Nuwayrah the foreigner’s passion

A question of trust

by @zahrabmrs02


A hankali Jawad ya rage volume din  waƙar , ya juyo ya kalle ta cike da kulawa. “What happened, pookie? Meke damunki?

A sanyaye Nuwayrah ta kalle shi, da ƙyar take iya buɗe baki saboda yadda yunwar ke sassaƙar ta ,Yunwa nake ji, har yanzu ban yi breakfast ba.

Zufa ne ya fara karyo mata a goshi. Jawad ya girgiza kai cike da damuwa. Ki daina zama da yunwa ɗan Allah, pookie. Bari na ƙara sauri yanzu za mu ƙarasa gidan Yaya Nabil ki samu ki ci abinci,Kafin ta ba shi amsa, wayarta ta fara ruri. Ta kalli screen ɗin: Ray❤️

 Hello Mimi, yanzu na ga motar Comrade kusa da asibitin 44 ,Eh muna tare ma, gidan Yaya Nabil zai sauke ni ,Kice masa ya yi parking zan ba ki sako. Ina kusa daku   daga asibitin na fito, kuma Dama  wajanki zan wuce. Kit ya kashe wayar 

Nuwayrah ta juyo wajen Jawad. Love, please ɗan yi parking, Ray zai ba ni sako.Kala Jawad bai ce ba, ya samu waje a gefen titi ya gyara parking. Ko minti biyu ba a yi ba, Rayyan ya tsallako titin , hannunsa riƙe da kwali ,Big head, Pizza na saya miki a Domino’s. Jiki na rawa Nuwayrah ta amshi kwalin . “Thank you so much, Ray! You’re a life saver. Tun safe ba abin da na ci wallahi, har ina tunanin kamar zan iya suma kafin mu ƙarasa gidan Yaya Nabil. Sai a lokacin Rayyan ya kalli Jawad ta window . “Oga, a daina barin Mimi da yunwa. Ka san yadda ulcer ke mata idan ta tashi. Murmushin yake Jawad ya yi, ya amsa a taƙaice, “Noted, insha Allah.

Rayyan ya yi musu sallama ya tsallaka ya koma motarsa. Tuni Nuwayrah  , ta fara cin pizza ɗinta cikin hanzari. Wani irin relief take ji yana ratsa ta, yayin da gumi ke ci gaba da karyo mata ,Allah ka raba mu da yunwa  nuwayrah ta ayyana a ranta ,Love, I’m thirsty, zan sha ruwa,Fita Jawad ya yi daga motar, ya dawo da  pure water guda biyu ya mika mata. Ta sha ruwan ta yi hamdala sannan ta ɗauki tissue a gaban motar ta goge bakinta. Ta buɗe ƙofar motar kaɗan ta wanke hannunta a waje Suka ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, inda Jawad ya ɗauki hanyar Unguwar Rimi, Kinshasa Road, gidan Yaya Nabil

Ba wanda ya ƙara magana   har suka isa kofar gidan Yaya Nabil. Jawad ya kashe motar ya yi parking, sannan ya juyo yana kallonta with total seriousness.

Nuwayrah, me ke tsakaninki da Rayyan?

Nuwayrah ta dubeshi cike da mamaki, ta sauke ajiyar zuciya. “Love, please kar mu fara haka da kai. You of all people should know. Ka manta ranar da ka fara ganina kana ta bi na   ba ka number na? Rayyan ya zo ɗaukata ya gan ka, ya kuma ba ka number na? Idan soyayya muke yi, me zai sa Rayyan ya ba ka number na?Jawad ya yi shiru yana tunano ranar, da irin yadda Rayyan ya shige  gaba  har ya sa Nuwayrah ta fara sauraronsa.Amma ya aka yi ya san kina jin yunwa? Har wani ce min yake na daina barinki da yunwa?

Ba ka ji abin da ya ce ba?. Dama waje na zai je ,kuma time to time yana sayo min dominos  pizza  Sabida favorite dina ne .

Jawad ya sauke numfashi . Shikenan, pookie. I trust you. Zan zo na  mayar da ke gida Anjima 

No, kawai ka bar shi. Motata nazo ɗauka, kiran da Yaya Nabil yake min kenan ɗazu. Wai mechanic ɗin ya ce zai kawo motar kafin Magriba,Jawad ya girgiza kai da sauri. No, pookie. Ba zan barki ki yi driving ɗin dare ba. Nayi alƙawari zan kawo miki motar da kaina insha Allah ,Shikenan, sai ka zo,Bayan Isha zan dawo, ki shirya .Nuwayrah ta yi murmushi har sai da dimple dinta ya fito ,Awwn that’s my girl cewar jawad yana hura mata kiss da hannu 

, door bell ta danna  mai Aiki gidan ce ta bude kofar tare da gaishe da nuwayrah cikin girmamawa , Anty Fiddausi (wacce suke kira da Anty Fiddo), da ke zaune a falo tana naɗe wasu kayayyaki, ta miƙe cikin sauri fuskarta ɗauke  murmushi.

