Chapter 2
by @umsar
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsar Arewapen
Wattpad umma mustapha
PAGE 2
Da misalin ƙarfe shida na yamma, Nihla ta shirya komawa gida. Ta kalli Fatima, wadda ta fito daga wanka tana shirin fita.
"Ko za mu tafi tare?"
Fatima ta ce, "Me kike tunani ne? Kina tunanin zan bar ki ki tafi ke kaɗai, ki zauna a wannan yanayin? Har yanzu ban san abin da yake damunki ba, amma duk wanda ya kalli fuskarki zai gane cewa kina cikin damuwa. Kuma alamun sun nuna kamar ba ki da lafiya."
Nihla dai ba ta da amsar da za ta bata. Don haka ta ja baki ta yi shiru, tana jiran ta gama shiryawa domin su tafi tare.
Bayan Fatima ta gama shiryawa, suka ɗauki jakunkunansu da sauran abubuwan da za su buƙata, sannan suka bar hostel ɗin. A ƙafa suka nufi gidan Nihla, domin ba ta son kiran Malam Musa ta katse masa uzurinsa. Gidan da Nihla take zama ba shi da nisa da hostel ɗin, don haka ba su ɗauki lokaci mai tsawo ba suka isa.
A ƙofar get ɗin wani madaidaicin gida suka tsaya. Nihla ta saka hannu cikin aljihun doguwar rigarta, ta ciro mabuɗin gidan, sannan ta buɗe get ɗin.
Gidan yana da ɗan girma. A ciki akwai filin ajiye mota wanda zai iya ɗaukar motoci kusan biyu. An kuma kawata farfajiyar gidan da furanni iri-iri waɗanda suka ƙara wa wurin kyau.
Da an tura ƙaramar ƙofar da ke jikin get ɗin, akwai wani ɗan ƙaramin ɗaki a hannun dama. Daga yadda aka tsara shi, alama ce Dake nuna ɗakin mai gadi ne. Ɗakin a kulle yake, abin da ke nuna cewa babu wanda yake amfani da shi a halin yanzu.
Akwai ƙofofi guda biyu da suka haɗa wajen da cikin gidan. Ƙofar farko tana cikin harabar gidan, tana kallon get. A gabanta akwai matakala guda uku da za a taka kafin a shiga wata ƙaramar baranda da ke gaban kofar shiga falon.
Ƙofar ta biyu kuwa tana can bayan gidan. Idan aka buɗe ta, za ta kai mutum kai tsaye zuwa kitchen, daga nan kuma a gangara zuwa cikin gidan.
Ƙofar da ke harabar gidan suka buɗe, suka shiga cikin babban falon gidan. Falon yana da girma kuma an tsara shi cikin tsari mai kyau. A ciki akwai wurin cin abinci, wato dining area, sannan akwai wata ƙofa da ta haɗa falon da kitchen.
Gidan yana da faluna biyu da ɗakunan kwana guda uku. An kawata falon da kujerun zamani masu kyau, waɗanda suka ƙara masa armashi da kyan gani. Haka ma ɗayan falon yake. Kowanne daga cikin ɗakunan kwanan an shirya shi da kayan ɗaki na zamani masu kyau.
A falon suka zauna suka ɗan huta, yayin da Fatima ta fita domin kunna musu hasken solar, saboda duhun magariba da ya fara gabatowa.
Bayan ta dawo, Fatima ta nufi toilet ɗin da ke cikin falon domin ta ɗaura alwala, yayin da Nihla kuma ta nufi wani ɗan ƙaramin corridor da kai tsaye zai kai ta zuwa ɗayan falon da kuma wani bedroom.
Ta tura ƙofar ɗakin ta shiga.
"Wai, Masha Allah!"
Ɗakin ya haɗu iya haɗuwa. Komai da ke cikinsa an tsara shi cikin tsari na musamman. Da alama wannan shi ne ɗakin maigidan gidan, domin a kusurwar bangon ɗakin ta hango wani babban hoto da aka jingina.
