ƊANƊANO
ƊANDANO🔜
“ Yeah, ba auren ta zanyi ba, kawai dai a sha nishad’i ne a wuce wajen, by the way she’s not my type, kawai dai burgeni take yi, and gidansu akwai kudi, kuma beb din classic ce; idan na tashi aure zan bar maka ita sai ka k’arasa”
Lumshe ido nayi wasu hawaye masu zafi suka zubomin, ko da wasa ban yi tunanin waɗan nan kalaman zasu fito daga bakin Reyyan ba, ko da wata ce take fad’amin hakan zan karyata ta, sai gashi da kunnena naji yana cewa ni ba type nashi ba ce, na dafe zuciyata da nakejin kamar zata tarwatse dan yanda take harbawa da sauri.
Nayi saurin saka hannu na goge fuskata, na aro murmushin karfin hali na shimfid’a, sannan nayi nocking motar tasa ya bud’e na shiga.
Wayan hannunsa yayi saurin kashewa ya ce, “ Beb, ashe kin iso, kin barni da kewarki tun dazu nake jiranki”
Ɗagowa nayi tare da zuba masa ido, hawaye naji sun soma sauƙowa ba tare da na shirya musu ba, tabbas ni me rauni ce akanshi, na ɗauki son duniya kaf na daura masa, ashe shi ba hakan bane a gun sa, bakina na rawa na soma cewa, “ Reyyan, me na maka da zafi haka?”
********
“ Ni ban damu da kudinka ko matsayinka ba Jalal, ni zan zauna da kai ba su ba, arziki kuma nufi ne na Allah In sha Allah zakayi, amma kar ka rabu dani dan Allah Jalal, zan iya rasa raina idan ka barni!!”
Ya zuba min ido yana kallon yanda nake kuka sosai, muryarsa a shaƙe ya kira sunana, “ Jidda,” Girgiza kai kawai nake yi ba tare da na ɗago ba, ya sake kirana a karo na biyu, “ Jidda,,, matsayin gidanku daban da namu, bance bana sonki ba, amma sorry to say bazan iya aurenki ba!!!”
Na d’ago cikin matsanancin kuka da murmushin da bansan dalilin zuwansa ba, na gyad’a kai tare da juyawa da sauri da niyar barin wurin, sai dai ko taku daya banyi ba na yanki jiki na fad’i a wajen…
******
Bansan sanda na zabga masa mari ba, na ja baya da sauri muryana na karkarwa na furta, “ Yanzu fa ni matar aure ce! lokacin da nake magiya ina binka akan ka soni kaki, sai yanzu? matar auren kake so?”
Hawaye na zuba a idanunsa yake fad’in, “ Jidda, a baya nayi kuskure amma yanzu zan gyara, ki bar gidanki ki dawo gareni, zan so ki fiye da kima, ni ne masoyin ki bashi ba, kuma kinji na rantse, wallahi sai na aureki ko ta halin ƙaƙa!!”
Dariyar rainin hankali na masa hadi da cewa, “ Anya Reyyan kasan ma’anar aure kuwa? na ce maka ina da aure ka ce na fito, are you out of your sense? ni fa?”
“ Ki kalla Jidda,” Ya matso kusa da ni, nayi baya ba shiri k’afana ya bugu da dutsi, na saki k’ara tare da rufe idanuna ina jiran naji na fad’i, sai ma muryan da naji yana cewa, “ Auren wa za’a kashe?…
Soyayyar Zamani🤩🔜
Labarin da ya kunshi yaudara irin na samari, cin amana, butulci, kaddara da sharrin maza.
Zai fara zuwa ne Ranar 20th ga watan September 2026, kuma zai fara sauƙa ne a kan Arewapen kafin channel, duk me bukatar ayi tafiyar nan dashi zai iya bibiya a wannan links din👇
Channel@ *** OR ***
Arewabooks@ https://www.arewapen.com/u/sahibarjajirtattu
Facebook@ ***
*** chat only