39-40
Ta sake kallon takardar Hawayenta suka sake zubo mata.
“Na yi alkawari...” ta furta cikin raɗaɗi, tana kallon hoton Jameelu da ke saman teburin, “ba zan bari mutuwarka ta zama sirri ba.Se nasa tayi tsawa,dole se duniya tasan me aka maka mijina,koda hakan na nufin kawo ƙarshen tawa rayuwarne”
kafin ta ci gaba da tunanin abin da za ta yi, wayarta da ta bari a gefen gado ta fara ringing.
Ta ɗaga ta kalli screen ɗin.Wani kira ne da ba ta zata ba dan batasan numbarba.
Hakanne ya sa zuciyarta ta sake bugawa da ƙarfi.A tsorace Aisha ta kalli Amna, sannan ta kalli ƙofar ɗakinta.
Ta san daga wannan daren, rayuwarta ba za ta sake zama irin yadda take ba.Abaya dan tayi ƙudirin fallasa gaskiya ko zata mutu.
Da sauri Ta ɗora Amna a kan gadon, ta gyara mata zanin jikinta, sannan ta zauna a gefen gadon tana kallon fuskarta, wadda take cikin nutsuwa dan ba ta san cewa mahaifiyarta ta gano wani babban sirri da ya shafi mutuwar mahaifinta ba.
Kiran wayarne ya katse tana ƙoƙarin ɗagawa hakanne yasa ta tafi tunanin Jameelu, ta tuna ranar da aka kawo sa asibiti, yadda ta tsaya tana roƙon Allah ya ba shi lafiya, yadda Moneer ya bayyana a gabanta a matsayin mutumin da zai ceci rayuwar mijinta, da kuma yadda ta sanya hannu a takardar saboda cikakken amincewar da ta yi da shi, ba tare da ta taɓa tunanin cewa wata rana za ta gano cewa wannan sa hannun nata zai zama abin da Moneer zai juya ya yi amfani da shi a kanta ba.
Ta ɗora hannunta a kan bakinta tana kuka.Tace“Na amince da kai ne saboda na ɗauke ka likita mai ceton rayuka...ban san cewa zan ba ka damar lalata rayuwata bane da kawo ƙarshen rayuwar mijina.”
A lokacin ne wayarta da ke saman teburin ta sake ringing.
Aisha ta ɗago kai da sauri.
Ta tsaya.Tana kallon wayar Kiran ya ci gaba.
Ɗaya daga cikin hannayenta ta kai kan kirjinta, domin bugun zuciyarta ya ƙara sauri, sannan ta kalli ƙofar ɗakin kamar tana tunanin ko Moneer ne ya kira daga ɓangarensa.
Wayar ta sake ringing.Ta tashi a hankali ta nufi teburin.Ta ɗauki wayar.
Amma kafin ta amsa, ta kalli numbar da ke saman screen ɗin.Aisha ta kasa ɗaga wayar.
Ta kalli Amna, sannan ta kalli ƙofar ɗakin.
A zuciyarta ta fara tambayar kanta: Shin wani ne ya gano abin da ya faru? Shin akwai wanda ya san gaskiyar mutuwar Jameelu? Ko kuwa Moneer ne ya riga ya fara ɗaukar wani matakin ban saniba,inba hakaba waye ke kirana ina yasamu numbata?
Wayar ta yi ringing na huɗu.Aisha ta haɗiye yawu.Daga ƙarshe ta danna answer.Ta ɗora wayar a kunnenta.
“Hello...?”Babu amsa.
Aisha ta sake cewa, “Hello, wa ke magana?”
Sai aka yi shiru na ƴan daƙiƙu, shiru mai nauyi wanda ya sa ta fara jin kamar mai kiran yana sauraron numfashinta ne kawai.
“Hello?”
Sai wata murya ta fito a ɗayan ɓangaren.
Muryar namijice, amma ba tare da sauriba, kuma bai yi magana da ƙarfi ba yace.
“Aisha...”
Jikinta ya yi sanyi.Sosai Taso tasan wannan murya.Saidai ta kasa tuno inda tasanta.
Muryar ta sake cewa, “Kada ki kashe wayar.”
Aisha ta zauna a hankali a gefen gado.
“Wa ke magana?”
“Kin karanta takardar?”
Hannunta ya fara rawa.
Ta kalli takardar da ke saman teburin sannan tace.
“Me ya sa kake tambaya?”
“Saboda nasan idan kin karanta ta, to yanzu kin san cewa mutuwar Jameelu ba ta kasance kamar yadda aka gaya miki ba.”
Aisha ta kasa magana.Seda ta nisa sannan tace
“kai to Wa ya gaya maka?”
Muryar ta yi shiru na ɗan lokaci.Daga nan aka ce mata:
“Ba lokacin tambayoyi ba ne yanzu. Lokacin da za ki saurara ne.”
Aisha ta kalli ƙofar.Ɗakin tanajin kamar motsin mutum awajen ta maida hankalinta kan wayar tace
“Me kake so daga gare ni?”
