Last free page
by @maidambu41
"A ce tsawon kwanaki bana nan amma babu gyara, haka kike ƙazanta ban sani ba?" D'ago kai tayi tana kallonshi. "Bar kallona!" Ya kara fada da dan murya a buɗe. "Kayi hakuri!" Iya abinda zata fada kenan yasan ko kashe ta zai yi abinda zata fada kenan. Shiru yayi yana mamakin yadda ba zata iya magana mai tsawo ba, shi har mamakinta yake ji yadda bata damu da dogon magana ba. "Na meye zama ba dan kwali?" Nan ma shiru tayi ta gaji da tsayawan da tayi a gabanshi. "Kayi hakuri!" Duka ya kaiwa kofar yana faɗin. "Nayi hakurin kaniya?" Fashe mishi da kuka tayi kanta a sunkuye, kyale ta yayi ya wuce dakinsa ya ga yadda ya bar gidan haka yake. Haushi yasa shi fita ya barta a parlourn. Bayan ta sha kukanta ta koshi, ta nufi bangarensu ta dauko duk abinda zata bukata. Tazo ta shiga gyara bangarenshi har da turaren wuta ta saka ta wanke ban dakin. Sannan ta koma bangarensu.
Dab zaa sha ruwa ta kai mishi abincinsa, bata san yana parlour ba, kuma su biyu suka kawo kayan. " Didih Yaya Uban ya iya zaɓar kome hadadde. " " Shiiii Batul!" Ta fada tana ajiye kome, d'ago kai da zata yi ta ganshi kwance hannunsa dukka biyu a kirjinsa, idanunsa rufe. "Didih!" "Shiiiiii yana barci!" Ta fada tana me jan hannunta suka fita, gabanta yana faduwa. Bude idanu yayi yana mamakin ita haka Allah yayi ta magana ma sai ka zaɓi yinsa ko shiru. Tashi yayi ya zauna yana kallon abinda suka kawo, dakinsa ya nufa ya sauya kaya. Sannan ya fito waje, masallaci ya nufa ya a bakin kofar shiga ya ga Abba Babba, da abokanshi suna ta hira gaishe su yayi ya koma gefe yana kallon kasa. "Adam kun yi waya da Hajiya?" "Wayar ta samu matsala ban kirata ba." Bai iya karya ba kuma idan yace zai yi nan da nan kake fahimtar haka a fuskarshi. Karar da wayarshi tayi Abba babba yayi kamar bai ji ba. Ya fahimci fushi yake da Hajiya har da shima wato da ya ce ya bar abinda yayi niyya shine yake fusace. Ciro wayar yayi ya kashe sannan ya cigaba da zama cikin kunya domin karya dai bata dace da shi ba. Kiran sallah aka yi duk suka mike shi ya shiga raba musu abin bude baki. Sannan shima ya sha na shi, ya kuma alwala ya shiga masallacin. Sai da aka yi sallah Magariba sannan suka dawo gida. "Adam!" "Naam!" "Kayi hakuri ka kira Hajiya ta damu na ji ance a can ma sai da tayi ta zazzaɓi!" "Allah ya sawwaka!" Yana fadar haka ya wuce zuwa bangarenshi. Yana shiga ya samu kome zama yayi, ya fara cin abincin kafin ya gama ya nufi ban daki ya dauko wiwi ya kunna sai da ya sha sosai sannan ya fito waje ya samu garin ya fara duhu.
Sallah isha aka kira ya nufi cikin yayi alwala sannan ya tafi masallaci. Sai da aka yi sallah sannan ya wuce yawonsa.
Tunda ta dawo hankalinta ya tsaya akan kannenta suka yi ta hira, koda yake ita nata eh aa ko tayi ta dariya can ana sako sunan Ya Moud tayi shiru. Tashi tayi ta nufi cikin dakinsu wayar Maamah ta dauka tare da kiran Ya Moud. Kashe kiran yayi ya kirata, ai kuwa ta shiga magana kamar ba ita ba. Tana yi tana biye ta ƙarshe ta ce mata bayan sallah isha zai zo. Haka ta fito ta me dawa Maamah wayarta. Bata gaya musu zai zo ba, haka suka yi ta hira har zuwa lokacin da aka sha ruwa suka yi sallah, a tsakar gidan suka cigaba da hira kasancewar Abba babba ya hana su kunna solar da Uban kowa ya kawo lokacin rashin lafiyarta. Hira sosai yan matan suke yayinda take kwance kanta a bisa matashi.
