DUHU BAYAN MURMUSHI

12

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 12.

Sarac Stars R Pen...✍️

Safiyya sai da tayi mako guda tana jinya a asibiti kuma zuwa lokacin ta samu sauƙi sai dai zubar jinin da take yi yanzu shi ne yasa ba a sallameta ba, anyi mata wani gwaji da hoton pelvic akan matsalar wanda sakamako ya tabbatar da mahaifarta ta samu matsala saboda tayi amfani da maganin tsarin iyali cikin rashin bin ka'ida shi ne ya haifar mata da yawan zubar jini da ciwon mara, sannan kuma a yanzu mahaifarta tayi raunin da ba zata iya ɗaukar ciki ba, idan kima ƙaddara yasa ta ta samu juna biyu to zai iya zama barazana ga ranta da abunda ke cikinta, shawarar da likita ya bayar a yanzu shi ne ta dakatar da duk wani tsarin iyalin da take yi sannan a ki yaye samun juna biyu, ta kuma riƙa shan magani cikin dokar likita, idan kuma tana da wasu yaran to zai fi a cire mahaifar gabaɗaya ta huta. Tunda likitan ya fara bayani Baffa ya shiga tashin hankali sosai, yaya Aliyu kuwa ya kasa seta kansa sai da yayi kwalla saboda tausayin Safiyya daya ke tsara masa zuciya, tayi komai dan taci ribar soyayya ta faranta ran Jabir, sai dai a hankali ya gama kashe rayuwarta gabaɗaya dan nashi farin ciki, yanzu idan Safiya ta samu labarin wannan abun ya tabbatar sai zuciyarta ta buga ƙila hakan ma ya zama silar ajalinta, haka suka baro ɗakin likita jikinsu a sanyaye bayan Baffa ya roƙi arzikin likita ya rufe maganar kar a bari Safiyya ta sani, suma ba zasu faɗawa kowa ba sun bar maganar a tsakaninsu, sai zuwa nan gaba idan hankali ya fara kwanciya. Bayan sun koma gida ta cigaba da samun kulawar daya dace, ba sa barin ta ita kaɗai, sannan Baffa yana ƙoƙarin yi mata tofi a ruwan zamzam wanda hakan ya zama hanyar samun natsuwar Safiyya har ta soma dangana ta karɓi ƙaddarar rabuwa da Jabir hannu biyu. 

******

Mujaheed. 

Da dare yayi bai iya dawo gida ba saboda tsoron abunda ya faru jiya da karkuna suka tsorata shi, sai ya kwana a rumfar wani shago cikin almajirai waɗanda suka saba kwana a gurin, sai ya saje da su saboda irin kayan dake jikinsa. Da safe a gidansu kamar yadda suka saba karyawa a tsakar gida matsawa ba ruwan sama ake yi ba ko sanyi yayi yawa, Inna ce take ta mitar tun jiya bata ga Mujaheed ba kuma taga kamar iyayen basu damu ba, ta riƙa faɗa tana cewa.

Bai dace ku riƙa yi masa riƙon sakainar kashi ba, idan ba shi da lafiya ai ku kuna da hankali sai ku riƙa taroshi kuna nuna masa dai-dai in ba haka ba wannan gantalin da yake yi mutane ƙara haukatashi zasu yi, kuma banda sakaci ace baku damu da ya dawo ko bai dawo ba amma kuna yin hidimarku hankali kwance.

Inna kuma ke da waye kike ta mita haka.? 

Cewar baba da fitowarsa kenan ya kammala shirin fita kasuwa, Mama ta taɓe baki.

Wai akan Mujaheed take wannan maganar, yaron da babu ruwansa da kowa ya zaɓi yayi rayuwa shi kaɗai. Kuma babu mamaki da sassafe ya fice daga gidan ya shiga gari.

To amma kince baki san ko ya dawo ba jiyan kike zancen ya fice da sassafe. Gaskiya Babangida banji daɗin wannan sakaci da kuke yi da yaron nan ba.

Cewar Inna cikin damuwa sosai dan sai da ya nuna akan fuskarta, Baba ya zauna ya tankwashe kafa ya yunƙura zai shiga yi mata bayani sai suka ji an kwaɗa sallama a ƙofar gida, dole ya miƙe ya saka takalmi ya yi hanyar wajen yana amsa sallamar. Ko da ya fita ya samu wasu Dattawa guda uku ne tare da Mujaheed kansa yana fitar da jini, gaban baba ya faɗi, ya miƙawa mutanen hannu suka gaisa sai ɗaya daga ciki ya fara korowa baba bayani. 

