BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 19

by @maidambu41


 Ita kan tsoro suka bata domin taɓa ganin faɗa haka ba, juyawa yayi cikin wani irin yanayi da salo ya ce mishi. "Kayanka suna hannuna, ka kula domin ba zan so ku fara zirga-zirga tsakanin hukumar tsaro ba zuwa na shige da ficce, ba barazana nake maka ba, kawai gaskiya nake gaya maka kowa a barshi akan raayinsa da abinda ya ga zai iya idan kuma aka cigaba da tafiya haka dole abubuwa dayawa zasu faru a lokacin da babu wanda zai so haka. A gare ni riba ce a gare ka asara ce." 


      "Me yasa kake gaya mishi magana haka Mahaifinmu ne?" Inji Fuad, "Eh kai mahaifinku ne, ni cire sunan yayi a jikina ya watsar da ni!" Ya fada yana me jan hannunta suka fita. Bude mata motar yayi ta shiga ya koma gefensa ya zauna ya ja motar suka bar gidan. Yadda yake dukar motar zaka dauka motar ce tayi laifi abinda ya janyo mata takura wuri guda. Sauka yayi gefen hanya ya sauka tare da fita a motar, inda take ya zo ya bude duk ta gama firgita da shi, bude aljuhun motar yayi ya ciro kwalin sigari ya kunna sannan ya rufe. Yadda ya kunna haka yayi ta bankawa cikinsa hayaki, yana sha yana kara har sai da ya shanye rabin ƙwalin ita kan tsoro ya bata ta kifa kanta tayi akan cinyarta. Yadda ya shiga motar tare da buga murfin motar tasa ta dole ta tashi zaune. 

      Yadda yake tukin yasa ta kara kame kanta, har suka isa kofar gidan, yadda bai bata damar fita ba, haka ta zauna a dakin shiru. Ya bude gate din Hajiya ya dawo ya shigar da motar sannan ya fita ya rufe gidan ya zo zai wuce ganinta cikin motar ya bashi mamaki. Zuwa yayi ya bude mata, sai lokacin ya lura da yadda take kuka kasa-kasa. "Me aka miki?" Shiru tayi tana toshe bakinta. "Nace me aka miki?" Ya daka mata tsawan da sai da ta k'amkame kanta a wurin. Jikinta yana rawa ta ce mishi. "Babu?" "Ai kawai zaki shiga wurinku ki janyo min bakin jini ne?" "A'a wallahi!" Ta fada cikin shashekar kuka, "to me yasa kike min kuka?" "Don Allah kayi haquri!" "Ok kara min takaici zaki yi akan wnada nake ji?" Ya fada da karfi har yana naushin gilashin motar, jin yadda glass din motar ta fashe yasa ta d'ago kai da sauri tana fadin. "Kayi hakuri na daina!" Wuce ta yayi ya barta a wurin ita kuwa bata tsaya ba sai dakinsu. Tana shiga ta zube a gadonta. Kuka tayi shi har ta godewa Allah kafin barci ya yi gaba da ita. 


***

Austria 

Mustapha Yusuf Ladan. 


Tunda ya isa Austaraliya, sau uku yana kaucewa duk wani wasan da zai buga. Gashi akwai wani meeting da za'ayi na attajiran kasar Europe kuma shi ne zai buga wasa a taron, amma iya yayi laushi ya kasa kome. Coach dinsa ya zo kofar dakinsa ya buga kofar. Bude idanu yayi, a hankali yake bin dakin da kallo, gabanshi ne ya buga da ƙarfi. Ba dai mafarkin da yayi jiya ya faru ba. Kurawa gadon idanu yayi zuciyarsa tana wani irin bugawa. Dafe kanshi yayi ba dai abinda yake gani a mafarki ba ne ya faru da shi. Haɗiye yawun bakinsa yayi maza tare da janye bargon, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani nutsuwa yana sauko mishi. Lokacin da ya fahimta babu abinda ya faru tsakaninsa da Olivia. A hankali ya sauko yana me ɗaukar rigarshi ya saka tare da nufar kofar dakin. Bude kofar yayi ya kurawa Coach ɗinsa idanu, Ladan amma kasan dai akwai abinda yake gabanmu ko? Ladan ka sha giya ne jiya?? " Shafa kanshi yayi yana jin wani irin kasala yana rufe shi ya juya ciki. Ban daki ya shiga, ya fara brush tare da alwala. Sai da yazo yayi sallah. Yana ta niman tuba domin ya sake sallah ya kwace mishi.  Babban kuskuren da ya aikata jiya kawai sai da yaji kome ya fita mishi. Yana fitowa ya tsaya a gaban mirror dinsa. Abu biyu ya aikata wanda Allah da kansa yake ƙyamarsu, ban daki ya shiga yayi wanka tare da brush babu iyaka, sai da yayi wanka ya kara fitowa ya samu an kawo mishi kayansa zai saka su tafi wurin wasan, tun asuba yake kokarin ganin ya daina warin giyar da ya sha.  Haka lokacin da sahur kafin ya kori Olivia, shiryawa yayi yana kallon yadda kome na dakin ya hagitse. Ji yayi wani irin bakin ciki yana zuwa mishi. Jiya saboda bai taɓa shan giya ba sai jiya. 


