ZALLAR SHA'AWA...

33-34

by @zahrasurbajo

Da gudu Aisha ta koma ɓangarensu, tana rungume da Amna a kirjinta kamar wadda take tsoron kada a kwace mata ita, numfashinta yana fita da sauri, zuciyarta kuma tana bugawa da ƙarfi har ta kasa gane ko abin da take ji tsoro ne, fushi ne ko kuma wani irin ciwo ne da ya mamaye zuciyarta bayan abubuwan da suka faru a cikin waɗannan mintuna kaɗan. tana shiga ɗakinta sai ta wurgar da takardar da ke hannunta a gefe, sannan ta fara neman wayarta da idanunta cikin gaggawa, amma kafin ta kai ga inda wayar take, wani rubutu da ke jikin takardar ya  faɗo mata  ido da yaja hankalinta.Ta tsaya cak.
A hankali ta juya, idanunta suka sauka kan takardar da ta faɗi kusa da kujera.
Wani sanyine ya fara  ratsa jikinta.Ta ƙara riƙe Amna ta ɗan gyara ta a hannunta, sannan ta sunkuya ta ɗauki takardar da hannunta yana rawa, idanunta suka fara bin rubutun da ke jikin ta
. Rubutune da harshen Turanci, amma wasu kalmomin sun isa su sa duk wani jini da ke gudana a jikinta ya tsaya na ɗan lokaci.Akwai bayanin wata yarjejeniya da ta shafi cire  ƙoda daga jikin Jameelu, sannan akwai wasu kalmomi da suka nuna cewa aikin yana da alaƙa da kuɗi da kuma sayar da ƙodar wanda ita aisharce duk ta shirya hakan kamar yadda takardar ta nuna.
Aisha ta buɗe baki, amma babu sautin da ya fito.Ta sake karantawa.Sau biyu Sau uku.Kamar ba ta yarda da abin da idanunta suke gani ba.
Hannunta ya fara rawa sosai har takardar ta kusa faɗuwa daga hannunta, zufa mai ɗumi kuma ta fara keto mata daga goshinta duk da cewa ɗakin ba shi da zafi. Ta ɗora ɗaya daga cikin hannayenta a kirjinta, ta ja numfashi mai nauyi, sannan ta kalli Amna wadda take  hannunta ba tare da ta san irin bala’in da mahaifiyarta ke ciki ba.

“Jameelu...” Ta furta sunan a hankali, muryarta tana karyewa. “Ya Allah... Jameelu...”A lokacin ne abubuwan da suka faru suka fara haɗuwa a cikin kanta.
Maganar Moneer ta cewa ba sa buƙatar kuɗin aiki.Yadda ya dage ita ce za ta sa hannu.Yadda bai ba ta damar fahimtar abin da takardar ta ƙunsa ba.Yadda ya hana sauran likitoci shiga.Yadda aka ce Jameelu halin da yake ciki ya ƙara muni bayan aikin.Yadda mutuwarsa ta zo da sauri farat ɗaya,yanzu Kuma wannan takarda.
Aisha ta rufe idanunta na ɗan lokaci, hawaye suka zubo mata ba tare da ta lura ba.
“Kenan Ba Allah ne ya kashe shi kawai ba...” ta furta cikin rawar murya. “An shirya duka wannan.Dan a kawar da shi,?”
A lokaci guda zuciyarta ta cika da wani irin ƙarfin da bai taɓa samuwa a jikinta ba, domin abin da ta gani ya wuce zargi. Wannan takarda ta sa abin da ya kasance a zuciyarta a matsayin tambaya ya koma wata babbar gaskiya mai firgitarwa.

Ba ta sake tunanin wayarta ba.Ba ta sake tunanin komai ba.Ta ɗauki takardar, ta rungume Amna sosai, sannan ta fita daga ɗakinta tana tafiya da sauri zuwa ɓangaren Moneer.

Kofar tana buɗe.Ta shiga ba tare da sallama ba.Moneer yana zaune kan kujera yana shan ruwa, sanye da gajeren wando, fuskarsa kuwa babu alamar damuwa.Ko  Da ya ɗaga kansa ya gan ta, sai ya yi wani murmushi mai cike da ma’ana, kamar mutumin da ya riga ya san abin da zai faru.