Ga sha tara nan mun kawo shi, ya zubarwa wani yaro da markaɗen kunu, to shi ne samarin dake wajen suka yi masa duka, da kyar muka raba rikicin. Dan Allah ayi masa faɗa ya daina saurin kai hannu jikin mutane domin wasu in sun haƙura wasu ba zasu haƙura ba, Allah ya kyauta. 

Nagode Allah ya saka da alheri In Sha Allah za a yiwa tufkar hanci ayi haƙuri. 

Cewar baba kafin mutanen suka yi masa sallama suka wuce, shima ya tasa ƙeyar Muhajeed suka shiga gidan yana ta yin faɗa zuciyarsa a dagule. Ganin yadda fuskar Mujaheed ya sauya da jini yasa su Inna duk suka miƙe tsaye suna salati, nan baba yayi musu bayanin yadda lamarin ya kaya, sai inna ta saka kuka dan tausayinsa, murya a karye tace.

Babangida Ina ganin a shirya masa kayansa mu tafi Ƙauye idan bikin Aina'u ya matso sai na dawo dashi, lokacin komai ya kwaranye kuma zanyi ƙoƙarin yi masa magani a can ɗin In Sha Allah.

Gaskiya wannan shawara ce mai kyau innata, Bari yanzu inna fita zan nima almajirai da suka saba yi masa wanki su zo su wanke masa kaya su gyara ɗakin. Amma yaushe zaki tafi.?

Ai ni ko gobe In Allah ya kaimu sai mu tafi hankalina zai fi kwanciya.

Amma inna ba zaki bari jibi ba saboda goben In Allah ya kaimu mutanen Magami zasu zo kan batun auren Aina'u.

Haba ai ko ina nan ko bana nan za ayi komai, kawai ka shirya mana tafiyarmu goben In Allah ya kaimu.

To Allah ya kaimu lafiya. Ni bari na tafi kasuwa lokaci ya tafi sosai.

Inna tace Ameen a dawo lafiya. 

Mama ma tace a dawo lafiya sai ya wuce. Sai suka koma suka zauna mama sai ta haɗa masa ruwan wanka ta tilasta shi akan sai yayi, yana cuzgune fuska yayi wankan dole, daya fito ya kuma sauya kaya ya nufi hanyar fita, inna ta dakatar da shi. 

Maigida ai yau babu kai babu fita sai gobe In Allah ya kaimu in zamu wuce Daura. 

Mujaheed yaja ya tsaya bai juyo ba bai tafi ba, mama ta daka matsa tsawa. 

Zaka dawo ciki ko sai na saɓa maka dan ubanka, ko innar zaka nunawa taurin kai shashasha mara lissafi, a hankali in baka yi wasa ba sai mutane sun gama haukata ka. 

Haba Uwale kiyi masa a hankali mana wannan faɗan da kike yi masa ƙara taurare zuciyarsa kike yi, a yanayinsa lallashi yafi buƙata. 

Cewar inna cikin sanyin murya, mama tayi kwafa. 

To na barki da shi Inna, kunfi kusa. 

Tana gama faɗar haka ta wuce ɗaki, inna ta jinjina kai. 

Allah ya kyauta, Ke Aina'u ɗauko min jakar kayana na cire masu datti ki ɗauraye min In Sha Allah da safe zamu wuce Daura.

Aina'u tace to kafin ta wuce ciki, Muhajeed kuwa ya dawo ya Zauna a ƙofar ɗakinsa ya jingina da bango yayi shuru yana tunanin faɗan da mama ta yi masa, in dai a waje ne bata yarda a taka mata yara dan ba tada kawaici, amma kuma a cikin gida karta masa rashin mutunci take yi ta zage shi tsaf in ya bata haushi. Mama ta sake fitowa ta cigaba da mita, inna ta riƙe baki. 

To mu dai gobe In Sha Allah zamu tafi, in mutane suka daina ganinsa shikenan ai wai-wai ya ƙare.

Ai ni nafi kowa farin ciki da zaku tafi a goben, Allah ya nuna mana lafiya.