A cikin hoton, Irfan da Nihla ne. Sun yi matuƙar kyau a jikin hoton, sanye suke da kananun kaya Riga da wando.Irfan yana tsaye kusa da Nihla, yayin da Nihla ta yi kwalliyarta cikin sauƙi. Gashinta ya zubo har zuwa bayanta, fuskarta ɗauke da murmushi wanda ya ba dimples ɗin da ke kumatunta damar bayyana. Sun yi kyau sosai a hoton.
Nihla kyakkyawar yarinya ce, kuma Allah ya yi mata halitta mai kyau. Duk inda kake neman black beauty, Nihla ta kai. Kyawunta ya kai a saka ta cikin jerin kyawawan mata.
Haka a ɓangaren Irfan kuwa, shi ɗan shekara talatin da bakwai ne. Yana da ƙuruciya da kyau. Dogo ne, farin tas, fuskarsa ɗauke da sake da saje. Idan ka gan shi, ka ga ƙaƙƙarfan namiji, kuma za ka iya tunanin ya haɗa jini da Fulani.
Ba ta inda Allah ya rage shi. Yana da kyau, ilimi da wayewa.
Nihla ta shiga bandakin da ke cikin ɗakin domin ɗaura alwala. Bayan ta fito, ta shimfiɗa abin sallah, ta kabbara sallar Magariba. Bayan ta idar, ta zauna tana zikiri a zuciyarta, tana fatan za ta samu sassaucin abin da ke damunta a zuciya.
Gyara zamanta ta yi, sannan ta ɗaga hannuwanta sama tana roƙon Allah, tana kai kukanta gare Shi, tana roƙonsa Ya kawo mata ɗauki da mafita a cikin wannan halin da take ciki.
Ta shafa addu'ar, sannan ta matsa gefe ta jingina da jikin gadon. Ta miƙa hannu ta janyo wayarta da ke kan gadon, ta shiga ta fara dube-dube. Amma dai babu wani sabon abu da ya shigo cikin wayar.
Wayar ta jefar gefe, ta yi shiru, sannan ta saka hannu tana dafe kanta. Ciwon kan ne ya takura mata kamar zai rabe gida biyu.
Tana nan a zaune har aka kira sallar Isha. Ta mike ta gabatar da sallar Isha. Bayan idar da sallar ne ta mike tana dafa bango saboda jiri da ke damunta, ta nufi falo.
Fatima ba ta falon. Ta ji motsinta a kitchen, don haka Nihla ta nemi wuri ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ke falon, tana mai jingina bayanta.
Ba ta daɗe da zama ba sai ga Fatima ta fito, hannunta ɗauke da plate da fruit a ciki. Gurinta Fatima ta nufa ta zauna kusa da ita, sannan ta ajiye farantin fruit ɗin a gaban Nihla.
Nihla ta kalle ta ta ce, "Ba na jin zan sha fruit ɗin nan. Taimaka min da tea, don Allah."
Mikewa Fatima ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ta je ta haɗo mata tea mai kauri, sannan ta kawo mata.
Nihla ta karɓa, tana gyara zamanta, sannan ta furta, "Nagode."
Gurin TV Fatima ta koma, tana ƙoƙarin kunna musu kallo ko zai ragewa karawarta damuwar da take cik,i da kuma wannan zaman shirun da suka yi kamar masu zaman makoki.
A hankali Nihla take kurɓar shayin, ba don tana jin daɗinsa ba, sai dai kawai tana jin wata irin yunwa kamar ta shekara ba ta ci abinci ba. Kamar ba dazu ta gama cin abinci ba.
Ta lura yanzu tana da saurin jin yunwa.
TV ɗin da Fatima ta kunna suke kallo, amma hankalinta baya kan TV. Domin idan ka tambaye ta abin da ake yi a TV ɗin, ba za ta iya baka amsa ba, saboda hankalinta baya can.
Suna nan a zaune har ƙarfe tara da rabi na dare. Nihla ta ɗora idanuwanta kan Fatima, wadda take fama da ɗumbin handout da calculator, tana faman karatu.
Nihla ta mike, ta yi mata sallama da cewa sai da safe, domin taga ba ta da niyyar kwanciya, sai ƙara baje takardunta take yi.
Da Fatima ta ɗago ta kalle ta, ta ce, "Da wuri haka za ki kwanta?"