“Mimi! Yau Kece a gidan Namu ya kike ya karatun ? . , karatu Alhamduillah Anty Fiddo. Mun dai kusa gamawa  , Ina 'yar gidan tawa Afrah banji motsin taba ?

Anty Fiddo tana nuna hanyar korido. “Afrah tana  ciki tana barci. Tun Wajan  biyu na rana ta gama Koke Koken ta tayi barci, saboda haka za ki samu salama kaɗan kafin ta tashi. Nuwayrah ta sauke ajiyar zuciya , , bari kawai na shiga daki  na huta, lectures ɗin Yau gaba ɗaya sun gama gigita ni. Abinci fa Mimi ?a koshe nake Anty fiddo yanzu na gama cin pizza 

Kai tsaye Nuwayrah ta nufi guest room . Tana shiga ta ajiye jakarta a gefe, ta wanke  fuskarta da ruwa sannan ta kunna AC. Nan da nan dakin  ya ɗauki sanyi mai daɗi.cikin Minti ƙalilan , barci mai nauyi ya kwashe ta.


A hankali Nuwayrah ta buɗe idanunta sakamakon sanyin AC da ya ratsa ta. Ta miƙe ta tana lalubar glasses dinta ,lokaci ya ja sosai. Ba ɓata lokaci ta tashi ta nufi bandaki , wanka tayi  tare da canza pad (wanda dama  tana  yawo da extra pad  a cikin jakarta).

Bayan ta fito, ta buɗe wardrobe ɗin jikin bangon .  abayar  ta gani da ta bari tun zuwanta na ƙarshe; an wanke  , an goge  Ta zura abayar a jikinta tare da gyara veil dinta , sannan ta nufi falon gidan.

Tana karasawa  cikin falon, Afrah da ke wasa ta hango ta. Nan take ta taso da gudu tana ɗaga hannaye, “Anty Mimiiiii!”

“Afrah babyyyy!” Nuwayrah ta faɗa cike da farin ciki tare da ɗaga ta sama, 

Gyaran muryar Yaya Nabil ne ya sa ta sauke Afrah a hankali tare da riƙe hannunta, suka nufi inda yake zaune.

Yaya, ina yini? Ashe ka dawo?

“Eh, na dawo. Maman Afrah tace kina barci.

Nuwayrah ta ɗan marairaice fuska, “Ai Yaya, I needed that sleep. Nan gidan ne kaɗai escape zone ɗina. A gida ina kwanciya Mama za ta ce na cika lalaci.

Shiru Nabil ya yi yana kallon  tilon qanwar tasa cike da tsantsar soyayya da tausayawa. Ba ya haɗa soyayyar Nuwayrah da komai a rayuwarsa; ya yi-ya yi Mama ta bar Nuwayrah ta dawo wajensa fir  ta ƙi.

Kiran sallar Magriba ne ya katse musu hirar . Yaya Nabil ya miƙe tsaye, Bari na tafi masallaci.

A daidai lokacin ne Anty Fiddo ta fito daga ɗakinta. Mimi, ga abinci nan a dining. Bari na yi sallah.Chinese fried rice Anty Fiddo ta dafa musu sai  ƙamshi take . Nuwayrah ta ɗiba wanda za ta iya ci, ta koma guest room hannunta riƙe da na Afrah suna ci tare.

Bayan ta kammala ta fito falo don maida plates , ta taddar da Yaya Nabil da Jawad zaune suna hira; probablya waje suka haɗu bayan an fito daga masallaci. Gaishe Su tayi ta wuce bedroom ɗin Anty Fiddo inda suke ta hira .Yaya Nabil ne ya shigo , “Ki zo ku tafi Mimi, Jawad ya ce zai kawo miki motar gobe. To Yaya, na gode. Anty Fiddo, goodnight .anty Mimi zan biki ,kiss nuwayrah ta mata a goshi kiyi hakuri afrah kinga gobe Akwai school zanzo weekend na dauke ki da kaina ,da haka ta lallaba afrah 


a mota ta same jawad suna  tafe suna hirar su gwanin ban shaawa har kofar gida ya ajiye ta sai da ya tabbatar ta shiga  gidan sannan ya tayar da motarsa ya wuce