     Tun jiya da abin ya faru ya sashi jin tsanar giya. Ko sunan giya baya kaunar ji ko ya tuna. Saura kiris da wani labari ake ba wannan ba. Da ya kusanci Olivia me zai cewa Ubangiji ya sha giya yayi zina, a cikin wata mai alfarma ya aikata abubuwa biyu masu muni har haka. Agogon hannunsa ya saka ya fito ya samu Coach dinsa yana tsaye har lokacin. "Kana da mutunci sosai, addininka ya haramta shan giya, ina rokonka da kada ka kara ka ji." Wani matsanancin kunya ce ta rufe shi haka suka cigaba da tafiya shi sai bai ce kome ba. Amma ya ji wani irin kunya da bai taɓa ji ba. 


  Tun dawowarsa daga Nijar, Olivia baturiya ce da suke aiki ɗaya. Tana mugun sonshi kai wannan ba so bane bukatar kai da kai ne, ta jima tana sonshi tun farkon haduwarsu amma yaƙi amincewa. Saboda yasan kabilarshi da danginsa ya aka kare da wacce yake gani a cikin idanunsa. Haka tayi ta bibiyarshi, amma baya barinta a jikinsa. Kai karshe sai da ya fito da hoton Naanah Asma'u y nuna mata domin ta haka ne zai kauce mata. Tunda ta ga Naanah Asma'u ta kuma fahimci sai dai ta nunawa Naanah Asma'u hasken fata amma ba kyau ba, haka yasa ta kyale shi sai suka kamo mutuncin wanda har ta kai tana ganin abu zata gaya mishi ta daukawa Naanah Asma'u. 


          Shi kuma sai ya amince saboda duk abinda zaka yi matuƙar zaka ce na Naanah Asma'u ne take zaka fahimci yadda yake kaunarta. Shi yasa kome take itama da Naanah Asma'u take amfani. To tunda ya san ya rasa Naanah Asma'u musamman da kannensa suka tura mishi da ɗaurin auren, daga nan ya fahimci ya rasa ta.. shi kenan ya koma wani irin mutum mara son hayaniya yana gida, duk lokacin da aka kawo wasa sai ya kwacewa wasan. 


        Haka yasa yayi wani irin sanyi wanda ko shiga mutane. Wannan yanayin da yake ciki da shi Olivia tayi amfani da shi tana zuwa ta dauko shi suka fita. Anan tayi amfani da damarta tare da bashi giya ta hanyar coca cola, ta ce mishi zai samu sauki sosai daga damuwar da yake ciki musamman da bai ɓoye mata an raba shi da Naanah Asma'u ba, a madadin ya sha ruwa da dabino, sai gashi ya sha giya har kofi daya. Wanda tun a lokacin ya mugun bugawa. Haka ya fito daga bar ɗin ya tsaya s cikin ruwan sama ruwa na dukanshi. Riko hannunsa tayi zuwa inda ta ajiye motarta. Tun a hanya take mishi wasu abubuwan da kanshi ya kasa dauka.. har suka isa apartment dinsa. Tunda suka shigo ta fara mishi wasu abubuwan. Wanda tun a parlourn yaji y fara fita hayacinsa. Basu zame ko ina ba sai a bedroom ɗinsa. Tunda ya yi nasarar cire mishi rigarshi. Kura mata ido yayi yana kallonta. "Ni ce Naanah Asma'u!" Kallon fuskarta yayi kafin ya kai hannunsa ya shafa fuskarta. "Ke ba Naanah Asma'u ba ce, domin ita na ajiyeta a matsayin rayuwata ce, sannan nayiwa kaina alƙawarin ba zan taɓa zina ba. Ki tafi gida ba zan iya saɓon Allah ba!" Daga haka ya ja bargon ya ci-gaba da barci. 


    Jikinta ne yayi mugun sanyi ba dai har ta fahimci ita, sai ta ji jikinta yayi mugun sanyi. Saka kayanta tayi tare da barin ɗakin bakiɗaya. Tasan da mutanensu da tuni an fara abinda bai dace amma shi duk da yana bugu amma ya gaya mata ba zai iya saɓawa Allah. Tun tsakiyar dare ya ya farka yayi ta amai sai da ya amayar da abinda ya sha sannan ya shiga kitchen dinsa ya dauko ruwan kal ya haɗa da ruwan dumi ya sha kafin ya dawo ya kwanta.