Nihla ta ce, "Ba na jin daɗi ne. Kaina yana min ciwo, zan je na sha magani na kwanta."
"Okay, sai da safe."
Daga haka suka yi sallama.
daman chan akwai ɗakin da Fatima take amfani da shi idan tazo tayata kwana ko Kuma ta gaji da zaman hostel din. A ciki take kwana. Wanda sun barshi a mazaunin dakin Baki.
Bayan wucewar Nihla, Fatima ta bita da Kallo har ta ɓacewa ganinta,
Me yake damun NIHLA ?? Ta tambayi kanta , Amma Bata da amsar tambayar, Ba wai rashin lafiya ne yake damunta ba, damuwa ce. Har ma tana iya cewa damuwar ce ta kawo mata rashin lafiya.
Amma za ta ba ta lokaci ta gani ko za ta fada mata abin da yake damunta, ko kuma za ta ci gaba da ɓoye damuwarta a cikin ranta.
Nihla kuwa tana shiga bedroom ɗinta, ta ɗauko magungunanta, ta ɗauki ruwan roba ta sha. Bayan ta gama shan maganin, ta fara ƙoƙarin cire kayanta.
Tsayawa ta yi a gaban madubi tana kallon kanta. Daga ita sai bra da pants ɗin da ke jikinta. Ta jima a haka tana kallon kanta, sannan ta saka hannu ta taɓa cikinta.
A hankali ta bar gaban madubin, ta nufi wardrobe domin ɗauko kayan bacci.
Hannu ta sa ta buɗe wardrobe ɗin, ta janyo wata rigar bacci mai hannun vest, wadda tsayin rigar bai wuce gwiwa ba.
Sai da ta ƙarasa cire abin da ya rage a jikinta, pants da bra, sannan ta zura rigar.
Tana ƙoƙarin rufe wardrobe ɗin ne idanunta suka sauka kan wata farar takarda. Ta ɗauko takardar cikin sanyi jiki, sannan ta rufe wardrobe ɗin.
Gefen gado ta samu ta zauna, sannan ta buɗe takardar.
Sunan wani private asibiti ne ya bayyana a jikin takardar. Sannan bayanan da ke cikin takardar sun nuna cewa tana ɗauke da ciki na tsawon wata biyu da sati ɗaya.
Shiru ta yi tana tuna ranar da ita da Irfan suka je asibiti domin a duba lafiyarta, sakamakon fama da zazzabin da take yi. Likitan da ya duba ta ya tabbatar musu da cewa tana da ciki na wata biyu da sati daya.
A ranar da suka je asibiti, bayan sun dawo da Magariba, ta ce wa Irfan tana son ta ci awara.
Ya ce mata, "Idan na fita masallaci, zan biya ta wani wuri da na ga suna yin awara mai kyau. Zan siya, na taho miki da ita."
Sai dai tun daga wannan fitowar da ya yi, shi ne fa bai dawo ba. Har yanzu ana kwana uku, ana shirin shiga na huɗu.
Shiru ta yi, hawaye suna ciko idanuwanta.
Ta saka hannu ta tallafi cikinta.
"Allah, Ka dubani da idon rahama. Ka bayyana min Irfan. Allah, Ka duba abin da ke cikina da halin da nake ciki. Ka fito da Irfan a duk inda yake."
Tabbas, idan Irfan bai bayyana ba, tana cikin masifa da bala'i. Tasan alƙiyamarta ta tsaya.
Ko wane ciki idan aka samu ana farin ciki da murna. Amma ita sam ba ta yi murna da farin ciki ba. Sai fargaba da kuma ɗanasanin samun cikin take.
Bayyanar cikin nan tamkar bayyanar ranar mutuwarta ce. Ba ta murna da shi, ba ta kuma maraba da shi.
Amma Irfan, da aka sanar da shi cewa tana da ciki tun a office ɗin likitan, ya yi sujudus-shukr.
Bayan kuma, ya fi kowa sanin cewa fitowar cikin tamkar fallasuwar sirrin da suka Dade suna ɓoyewa ne.
Umsar ✍️
08932144182