Chapter 23
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 23
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
Tun da ya ɗaura idanunsa cikin nata yake jin sauƙar nutsuwa da farin ciki na ratsa duk wani ƙofa dake cikin jinin jikinsa, ji yake kamar ya sami abin da ya jima yake nema, zuciyarsa ta yi masa wasai. Duk da yaji babu daɗi na rashin ganin ta da kuma abin da wannan matashin ya yi masa amma yana ganinta ya nemi ɓacin ran ya rasa.
Sanye take cikin niqabi kamar kullum, yadda ta kura masa fararen idanunta yasa ya fahimci tana cikin damuwar rashin haɗuwar su. A hankali ta matso kusa dashi ganin yana tsaye ne don neman abin hawa, ta yi magana cikin siririyar muryarta wacce ke ɗauke masa hankali
"Yaushe ka zo?"
Lumshe idanunsa ya yi na wani lokaci sannan ya buɗe su ya watsa su akanta kamar ba zai yi magana ba, kuma ya ce
"Na ɗan jima"
"Mu bar bakin titi, mu koma cen"
Ta nuna masa in da za su zauna kusa da wani dakali dake gaban wani shop, kamar ba zai je ba, ya wuce tabi bayansa, bai zauna ba, ita ce ta zauna cikin kulawa ta ce
"Uncle ban yi tunanin za ka zo ba"
"Look Angel, I'm tired of everything, you lied to me"
"A'a uncle i didn't lied to you, i....
"Sheeet!"
Ya sanya ta yin shiru ta hanyar rage tsawonsa daidai tsawonta da take zaune, suna kallon juna ya ɗaura yatsansa kan laɓɓansa sa, alamun baya son jin komai daga gare ta. Yana kallon cikin ƙwayar idanunta da ta kura masa su, a hankali wani al'amari ke ziyartar zuciyar sa, yaƙi yarda da abin da idanunsa ke gaskata masa akan ta, zuciyar sa na ƙaryata hakan, yana sake jin ita ɗin ta musamman ce, ganin idanunta sun ciko da ƙwalla, duk da fuskarta a rufe take amma yana iya karantar yanayinta. Ya sauke numfashi a hankali ya yi magana
"Kina da aure!"
Ta sake waro fararen idanunta waje, ta maida kallon ta kan laɓɓansa saboda gaskata abin da ya faɗa, tana da aure! A hankali ta sake maida idanunta cikin nasa ta soma girgiza kanta alamun a'a, ya lumshe idanunsa yana jin wani yanayi shi ba farin ciki ba shi ba farin ciki ba.
Angel mamakin zancen ta yi, waye ya faɗa masa tana da aure? Tana son sanin abin da ya sani game da ita...
"Waye ya faɗa maka ina da aure?"
"Mijinki"
Ya faɗa ba tare da ya buɗe idanunsa ba, ta sauke numfashi, mijinta kuma? Waye wannan? Ba dai ya shiga cikin gidansu ba..
"Ka shiga cikin gida ne?"
A hankali ya buɗe idanunsa ya zuba mata su, karon farko yaji ransa ya ɓaci wannan take kira da gida, inda ake shaye shaye da zinace zinace, gidan da ya tara maza da mata suna abin da suka ga dama suna saɓon Allah.....
"Anan na haɗu da wannan guy dana ganki da shi rannan a gefen hotel"
Ƙirjinta ya buga, ya haɗu da Abraham! Kenan shi ne ya ce shi mijinta ne? A hankali ta haɗiye yawun da ya tokare mata maƙoshi ta ɗan sassauta murya ta ce
"Ba musulmi bane"
"Uhm really?"
"Uncle ka yarda dani ban yi maka ƙarya ba"
"To me yasa kika ɓuya bayan kin san zan zo wajen ki"
"I'm waiting for your call"
Ya ɗan miƙe tare da dafe goshinsa, sam ya manta da ya kira ta a waya, da bai sha wahala ba. Ta tashi ta tsaya cikin nutsuwa ta ce
"Na ji shiru baka kira ba shine na fito na duba ko ka iso, sai kuma naga kana ƙoƙarin tafiya"
A hankali ya juyo ya kura mata idanu, ya yi taku biyu zuwa uku ya iso dab da ita har tana iya jin bugun zuciyarsa, ya yi magana cikin ɗaga murya
"I need to see your face"
A take jikinta ya soma rawa, muryarta na rawa ta ce
"Not at this time"
"When?"
