Chapter 11
CHAPTER 11
Makwafta ne suka shigo gidan aka hau yayyafawa Inna Asibi ruwa. Ko da ta farfaɗo tambayar duniya anyi mata amma sai faman kuka take tana tsinewa Malam Bawa.
Da kyar suka samu ta sanar da su halin da ake ciki.
Salati da sallallami suka hau yi cike da mamakin wannan ɗanyen hukunci da Malam Amadu ya yanke, ba tare da sanin abinda ita ta aikata ba.
Hannun Nadiya Jamila ta kama suka shiga dakinsu.
"Anti kina Jin abin da ke faruwa, da gaske ke kika ce kina son Malam Bawa?"
"Jamila ina son Shi Ina kaunarsa idan ba a bani shi ba mutuwa zanyi"
Ta karasa maganar hawaye na wanke mata fuska.
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Kunga abin da nake fada maku ke da Inna, bin malamai ba shi da rana yanzu ki duba ki ga yadda ya juye miki ƙwaƙwalwa aurenku fa aka daura da shi"
"Da gaske Jamila?"
Ta karasa maganar cikin zallar farin ciki tana mai damƙar hannun Jamila.
"E" Jamila ta fadi da kyar
Girgiza kai Jamila tayi cike da takaici ba shakka duk wanda bai tsaya ga Allah ba yana cikin hasara. Ga shi dai Inna da Nadiya sun tsinci talatarsu a Laraba. A kokarin neman a auri mai kudi Nadiya ta ƙare a auren mushiriki wanda ya girmi mahaifinta.
Shigowar ƙanwar Inna Shi ya Kara hargitsa Gidan. Malam Amadu ya shigo ya sanar masu zuwa dare za a mika Nadiya gidan mijinta. Nan fa gida ya karasa yamutsewa.
Gidansu Wasila
Shirye-shirye suke yi saboda an tsaida magana tunda dai an daura aure yau za a wuce da ita gidan miji. Lefenta ma idan an kaita sai ta iske shi.
Umma bata so haka ba, so tayi a ɗaga tarewar kamar mako biyu masu zuwa haka. Saboda Boka ya kara harhaɗa mata wasu abubuwan, amma ba yadda zata yi ba zata bari suyi wasa da wannan arziki dake kwankwasa masu kofa ba.
Haka ta kira yan uwa da abokan arziki suka cika gidan amarya hidima.
Labarin abubuwa biyu masu ban mamaki tuni suka kewaye unguwar maƙera. Babban abin da ya tayar da hankulan mutane shi ne auren Nadiya da Malam Bawa, yarinyar da bata kula talaka rayuwarta ma hasali ta tsani talaka. Bugu da ƙari kishiyoyinta duk sun haifeta Ita ce zata auri ruɓaɓɓen tsoho. Sai kuma irin cin amanar da Wasila tayi.
Wasila kam baki ya ƙi rufuwa musamman da labari mafi soyuwa ya sameta na auren Nadiya. Ji tayi ina ma ta zuba ruwa a ƙasa tasha. Kayan da Kasim ya aiko mata da su ta kwasa suka nufi wurin Makeup duk da jiya zuwa yau Allah kadai yasan tarin magungunan da Umma ta bata tasha.
Karfe biyu daidai rantsatstsun motocin daukar amarya suka yi parking kofar gidansu Wasila.
Ƙanwar Umma Anti Nafisa ITA suka shiga Mota guda da amarya kai tsaye suka nufi Katsina...
Gidansu Nadiya.
"Yanzu Yaya Asibi kina ji kina gani haka ake shirin mika yarinyar nan gidan tsohon banza"
Hawayen fuskarta ta share ta ɗora da faɗin
"Ya zanyi? An riga da anfi ƙarfina. Amma Malam Bawa ya cutar damu"
"Amma Yaya kinsan da yana son Nadiya Amma kuka bari take zuwa wurinta?"
"Talatu ki rufe mini baki. Maganganunki suna kara fusata ni na gaji da abubuwan da kike."
Inna Asibi ta karasa maganar cikin ƙaraji.
"Ubangiji ya huci zuciyarki, ni banyi don In ɓata miki Rai ba domin har ga Allah nayi mamakin yadda aka haihu a ragaya"
"Ki bari kawai ita da kanwarta Wasila su suke zuwa wurin malamin tun kafin a san da maganar Kasim. Ya na yi masu aikin taimakon cin jarabawa da haka fa suka saba da shi har ya yi nasarar cin amanarmu. Amma nafi tunanin bakinsu ɗaya da Wasila domin yanzu haka labari ya riskeni an tafi mikata gidan miji."
