35-36
ya ce cikin sanyin murya, yana ajiye gilashin ruwan. “Nasan zaki dawo. Dole”
Aisha ta tsaya a gabansa, Amna tana rungume da ita a ƙirjinta, takardar kuma a ɗaya hannunta.Ta kasa magana na ƴan daƙiƙu.
Moneer ya kalle ta, sannan idanunsa suka sauka kan takardar.Murmushin da ke kan fuskarsane ya ɗan ƙara bayyana.Sannan yace
“Me kika gani?” ya tambaya.
Aisha ta ɗaga takardar.
“Ka san me wannan yake nufi?”
Moneer bai amsa mata ba.Se murmushi da yake mata
“Ka san me wannan yake nufi, Moneer?” ta sake maimaitawa, wannan karon muryarta da ƙarfi duk da cewa jikinta yana rawa. “Kana so ka ce min mutuwar mijina ba ta Allah da Annabi ba ce? Kai ne ka shirya ta?”
Moneer ya yi shiru yana kallonta,Shiru mai tsawo.
Daga ƙarshe ya ajiye gilashin ruwan gaba ɗaya, ya jingina bayansa da kujera, sannan ya kalli Aisha kai tsaye.Yace
“Eh nine na shirya mutuwarsa.”
Kalmar guda ɗaya daya furta wacce ta faɗo kamar dutse a kan zuciyar Aisha.
Ta ja da baya.Tace“Me ka ce?”
“Na ce eh nine na shirya mutuwarsa.”
“Kai ne ka shirya mutuwar Jameelu?”
“Na shirya abin da ya kai ga mutuwarsa kuma ya mutun.”ya bata amsa
Aisha ta fara kuka, amma wannan karon kukan bai fito da ƙarfi ba. Kamar zuciyarta ta gaji da kuka, ta bar mata kawai hawaye masu gudana ba tare da katsewa ba.
“Me ya sa?” ta tambaya. “Me ya sa ka yi haka? Me ya sa ka kashe mutum da bai yi maka komai ba?”
Moneer ya kalleta ba tare da nuna nadama ba.Yace
“Saboda shi ne yake tsakanina da ke.”
Aisha ta kalli fuskarsa cikin mamaki.Tace
“Saboda ni ka kashe mijina?”
“ƙwarai Saboda ke na yi duk abin da na yi.Sabida ina sonki aisha”cewar moneer
Aisha ta girgiza kai, hawaye suka ƙara zuba.Daga idanunta tace
“Ba haka soyayya take ba, Moneer. Wannan ba soyayya ba ce. Wannan hauka ne. Wannan zalunci ne.”ta faɗi cikin matsanancin kuka
“Ki kira shi duk abin da kike so.Nide Na san abin da na yi.Soyayyace tasa da kuma ZALLAR SHAAWA da nake miki”
“Ka kashe mijina!Sabida ni sannan ka kira hakan da soyayya moneer”
“Na sani, Aisha,dama nasan hauka zaki kira hakan amma ni agurina soyayyane!”
Muryar Moneer ta tashi a karon farko cikin daka tsawa yay maganar,da har Aisha ta firgita ta matse Amna a jikinta.
Moneer ya tashi a hankali daga kan kujera.Yana faɗi
“Kin yi tunanin komai zai tafi yadda kike so ne? Kin yi tunanin zan zauna ina kallon ki kina rayuwa da wani mutum, bayan na san cewa tun kafin ki auri Jameelu ina son ki?”
Aisha ta ɗaga takardar.Hannunta ta“Wannan kenan Wannance soyayyar da kake magana akai?”
“Wannan takarda kuskurene da ke kika yi.”ya bata amsa
“Ni?”
“Eh, ke.”
Aisha ta yi masa kallon rashin fahimta.
Moneer ya fara magana cikin sanyin murya, amma kalmominsa suna da nauyi yace.
“Ay de kinsan Kin sa hannu a takardar?.”
“Ban san abin da nake sa hannu a kai ba!”ta bashi amsa
“Amma kin sa hannun ay?”
“Saboda na amince da kai!Ne nasa”
“Shi ne matsalarki.Aisha yarda dani da kikayi shine matsalarki!”ya faɗi cikin ɗaga murya
Aisha ta yi shiru.Moneer ya matso kaɗan, sannan ya tsaya nesa da ita.
“Kin amince da ni lokacin da na ce Jameelu yana buƙatar aiki. Kin amince da ni lokacin da na ce ba sai kun biya komai ba. Kin amince da ni lokacin da na ba ki takarda kika sa hannu ba tare da kin karanta ta ba.Ba tare da kin tuno bayaba kin ƙi amincewa na aureki sabida jameelu, Yanzu kuma kina son ki dawo ki ce komai laifina ne?”
“Saboda kai ne likita! Na ɗauka kana son ceton rayuwarsane!”ta faɗi cikin kuka
“Wannan shi ne abin da kika zaɓa kuma dole ki yarda da shi.”
Aisha ta kasa magana.Moneer ya ɗan yi murmushi.Yace
“Kin sani abin da ya fi bani mamaki?”
Aisha ba ta amsa ba.Yaci gaba da cewa
“yanzu kina tunanin za ki iya ɗaukar wannan takarda ki fita da ita ko?.”
Aisha ta kalli takardar da ke hannunta.
Moneer ya ci gaba da cewa, “Kin manta cewa ba takardar ce kawai kike riƙe da ita ba. Kina riƙe da wani abu ne da zai iya lalata rayuwarki.”
Aisha ta ɗago kai.Tace“Me kake nufi?”
“Na san yadda za a fassara takardar nan. Na san yadda za a ce kin sa hannu da cikakkiyar fahimta. Na san yadda za a ce kina tare da ni a duk abin da ya faru. Kuma idan aka fara bincike, ba za su fara tambayar ni kaɗai ba kece mutum ta farko da zaa tambaya,.”
Aisha ta kalli fuskarsa.Tace“kan me Za su tambaye ni ni me nayi.Tabbas nasan Za su ce na sa hannu.“Za su ce na amince.Nasan Za su iya cewa haka.Amma kuma ay kai ne ka yaudare ni.”cewar aisha cikin kuka
Moneer ya ɗaga kafadarsa.Yace
“Wannan ita ce maganarki?,to Amma idan babu wanda ya yarda da ita fa?”
Take yanke Aisha ta ji jikinta ya sake yin sanyi.
Moneer ya ci gaba, “Kin zo wurina a lokacin da mijinki yake cikin matsala. Kin sa hannu a takarda. Kin kasance tare da shi kafin mutuwarsa. Kin amince da aikin. Kuma bayan mutuwarsa, kin bar komai ya tafi cikin gaggawa saboda kin shiga cikin tashin hankali shiyasa shaida ko alama babu da zata nuna cewa nine na shirya komai sabida zuwa yanzu asa tuni jameelu ya ruɓe acikin ƙasa.”
“Ka daina faɗin haka moneer!”
“Me zan daina?”
“Ka daina juya laifinka a kaina!”
Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, “Ba ni nake juya komai ba, Aisha. Ina nuna miki yadda duniya take ne.”
Ta matse takardar ta ɗago ta dubeshi tace ba tare da tsoroba..