MATAR GIDA PAGE 47
MATAR GIDA*047
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P47
Cike da ɓacin rai Ɗalha ya wuce ɗakin Unaisa tare da ɗaukar jakar kayansa da ya shigo da shi ɗazu,ɗakinsa ya wuce,bayan shigarsa ɗaki saif ya buɗe tare da sa jakar da yake riƙe da shi a ciki,jiki babu kwari ya rufe kofar saif ɗin daga haka ya samu waje ya zauna bakin gado yana dafe kansa zuciyarsa cunkushe da takaici,Unaisa kullum ƙara basa mamaki take,wai a ce mijinki ya maki siyayyar kayan abinci ki kwashe ki ba ƙawaye,Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina goma zaune bakin gado yana tunani kan halaiyyar Unaisa can dai ya tashi ya shiga bathroom ya yi wanka,bayan fitarsa shirya kansa ya yi cikin wasu riga da wando jeans, yau ya kasance ranar hutu ce garesa, dalilin zuwa training a legos yasa an basa hutun kwanaki biyu Alhamis da juma'a ya so ya kwanta ya huta amma ya ji sam bazai iya zama gidan ba dalilin ɓacin rai da Unaisa ta cusa masa,bayan fitarsa ya tarar Unaisa bata parlourn,hannusa riƙe da waya yana duba lokaci karfe goma da mintina ashirin na safe,ɗaya hannunsa riƙe yake da makullen mota,ya fita daga parlour zuwa compound inda ya yi parking motarsa,buɗe motar ya yi tare da kunna daga haka ya je ya buɗe gate daga haka ya koma ya fitar da mota kafin ya kulle gate ɗin gidan,kofar wani eatry ya yi parking mota kafin ya fita daga mota ya shiga eatry bayan shigarsa ne ya samu waje ya zaune tare da yin order breakfast ba shi ya bar eatry ɗin ba sai misalin ƙarfe sha ɗaya da wasu ƴan mintina,tafiyar mintina talatin ne daga eatry zuwa Company da yake aiki,parking motarsa ya yi a harabar kamfani,ba tare bata lokaci ba ya wuce ofishin sa bayan shigar sa zama ya yi yana sauke ajiyar zuciyar idanunsa lumshi ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune a kai,ya dauki a ƙalla mintina uku zaune a haka can ya ji ana buga kofar ofishin a hankali ya buɗe idanunsa tare da gyara zama kafin ya ce ''yes come in'' Muhsin ne ya shigo fuskarsa dauke da murmushi yana ƙarewa Ɗalha kallo shi dai Ɗalha kallon Muhsin kawai,zama Muhsin ya yi kan kujerar da aka tanadar dan baƙi yana miƙawa Ɗalha hannu tare da faɗin ''ango kasha khamshi'' ba yabo ba fallasa Ɗalha ya miƙa masa hannu suka yi musabaha ''me ka zo yi kamfanin kai da aka ba hutun kwanaki biyu?" numfawa Ɗalha ya yi yana mayar da dubansa ga Muhsin dake duba wani saƙo a wayarsa kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ''ya ku ke ya aiki?" Muhsin ya ajiye wayar hannusa kan tebur ɗin Ɗalha ya ce ''gamu nan aiki mun gode Allah''...shiru Muhsin ya yi na wasu ƴan sakanni yana ƙarewa Ɗalha kallo kafin ya ce ''ya na ganka haka kamar baka da lafiya ko dai duk gajiyar hanya ce?" ''lafiya ta ƙalau l'm just tried'' cewar Ɗalha kallon mamaki Muhsin ya yi masa kafin ya ce ''you are tried,daman wa ya ce ka zo aiki kai da aka bawa hutu amma ka kama hanya ka zo aiki yanzu ka ce you are tried'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ba gajiyar jiki nake nufi ba'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''Unaisa ce ta caza min kai'' bai kai ga idah zancen sa ba Muhsin ya ce wata Unaisa wacece kuma Unaisa?" ya kare magana fuskarsa cike da mamaki gyara zama Ɗalha ya yi tare da ɗaukar biro dake daure kan wata littafi dake kan tebur ɗinsa ya ce ''Unaisa dai wacce ka sani,yarinyar da na aure sati biyu da suka wuce'' gyara zama Muhsin ya yi yana ma Ɗalha wani irin kallon raini wayo ya ce ''mallam yaushe a ka yi dare gari ya waye? aure ko wata ɗaya baku yi