DUHU BAYAN MURMUSHI

11

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 11.

Sarac Stars R Pen...✍️

Jabir yayi farin ciki da aurensa sai dai haka kurum yake jinsa kamar bai kyauta wa Safiyya, a lokacin sai ta dinga faɗo masa a rai yana tuna ranar ɗaurin aurensu wanda aka ɗaurashi a kofar gidansu, ana ɗaurawa ya kirata yace ta fito yana son ganinta,  Safiyya ta nuna masa tana jin kunya ba zata fito ba sai ya kashe kiran ya nufi shiga gidan, Abokinsa Jamil ya kama masa riga. 

Kai ina zaka je.? Ka bari mutane su ragu sai mu shiga. 

Jamil wlh Safiyya nake son gani yanzu. 

Ya faɗa a raunace kamar zai fashe da kuka, dariya sosai Jamil yayi ya shiga yi masa tsiya, da kyar ya haƙura ya fasa shiga gidan sai bayan sallar la'asar da suka dawo daga walimar da suka yi shi da abokansa, suka shiga cikin gidan bayan an sanar da shigowarsu kusan su goma, suka yi gaisuwar iyaye kafin suka fito wajen gate suka jira Safiyya ta ƙaraso da
Ƙawayenta, cikin sauri Jabir ya isa inda take ya rungumeta tsam a ƙirjinsa ya fashe da kukan murna itama ta fashe da kuka, sai suka zama abun kallo da mamaki, wasu na ɗaukarsu a waya, a wannan ranar da kuma shekarar video ɗinsu yayi tashe a yanar gizo, sosai suka bawa masoya sha'awa suka burge su dan sun hango ruwan ƙauna a tsakaninsu. 

Jabir yane muje gidansu Zaliha ko.?

Cewar Yaƙub yana dafashi wanda ya sashi dawowa daga gutun tunanin aurensa da Safiyya, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi. 

Ina ga mu bari kawai sai anjima in zamu ɗauke su zuwa wajen dinner sai muyi gaisuwar iyaye gabaɗaya. 

Kai Jabir ashe zaka girma, na ɗauka zaka maimaita irin abunda ya faru na aurenka da Safiyya, Anya Amaryar nan ta samu gurbi a zuciyarka kuwa.?

Cewar Jamil yana dariyar shaƙiyanci, Jabir ya kai masa duka yana murmushi ya goce. 

Ai kasan na zama Dattijo, wancen lokacin muna cikin ƙuruciya. 

Cewar Jabir sai duk abokan suka saka dariya suka shiga yi masa tsiya yana kare kansa. 

****

Safiyya duk yadda taso ta yakice damuwar Jabir ta kasa, domin tunani shi ke yin kansa, sai dai mutum yayi yaƙi da zuciyarsa, babban mamakin daya ƙara kashe mata jiki shi ne yadda Jabir bai biyo bayan kiranta ba, ada tasan kukanta abune da yake ɗaga masa hankali wanda sai ya san yadda yayi ya rarrasheta, amma sai gashi ya nuna ko inkula akan kiran da ta yi masa tana kuka, ta tabbatar shima ya ɗauki fushi ne da ita shiyasa ya zaɓi yin aure dan ya ƙunsa mata baƙin ciki, bata taɓa zaton irin son da Jabir yake yi mata zai ƙara aure nan kusa ba, ta san bai taɓa yi mata alƙawarin ba zai ƙara ba amma a yadda yake tsara musu rayuwa baya kawo zancen zai ƙara aure, kullun burinsa ya bunƙasa yayi kuɗin da zai kula da ita da abunda zata haifa, kuma tana zargin ko da mahaifiuyarsa ce ta sa shi auren shima yana so, hakan yana nufin koda ya mayar da ita haka za ta cigaba da zama da shi ba haihuwa kuma tana kallo matarsa zata fara haihuwa ita kuma baƙin ciki da ciwo ya yi ajalinta bayi da asara, ta tabbatar da Jabir ya gama lasa mata Zuma a baki, yanzu harbi kawai yake ɗana mata ta ko'ina tana jin ƙuna da raɗaɗi, tabbas a yanzu tana cikin duhu bayan murmushin da bata taɓa tunanin zai gushe ba. Haka a cikin kwanakin ta zama sukuku kowa ya zuba mata ido babu mai takura mata sai tausayi da take basu, sun tabbatar cewar soyayyar Jabir shi ne babban jarabawar da Allah ya yiwa Safiyya domin tana cikin izaya, ta kasa seta kanta akan Ƙaddarar da take ciki, kullun cikin lissafin zuwan ranar auren Jabir take wanda shine yake ƙara raunata kuzarinta dama garkuwa lafiyarta. Shiyasa koda aka aiko wa Baffa da katin auren basu bari taji ba tunda sunsan aike ne da gayya dan su nuna musu iyakarsu.