"Uhm for the right time"
"Why? Na ce me yasa Angel, wacece ke? Ina son sanin ki"
Yadda jikinta ke rawa ya ba shi mamaki, me take tsoro? Me yasa take shakkar nuna masa asalinta, yana son ganin fuskar da ta hana shi sukuni, a hankali ya duba agogo yaga lokaci ya ja sosai, 11:00 pm, ya sauke numfashi ya kalli bakin gate yaga motoci sun fara raguwa, ya kalleta yaga ta sudda kanta ƙasa, ya sauke ajiyar zuciya, ya fahimci tsoron buɗe fuskar ta take..
"Ba kya so na kalli fuskar ki?"
"Eh"
Ya ɗan yi murmushi jin amsar da ta ba shi, ya ɗan sassauta murya ya ce
"Don me yasa?"
"Ba za ka so ganin asalin fuska ba"
"Don me yasa ba zan so gani ba?"
"Ba za ka sake zuwa inda nake ba"
"Shi kenan na tafi, ba zan sake zuwa ba, ba zai yu ina tare da wacce ban taɓa ganin fuskarta ba"
Ya juya ya yi taku biyu zuwa uku, ta ce
"Ya Waahab"
Ya tsaya a hankali ya juyo jin sunan da ta kirasa da shi, yana kallonta kamar yadda take kallon sa a hankali ta ce
"Kana da kyakkyawar zuciya"
Ya sauke numfashi ta juya zata tafi ya ce
"Kyakkyawar Aunty"
Ta juyo ya ce
"Kina da ɓoyayyiyar fuska"
Ta yi murmushi duk da rufaffiyar fuskarta amma ya fahimci murmushi take yi, ta juya da sauri ta bar wajen. Ya sauke ajiyar zuciya ya dawo bakin titi ya tari mashin ya hau suka bar wajen....
*******
Angel tana shiga ciki ta ji an riƙe ta tare da haɗa ta da jikin bango, a sorace ta waro idanuwa waje, ya yaye mata niqabin tare da cewa
"Who is that Man?"
Kiciniyar kwace kanta take yi bai bata dama ba, kamar tayi kuka don takaici ya riƙe ta, ta ce
"Let me go"
Ya kurawa kyakkyawar fuskar ido yana ji kamar ya haɗiye ta, yana son Angel sosai amma ita sam baya gabanta, murmushi ya yi ya ce
"Ni fa abokinki ne, ba ki da aboki da ya fi ni"
"Ka rushe wannan alaƙar"
Ta faɗa tana ƙoƙarin ture shi, ya ce
"Saboda wancen mutumin ne? Kin faɗa a soyayyar sa"
"Yayana ne, mutumin kirki ne"
"Yaya! As how?"
"Ka kyale ni na shiga ciki"
A hankali ya cika ta, yana gani ta shige ciki ya zauna a wajen kamar ya yi kuka....
Dr Waahab yana isowa hotel ya wuce side nasa, shiru babu motsin kowa, da alamu sun yi bacci, ya tura ƙofar ɗakinsa ya shiga, ya rage kayan jikinsa sai da ya watsa ruwa sannan ya yi shirin kwanciya ya kwanta, yana ci gaba da tunani akan Angel, yana ji kamar ba zai sake zuwa gidan su ba, amma wata zuciyar tana cewa ya san fuskarta tukuna...
Saƙo ya shigo wayar sa yana dubawa daga Angel ne da Hausa ta turo masa saƙon
_"Da fatan ka isa lafiya?"_
Kamar ba zai yi reply ba amma ya tura da
_"Alhamdulillah"_
Ba a ɗau lokaci ba ta dawo mishi da saƙo
_"Na gode"_
Bai yi reply ba ya maida wayar ya ajiye ya kwanta bacci...
