafiya sam baya shan maganin ƙarfi da wasu suke sha saboda yana mugun tsoron abun da zai kawo masa tawaya ga lafiyarsa nan gaba, amma fa yana amfani da fruit da kayan islamic da suke ƙara wa mutum lafiya, a koda yaushe yana yawan bincike akan haka dan shima yana mugun son harkar oza room gashi kuma Allah ya bashi Safiyya dai-dai shi, wannan yana ɗaya da ga cikin raunin Safiyya da ya sani da yake ganin tabbas zata dawo masa. Abokinsa Yaƙub ne ya shigo yace.
Maza wannan farin cikin fa.?
Kasan Safiyya yanzu ta kirani tana kukan zan ƙara aure.
Wow kace an zo gurin, ai malam ka rabu da ita kasha shagalinka da amarya sai ka huta kafin zaka waiwaye ta, lokacin ta gama yanke zata dawo gidanka, kaga sai ka shimfiɗa mata dokokinka, nasan dole zata bi dan zaman gidan iyayenta ba zai taɓa yi mata daɗi ba. Ni kaga da wannan nake juya Salma bata kawo min wargi wlh, in ba haka ba ta kwana gidan Ubale.
Ya ƙare maganar yana sheƙewa da dariya, Jabir shima ya kwashe da sabon dariya suka cigaba da magana cikin nishaɗi abun yana yiwa Jabir daɗi in ya tuna Safiyya ta kira shi. Kuma koda ya koma gida sai da ya kira Ummi ya faɗa mata Safiyya ta kira shi, Ummi ta ja tsaki tana cewa.
Ka rabu da ita dan karta burkita maka lissafi, kaga dai bikin nan ya matso, idan an gama in ta gyara halinta zata bika sau da ƙafa sai ka mayar da ita, in taƙi ka rabu da ita ta ɗanɗani zawarci.
Ai ummi abunda na yanke kenan ba zata ɓata farin cikin da nake ciki ba, In Sha Allah nan da kwana uku ko huɗu zan zo Kano dan na riga na rubuta hutu har sai an gama biki.
Alhamdulillahi gwara kazo da wuri ayi komai da kai. Kuma abunda nake so da kai tunda Safiyya ta sani to ka cigaba da yin hidimarka kana sakawa a status yadda ita da 'yan uwanta su gane zaka rayu ko babu ita.
Ummi ai ni baki ji farin cikin da nake ciki ba, kuma idan nazo har gida zan aika driver ya kai katin aurena gidansu.
Da kyau ɗan Ummi, in kayi haka ka ƙara faranta mini.
Haka suka cigaba da hira cikin nishaɗi ummi tana ƙara zugashi, da suka gama wayar Ikilima da ta gama sauraren ummi duk jikinta a sanyaye dan bata jin daɗin yadda Ummi take nuna ƙin komen Safiyya, ta kuma lura yayansu bai gane manufarta ba tace.
Ni ce fa na faɗa mata ɗazun.
To ai kin kyauta munafuka, In Sha Allah auren nan za a yi shi idan ma kina da wani ƙulli a cikin ranki.
Kai ummi ni me nace kuma, ai ina son auren yaya da Zaliha, amma ina fatan anty Safiyya ma ta koma suyi zamansu.
Kyaji da shi, idan kin gama gulmar ki taso zan aike ki.
Cewar Ummi a kufule, Ikilima dariya tayi kawai ta miƙe ta wuce ɗakinta dan ta shirya. Jabir kuwa haka yayi kwanan farin cikin dan har sai da yayi mafarkin Safiyya da ya saka shi wanka, sai ya wayi gari cikin tsantsar Kewarta, bai san ma yana mugun sonta ba sai da ta kira shi jiya, ashe shima ya damu da rashin ji daga gareta, kawai ya daure ne da tunanin zai jata a ƙasa dan ya cim ma manufarsa, kuma gaskiya Zaliha tana ɗebe masa kewarta sosai shiyasa yake jin baya damuwa, amma jiya data kira shi ya ƙara jinsa cikin wani irin fari ciki daya jima bai samu kansa a ciki ba, ga shi ya wayi dari da son ganin ta sai ya shiga bitar kallon hotonanta da suke cikin wayarsa, wani shi da ita wani kuma ita kaɗai, haka ya shagala har lokaci ya wuce bai samu zuwa wajen aiki da wuri ba sai da yayi latti.