Saura kwana biyu bikin take ta fama da zazzaɓi har asibiti mama ƙarama ta rakata aka haɗa mata magani, wanda ba iya zazzaɓin ke damunta ba harda jinyar zuciyarta da ta kasa samun sukuni da tunanin rayuwar da ta gudana a tsakaninta da Jabir, kullun gani take kamar mafarki take ta farba, sai kuma ta riƙa tunanin shin irin rayuwar da suka yi shi ne zai yi da amaryarsa.? sai taji wani abu mai ɗaci ya taso mata daga ƙirji zuwa maƙoshi, ta kasa ci ta kasa sha sai mama babba tayi da gaske take kurɓan tea.

Washrgari juma'a ƙannenta maryan da Abida suka zo gidan yini, can sai ga matar yaya Ali da kuma Anty Indo, gida ya cika da iyalin Baffa da jikokinsa dan sada zumunci, a ɗakin mama babba suka yada zango suna ta hira Safiyya dai tana ciki tana wanka, kuma koda ta fito shiryawa tayi cikin doguwar riga mara nauyi ta shafa mai tabi lafiyar gado, mama ta leƙo tana duban ta. 

Yanzu Safiya haka zaki cigaba da rayuwa cikin ƙunci, ga 'yan uwanki sun zo amma kin kasa fitowa kuyi zumunci, hirar da zaku yi sai ya rage miki wani mikin da zuciyarki take ciki, tunda kin kasa karɓan ƙaddara. 

Rabu da ita mama ai in ta kashe kanta Jabir bai da asara tunda gashi ya nuna mata cewar ko da ita babu zai yi rayuwar da yake so, na rasa meyasa ma tasa ya saketa tasan tana son zama dashi da matsalarsa, mara zuciya kawai kin yar kare ya ci, ni wlh da ni ce ke dana bawa banza ajiyarsa nayi rayuwata mai daɗi da 'yanci. 

Cewar anty Indo cikin faɗa dan tana mugun takaicin abunda Safiyya take yi a gidan, sai ɗagawa mutane hankali take yi, mama ta juya tana kallon Indo.

Babu ruwan ki, bansa da ke ba. 

Ki barta ta faɗa, ai dama nasan Anty Indo ko mutuwa nayi ba zata yi kuka ba balle kewata.

To yaushe zanyi kuka bayan kin kashe kanki akan mutumin da bai san darajarki ba. Haba Safiyya ke ba yarinya ba ce amma kina mayar da kanki baya, abu yaƙi wucewa a gurin ki. Kina ma yin addu'a da niman zaɓin Allah ko damuwar ne zai kawo miki mafita, wlh duk wanda ya bar Allah shima sai ya barshi, ga Al-Qur'ani maganin ƙunci da damuwa, ga salati Annabi s.a.w waraka daga kowani irin mikin zuciya, ga Nafila mai ƙunshe da tarin lada da buɗewar falala ga lamuranki. Safiyya ina kika bar duk tarin Ni'imomin da Allah yayi miki, ya baki iyaye, ya baki ilimi ya baki hankali ya baki lafiyar da zaki bauta masa, meyasa dan kin rasa wani abu da ya baki ya amsa ba zaki gode masa ba ki dage wajen niman zaɓinsa, kin zauna damuwa tana kassara lafiyarki saboda wani halitta wanda Ubangiji zai iya yi miki maganinsa, ki kai masa ƙarar Jabir ki gani in ba zai duba lamarinki ba. Allah ya yaye miki. 

