Nuwayrah the foreigner’s passion

A door opens

by @zahrabmrs02

Bayan Nuwayrah ta fito daga  (department), ta nufi M Square inda Rayyan yake buga wasan Polo lokaci zuwa lokaci. 

Tana parking , ta hangi wata Benz ta faka a gefenta . a kusan lokaci ɗaya suka buɗe ƙofa  wata kayyawar buduwar ce ta fito face dinta yasha makeup tayi kyau abinta  da ganin ta Kaga yar gayu ,rayyan ne ke tahowa kusa dasu cikin Kayan polon sa da suka Kara masa kyau 

 Hey, girls!Rayyan ya faɗa cikin farin cikin ganin babe ɗinsa da kuma bestie ɗinsa lokaci guda.

Hello , Ray,suka faɗa a tare. 

Nuwayrah kalli  Susu  fuskarta a sake Suhaila, ya kike? Long time.A ɗan ɗakile, Susu ta amsa mata, “Lafiya. Nuwayrah ta yi murmushi , sannan ta juyo wajen Rayyan. “Yau ma ka gayyace mu ne mu zo mu kalla yadda zaka  wahalar da dokin nan?

Rayyan ya kwashe  da dariya, yana girgiza kansa cikin  nishaɗi. mimi kenan  Wato  dokin kawai kike tausayawa ko? Shi wanda yake saman dokin ba a damu da shi ba?Ya ƙarasa maganar yana kashe mata ido ɗaya cikin wasa.

Suhaila (Susu) wacce ke tsaye a gefe tana tura  baki, ta taka a hankali ta tsaya daf da Rayyan. Ta sa hannu ta gyara masa kwalor rigarsa ta Polo, gami da juyowa ta dubi Nuwayrah da wani irin kallo na isa.

“Ray baby , bari na shiga ciki na zauna kasan ban fiye son tsayawa a rana for long ba kafin ku gama wannan hirar taku, rana ta mun illah Susu ta faɗa cikin muryarta mai ɗauke da gajiyawa.

Alright, babe. Shiga ciki, Gamu nan  ƙarasowa yanzu, Rayyan ya amsa mata cikin kulawa.

“To Mr. Player, ni ma bari nabi sahu   Kafin madam Dinka ta yi fushi ,nuwayrah ta faɗa tana murmushin tsokana.

Just watch me win this round for you, Big head nidai  am team doki ,babe Dinka susu zaka birge bani ba 

sit  dinta na kusa da susu Wanda tayi Kamar bata San nuwayrah ba ,ganin hakan yasa itama ta Kama kanta,ta mayar da hankalinta kan rayyan dake wasan sa cike da kwarewa 

 ihu nuwayrah take tana tsalle rayyan yayi nasara ,wani Kallo susu tayiwa nuwayrah ,tare da Jan tsaki ,a hankali nuwayrah ta nema waje ta zauna jikin ta a sanyaye .bayan an gama wasan parking lot nuwayrah ta nufa jingina tayi jikin motar ta tana jiran rayyan  five minutes later sai ga rayyan da susu sun jero sosai suka dace da juna ,da susu zata gane data daina kishi da ita ,cos kamar su yaya sadiq take kallon rayyan .kusa da ita suka karaso kafin rayyan yayi magana nuwayrah ta riga shi  congratulations ray you’re the best player in the field proud of you  ,thank you big head thanks for your support .ko  kallon susu batayi ta shige mota murmushin yake nuwayrah tayi ,bye ray ka gaishe dasu hajia ,itama bata jira amsar sa ba shige tata motar .

 Tana Isa gida ta nufi kitchen ,jolof din taliya ne a time table ,cikin kankanin lokaci ta gama 

email tagani idan aka bukaci ta turo sample dinta na Aikin embodirey hannunta na rawa ta dauki designs Kala uku ta tura tana adduar Allah yasa a zabe a cikin wanan gasa 

A bakin yaya sadiq  taji ji labarin jawad ya kira yaya nabil akan zai turo da magabatansa inda abban yace nabil yayi bincike akan jawad din idan an gama binciken ba wata matsala sai  a bashi damar  turo iyayenasa 

 wai yau ita ake maganar aurenta ashe zata ga lokacin nan ? bata taba kaiwa wanann stage din ba da saurayi ,duk wanda tayiwa maganar ganin abba zata nema shi ta rasa ,ko yace be shirya aure ba ko wani abun ya faru .ya Allah nasan jawad ne maifi alkairi a gareni Allah ina rokon ka sa binciken yaya nabil ya zama successful Allah ka taimake ni kasa ina da rabon zama matar jawad .


a week later (bayan sati daya )