Cewar mama data shiga kitchen inna da kallo ta bita harta ɓacewa ganinta tana mamakin sabbin halayyar Uwale waɗanda bata santa dasu ba. A wannan ranar Mujaheed a gida ya yini bai fita ba dan ya ƙara yin wani irin sanyi jikinsa a sake kamar yana cikin damuwa sosai. Kuma kamar yadda baba yace almajirai sun zo sunyi masa wanki da gyaran ɗaki sun tafi, kuma Inna tayi nasarar tilasta masa yayi wanka ya saka wasu kayan wankakku, a daren ranar ta samu damar fara yi masa turaren hayaƙin maganin data kawo masa.

Washegari da wuri Mama ta haɗa abun kari dan tasan inna tafiyar safe take yi, yau dai kam komai ta bata a wadace har sai da inna ta rage abun kari saboda yawansa, sannan mama sai wani haba-haba take yi da ita har wani nuna alhinin tafiyarta take yi a gaban baba tace. 

Inna ko dai a ɗaga tafiyar nan ne kwanaki uku da zuwan ki amma ace kin juya, dan Allah ko sati ki ƙara yi mana sai ku tafi.

Mamakinta yasa inna bata iya cewa komai ba sai murmushi da gyaɗa kai da take yi, ita kanta mama ta fahimci inna tana mamakinta ne tare da harbo jirginta, sai baba ne yace.

Ai tafiyar ne ba shiri nima zanfi samun nutsuwa Mujaheed ya bar unguwar nan na wani lokaci, kuma inta dawo bikin Aina'u zata kwana mana biyu kafin ta koma.

Hakane kuma to Allah ya kaimu.

Cewar mama tana rusunar da kai cike da girmamawa ga Baba, inna dai murmushi kawai take yi tana kallon kissa irin ta mama. Ba jimawa motar da baba yayi musu shata ta ƙaraso ƙofar gida, drivern daya saba kai inna Daura ne duk in ta zo Kaduna shi ne ma yau yazo, baba ya fita bayan mai motar ya shaida masa yana waje, yace su Aina'u su fitar da kayan abincin daya siyowa inna jiya na tsaraba, katan ɗin taliya ne da makaroni sai sugar da madara loka bibbiyu da lipton kwali biyu sannan wake loka uku, baba ya saba duk in inna tazo sai yayi mata wannan siyayyar domin acan bata rasa masara da shinkafa ba sai su taliyar ne tafi buƙatarsu, haka yaran suka fitar da komai har da kayan Mujaheed wanda tuni yayi gaba ya shiga mazaunin kusa da driver ya hakimce, Inna da ke cikin gida ta gyara zaman hijab ɗinta ta kalli mama da murmushi.

To Baƙo zai yi halinsa a yayyafe, idan mutanen Magami sun zo a miƙa min gaisuwata sannan ina fatan Allah yasa a ƙulla alkhairi yasa ayi damu.

Amin ya rabbi inna, Allah ya tsare hanya. Ni wannan tafiya ban so shi ba Inna saboda baki daɗe ba.

To ya za a yi haka Allah ya tsara.

Inna ta faɗa ta wuce gaba, mama kuma ta bita da makirin murmushi ranta fal da farinciki na samun nasarar tafiyar inna cikin sauri da sauƙi ba tare da tasha wahala ba, haka tabi bayanta tana auna aikin da zasu sha yanzu na abincin tarba mutanen Magami, dama bata son sa idon inna balle tace anyi almubazzaranci da abinci, dan ta shirya girki kala biyu tare da snacks data yi oder ɗinsa daga wajen RKtestybite donot da samosa. Bayan inna ta shiga mota nan suka ƙara yin sallama baba yana jikin window ɗin gefen Inna yana jera musu addu'ar sauka lafiya, inna tana amsawa da Amin tare da sanya masa albarka, duk cikin yaranta shi ne ɗa mafi soyuwa a ranta amma kuma saboda kunyar ɗan fari baisa ta nuna masa tsantsar son da take yi masa a zahiri ba, sai ma yanzu da alkunyar ta ragu mata shi ne duk in zata zo take yi masa tsaraba da duk abunda tasan yana so, sannan duk cikin yaranta yafi kowa yi mata biyayya, baya taɓa saɓawa umarninta yana binta sau da ƙafa tare da bata dukkan kulawa, gashi dai a ƙauye take rayuwa amma bambancinta da binni kaɗan ne domin baba ya wadatata da cimaka da binni da kuma mazauni mai kyau, dan shekarar daya gabata yayi mata gyaran gida har da fenti na zamani, ba tada matsalar wutar lantarki dan solar ya saka mata kullun cikin haske take wanda gashi anan gidansa bai saka solar ba sai ya samu halin sakawa, ta sauke ajiyar zuciya bayan motarsu ta nausa kan hanya tana shakar iska mai daɗi na sanyin Safiya.