**********************************
WASHEGARI
Bilqees ta shirya cikin uniform na wajen aiki, ta zauna Mamanta ta zuba musu abincin karin kumallo, su ka ci sannan ta maƙale jakarta a baya tare da cewa
"Mama na tafi"
"To sai kin dawo"
"Yawwa Mama"
"Bilqees"
"Na'am Mama"
"Ya aikin da kike yi a hotel?"
"Ina yi fa sai godiya"
"Da fatan ba matsala?"
"Ba matsala Mama, mutumin nan ma ya ce na daina kai masa abincin dare na safe zan dinga kai masa"
Mama ta sauke numfashi tare da cewa
"Cewa za ki yi yaron ki"
Ta kwashe da dariya ta ce
"Uhm ƙato ne fa yake ce min Maman sa"
Murmushi Mama ta yi, ta ce
"Ai yana daraja sunan ne tun da kin ce sunan Mamansa ne"
"Haka ne Mama, na tafi"
Tana faɗin haka ta wuce ɗakin ALAJA ta tadda tana ƙoƙarin fitowa ta ce
"Barka da safiya Maa"
"Bilkisu har kin shirya?"
"Eh Maa"
"To mu tafi"
Suka fito mashin suka hau ya kawo su Alaja restaurant, suna shiga Bilqees ta wuce side na Server's ta cire jakarta ta dawo kitchen ba tare da ta kula kowa ba, ta haɗawa likita breakfast ta saka a food carrier ta fito, suka haɗu da Alaja ta ce
"Yau za ki shiryawa baƙo abincin dare ki kai masa hotel"
"To Maa"
Bata musa ba don ta san halin ALAJA,
"wannan na Yallaɓai ne ko?"
"Eh Maa"
"To ki yi sauri ki kai masa"
"To Maa"
Ta fice kai tsaye ta wuce international hotel, tana isowa ta shige ɗakin Dr Waahab ta ajiye food carrier jin shiru ya tabbatar mata da wanka yake yi, don haka, ta shiga palour ta soma gyare-gyare a hankali take karanta Mulk tayi nesa a aiki taji motsi da sauri ta ɗago Yallaɓai likita ta gani yana tsaye ya kura mata idanu, ta yi sauri ta mik'e tsaye tare da cewa
"Barka da safiya"
A hankali ya sauke numfashi ya amsa da
"Yawwa sannu da ƙoƙari"
Yana mamakin yadda take karatun Alqur'ani, ita da take aiki a restaurant kamar bata da lokaci shine har ta iya karatun Alqur'ani fiye da tunanin sa, ya ɗan juya ya dawo ɗaki ya ɗauko food carrier ya dawo da shi palour ya san ta kusa kammala gyara palour, ya zauna ya zuba yana ci ta fice zuwa ɗakin shi, a nutse ya gama breakfast ya mik'e ya fito tare da cewa
"Malama na tafi"
A ranta ta ce "Malama kuma?" A fili ta ce
"Allah ya kiyaye hanya"
"Amin"
Ya faɗa ya fice, ta kammala gyara wajen sannan ta koma restaurant.....
****
Ta iso wajen as usual ta tadda suna zaune, a hankali ta iso basu an kare ma, ta ce
"Morning my friend's"
Aiko da murna suka mik'e suna
"Oyoyo kyakkyawar Aunty"
Suka rungume ta, ta ce
"Shikenan kowa ya zauna"
Suka zauna, gaisuwa aka fara sannan ta raba musu Alawa da biscuit, suna sha suna hira, Haneef ya ce
"Yau ma uncle ba zai zo ba?"
Ta ɗan yi jim ta kalli hanyar da yake ɓullowa taga ba alamun sa, ta ce
"Ina ga aiki ne ya riƙe shi"
"Mun yi kewarsa"
"Haneef shi ma ya yi kewarku"
Sun jima a zaune tana kwantar musu da hankali har suka tafi, ita ma ta mik'e ta bar wajen.
********
8:00 pm Bilqees tana zaune a kitchen ta kammala aikinta, Alaja ta shigo tare da cewa
"Yawwa Bilqees, ki shirya abinci a food carrier ki kai masa abincin"
"Ma waye maa?"
