08
by @oumfatima33
*MEERAH*
*OUM FATIMA*
*08*
Muna isa airport aka yi mana masauki a VIP, zaman mimtuna 10 muka yi aka sanar da saukar jirgin da Dady ke ciki. Cike da farin ciki na miƙe don nayi matuƙar kewar Dady, sati uku kenan rabon dana gansa.
"Allah na matsu naga Dady, ji nake kamar na fita ta taro sa a bakin jirgin Momy!." Na faɗa cike da murna ina kwantar da kai na a saman cinyar Momy dake zaune saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun Couches ɗin da aka ƙawata waiting room ɗin da aka sauke mu.
Murmushi Momy tayi tana shafa kaina tace.
"Kwantar da hankalinki Auta yanzu zaki gan sa in sha Allah, ba ma sai kin je bakin jirgi ba." Gaba ɗaya dariya su Ya Sultan dake jin mu suka yi, in ka ɗauke miskilin da kansa ke ƙasa yana faman daƙilar waya tamkar baya wurin.
Ya Aryan ne ya harare ni yace.
"Ita fa yarinyar nan ji take kamar tafi kowa yin kewar Dady a gidan nan, sai kace Dadyn nata ne ita kaɗai." Ɗagowa nayi na kalle sa ina ɓata rai nace.
"Eh mana nafi kowa yin kewar Dady a gidan nan, ko ba haka ba Ya Sultan?." Na ƙare maganar da juyawa na zuba wa Ya Sultan ido cike da rigima, ina don dole sai ya goya min baya.
"Haka ne kam, da gaskiyar ki Meerah." Yaya Sultan ya bani amsa. Murmushi na saki na juya zan yi wa Ya Aryan gwalo securities ɗin da ke bakin ƙofa suka sanar da shigowar Honorable Abbas Mamman Gwangwazo.
Duk miƙewa muka yi cike da farin ciki muna son ganin Dady, ɗaya daga cikin securities ɗinsa ne yayi nocking kafin ya buɗe ƙofar. Kyakykyawan dattijo mai cikar zati da kamala ne ya bayyana a gaban mu.
Ai da gudu na kwasa na nufi inda yake, ina zuwa kuma na shige cikin jikinsa na ƙan-ƙame sa ina faɗin.
"Oyoyo Dadyna, I miss you!." Na faɗa cikin tsananin murna.
"Oyoyo Manana, I miss you more." Dady ya faɗa cike da matsanancin farin cikin ganin ƴar tasa da yake tsananin so da ƙauna.
Ƙarasowar su Ya Sultan suna masa sannu da zuwa ya katse ni daga maganar dana yi niyyar yi.
"Barka da zuwa Dady." Ajmal ya faɗa fuskarsa ɗauke da kyakykyawan murmushin da ake jimawa ba'a gani a fuskarsa ba. Cike da farin cikin shima Dady ya bashi hannu suka yi musabiha yana faɗin.
"Yauwa My Son, fatan na same ku lafiya." Ya faɗa da kulawa sosai, saboda akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsa da yaron.
"Alhamdulillah Dady." Ya bashi amsa sannan ya matsa ya bawa su Ya Sultan wuri suka ƙaraso suma duk suka rungume Dadyn da yi masa sannu da zuwa. Suma duk hannu ya basu suka yi musabiha sannan ya juya ga Momy dake tsaye a gefe tana murmushi.
Hannu ya buɗe mata alamar tazo ya rungume ta ita ma. Murmushi ta saki tana nun masa yara da ido, murmushin ya mayar mata ya mata alamar shike nan to zasu haɗu a gida. Fuskewa tayi ta gaishe sa haɗi da masa sannu da zuwa. Da kulawa ya amsa mata sannan muka fito don tafiya gida.
****** Koda muka isa gida Dady ɓangarensa ya wuce tare da Momy wacce ta bishi don taimaka masa yayi wanka, bayan ya fito daga wanka ta taimaka masa ya shirya cikin kaya mara sa nauyi. Tare suka fito zuwa table cin abinci, kasancewar babu wanda yaci abinci saboda murnar dawowar tasa.
Lokacin da suka iso Meerah suka samu tana ƙara gyara table ɗin.
"Yauwa Dady yau zaka ci abincin dana girka maka da kai na." Na faɗa cike da murna ina zuwa na kama hannunsa, muka ci gaba da tafiya tare.
"Kice yau zanci abincin da Mamana ta girka min?." Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Yes Dady, it's your favorite." Na faɗa ina ja masa kujera ya zauna.
"Thank you daughter, Allah ya miki albarka." Ya faɗa yana zama, zama nayi nima a kujerar dake kusa da shi, dai-dai lokacin Ya Aryan da Ya Jawad suka shigo. Suna zama Ya Sultan da Ajmal suka shigo suma.
Cike da farin ciki nayi serving Dady sakwara da miyar hanta da nayi masa da taimakon Momy. Momy dake zaune tana kallon ƴar tata ta amshe mata aikin kula da Mijinta. Don haka ita sai ta miƙe ta fara serving yaranta, don ba zata iya da rigimar Meerah ba.
