ZALLAR SHA'AWA...

45-46

by @zahrasurbajo

Moneer ma  kukan yakeyi yana faɗin“Allah ya jikanki, Aisha...”Mai gadin ya dube shi yana kuka.

“Doctor, mutuwar nan ta girgiza ni wallahi. Jiya ma fa na gan ta lafiya.”

Moneer ya share fuskarsa yace.
“Ni ma hakane naji mutuwarnan sabida ban san abin da ya same ta ba.”

Amma a zuciyarsa ya san komai.Kuma abin da ya fi tsoratar da shi ba mutuwar Aisha ba ce.
Abin da ya fi tsoratar da shi shi ne sirrin da ya sani bai mutu tare da ita ba dan se alokacinne idanunsa suka sauka kan fasasshiyar wayar aisha wanda yasan bashine ya fasataba,tabbas akwai abinda aisha tayi kamin shigowarshi ɗakin ya kasheta.
*********
Da gari ya waye, bayan an yi sallar asuba, mai gadin ya sanar da mutuwar Aisha a masallacin da ke kusa da gidan, labarin ya bazu cikin unguwa cikin ɗan lokaci, mutane suka fara zuwa gidan Moneer domin yi wa marigayiyar sallama da kuma taimakawa wajen shirye-shiryen jana'izarta.

Tsofaffin mata biyu suka zo domin yi mata wankan gawa, suka shiga ɗakin cikin tausayi da hawaye, suka yi abin da ya kamata, sannan suka shirya Aisha cikin likkafani.
Mazan suka ɗaukota suka fito da ita waje akai mata sallah

Amna kuwa aka bar ta a hannun tsofaffin matan bayan sun gama, domin babu wanda wanda ya kamata a damƙawa ita sai su ɗin.

Moneer da mai gadin da wasu daga cikin mutanen unguwa suka wuce da gawar zuwa maƙabarta.

A lokacin da suke wuce can, ɗinne wata baƙar mota ta tsaya a ƙofar  gidan.Wani mutum ya fito daga cikinta fuskarsa ɓoye cikin facemarks.Bai shiga gidan da kansa ba.Ya kalli wani yaro da yake wasa kusa da wurin sannan ya ce masa, “Je ka cikin gisannan ka ce su kawo Amna. Moneer ne ya aiko ka, sun dawo daga maƙabarta.”

Yaron ba musu ya shige cikin  gidan.Ya sami tsofaffin matan zaune tare da Amna, sun gaji da kuka da take musu se rarrashinta suke taƙi shuru
Sallamar yaronce tasa suka ɗago suna amsawa.Sannan yace“ance wai Ku ba ni Amna,Inji Moneer ya aiko ni.”

Matan suka kalli juna.Sukace

“oh shi Ya aiko ka?”

“Eh.”ya basu amsa
Ba su ga dalilin shakka ba, domin tun farko Moneer ne yake kula da Aisha da Amna, kuma yanzu da suka dawo daga maƙabarta suna iya tunanin yana son a kawo masa jaririyar.Ya ganta Saboda hakane suka damƙa masa Amna.

Yaron ya ɗauke ta ya fita  yana isa wajen baƙar motar, mutumin ya karɓe ta daga hannunsa.“Na gode,” ya ce.Ya shiga motar.Ya kunna Motar ta tashi.Ta bar ƙofar gidan cikin sauri.

Ba a jima ba sai ga Moneer da sauran mutanen sun dawo daga maƙabarta.Fuskarsa cike da baƙin ciki, yana kuka yana nuna kamar mutuwar Aisha ta ratsa shi sosai.Sallamar kowa yayi inda ya shaida musu ba zaman makoki ayko kowa ya watse

Tsofaffin matan ne suka fito daga gidan.Moneer ya kalle su.Yace“Amna tana ina?”
Matan suka yi shiru.Suna kallonshi cike da mamaki
“Amna kuma?”
Daya daga cikinsu ta ce, “Ai an zo an ɗauke ta.”

Moneer ya tsaya cak yana kallonsu yace.
“Waye  ya ɗauke ta?”
“Wani yaro.”

“Wane yaron?”

“Ya ce kai ne ka aiko shi.Mu kuma muka bashi ”

Jinin da ke gudana a jikin Moneer ne yaji kamar ya tsaya.

“Ni yace muku?”cewar moneer

“Eh, ya ce kai ka aiko shi.”

