ZALLAR SHA'AWA...

41-42 Akwai Allah

by @zahrasurbajo

Ta ruga cikin ɗakin baccinsu, ta ɗauki wayarta da hannayenta dake rawa, ta kunna kyamarar bidiyo, sannan ta fara magana cikin sauri, numfashinta yana katsewa saboda tsoro.

“Sunana Aisha... idan wani ya samu wannan bidiyon, ina so ya san cewa duk abin da ya faru da mijina Jameelu ba yadda aka faɗa ba ne. Moneer... Moneer ne ya shiga cikin abin da ya faru da shi. Na samu wata takarda da ta nuna cewa an shirya wani abu da ya shafi ƙodar Jameelu, kuma na sa hannu a kanta ba tare da sanin abin da ta ƙunsa ba. Yanzu ya san cewa na gano gaskiya... ya san cewa na yi magana da wani mutum a waya.. .”Ta share hawayen da suka zubo mata, amma kafin ta ci gaba sai aka sake jin wata ƙara daga ƙofar.Ɗakin dan yaji alamun tana magana wanda yake zaton ko wata wayar takeyi

“Buɗe ƙofar mana!”ya faɗi cikin ɗaga murya

Aisha ta kalli Amna wadda take kuka, sannan ta koma kallon kyamarar.Sannan taci gaba da cewa

“Idan wani ya ga wannan bidiyon, ina roƙonsa ya taimaki ɗiyata. Kada a bar ta ita kaɗai. Sunanta Amna... ita ce duk abin da ya rage mini daga Jameelu.”

Ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar zuciyarta ta kasa jure abin da take shirin faɗa sannan tace.

“Ban san ko zan fita daga wannan ɗakin da rai ba.”Hawaye suka zubo mata.
“Amma idan ban fita ba, ku sani cewa na yi ƙoƙarin faɗin gaskiyane. Kuma ina roƙon duk wanda ya samu wannan bidiyon kada ya bari a binne gaskiyar mutuwar Jameelu tare da shi.Yanzu haka nima tawa rayuwar tana cikin hatsari domin ga moneer nan abakin ƙofata yana ƙoƙarin ɓallata,wanda bansan me zeyiminba,kamar yadda kuke iya jiyo muryarsa”ta faɗi gamida kashe recording ɗin.

Sai kuma ta tsaya tana kallon wayar, zuciyarta tana gaya mata cewa wannan na iya zama abu na ƙarshe da ta taɓa yi a rayuwarta.Amma sai wani tunani ya faɗo mata.Ta buɗe wani ƙaramin kwaɗon sarƙar wuyanta, ta cire ƙaramin memory ɗin da ke cikin wayarta, sannan ta riƙe shi na ɗan lokaci tana kallonsa, kamar tana kallon duk wata shaida da ta rage mata. A hankali ta sanya shi cikin kwaɗon sarƙar, ta rufe shi, sannan ta ɗaura sarƙar a wuyan Amna.

Ta sumbaci goshin jaririyar.

“Ke ce abin da ya rage mini, Amna.”Ta rungume ta.Tace cikin kuka“Allah ya kare ki.”

Daga waje sai ta ji ƙarar ƙofar tana girgiza.Alamun ya kusa buɗeta

Aisha ta ɗauki wayarta da sauri ta rubuta saƙon ga lambar mutumin da ya kira ta.

“Ba lallai gobe in samu damar zuwa inda ka ce ba, amma idan har taimakona za ka yi, ina so ka taimaki rayuwar ƴata, domin tawa rayuwar ta zo ƙarshe.”

Ta aika.Masa hawaye na biyo danunta
Nan take ta ɗauki lambar mutumin yayarta dake sudan mariya ta tura mata, sannan ta rubuta:

“Idan kina neman Amna, ki kira wannan lambar. Shi ne mutumin da na damƙa amanarta a hannunsa.”

 ta tsaya.Iya haka dan Ba ta son ƙara mata tsoro.Ba ta son rubuta mata abin da yake faruwa.Don haka ta ƙara da cewa:
“Ki kula da ita sosai bissalam.”Ta aika saƙon.Tana ganin ya shiga Sai ta cire SIM ɗin wayarta, ta tauna shi, sannan ta jefar da wayar a bango ta fashe.

A daidai wannan lokacin ƙofar ta buɗe da ƙarfi.Moneer ya bayyana a bakin ƙofar yana haki.

Aisha ta juya.Ba tare da tsoron komaiba Idanunsu suka haɗu.
Ya tsaya yana kallonta, fuskarsa ta canza gaba ɗaya saboda ya fahimci cewa abin da ya ji a wayar ba magana ce marar muhimmanci ba.

“Wa kika kira?”

Aisha ba ta amsa ba.

“Na tambaye ki, wa kika kira?”

Ta rungume Amna.Moneer ya matso.

“Me kika gaya masa?”

Aisha ta yi shiru.
“Me kika gaya masa, Aisha?”

Ta kalli Moneer cikin hawaye.Tace

“Gaskiya,na faɗa masa.”ta bashi amsa

Fuskarsa ta sauya yace

“Wacce gaskiyar?”

“Wadda ka yi ƙoƙarin binne ta.”

Moneer ya fusata, ya matsa zuwa gare ta cikin hanzari, yayin da Aisha ta ja da baya tana ƙoƙarin kare Amna.

“Ka bar ni! Moneer ka fita rayuwā”yasa hannu ya shaƙota Kuka da ihun Amna ne suka cika ɗakin.
Aisha ta yi ƙoƙarin neman hanyar tserewa, amma Moneer ya hana ta.
“Kin yi kuskure,” ya faɗa cikin muryar da ta razanata. “Na gargade ki.Bakijiba”

“Ka bar mu!Moneer kabarmu da baƙincikin daka ƙunsa mana”Amma bai saurare ta ba.
Ya maketa ta faɗa kan gadon amna ta faɗa can ƙasa tana kuka kamar zata shiɗe,aisha na ƙoƙarin miƙewa moneer ya bita ya danne ya ɗauki filo,ya danne mata kanta cikin rashin imani yana kallon yadda take buge buge har ta dena rai yayi halinsa domin itama ya kasheta.

Moneer ya tsaya cak.Ya kalli gawar Aisha.Daga nan idanunsa suka sauka kan Amna wadda take kuka a gefe.
Fuskarsa ta nuna firgici na ɗan lokaci, domin a wannan lokacin ne ya fahimci cewa abin da ya aikata ya wuce duk wani matakin da zai iya komawa baya.

Sai ya juya ya kalli ƙofar.Ya saurari motsin gidan.Babu wanda ya zo.Babu wanda ya san abin da ya faru.Ya kalli Amna wadda har yanzu take kuka.Wacce da yay niyyar kasheta sai kuma ya fasa dan yanaso mutuwar aisha ta tashi a mutuwa kawai ba kisan kai ba.
 ya ɗauki wasu abubuwa daga cikin ɗakin, yana ƙoƙarin fahimtar abin da zai yi gaba.Be bar kowacce shedaba da zata iya tona masa asiri,a iya tunaninsa,Amma bai san cewa kafin komai ya faruba, Aisha ta riga ta bar wata shaida a duniya.

Bidiyon.Kuma mafi muhimmanci...sirrin da ke cikin sarƙar wuyan Amna.

Ya juya da sauri ya wuce ɓangarensa ba tare da tunanin abinda ze biyo bayaba,dan zatonshi,aisha bata kai ga faɗawa kowaba tunda yasan bata da kowa ay a garin shiyasa be damu da son sanin da wanda tai wayaba.