"Ok so ki ke yi na sake miki bayani daga farko"
"A'a Maa a ina zan kai?"
"Cikin international hotel mana"
Tana faɗin haka ta rubuta room number a jikin, Bilqees ta mik'e ta shirya masa abincin, ganin room number kusan na Yallaɓai likita ne yasa ta tafi kai tsaye tana isowa ta tsaya a bakin ƙofar ta yi nocking idanunta akan side na Yallaɓai likita, aka buɗi ta shiga ba tare da ta kalli me ɗakin ba, kawai ta ajiye kamar yadda suke yi don da ta shigo ma bata ga wanda ya buɗe mata ƙofa ba. Ta juyo don komawa restaurant idanunta suka sauƙa kan wannan mutumin da ya kusa yi mata fyaɗe a ɗakin Yallaɓai likita.
Baya ta yi tana waro idanuwa waje, gabanta ya bada ras, tsoro ya kamata amma ta dake tare da cewa
"Abinci na kawo maka"
Murmushi ya jefa mata yana lashe bushashun laɓbansa yana zura mata jajayen idanunsa ya tako zuwa inda take tare da cewa
"Na gode da hidima"
"Uhm zan tafi"
"Ki tsaya tukuna"
Bata tsaya sauraron shi ba tayo bakin ƙofa tana ƙoƙarin buɗe wa amma gam ƙofar a kulle, key dake jikin ta soma murɗawa ya fizgota ta yi baya zata faɗi ya dawo da ita a tsorace ta ce
"Meye haka Yallaɓai?"
"Ba ki sani ba? To zan nuna miki"
Ya riƙe hannunta yana murzawa da ƙarfi tana jin raɗaɗi har cikin ranta ta tattaro ƙarfinta ta wanke shi da mari da ɗayan hannunta tare da janye ɗayar ta ce
"Wato sai da ka san yadda ka yi ka sayi Alaja don ta turo maka ni, to kayi kaɗan....
Wawan mari ya kwasheta dashi sai da ta yi baya ta haɗe da jikin bango tana sauke numfashi ta dafe wajen...
"Ke don kin ga ina bin ki cikin lallami shine kike wani ja min rai, to ko mutuwa za ki yi sai nayi, yau babu me ƙwatarki a hannuna, ko kin yi ihu babu me ji"
Da ƙyar ta mik'e tana ganin dishin² ta sake zuwa bakin kofa kan ta ƙarasa ya damƙota ya jefa kan bed ƙafarta ta buɗe ta saka ƙara sabar raɗaɗi da azaba, don rashin imani ya hayo kan bed yana ƙoƙarin cire mata kaya ya rabata da hulan kanta gashinta ya bayyana ya sake haukacewa ya damƙota yana ƙoƙarin cire mata rigar uniform nata, ta tattaro ƙarfinta ta ture shi ya faɗo daga kan gadon ya buge da bedside ya saka ƙara, ta sauƙo da ƙyar take iya tafiya ga jini na zuba tayo bakin ƙofa ta murɗa key ta buɗe, ya yo kanta kamar zai cef ke ta amma bai samu dama ba ta faɗa jikin mutum tana neman a ceceta.
A tsorace ya yi baya jin mutum ya faɗi jikinsa yana duba fuskar yaga Bilqees ce, kan ta yi magana kuma numfashinta ya tsaya, cikin tashin hankali ya kalli inda ta fito kan ya yi wani yunƙuri da sauri ya rufe ƙofar, ɗakinsa ya dawo da ita ya kwantar da ita kan carpet ya yi mata matashi da pillow, yana ƙoƙarin ceto numfashinta amma abu ya gagara, ya ɗan zauna tare da dafe goshinsa yana jin ɓakin ciki da takaici me ya kawo ta a wannan lokacin? Ganin jini da yake bin ƙafarta yasa ƙirjinsa sananta bugu, ya riƙe ƙafar yana dubawa idanunsa suka sauƙa kan sarka dake ɗaure a ƙafarta gaban sa ya faɗi yana tuno a ina yaga irin wannan sarkan?.....
Ayi hakuri da typing errors
Comment and share fisabilillah