ba ka fara ƙorafi dan Allah kar ka bani kunya kai da ka auro wayayya mai tsafta wacce ta san abinda take ba irin Amirah ba'' murmushin da ya fi kuka ciwo Ɗalha ya yi tsaf ya gane inda kalaman Muhsin suka dosa amma sai ya basar kawai ya ce ''pls man be seroius bafa zancen wasa nake maka ba'' Muhsin ya ce ''na sani amma aiy ya yi wuri a ce tun yanzu ta fara baka ciwon kai,naga ko amarci baku gama ci ba,abinda yafi bani mamaki shine zuwan ka aiki yau,ina zaune a ofis Mubarak ya ce min ya ga wucewarka kana ofis ɗin ka na ce masa ba kai bane amma ya dage ya ce lallai kaine shine fa na zo naga kuma da gaske kai ɗin ne''
Gyara zama Muhsin ya yi a karo na babu adadi ba ƙaramin mamakin Ɗalha yake ba yadda Ɗalha ya nuna wa Unaisa so da kauna kafin aurensu sannan ya gama yarda cewa Unaisa mace ce ta gari kuma ita zata fi dacewa da shi kan Amirah sai kuma gashi ko wata ɗaya basu yi da aure ba ya fara ƙorafi kan halaiyarta ''tun bayan auren ka da yarinyar nan kusan kullum sai mun yi waya amma baka taɓa faɗa min kana cikin damuwa ko wani abu makamancin haka ba ka ga kuwa dole na yi mamaki'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya fara bawa Muhsin labarin zamansa da Unaisa a Kano har kyautan kayan abinci da ta rabawa ƙawayenta Ɗalha ya faɗa masa komai,rashin lafiyar Unaisa ne kaɗai Ɗalha ya ɓoye bai fadawa Muhsin ba a tunanin sa wannan sirrin su ne,tun sanda Ɗalha ya fara magana Muhsin ke kallonsa cike da mamaki gani yake kamar ba gaskiya bane,a tunaninsa wasa Ɗalha ke yi,ya za a yi yarinyar da aurensu bai yi ko wata ba a ce ta fidda salon ƙazanta iri daban daban ina laifin ta bari sai ta fara laulayi kafin ta fidda wasu halaiyarta,Muhsin ya dauki sama da mintina goma yana nazari kan maganganun da Ɗalha ya faɗa masa kan Unaisa, can ya ɗago ya mayar da dubansa ga Ɗalha ganin fuskar Ɗalha cike da tsantsan damuwa da kunci yasa Muhsin yarda da maganganun da Ɗalha ya faɗa masa, in ko haka ne to tabbas hakkin Amirah ke binsa Amirah yarinya mai kirki ga ladabi da biyayya amma Ɗalha ya rufa ida ya riƙa mata rashin mutunci,duk waɗan nan zantuka cikin zuciyarsa yake yi,gaba ɗaya Muhsin ya rasa abin faɗa kawai ya ce ''Allah shi kyauta'' shiru Ɗalha ya yi kafin ya daura da ''tun da nake da Amirah ban taɓa faɗa ta faɗa ba shekararmu goma da aure duk yadda zamu kai ga samun saɓani ni da Amirah bata taɓa faɗa min baƙar magana ba duk yadda ranta ya kai ga ɓaci bata taɓa nuna min ba abu ɗaya ne in ta yi nake gane tana fushi da ni,shine gaisuwar safe da take haɗa kan yara su zo har ɗakina su gaida ni to in na ɓata mata rai sai dai ta zo ita kaɗai yaran su zo daga baya wata rana ma basa zuwa ita kam kullum sai ta gaida ni'' taɓe baki Muhsin ya yi kafin ya ce ''mace ta gari kenan wacce ta san darajar aure'' wayar Muhsin ce ta yi ƙara alamar shigar saƙo mayar da dubansa ya yi ga fuskar wayar ya dauki a ƙalla sakan biyar a haka kafin ya ajiye wayar yana mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''ga wata muguwar kazanta,ni fa ko a flim ban taɓa ganin ƙazama irin matarka ba tsakanin da Allah har brush..brush dai wannan bawan Allah ka dage da addu'a ka kuma nime yafiyar matarka shine kawai'' shiru Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ta ce ta yafe min'' ɗage kafaɗu Muhsin ya yi kafin ya ce ''ok sai ka dage da istigfari'' murya can ƙasa Ɗalha ya ce ''insha Allah''shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni murya can ƙasa Ɗalha ya ce ''zan sama mata islamiyya ta fara zuwa saboda ga dukkan alamu bata san me ake