43-44
Bayan Moneer ya bar ɓangaren Aisha, gidan ya sake komawa cikin wani irin shiru mai ban tsoro, sai dai kukan Amna ne kaɗai ya kasance yana yanke wannan shirun, kukan da yake ƙara tashi lokaci zuwa lokaci kamar jaririyar tana neman mahaifiyarta,. A cikin wannan lokacin ne kukan nata ya fara shiga kunnen mai gadi, wanda yake can cikin ɗakinsa yana cikin wani nannauyan bacci, har sai da ya farka gaba ɗaya saboda yadda kukan ya ci gaba ba tare da yankewa ba.
Ya zauna a kan gadonsa yana sauraro.
“Amna ce take kuka haka?” ya furta cikin mamaki.
Da farko ya yi tunanin wataƙila Aisha tana tare da ita kuma za ta iya kwantar mata da hankali, amma da ya fahimci cewa kukan bai daina ba, sai ya tashi ya saka rigarsa ya fito daga ɗakinsa.
Ya nufi ɓangaren Aisha.
Da ya isa ƙofar, sai ya ƙwanƙwasa.
“Aisha?”
Babu amsa.Ya sake ƙwanƙwasawa.
“Aisha, lafiya kuwa? Amna take kuka haka?”
Shiru.
Kukan Amna kawai yake ƙara bayyana.
Mai gadin ya ɗan karkata kansa yana saurare, sannan ya sake ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi.
“ Aisha?”Har yanzu babu amsa.Wani irin fargabane ya fara shiga zuciyarsa.
“Kai daga dukkan alamu Wataƙila ba lafiya ba,” ya furta a hankali.Ya juya ya koma wajen Moneer.Da ya isa ɓangarensa sai ya fara bubbuga ƙofar.
“Doctor!”
Bayan ɗan lokaci Moneer ya fito, kamar mutumin da yake cikin bacci mai zurfi, zuciyarshi cike da tunanin in kiran da me gadin ke masa nada alaƙa da tonuwar asirinsa t shima hallakashi zaiyi, amma da ya ga mai gadin a gabansa sai ya daidaita fuskarsa tunda bega alamun zargiba afuskar megadin..
“Me ya faru?”
“Doctor, ina jin akwai abin da ba lafiya ba a wajen Aisha.”cewar megadin
Moneer ya yi kamar bai fahimta ba.Yace“Me ya faru da ita?”
“Amna ce take ta kuka sosai, na je na ƙwanƙwasa ƙofar amma Aisha ba ta amsa ba. Na sake kira, amma shiru.”
Moneer ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, “Amna take ta kuka kuma?”
“Eh, doctor.”
“Wataƙila Aisha ta yi barcine shine yasa.”cewar moneer
“Amma kukan jaririyar ya yi yawa, kuma har yanzu gashi can kana iya jiyota ba ta daina ba.”
Moneer ya ɗaga kansa yana kallon mai gadin, zuciyarsa kuwa tana bugawa saboda ya san ainihin abin da ya faru, amma sai ya nuna damuwa kamar shi ma yanzu ne yake jin labarin.
“Mu je to mu gani.”Suka nufi ɓangaren Aisha tare.Moneer yana gaba, mai gadi a bayansa.
Koda suka shiga ɗakin, Amna tana kwance a gefen aisha akan gadon tana ta kuka, yayin da Aisha take kwance a kan gadon kamar wadda ta yi barci mai nauyi.
Mai gadin ya tsaya.Aruɗe yace
“Subhanallah...”ganin yadda amnar ke ksa da ashar take wannan kukan amma bata jitaba
Da sauri Ya ƙarasa wajen gadon.
“ Aisha?”ya kira sunanta amma Babu amsa.Ya kalli Moneer.
“Doctor...”
Moneer ya matso, ya kalli Aisha na ɗan lokaci, sannan ya zauna kusa da ita kamar wanda bai yarda da abin da yake gani ba.
“Aisha?”ya kira sunanta yana kamo hannunta
Shiru.Bata amsaba,Mai gadine ya fara firgita.
“Doctor, ko lafiya?”
Moneer ya ɗora hannu kusa da ita, sannan ya yi shiru na ɗan lokaci.Daga ƙarshe sai ya sauke kansa.
“Ta mutu.”ya furta a hankai wasu hawaye na biyo idanunsa
“Me?”cewar me gadin agigice
Mai gadin ya ja da baya kamar an ture shi yace“Ta mutu fa kace doctort?”
Moneer ya kalli fuskarta, sannan ya sauke numfashi mai nauyi yace muryarshi na rawa.
“Eh ta mutu.”
A nan ne kuka ya fashe wa mai gadin.
Yana faɗin “Ya Allah! Aisha!”Ya kama kansa, yana kallon matar da har zuwa jiya da yamma sunyi magana da shi cikin nutsuwa, , amma yanzu wai ga ta kwance babu motsi ta mutu.