   Wannan shine abinda ya faru, tunda ya shiga filin yayi duk abinda zai yi kafin ya ya fara wasa,  gashi abinda coach dinsa ya fada mishi wasan yana da mugun muhimmanci, domin yan kasuwan kasashen Turai ne suka haɗu akan kasuwancinsu, don haka an zuba musu kuɗi. 

      Haka yasa yake bugawa wasan da zuciyarshi. Har aka gama taron ya koma gefe ya zauna tare da ciro wallet dinsa, hotonta ta ne, sanye da labcoat, tana murmushi. A hankali ya mai da wallet din aljuhunsa. Bayan Olivia bai gayawa kowa ya rasa Naanah Asma'u ba, shi kaɗai yasan yadda yake ji. Bai taɓa sanin haka mutum yake ji idan ya rasa abinda yake so ba. 

***

Agadaz. 

Uban kowa ne a gaban Abba Babba, kura mishi idanun. "Naanah Asma'u ta zauna idan ta tare a gidanka sai ka biya mata duk abinda ya dace amma a yanzu na fahimci dalilin da Rukayyah take kin duk wani abu daga gare ka. Don Allah ka bar Hajiya ta tafi ka ji." 

          Shiru yayi yana kallon kasa, "kayi hakuri ni da ina da yadda zan yi da na saka ka sake ta." Da wani irin sauri yake kallon Abba babba yana jin wani abu me karfi yana dukan kirjinsa. "Abba babba!" Gyada kai yayi yana faɗin. "Nasan ba zaka amince ba ne, amma da zaka amince da ka sawwake mata. Domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankalin Hajiya." 


      Kallon kasa yayi kafin ya ce mishi. "Kayi hakuri ba zan iya sake ta ba. Koda kuwa kashe ni zaa yi sai dai a kashe ni akanta. Amma ni ba zan iya sake ta ba" daga haka ya mike ya bar gidan. 

        La Coffee shop ya tafi a can ya zauna na tsawon kwanaki uku. Sannan wani abun da ya kara sakawa yayi haka yadda Hajiya zata ji idan bata ganshi ba. Har ta bar Agadaz zuwa ƙasa me tsarki. Bai koma gidan ba sai da tayi kwana biyu da tafiya.  Sannan ya tafi gidan bayan sallah la'asar, bangaren Hajiya ba kowa  bangaren Maamah ya nufa duk suna tsakar gidan. Ganin yadda suke ta aikinsu. Sun saka karatun Alkur'ani, suna bi. Ko sallamarshi basu ji sai da ya kara maimaitawa suka kashe tare da nutsuwa. Daga bakin kofar ya tsaya yana musu wani irin kallo. Musamman ita da kanta yake babu daurin dankwalin.  Da sauri ta shiga niman dan kwali. "Ina jiranki."  Ya juya tare da barin bangaren, ita kan bata san yaushe zata saba da wannan auren ba, domin tana ganinsa zata ji gabanta ya fadi musamman shi ɗin. "Tashi Didih!" Faɗime ta mika mata hijab ɗinta. Jikinta yana rawa ta nufi lungu ta shiga ta wuce har bangarenshi. Da sallama ta shiga cikin parlournshi. Kura da datti yayi ya kalleta da kyau yadda take rawan jikin yasa shi cewa. "Bana nan na kwanaki amma ki gaza zuwa ki gyara min daki? Me yasa?" Yadda yake maganar rai a ɓace yasa tayi kasa da kai. Takowa yayi yana me zuwa inda take ta d'ago kai tana me yin baya.

  

          Tunda ya fara zuwa gare ta, ta shiga ja da baya har ta isa jikin kofar dakin, hannunsa daya ya kai tare da danne kofar. "Me yasa?" Dan kare kanta tayi tana jin wani irin kuka yana zuwa mata. "Kada ki min kuka!" D'ago kai tayi tana kallonshi. Saboda yadda ya mata maganar babu hayaniya sannan babu kwarjini ko firgitarwa a muryansa. "Me yasa!" Janye idanunta tayi a hankali tare da yin kasa da kai. "Tambayarki nake!" Shi kanshi bai san me e yake tura shi gare ta ba, domin shi ba ne dalilin da yasa yake gabanta. Matsawa tayi zata kauce mishi amma ya kai hannunsa gefen kugunta. Da sauri ta d'ago kai idanunta waje, janye hannunsa yayi shima da sauri, yadda ya a cika mata idanu yasa tayi kasa da kai ya ce mata. "Amma ai na ga kina magana ko?" Girgiza kai tayi. "Tow gaya min me yasa?" Haɗiye yawun bakinta tayi tana raba idanunta, amma taki kallonshi....