"Mun shiga uku! Yaya kin san da haka kuma duk baki nemo Ni ba muka fantasma wurin bokaye da malamai. Ni fa tuni na rena irin wadannan malaman da kuke bi saboda gudun irin haka, yanzu ga shi nan ya mallake mana diya. Amma wallahi ba zamu hakura ba sai dai a mutu har liman. Ita kuma waccan da taci amanar mu sai ta gane Allah ɗaya ne"
"Amma Talatu muna ji muna gani haka za a tura ɗiyar nan gidan wancan mutumin?"
"Ki share hawayenki Yaya. Zama ne zata yi na ɗan lokaci ba zamu tsaya muna kullonta ba"
Ɗaya daga cikin dangin Malam Amadu ce ta shigo dakin hankali a tashe.
"Asibi, Talatu. Ku fito a yi saurin miƙa yarinyar nan gidan miji, wallahi idan aka sake daukar wani lokaci zata bar mana abin fada ne a cikin gari."
A fusace Talatu ta tari numfashinta.
"Kada ki fada mana maganar banza mana. Abin fada ya wuce wanda ɗan uwanku ya aikata, kun gama janyo mana bala'i da masifa a cikin zuriyarmu"
Inna Asibi ce ta karɓe zancen. "Ki fita ki bamu wuri tun kafin in sauke duk wani haushina a kanku. Sannan kuma ku sani ina sane da ku ne ke ƙulla mini munafurci a wurin ɗan uwanku. Hatta wannan auren na sani yana daga cikin sharrinku"
"A hayye nanaye. Hausawa suka ce daɗina da gobe saurin zuwa, aww ashe mune munafukai ko? To bude kunnuwanki da kyau ki ji Ni. Asibi kada kiyi tunanin bamu san mene faruwa da ke ba, wallahi duk mun sani. Kun samu mai kudi ke da diyarki idanunsu sun rufe wurin bin malamai da bokaye har ta kai ku ga fadawa hannun mushiriki ya asirce diyarki da ke kanki. Yaya Amadu ya fada mana kaf abubuwan da suka faru in fada miki kar muke kallonku."
Wata uwar ashar Talatu ta danna tana mai yin ɗamara a ƙugu.
"Shi Amadun ne ya fada maku haka bakaken munafukai. To ku me ake yi da irinku. Irin masifa da bala'i ga bakin talauci, na rantse miki ko ki fita ko kuma in yi ƙasa-ƙasa da ke"
Murmushi Sahura tayi. "Kinga Talatu yanzu ba lokacin fada bane. Kamata ya yi mu fita waje ku ganewa idanuwanku halin da ake ciki. Nadiya ce gata can tunda baku kaita gidan malam Bawa ita ta dauki hanya"
Inna Asibi da Talatu rige-rigen fita suke cike da tashin hankali.
Gida ya cika maƙil da makwafta sai faman rukon Nadiya ake yi tana fizgewa.
Kyakkyawan mari Inna ta tsinketa da shi.
Zafin marin ya saka Nadiya faduwa can gefe tana kuka.
"Wallahi duka ko hantara ba zata saka in ƙi tafiya ba. An ɗaura muni aure da mijina kun tsaya kun ƙi kaini gidana ajiyar me kuke yi mini"
Salati mutanen wurin suka dauka cike da zallar mamaki.
Damƙo wuyanta Inna Asibi Tayi. "Da ki kasheni da bakin ciki kara ni in kasheki" jibgarta ta hau yi kamar Allah ya aikota"
Ganin za a yi abin kunya ya saka jama'ar wurin kwaceta.
"Ku kasheni amma sai na tafi ko da rarrafe ne. Aure da Malam Bawa ba fashi"
Nadiya ta fada cikin kuka.
"Share hawaye ki Nadiya. Kai ki ai ya zama dole yanzu zamu kai ki ba sai an jima ba"
Talatu ta fada.
"Sai ki je ku kaita. Shugabar munafukai, Indai mu muka haifeta babu inda za a kaita"
"Ba zan tsaya ba, sai kun taho"
Tana karasa fadar haka ta falala da azababben gudu ta fita.
Sabon salati jama'ar gidan suka dauka.
"Mun shiga uku Amarya ta tafi ta kai kanta gidan miji"
Talatu ta fada tana dora hannuwa saman kai.
"Ba zan tsaya ayi wannan abin kunyar dani ba dole In bita in munyi Sa'ar kamota sai a karasa da ita gidan mijin"
Sahura na kaiwa nan ta takewa Nadiya baya..