Cewar Anty Indo a fusace ta bar ɗakin, mama tayi jim tana lissafin maganar Indo wanda zallar gaskiya ce, sai ta girgiza kai ta kalli Safiyya. 

Idan zaki yi duba da maganar ya'yarku gaskiya ta faɗa domin Allah baya ɗaurawa bawansa abunda yasan ba zai iya ɗauka ba, sai dai in mutum ya kasance mai raunin imini da gajen haƙuri, dan haka nima ina tunanin zan fita daga lamarinki tunda haka kika zaɓarwa kanki. 

Tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin zuciyarta a dagule, tun dawowar Safiyya itama lafiya tayi mata karanci saboda hawan jininta da yake yawan tashi kullun cikin shan magani take, uwa ita ce kaɗai tasan irin damuwar da take shiga idan 'ya'yanta suna cikin matsala, balle lamarin Safiyya da sunata ƙoƙarin kwantar mata da hankali amma taƙi basu dama sai ƙara lalacewa take yi, yanzu babu bambanci da zaman gidan mijin nata da nan gidan iyayenta, a baki tana cewa ta bar Jabir amma taƙi seta zuciyarta da gangar jikinta akan suma su bar shi har abada. Ko da mama ta fita Safiya ta tsurawa ƙofar ido tana kwalla, tasan gaskiya suke faɗa mata amma kuma ta kasa hana kanta tunanin Jabir dama rayuwar su ta baya, shiyasa ta burkice ta kasa shiga cikin hankalinta.

Washegari da nauyin zuciya ta tashi wanda shareta da mama tayi ya ƙara haifar mata da shi, tana a kwance tun bayan data sha tea dan ta kawar da yunwa, wayar ta tana hannunta tana kallon tiktok a haka ta shafe awa guda da rabi kafin bacci ya ɗauketa. Ta farka wajen ƙarfe sha biyu saura ta duba wayar taga ta bar data a buɗe sai ta cire password ta ga kira daga Salma matar Yaƙub dama kiran ƙawayenta guda biyu, sai saƙonnin WhatsApp da yawa ta saman wayar, sai ta shiga ciki ta fara duba saƙon Farida ƙawarta. 

Fiyya wai da gaske Jabir yayi aure.? ɗazun naga sanarwar a TV, na kira ki dan na tambaye ki baki ɗaga ba. 

Zuciyar Safiyya ta buga tare da jin kanta ya sara. Bata iya bata amsa ba ta fita ta isa wajen status ta fara dubawa, kusan numbobin ƙannen Jabir ne ta gani jere duk sun saka hotuna, ta shiga na Nura taga hotonsa ne da abokansa cikin manyan kaya da ya nuna suna wajen ɗaurin aure, sai ta fita daga nashi ta shiga na Rahma, hoton Jabir da Zaliha ta gani cikin shigar aure kamar free wedding pics, a wannan lokacin gabanta ne yayi mummunar faɗuwa ganin Zalihar data sani itace matar daya aura, sai wayar ta faɗi daga hannunta saboda sarƙewa da numfashinta ya yi yana yi mata wuyar fita, sannan jikinta ya ɗauki zafi yana kakkarwa, daga haka taga duhu yana gilmawa ganinta, ta yi wani jan numfashi da ƙarfi daga haka jikinta ya saki bata sake sanin inda hanka yake ba. 

Kausar ita ce ta shigo ɗakin da nufin ta amsa wayar Safiyya, kamar yadda Yaya Ali ya kira mama ƙarama ya faɗa mata a amsa dan yasan in ta ga wani abu da ya danganci auren Jabir zai tashi hankalinta, da yake mama babba ta fita zuwa wani biki na danginta da ake yi a ranar, Kausar tayi mata magana amma taji shuru sai ta tsaya tana duban yanayinta amma taga kamar bata motsi, da sauri ta fita ta kira mama ƙarama suka dawo tare itama ta duba ta taga bata numfashi mama ta saka salati ta fita tana kwalawa Salim kira da yake can sashin mazan gidan, da sauri ya ƙaraso tace ya samo musu abun hawa zasu kai Safiya asibiti, sai ta koma ɓangarenta ta ɗauko mayafi suka zo suka kama Safiya data sanƙare ita da Kausar, Hafsa da ma Salim ɗin suka wuce da ita asibiti a napep saboda babu mota a gidan, Baffa ya fita da nashi, ɗayar kuma ta lalace tana gareji a rufe. 