"Assalamu alaikum! Ya baanat!" "Laaa Ya Moud!" Suka fada lokaci guda. Tashi tayi tana me niman dan kwali ta rufe kanta. "Ya Moud sai yau?" "Ina Maamah?" "Yanzu zata fito!" Haskata yayi da wayarshi yana faɗin. "Duk cikin amarcin ne haka?" Kauda kanta tayi tana tura baki. "Yi hakuri tsokanarki nake!" Ya fada yanaai gyara zama ya mika musu ledar da yazo da shi, "Allah ya kara budi!" Fitowar Maamah yasa wurin ya sake armashi. Hasiya tana daga parlournta amma tana kallonsu bakin ciki da kishi yake cin ranta. Musamman yadda hankalin kowa yake kan Naanah Asma'u, ita fa ta tsane ta sosai kamar ta kashe ta take ji, kallonsu take kawai.
Janyo wayarta tayi ta shiga duba number Uban kowa da ta dauka tare da jin a ranta lokaci yayi da zata lalata auren ko ta halin kaka ne. Don haka ta ɓoye number tare da tura mishi sako. Murmushi tayi tana jin a ranta matukar tana raye sai ta cusawa Maamah bakin ciki, Allah yasa yana zuwa ya sake yarinyar ta ga yadda Maamah zata ji. Ai duk kiyayyarta ba zata so ta ga yarta tana Zawarci ba.
Su kan a waje hira suke suna cin abinci da Ya Moud wanda yake hira da Khamilah, sai Mairoh da take ta raba abinda ya zo da shi. Hira sosai fa, domin yadda suke hiran zaka fahimci yadda suke farin ciki. Musamman ita da take ta dariya.
Hira tayi daɗi domin hankalinsu ya tafi akan hiran, ai kuwa sai ga wuta an kawo. "Alhamdulillahi ni yanzu...." Shiru tayi tana kallon lungu da yake kai ka bangaren Hajiya, ganin yadda ya zuba mata idanu. Jikinta ne ya dauki rawa, har su Maamah kowa ya mai da hankali wurin. Mahmoud bai san abinda yake faruwa ba, ya mika mata nama kenan. "Mahmoud na gaya maka , ka nisanta kanka da matata." Ya fada muryanshi a buɗe. "Amma ai kasan kanwata ce ko?" Yadda ya tako da wani irin sauri me hade da gudu, ya d'ago Mahmoud din ya zabga mishi naushi, dama ya ce zai rama, zai kara na biyu Maamah tace mishi.. "ai kasan dai ɗana ne shi ko? Sannan fa hankalina da ilimina ba zan bari wani abu mara daɗi ya shiga tsakaninsu ba. Ai kin gani da idanunki idan ya miki sai ki cigaba da zama har mu isko gawarki!" Sauke hannunsa yayi ya nufe ta tare da janyota, ita kan ai tun ganinsa ta sume a zaune.
Rike hannunta Mahmoud yayi yana faɗin. "Ba zan bari ka cutar da ita ba, wannan halin naka dabbobi suke." Juyawa yayi ya kalli Naanah Asma'u, akwai wasu abubuwan da baki yafi karfin furtasu, idanun da zuciya suke iya bayyana su. Akwai labarin da lebbe da harshe basu da ikon bayyana su. A tattare da Naanah Asma'u ya ga roko da niman afwa, wanda suke bayan tsoronshi da take ji. Izuwa yanzu sai ya fahimci ba magana ce bata yi ba, maganar ce ba kowa yake gane shi ba. Yarenta ne a haka dabi'arta ce a kwance bisa fuskarta. A hankali ya janye hannunshi daga nata. Wani abu da Allah ya karrama dan Adam da shi, akwai kwarjini, kawaici, da hakuri, yakana, matukar mutum ya haɗa wannan to zaka wayi gari kowa yana girmama lamarinsa, abin da ya hango kenan a tattare da ita. Ta juya tare da zare hannunta a cikin na Mahmoud, ba musu tayi gaba. Shi kuma yana bin bayanta. Duk da kishi da zafin da yake ji sai ya tsinci kanshi da wani irin sanyi lokaci guda. Har bangarenshi suka shiga. Ta koma gefe can ta zauna tare da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. "Me yasa take tsoronsa? Ai shima mutum ne kamar kowa? Me yasa to ubangiji ya haɗa su wuri guda? Yaushe zata cigaba da gudun ƙaddaranta? A'a wannan ba shine mafita ba. Mafitan shine ta zauna da wanda Allah ya bata amma taya zata zauna da wanda zuciyarta bai taɓa so ba? Duk wani hanyar da zata bi domin kaucewa auren abin ya ci tura akan me zata cigaba da cutar da kanta da zuciyarta?* Haka suka cigaba da zama a parlourn, har dare ya raba." Tashi muje ki kwanta!" A hankali ta sauke kafarta kasa, sannan ta mike, cikin yanayinta me sanyi da rashin kuzari ta cigaba da takawa a hankali. Yana bin bayanta har suka fito waje. Yadda ta sauke ajiyar zuciya tare da ɗan mika, kafin ta cigaba da tafiya bata ce mishi cikanka ba ta wuce ɓangarensu. Yana bin bayanta har ta shiga cikin parlournshi.