“Abu guda.”
“Menene shi?”
“Kada ki sake ki gaya wa Moneer cewa na kira ki ko ki bari ya gane hakan.”
Zuciyar Aisha ta buga da ƙarfi.Ta yi shiru.
“Kin ji ni?”
“Eh...”
“Kuma kada ki gaya wa kowa cewa kina da wannan takardar.”
isha ta ɗago idanunta zuwa kan takardar.
“Amma ay kai ka san da ita.”
“Saboda ba ke kaɗai ce kika taɓa ganin irin wannan takarda ba.”ya bata amsa
Ta rufe bakinta da hannu.A tsorace tace
“Me kake nufi?”
“Zan gaya miki duk abin da ya kamata ki sani, amma ba a waya ba.”
Aisha ta ji wani irin tsoro ya mamaye ta.Tace
“Yaushe?”
“Gobe.”
“a ina kenanfa?”
Muryar ta yi shiru.Zuwa can Sai aka ce:
“Ki je bayan wurin da kika fara zama da Jameelu bayan kun bar gidan haya,wannan kangon.”
Aisha ta yi mamaki.Tace
“Me ya sa sai nan?”
“Saboda a can ne za ki fahimci yadda komai ya fara.”
Kafin ta sake tambaya, kiran ya katse.
“Hello? Hello!”
Ta duba wayar.An kashe.
Aisha ta zauna bata motsi, wayar tana hannunta, idanunta kuma suna kan screen ɗin da ya koma babu komai.
wani sauti taji daga wajen ƙofar.Ɗakin nata
Knock... knock...Ana bubbuga ƙofar
Ta firgita.Ta ɗago kai.Tace
“Waye?”
Babu amsa.Sai aka sake kwankwasa ƙofar.
Knock... knock...
Aisha ta matse wayar a hannunta, sannan ta kalli Amna da take kwance tana barci.
A hankali ta ja takardar ta ɓoye a ƙarƙashin wani littafi da ke saman teburin.
“Waye?” ta sake tambaya.
Sai ta ji muryar Moneer daga wajen ƙofar.
“Aisha?”
Zuciyarta ta buga da ƙarfi.
Ta kasa amsawa.
“Aisha, kina ciki?”
Ta kalli ƙofar, sannan ta kalli Amna.
A lokacin ne ta gane cewa Moneer yana tsaye a wajen ƙofarta, bayan mintuna kaɗan da mutumin da ya kira ta ya gaya mata kada ta sanar da shi ya kira ɗin,inda take kyautata zaton yaji wayar da tayin..
Ta ja numfashi a hankali.
“Eh...” ta amsa cikin muryar da take ƙoƙarin ɓoye rawar da ke cikinta. “Ina ciki.”
“Me kike yi?”
Aisha ta kalli takardar da ta ɓoye.
“Babu komai.”
Daga wajen ƙofar aka yi shiru.
Zuwa can Sai Moneer ya sake cewa cikin wata murya mai sanyi:
“Na ji kamar kina magana da wani.”
Aisha ta daskare.Hannunta ya fara rawa.
“Waye kika kira?”moneer ya buƙata
“Ba kowa.”ta bashi amsa
“Ko kuwa wani ne ya kira ki?”Aisha ta kasa magana.
A wajen ƙofar Moneer ya sake yin shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce:
“Ki buɗe ƙofar.”
Aisha ta kalli Amna.Ta kalli takardar.Ta kalli wayar.Sannan ta kalli ƙofar.
A cikin dare guda, ta gano gaskiyar mutuwar mijinta, ta samu wani mutum da ya ce zai bayyana mata ƙarin sirrin da ke bayan wannan mutuwa, kuma yanzu Moneer yana tsaye a bayan ƙofarta yana neman sanin wanda ya kira ta.
Ta fahimci abu guda.Lalai Wannan daren ba zai ƙare lafiya ba dole se wani abu ya faru da ita.
Moneer ya fara buga ƙofar da ƙarfi, bugun farko ya sa Aisha ta yi tsalle kamar an jefar da wuta a jikinta, yayin da bugun na biyu ya sa ƙofar ta girgiza, daga nan kuma ta ji muryarsa tana ƙara tashi, ba kamar mutumin da yake son shiga ɗaki kawai ba, sai dai kamar wanda ya fahimci cewa akwai wani abu da aka ɓoye masa kuma yana neman ya gano shi kafin lokaci ya ƙure.
“Aisha! Buɗe ƙofar nan!”
Ta rike bakinta da hannu, tana ƙoƙarin hana kukan da ke son kufce mata, domin a lokacin ne ta fahimci cewa Moneer ya ji wani ɓangare daga cikin maganar da ta yi a waya, kuma idan ya fahimci cewa akwai wani mutum da ya san sirrin da ta gano, to babu abin da zai hana shi ɗaukar matakin da zai sa ta kasa kai wannan gaskiyar ga kowa.
Bugun ƙofar ya sake ƙara ƙarfi.
“Aisha!”