Wajen ƙarfe biyu da rabi su Kawu Tijjani suka ƙaraso gidan baba, sun samu tarba mai kyau dan mama ba ƙaramin shiri na fita kunya tayi musu ba, danginta ne dole kuma ta nuna musu tana cikin wadata da rufin asiri ba zata yarda su koma suna tunanin ko wahala take sha ba, kuma sun tabbatar da gaske Uwale tana cikin rufin asiri sosai kuma hakan yana daya daga cikin ƙara kaimin son haɗa zuri'arsu auren zumunci ko zasu dangwali arzikin baba. Sai bayan sallar la'asar baba ya dawo tare da mutane biyu da zasu taya shi karbar maganar auren, ɗaya Abokinsa ne Alhaji Sani ɗanbatta, sai kuma abokin mahaifinsa Alhaji Sanusi wanda shi ne ya zame masa tamkar uba a Kaduna, hasalima shi ne idonsa dan ta sanadinsa ne yazo Kaduna har Allah ya bashi damar kafa kasuwancinsa, saboda bayan rasuwar mahaifinsa Muhammad Salisu a lokacin da Alhaji Sanusi yazo gaisuwa shi ne yayi wa Inna magana akan in babu matsala zai tafi da Musa Kaduna ya riƙe shi dan ya taya shi kula da kasuwancinsa, inna tayi murna dan dama anan gida noma da kiwo kawai suka sani, to bayan anyi addu'ar arba'in ɗin babansu shi ne Alhaji Sanusi yazo ya ɗauki Musa zuwa Kaduna ya ɗaurashi akan kasuwancinsa wanda gashi shima yanzu ya kafu sosai dan ya tsayu akan ƙafafunsa, shagon baba guda biyu a kasuwar gari, ɗaya na atamfofi da lesuna tare da shaddodi da yake bayarwa sari, ɗaya kuma na takalma ne na maza da mata harda na yara sai jakukunan mata da hular maza, shagon suna manne da juna, yana da yara biyu a ƙarƙashinsa da yake biyansu suna taya shi aiki.

Bayan sun gama gaishe-gaishe sai suka gabatar da juna sannan suka fara tattauna abunda ya kawo su, nan take baba Sunusi yace tunda abune na gida washegari za a ɗaura aure anan masallacin unguwar dan a taƙaita wa mutanen magami wahala da ɗawainiya musamman da hanyar Zamfara ba kyau saboda 'yan bindiga, in yaso sai a saka lokacin tarewar amarya cikin natsuwa, kuma cikin ikon Allah duk sunyi na'am da haka wanda suka yanke bayan wata biyu Aina'u zata tare lokacin an kammala duk wani shiri sai ayi taron biki, haka suka ɓata lokaci suna zantawa daga bisani suka shiga hirar duniya sai gabda magrib mutanen baba suka tafi akan washegari zasu dawo ɗaura aure, su kuma su Kawu suka wuce masallaci suna cike da farin cikin sauƙin da suka samu. A wannan ranar mama kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha dan farin ciki ganin komai yazo musu cikin sauƙi da salama, Aina'u kuwa duk da tana ɗokin aure sai da taji wani iri da jin kamar anyi gaggawar ɗaura auren, dan bata gama shiri ba duk da ance sai nan da wata biyu zata tare, wanda hakan ya tabbatar da zata fara lissafin barin gidansu na kwata-kwata ta faɗa wata rayuwar da bata taɓa kawowa kanta nan kurkusa ba.

Su Kawu a ɗakin Mujaheed suka kwana, Allah yasa a gyare yake dan har turaren wuta mama ta saka musu dan ta kasa yarda da ɗakin, gani take zasu ji warin datti kayan Muhajeed da ya so kama ɗakin.

Rahma ce.