Four hours back
Yana tattaunawa akan wani kaya da kwayoyi da aka zuba mishi kudi akan ya shigar dasu kwatano za'a shigar dasu Nigeria, ya tsaya yana lissafin yadda kayan zasu fita ba tare da an san da motsinsa ba. Aka turo mishi sakon cewa,
*Anya kuwa kai namiji ne? Au ba mamaki labarin da muke ki na yan luwadi basu ajiye mata sai maza idan kuwa haka ne lallai Mahmoud yana cikin alkhairi sosai.*
Bai da niyyar barin abinda yake amma tunawa da yayi da Mahmoud yasa shi watsar da kome ya nufi gidan. Koda yazo yafi minti goma a tsaye yana kallonsu ta cikin duhu. Bai san me yake saka shi haka ba, amma kalmar ɗan luwadi ya mishi ciwo. Gashi wanda ya tura sakon bai bayyana number shi ba. Kuma har zuwa abinda ya faru sai yake jin kamar kasa ta bude ya shiga cikin.
Lokacin da ta shiga ta samu Maamah a parlourn, ganin yadda take takawa a hankali. Ta ce mata" akwai ruwan dumi a ban daki, ki yi amfani da shi." Ta mike tare da barinta tsaye a parlourn, *Me Maamah take nufi? Innalillahi wainnalihir rajoun* ta furta a kasan zuciyarta Maamah tana nufin wani abu na daban, kai Innalillahi, da sauri ta shige dakinsu. Kwanciya tayi tare da lumshe idanunta, bata son kara bude ido har ta tuna abinda Maamah ta faɗa.
***
Washe gari
Ita da Mairoh aka bari a gidan Maamah sun tafi wurin tafsiri, tana tsakar gida tana aiki da laptop ɗinta. Baba karami ya zo ya zauna yana mata surutu. Barin abinda take yi ta shiga saurarensa. Daukar littafinta yayi zai yi wasa da shi ta amsa tana murmushi. "Ba'a wasa da shi!" Kallonta yayi ya tsalla kuka , wanda ya tilastawa Uwarsa fitowa. "Wani Shegen ne zai taɓa min magajin gidan nan!" Kashe laptop din tayi tare da sakawa a jaka da kayanta. Ai kuwa ta zuburo kamar zata buge ta. Gyaran murya yayi a bayanta ta juya tana zare ido. "Ina jiran ki!" Ya juya tare da komawa lungun, mikewa tayi ta dauki hijab din Mario ta saka. Sannan ta bi bayanshi. Idanunshi yana kan hanyar har ta fito, yana jingine da motar. Ya kura mata ido.
"Kina azumi?" Gyada kai tayi, tana wasa da yatsun hannunta. "Kirjin naki fa?" Nan ma gyada mishi kai tayi. Shiru yayi na tsawon minti uku kafin ya ce mata. "Me ya hada ku?" Girgiza kai tayi, wato ita dai shine take yiwa wannan renin hankalin, "yaushe zaki koma makaranta?" Da sauri ta d'ago kai suka kalli juna na sakwani sannan ta mai da kai kasa, ganin yadda take murd'a hannunta yasa shi kura mata idanun, yadda take motsa hannun ya fahimci, sallah da sati biyu ne, domin yadda ta dunƙule hannunta tare da matse yatsu hudu ya fahimci sallah da sati biyu. "Bakya magana ne?" Bakinta ne ya fara rawa tana son yin magana amma ta kasa toshe bakinta tayi, hawaye na cika a idanunta. "Kalle ni!" D'ago kai tayi ya ce mata. "Sai na yanke harshen kika min kuka!" Da sauri tayi kasa da kanta. "Ke kin ga haka Maamah take yiwa Abba Babba ne?" Kasa hijab din ta ɗauka tana share hawayen da ya makale mata. "Ok so kike ki tare?" Da sauri ya d'ago kai suka yi ido huɗu. Gira ya d'aga mata, ta sauke kanta kasa tana mamakin yadda yake wannan maganar. "To meye don na kasa gane kanki, nima fa auren dole aka min akanki. Ina da wacce nake so!" A kaikaice ta wani kalle shi, sai tayi kasa da kai domin ya bata mamaki dama yana da wacce yake so ya katse mata nata farin cikin? Yadda take wasa da hijab din ya ce mata. "Kina kishin don na ce ina da budurwa ne?" Girgiza kai tayi tana wasa da kafarta. ....