Koda ta tambayi Ya Ajmal abinda zai ci, shima sakwaran yace a zuba masa, cike da farin ciki muka ci abincin ina ta yiwa Dady hira. Sosai ya yaba da abincin dana girka, har kyauta yace zai yi min.
Ai kuwa sosai farin ciki ya kama ni na kasa rufe baki na sai faman murmushi nake yi.
Bayan kammala cin abincin Palo muka dawo muka zauna da Dady yana yiwa su Ya Ajmal maganar tafiyar da zasu yi London ƙaro karatu.
"An riga an kammala komai sai ku fara shirin wucewa kawai." Dady ya faɗa. Godiya suka yi masa ya juyo gare ni yace.
"Mamana kema an kammala maki komai na komawa SS ɗinki."
"Thank you Dady." Na faɗa ina jin daɗi zamu shiga Senior section, mun bar layin ƙwailaye. Sallar la'asar da aka kira yasa duk muka miƙe, Mazan suka fita Masallaci ni da Momy kowa ya shige ɗakinsa don yin tasa.
******* Dady yana dawo wa ɓangarensa ya wuce saboda yana da buƙatar huta wa, ni da Ya Aryan kuwa shirin Islamiyya muka yi driver ya kai mu. Ya Sultan zance ya tafi wurin budurwarsa da suke soyayya, koda ya buƙaci Ya Ajmal ya raka sa ce masa yayi.
"Ka san dai babu ni a wannan shirmen zuwa zancen ko?." Cike da mamaki Sultan yake kallonsa, zuwa can yace.
"Don kai baka soyayya shike nan sai aka ce maka shiririta ce?." Ya tambaya yana kallon sa cike da takaici, don manyan Babys ke farautar soyayyar Ajmal ɗin yana yanƙwana su. Ciki kuwa har da ƴanmatan Abuja masu ji da Class.
"To idan ba shirme ba miye, kawai ƙato da kai kaje ka saka ƙaramar yarinya a gaba kana mata ƴar ƙaramar murya da sunan soyayya, shirme kawai." Ajmal ya faɗa yana tsare sa da ido. Dariya Sultan ya sheƙe da ita har da riƙe ciki.
"Allah ya nuna min ranar da Guy ɗin nan zai zare a soyayya, in ga ƙaryar riƙe girma." Ya Sultan ya faɗa yana nuna Ajmal.
Wani miskilin murmushi kawai Ajmal yayi ya kaɗa kai ya shige part ɗinsu ya bar Sultan na bin sa da kallon mamaki.
"Allah ka kawo wacce zata susuta zuciyar ɗan'uwana." Ya Sultan ya faɗa yana bin bayansa, kwance ya same sa saman sofa yana aikin daƙilar waya.
Bai kula sa ba yaje gaban Mirror ya ƙara fesa turare, ya gyra hularsa sannan ya juyo ya kalli Ajmal cike da son ya tsokane sa yace.
"How do I look Man?." Ɗagowa ya yi ya manna masa harara ya mayar da kansa kan abinda yake yi. Cike da son saka shi magana yace.
"To mu dai mun tafi bawa fure ruwa, bishiyoyi kuma sai su koma daji wurin ƴan'uwans...." Da gudu ta ƙara sa fice wa a ɗakin yana dariya saboda pillow case da Ajmal ya ɗauka ya jefa masa.
"Zaka dawo ka same ni ne." Ya faɗa yana yin ƙwaffa sannan yaci gaba da abinda yake yi.
_________★
Washe gari Dady ya bani uwar tsarabar daya kawo min, wacce rabi duk kayan zaƙi ne su chocolate da biscuits da sweet masu tsada. Sai kuma kayan sawa designer's da baya gajiya da sayo min duk ƙasar da yaje.
Sosai nayi farin ciki da tsarabar musanmma ƴar tsanar Labubu daya kawo min, kasancewa ta mai son teddy bears sosai.
Kwanan Dady biyu tare damu sannan suka wuce Abuja tare d Ya Ajmal, don dama jiran Dadyn ya tsayar dashi. Kasancewar yanzu ya koma hannun Mahaifiyarsa kamar yanda take so, don tunda suka tafi karatu can rayuwarsa tafi yawa a can. Sai dai idan sun samu huto suke zuwa Kano, ko kuma weekend.
Yanzu kuma zai je ya kammala shirin wucewar su London ne, wanda Dady ne ya sama musu makarantar kuma ya ɗauki nauyin komai. Yana tafiya naji kamar an raba ni da ƙaya, don haka na buɗe sabon babin taɓara a gidan.
***** Yau saura kwana biyu Birthday partyn ƙawata Zeezee wacce zata cika 16 years, don haka muka yi busy muna ta shirye-shirye. Saboda gaggarunin party muke son yi, wanda wannan partyn shine silar haɗuwa ta da Nawaz wanda ya cece ni daga mummunar ƙaddarar da taso giftawa rayuwata......
Oum Fatima
***