Safiyya sai da ta kwana bata san in da kanta yake ciki ba, sai washegari ta farka amma ba um ba um-mu, likita ya hana a shiga saboda bata buƙatar hayaniya domin har lokacin bata gama dawowa hayyacinta ba. Haƙiƙa suman data yi ya samar mata da wani itin hutu da bata taɓa tunanin samu ba, domin zuciyarta ta huta, gangar jikinta ya huta, haka ma idanun ta sun huta daga zubar hawaye, kuma ko da bata dawo hayyacinta ba har lokacin tana cikin hutun da Allah ya samar mata, dan ta mance kowa da komai, wataƙila zuwa lokacin da ta dawo hayyacinta zata iya seta kanta tare da karɓan ƙaddararta, a yanzu sai ware ido take yi wanda haske kawai take gani da mutane dishi-dishi bata ma san duniyar da take ciki ba. A bayanin likita ya tabbatar kwakwalwarta ne bai gama dawowa daidai ba saboda dogon sumar data yi, sannan kuma ya kwantar wa 'yan uwanta da hankali wanda duk a furgice suke ganin Safiyya tana tsakanin rayuwa da mutuwa, duk sun gama sarewa saboda halin da take ciki bata san wanda ke kanta ba. 

Da rana Baffa ya ƙara dawowa dan tun safe da ya zo yaga halin da take ciki ya kasa samun natsuwa sai ya koma gida yayi mata tofi a ruwan zamzam ya bawa Ali ya kawo akan a bata, sai ya kasa dawowa sai yanzu, koda ya shigo yaga matansa jugum-jugum bai ce komai ba ya nufi ɗakin likita suka yi magana akan abunda ke damunta, likita yace depression ne ya kamata sannan zuciyarta ta kumbura tana buƙatar hutu na ɗan wani lokaci cikin kulawarsu, sannan a kiyaye ɓata mata rai ko tuna mata wani hali da take ciki na damuwa, domin a yanzu memory ɗinta bai gama dawowa ba bata gama sanin me take ciki ba saboda dogon sumar data yi, Baffa yayi masa godiya yace a yi mata komai daya dace kafin ya fito ya kira Ali da yake tare dasu mama, suka fita wajen parking suka yi magana akan matsalar domin baya so iyayenta mata su ji hankali ya kuma tashi, Ali yace. 

Baffa idan aka sallame ta ko za a shirya mata tafiya ne zuwa Yola ta samu ta huta sosai. 

A'a Gadanga ta zauna a nan ta koyi juriya da haƙuri, domin duk inda taje ma in bata daina damuwa ba to ba za ta samu yadda take so ba. Itace zata gyara tunaninta ta karɓi ƙaddara. Na tabbatar tunda tace ta haƙura da aurensa haka ne har zuciyarta, tunanin baya ne yake dawo mata da damuwa shi yasa ta samu kanta a haka. Amma In Sha Allah idan ta sha wannan ruwan tofin zata samu natsuwa.

Hakane Allah ya bata lafiya. Ɗazun ma mama ƙarama ta zuba mata ruwan a baki ta haɗiye.

To Alhamdulillahi, muna fatan Allah ya saka mata dangana da juriya, yasa kaffara ce.

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

Cewar Yaya Ali kafin suka koma ciki suka cigaba da jiran tsammani. Baffa bai jima ba ya koma gida. Wajen biyar na yamma yaya Ali ya mayar da mama babba gida saboda tun juya tana tsaye bata huta ba ga shi jininta ya hau ɗazun da aka gwadata, sai mama ƙarama da Kausar ne suka cigaba da zaman jinyarta.

Rahma ce.