Yaya Nabil ya kammala bincikensa tsaf  a kan Jawad, iyayensa, harta inda yake aiki  Magana daya ce ,Jawad mutum ne mai mutunci, babu wani aibunsa da nabil ya samu Alhamduillah ya cika sharruda

direct gidan iyayensa dake badarawa ya Nufa.da mama ya fara cin karo ,yadda ya ganta ta rashe a kasan carpet saitin fanka yasan bata dade da dawowa daga Wajan aiki ba  cikin girmamawa ya gaishe da maman 

 wani kallo maman ta watsa masa ,shanyayye sai Yau Allah yayi ka tuna da kana da uwa kenan ? Sai Yau Firdausi ta Baka izinin zuwa ko ?shiru nabil yayi ,ita dai mama bata da gwani ya rasa me Firdausi tayi mata .

ba haka bane mama na dan yi rashin lafiya ne kwana biyu ko  office bana zuwa ,Ayya Allah sarki Kaga dayake Baka dauke ni da mahimanci ba ay  San Baka da lafiya ba ,Ina Afrah ?tana gida mama zasu zo cikin satin nan kullum maganar zata wajan anty mimi da mama .bazan maman tayi da nabil 

Abba yana nan ne mama ? Eh yana nan.

mubeen ne ya shigo ,Kafin ya karaso mama ta bashi umarnin ya Kira Abban nasu yana majalisar su 

sosai  suka gaisa da Abban yana tambayar Firdausi da Afrah ,mubeen ne ya kawowa nabil  kunun aya ya ajiye masa cikin girmamawa Bayan Sun gaisa 

uhmm  abba na kammala binciken daka sani Akan jawad kuma Alhamduillah bashi da wani aibu.

ah to masha Allah nabil hakan ma yayi ,sai Ka Kira shi jawad din ya  tura iyayen nasa Allah ya tabbatar da alkairi 

Bilkisu kinyi shiru ko har kin fara kewar autar taki ne ?abba ya kalli mama cikin tsokana Abban su kenan ,kewa ay ta zama dole Allah ya sa alkairi zaa kulla.

Haka zaman ya tashi nabil ya masu sallama. har waje mubeen ya raka shi 

Suna tafe suna maganar tafiyar mubeen din Lagos nanda sati biyu 

Ka gaishe da Sadiq da Mimi idan Sun dawo cewar nabil yana shigewa motar sa 

Nabil bai ɓata lokaci ba ya Kira  Jawad ya shaida masa saƙon Abba. Wannan kiran  shi ne ainihin abin da Jawad yake dakon sauraro tun ranar da ya buƙaci hakan. Godiya ya dinga yiwa yaya nabil har sai nabil din ya kashe wayarsa .ba Wanda yayiwa nuwayrah maganar har ta shiga daki ta kwanta 

WhatsApp call ke shigowa sunan Jawad ❤️ ke  rawa a kan screen ɗin. Tana ɗagawa, muryarsa mai dadi ta ratsa kunnenta 

“Pookie! Guess what?“dazu Yaya Nabil ya kirani . Ya shaida min cewa Abba ya bani damar turo iyayena! Am so happy wallahi .

Nuwayrah ta ji wani irin  farin ciki ya ratsa zuciyarta, ta rufe fuskarta da tafin hannunta cike da kunya sai murmushi take mai sauti 

Jawad ya sauke numfashi, Nuwayrah , ina son na tabbatar miki da abu ɗaya yau... da farko dai na gode da kika zaɓe ni, kuma na miki alƙawarin ba za ki taɓa yin nadamar wannan zaɓin naki ba ,Zan zama silar farin cikinki a ko da yaushe, insha Allah.

Wani irin dadi ne ya  lalleɓe zuciyar Nuwayrah. “Nima zanyi kokari inshaAllah na zama matar rufin asirin ka inshallah love ,network din wayar Keta daukewa katse kiran nuwayrah tayi ta Kira shi ta normal call suka cigaba da hirarsu yace mata baya so a ja lokacin da tsayi kuma baya son wani event daurin aure kawai zaayi ,nuwayrah taso tace masa tana son koda kamu ne ,amma gudun bacin ransa yasa tayi shiru da bakinta .har ta fara hango rayuwar da zasuyi da jawad ,da irin girke girken da zata dinga masa ,wanka kuwa sau biyar zata dinga yi a kullum kamar dai yadda ta karanta a wani littafi ,sai ta zage damtse wajan birge jawad ,dan yadda taga yan matan dake sonsa wanda yake nuna mata chats dinsu. tasan soyayya ce kawai tasa jawad zabarta dan wasu yan matan nasa sunfi ta kyau nesa ba kusa ba .