MIJIN AMAL

Chapter 2

by @sreza12

MIJIN AMAL 

S-Reza...✍️

Chapter 2
Daidai ya kusa shiga unguwar su yaga motar yayansa zai shigo unguwar. Kallo ɗaya yayiwa motar ransa ya ƙara ɓaci. Shi sam ya tsani yaga wannan mutumin a hanyar gidan sa wallahi. Hakan yasa ya tsaya ya faka mashin ɗin saboda baya so ya ƙarasa gidan . Ya fito ya ce "Dama yanzu gidan ka zanje sai gaka". Yasir ya gaida shi ciki-ciki yana kawar da kai. Sosai yake Kunyar haɗa ido da shi. (Daga shi sai Salim suka suka rage 
Allah yayiwa uwa da uban nasu gaba ɗaya rasuwa. A cikin gadon su ne ya tsira da gidan da yake ciki da kuma shagon sa. Salim ya fishi rufin asiri sosai, hakan yasa yake son taimaka masa amma Yasir baya so dalin irin sana'ar sa ta neman maza da yake yi, wanda tun yana ɓoye wa har Yasir ɗin ya kama shi dumu-dumu taɓarya da taɓarya. Tun daga nan kuma Salim ɗin ya daina ɓoye masa, kuma ko a jikinsa. Dama kuma masu irin wannan halin basu jin kunyar uban kowa.) Ya ɗan tsaya nesa da shi ya ce "Na gode Allah ma da yasa baka je gidan ba". Salim yayi murmushi mai sauti ya ce "Har ta kai haka Yasir?" "Yanzu dai meye kake nema na?" "Takardun ka zaka je ka kwaso min, kasan mune masu garin, gaba ɗaya manyan kasar mune gadon barcin su, to shine na bi ta irin hanyar alfarmar da muke da ita na sama maka aiki a guri mai tsoka. Dama tun ba yanzu ba nake maka shiri, yanzu dai an samu, kuma ka ajiye wannan bakar zuciya da ra'ayin nan naka ka zo ka samu aiki ka rabu da wannan kallace-kallacen banzan da kake yi". Ya karasa yana nuna shi. Yasir ya ce "Ham Yaya kenan! Wallahi muddin ta irin wannan hanyar zan samu aiki gara na rayu na mutu a haka. Aikin da za'a bani ba dan na chanchanta ba, kuma ina aikin ana min kallon ƙanin wanda ake kwanta..." Sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa. Ya girgiza kai kawai. Salim ya ce "Bari na karasa maka, ake kwantawa da shi ko? Ai dama nasan halinka, Allah ya gani irin kokarin da nake yi da kai, ko na mutu Allah ba zai tambaye ni a kanka ba, ko su Abba ba zasu ce na samu na manta da kai ba". Yana faɗa ya shiga mota, sai kuma ya fito da kansa ya ce "Zansa Maryam tazo gidan ka, ta fadawa Amal, nasan idan ita tai maka magana zaka ji". Ya na faɗa ya bar gurin da sauri. Sai da yayi nisa kafin ya tada mashin ɗin sa ya karasa unguwa.

Amal na Palo lokacin ta sake wanka ta saka riga da wando shima ta fito masa da wanda zai sa irin nata tun kafin ma ya dawo. Zamanta kenan ta jiyo kamar muryar mamarta. Hakan yasa sai da gabanta ya faɗi. Har ga Allah bata son tana zuwa gidan nan sam. "Ko ba kowa a gidan ne?" ta tsinkayayo muryar mamar tana magana. Hakan yasa ta je da sauri ta dauko hijjabi ta ɗora a kan kayan jikinta ta buɗe tana mata barka da zuwa. "Yar iskar yarinya ashe kina kusa kina jina har sai makofta sun san nazo gidan ki ko? To uwar meye a cikin gidan naki ma da har zaki rufe sai kinga dama zaki buɗe. Wannan akulkin gidan da bai fi ɗakin mai gadi ba, shine akewa wannan tsaron".