nufi da aure ba,a takaice ma bata san abinda take ba gaba ɗaya'' Muhsin ya jinjina kai kafin ya ce ''gaskiya kam ya kamata ta fara zuwa Allah ya ganar da ita'' a hankali Ɗalha ya ce ''ameen'' shiru ne ya biyo baya kowanne su da tunanin da yake,da wani irin sauri Muhsin ya mayar da dubansa ga Ɗalha kamar wanda ya tuna wani abu yana kallonsa,shima Ɗalha shi yake kallo kafin ya buɗa hannu alamar tambaya ya ce ''what'' wata iriyar shu'umar murmushi Muhsin ya yi kafin ya ce ''ko dai ka hango wata ce ka ke son ƙaro ta uku'' wani mugun kallo Ɗalha ya jefa wa Muhsin ba tare da ya sake cewa komai ba ya buɗe laptop ɗinsa ya fara aiki dariya ne ya kawfcewa Muhsin da ya tuna wai Unaisa ba ta yi flushing ba har na tsawon kwanaki biyu nan ya shiga babbaƙa dariya har da riƙe ciki sai da ya yi mai isarsa kafin ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''ikon Allah haka taka amarci ta zo maka'' yana gama faɗin haka ya cigaba da dariya shi dai Ɗalha bai tanka sa ba
Bayan fitar Ɗalha Unaisa ta fito daga ɗaki ta daura indomie,ba ta bar kitchen ɗin ba har saida indomie ya nuna, plate ta samu ta juye kafin ta wuce ɗaki,bayan ta gama ci kwanciya ta yi kamar yadda ta saba ta shiga chating har karfe biyu na rana tana nan kwance riƙe da waya daga whatsApp ta shiga facebook daga nan ta wuce tiktok haka dai ta riƙa yi daga karshe bacci ya dauke ta,ba ita ta farka ba sai karfe uku a firgice ta buɗe ido ganin lokaci ya ƙure gashi bata yi gyaran gida da Ɗalha ya ce ta yi ba hatta ɗakinta bata gyara ba sanin kanta ne huɗu yake tashi a ofis zuwa biyar ya dawo gida gashi ko sallar azahar bata yi ba,yunƙurawa ta yi tare da sauka daga gado wayarta ta dauka ta kashi data nan ta fara tunanin abinda ya kamata ta fara yi bayan wasu ƴan mintina ta wuce kitchen morper ta dauko kafin ta dawo ɗakinta,sharar ɗaki da parlour da morping ya dauke ta sama da awa guda tun karfe uku da fara ba ita ta gama ba sai karfe huɗu da rabi ta haɗa zufa kamar wacce aka bawa babban aiki, dake bata saba yi a gidansu ba siminti ne a gidan mahaifinta bata kuma damu ta koya ba hakan yasa
ta wahala sosai,pot ɗin da ta dafa indomie da plate ɗinda ta yi amfanin da su bata yi wahalar wankesu ba haka ta barsu da datti,bayan ta gama morping bathroom ta koma tare da wanke hannunta kafin ta dauro alwala nan ta shiga jero salloli azahar da la'asar bayan ta idar ta cire hijab da wani irin sauri ta yi wurgi da shi saboda yadda take jin zufa gaba ɗaya ta haɗa zufa yunƙurawa ta yi tare da kunna fankar sama,dai dai lokacin da fankar ta fara hura iska ta sauke ajiyar zuciya,zama ta yi kan darduma tana sauke ajiyar zuciya a hankali, wani irin yunwa ne ya fara ɗawainiya da ita hakan yasa babu shiri ta tashi ta wuce kitchen bayan shigarta kitchen ta dauki a ƙalla mintina biyu tsaye tana tunanin abinda zata dafa can dai ta wuce pantry ta dauki indomie da wani sabon pot ta ɓare daga leda kafin ta daura kan wuta kamar ɗazu bata bar kitchen ɗin ba saida indomie ya dahu daga haka ta juye cikin plate kafin ta wuce ɗakin,Ɗalha bayan ya tashi daga ofis shoping mall ya wuce ya siya kaji biyu da namar rago kilo biyu,tun ɗazu yake son kiran Unaisa ya ji me ta dafa sannan ko tana bukatar nama amma bai samu damar kiranta ba saboda aiki ya masa yawa,a hanyarsa ta dawowa gida ne ya haɗu da yaran almajirai da suke zubar masu da shara, paka mota ya yi, cike da girmama suka gaida Ɗalha amsa masu gaisuwar ya yi kafin ya ce da su gobe da safe su zo gidansa su yi masa shara,cike da girmama suka amsa masa
SHUUKRAN