Kamar yadda ya yanke shawara bai sake niman Safiyya ba ya cigaba da shirin biki, a ganinsa ya gama ɗana duk wani tarkon dawowarta gidansa. Duk yadda Jabir yaso yaje Kano a saura kwana goma bikinsa hakan yaci tura dole sai biki saura kwana biyar kafin ya tafi a gurguje, aiko yasha faɗa wajen Ummi har tana cewa ko zai saki aikin ya dawo su cigaba da kasuwancinsu da Nura tunda aikin nasa akwai takura, dama bata son yayi nesa da ita, Jabir ya shiga bata haƙuri tare da nuna mata muhimmancin aikinsa wanda shi ne zai kai shi ga matakin cim ma muradin buɗe campaninsa a nan Abuja da yake fata, jin haka yasa ummi ta sarara masa sai ta shiga yi masa maganar shagalin biki da abubuwan da zasu gudana. A daren ranar ya samu zuwa gidan su Zaliha suka yi magana da ita wanda duk dai na hidimar bikin ne, sai dare sosai wajen sha ɗaya da rabi ya shigo gida, a sannan ne ya samu ya watsa ruwa yayi shirin bacci dan gaskiya bayi da yunwa yaci abinci a wajen Zaliha wanda ta girka masa na musamman, ba laifi itama ta iya girki dan yaji daɗin abincin, duk da bai kai masa na Safiyya ba, shifa har gobe ya kasa daidaita son Zaliha akan na Safiyya a ma'aunin zuciyarsa, har abada baya jin zai so wata mace kamar Safiyya domin ita ce zaɓinsa, sai ya saki murmushi tunawa da wani lokaci mai daɗi da ya gudana a tsakaninsu, suyi wasa, suyi tsalle-tsalle da guje-guje a falonsu ko ɗankin baccinsu, suyi bacci maƙale da juna kamar zasu zama abu guda, ya sauke ajiyar zuciya.
Nayi kewarki Safiyya sosai, duk ranar da kika dawo hannuna zamu raya daren tare da bashin sauran dararen.
Sai ya lumshe ido yana lissafin bai wuce wata ba zata fita Idda, yana so a gama bikin ne kamar da sati guda sai ya waiwayeta, zuwa lokacin yasan ta gama laushi sannan ma daya ce zai mayar da ita zata amince, da wannan tunanin yayi bacci mai cike da mafarkinta. Wasu na ɗokin aure amma shi gabaɗaya ɗokinsa yana ga Safiyya, yana jin kamar ya rufe ido yaga adadi kwanakin da ya ɗiba sun cika ya kirata suyi magana. Sai dai kuma a shirin Ummi tana fatan auren ya ƙare kenan, shiyasa take ta shirya yadda zai manta da batun Safiyya har sai ta fita Idda, musamman ta shirya taje gidan Hajiya Maryam ta tasa Zaliha a gaba da bayanin ta kula da Jabir sosai in an kaita gidansa, tayi duk yadda zata yi wajen ɗauke masa hankali, kar ta bari ya samu damar tunanin Safiyya a kwanakin honeymoon ɗinsu, shiyasa ta shirya musu tafiya zuwa ƙasar waje baima sani ba, sai a washe garin auren zata bashi Visa a matsayin kyautar da ta shirya masa, daga Hajiya Maryam har Zaliha ba ƙaramin murna suka yi ba musamman data tabbatar musu bata son Safiyya ta dawo rayuwar Jabir, suma kuma sun amince da hakan dan dama Hajiya Maryam bata son 'yarta tayi zaman kishi, shiyasa ta cigaba da yi mata gyara na musamman dan su samu makamin da Zaliha zata riƙe zuciyarsa gam ya rasa lokacin yin tunanin komai da kowa sai nata.
.....
Ranar Asabar da misalin sha ɗaya na safe da minti goma aka ɗaura auren Jabir da Zaliha a bisa sadaki dubu ɗari biyar, wanda ɗumbin jama'a suka shaida domin an yaɗa ɗaurin auren a gidan tv da ma na radio, kuma wannan aikin Ummi ce da tasa a yi shela saboda gidansu Safiyya su tabbatar da auren ɗanta, kuma ta tabbar saƙon data tura zai isa garesu cikin sauƙi ta yadda suma zasu ƙara ɗaukar ɗamarar hana Safiyya ta koma gidan ɗanta, saboda tasan zasu ji haushin auren daya yi tun da bai je ya mayar da igiyar auren 'yarsu ba.
*Akwai kura a tafiyar nan da. Ko kun hango*
Rahma ce.