Moneer ya kalli mai gadin.Mai gadin ma yana kallonsa cikin mamaki.Yace“Doctor, ni ban san komai ba.tunda muna tare acan maƙabarta ay”

Moneer bai amsa ba.Zufa ta fara keto masa a goshinsa.Ya sallami matan suka wuce
Sai A wannan lokacin ne tsoro na gaskiya ya fara mamaye shi.

Aisha ta mutu.Amma Amna ta bace.Wannan ba abu ne da zai iya ɗauka da wasa ba.Tabas Wani ya san sirrinsa.
Wani ya san cewa mutuwar Aisha,kasheta akayi kuma  jaririyar ita ce kadai abin da zai iya kai mutum zuwa ga gaskiyar abin da ya faru.

Moneer ya kalli hanyar da motar ta bi dan ga sawuntanan, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi.

“Waye wannan?” ya furta cikin raɗaɗi.

“Waye wannan?Wanda ya san aynihin gaskiyata?”cewar moneer jikinsa na rawa
Mai gadine ya matso.Kusa dashi yace“Doctor, me ya faru?”

Moneer ya juya ya kalle shi.Yace“Babu komai.”Amma wannan karon muryarsa ba ta da ƙarfi.
Bayan wasu mintuna  ya ja mai gadin gefe yace.
“Na yi shawarar zan bar maka wannan gidan.”
Mai gadin ya yi mamaki yace atsorace.

“Ni kuma?”

“Eh. Gidan nan da duk abin da ke ciki naka ne.Yanzu na baka duniya da lahira”

“Amma to Doctor, me ya sa da gaggawa haka?”cewar megadin.

“Zan tafi Sudan.Ne shine yasa”

“Sudan kuma?Na ɗauka neman amna zamu tafi?”cewar megadin

“Eh. Zan je wurin dangin Aisha. Bayan abin da ya faru, ba zan iya ci gaba da zama a nan ba.Amna kuma nasan inda zan sameta”
Shi dai Mai gadin ya yi shiru, har yanzu bai fahimci dalilin da ya sa moneer yake yin wannan gaggawar ba.

Moneer juyawa yayi  ya shiga cikin ɓangaren nasa ya tattara kayansa, ya ɗauki duk wani abu da yake ganin zai buƙaci tafiya da shi, ya saka cikin mota, sannan ya dawo ya yi wa mai gadin sallama.

“Ka kula da gidan.Baba Allah ƙaddara saduwa”

“Allah ya kiyaye, doctor.”cewar megadin jikinshi a sanyaye

“Idan wani ya tambaye ka, ka ce na tafi Sudan ne.”cewar moneer yana yiwa motar key

“Amma doctor...”

Moneer bai tsaya ba.Dan yasan cifaba da zamansa agidan tamkar jefa rayuwarshi cikin haɗarine sabida Amna ta bace.Kuma duk wanda ya ɗauke ta ya san ainihin abinda ya faru
A gefe guda kuwa, a cikin baƙar motar data ɗauki amna , mutumin ya kalli jaririyar da take kuka a kujerar baya.

Ya ɗora hannu a kan akwatin da ke gefenta, sannan ya yi murmushi ƙarfin hali yace .
“Ki yi haƙuri, Amna,” yaci gaba da  furtawa cikin sanyin murya. “Mahaifiyarki ta bar mana aiki mai girma wanda ko ba daɗe ko ba  jima sai mun kammalashi,jinin iyayenki baze tafi abanzaba wannan alƙawarine,zan reneki amna,zan maidake zakanya sannan in sakeki acikin jeji ki fita farauta,na rantse da buwayin daya busa min numfashi sena cika alƙawarina"cewar  mutumin gamida ƙarawa motar gudu suka cilla kan titi.
Tirƙashi,!
Waye wannan daya ɗauki amna?
Me zeyiwa moneer,taya yasan sirrin mutuwar jameelu,?
Taya asirin moneer ze tonu,in tonun me ze biyo baya,?
*da gaskene wannan mutumin yana maida amna zakanya kamar yadda yay alƙawari cewa ze saketa a jeji ta shiga farauta,?,in har hakan ta kasance to menene abinda amna zata fara hari in har da gaske ta zama zakanyar*
Wainnan amsoshi dama sauran wasu se. Wanda ya cigaba da bine zesani

Nagode