"Mama wallahi ban ji bane bafa sai yanzu, ke kuma kina ta faɗa" "To dama yaushe zaki ji, an ƙulleki a wannan tsukukun gidan kamar ramin mutuwa, to ba wata uwar ce ta kawo ni ba, dubu biyar nazo ki bani na cika na biya masu mana gyaran masai. Yanzu suna cen wai sai dubu sha biyar, Allah yasa a kwai sauran kuɗaɗen da Fati ta bayar dubu goma, shine nace bari nazo gurinki, da ita zan turo ma, nace gara dai nazo da kaina kafin ki kira mata babu kamar a gidanku aka yanke mata cibiya". Ta ƙarasa tana bin Palon da kallo tana neman abun zagi. Tayi shiru tana ta addu'a a ranta Ubangiji ya ƙwace ta domin dai wallahi ko biyar bata maganinta, kuma tana cewa bata da shi, to da ita da Mijin nata sun shiga ashirin da zagin tsamar nama. "Dan ubanki ba dake nake bane kin barni tsaye kamar wata mabaraciya, ko baki ji nace Fati ce ta bada dubu goma ba, shine ke a matsayin ki ta babba ance ki bada dubu biyar kike zare ido kamar an ritsa barawo. Ina amfanin auran matsiyaci ɗan iska mara aikin yi, wanda idan abun kunya ya taso ba zai iya maka magani ba". Ta ce "Amma mama kin san bana fa sayar da komai, kuma..." "Kuma uwarki ba, ta ina zaki ma iya sayar da komai ɗin kina tare da wannan matsiyacin yaron, ni dai Allah wadai da wannan auran wahalar, yanzu za'a samu ne ko na ƙara gaba?" "Wallahi Mama bani da ko nera biyar". "To shi matsiyacin fa idan ke baki da?" "Mama ai baya nan". "Na sani ai, to ki laluba kayansa mana ko ya ajiye?". Ta faɗa da gaskiyar ta. Amal ta waro ido waje domin idan Yasir na da shi ta sani, haka idan bai da shi tafi kowa sani. Ta ce "Wallahi mama shima bashi da shi, da yana da shi da..." "Allah ya tsinewa wannan babun naku Amal, wannan aure dai ya zama auran tsiya da asara da tsiyatakewa". Tana faɗa ta nufi kiching ta na cigaba da masifa kamar zata ari baki. Kuma fa wannan fadan wallahi ko a gaban Yasir ne haka take yi, har ma fiye da hakan amma bai taɓa sauya min ba, nakan nuna damuwa amma idan ya faɗa min wata kalma da yake yawan faɗa kan iyaye sai na kafe shi da kallo ina sake godewa Allah da ya bani shi. Ta biyota a baya tana ta addu'ar Allah yasa ta bar gidan nan lafiya bata mareta ba.

Wallahi wannan sauran taliyar guda biyun da ita kaɗai ta rage mana a gidan namu ta kwashe ganin bata samu komai ba. Ta ce "Ba zan zo na fita hannu rabbana ba wallahi, duk da dai haka kike so, amma dai wannan auran naki Amal da shi gara babu a gurina". Amal dai tayi shiru har ta rakota ƙofar gida ta fita. Ta dawo ta rufe gidan ta cire hijabin jikinta tana godewa Allah da ya bata miji mai fahimta irin Yasir. Ta zauna a palo tana ta tunanin yadda Mama bata ganin irin farincikn da take ciki, ita dai damuwarta auran mai kuɗi, kuma ita anan ɗin ma bata rasa Komai ba, ga kuma kulawa da farincikn da tasan ba a kowane gida za'a iya samu ba. Sai kuma ta fara wani tunani akan da ace Yasir nada kuɗi zai bata irin wannan kulawar kuwa, anya kuwa. Ta sauke ajiyar zuciya ta na tashi ta dauko wayarta domin ta kira taji ko yana ina ne. Tana buɗe wayar taga kiran ƙawarta har uku. Tayi dariya a fili tana tuno hirarsu ta karshe da ita a waya jiya akan wai ita abokin Yasir take so Ali. A fili ta ce "Hafsa kenan Sarkin soyayya". Har zata kira number Yasir ɗin sai ga kiran Hafsa ɗin ya sake antayowa. Ta ɗaga da dariya. "Idan kin gama dariyar gani a hanyar gidan ki, banza mara mutunci kawai". Tana faɗa ta kashe wayar. Tabi wayar da kallo tana mamakin da gaske fa yarinyar nan take. Kafin ta kai ga kiran sa taji ana buga ƙofar gidan. Daga Iya yanayin buga ƙofar ma kawai ta san shine, duk da bata ji ƙarar mashin ɗin sa ba. Hakan yasa ta tashi da sauri ta nufi Kofar ta buɗe suka haɗa ido. Da sauri ta faɗa jikinsa tana masa barka da zuwa. Ya rungume ta yana kwantar da kansa a wuyanta, yana shaƙar karmshin da ke fita daga jikinta. Sosai haushin da ya kwaso suke barin jikinsa har sai da ya ji shi wasaii. Ya ce "Nayi kewar mata ta kamar na shekara bana gari". Ta ɗago daga jikinsa ta kalleshi ta ce "Nima fa ji nake Kamar na tashi nazo shagon, duk gidan ba dad'i idan babu kai". Ya lakuto kumatunta ya ce "Tom yanzu ai gani, mai dame aka tanadar min?" Ta kama hannun sa. Ta ce "Na ɗaya dai shine muje nayi maka wanka, na biyu kuma na shafa maka mai, na sa ma kaya, na uku kuma muzo muci abincin da na girka mana mai daɗi da manɗon da baka taɓa cin irinsa ba, na huɗu kuma muje gado nayi maka tausa har sai kayi barci gajiyar nan da ka kwaso duk sun gudu". Ta faɗa suna shiga cikin uwar ɗakin. Yasir ya ce "Baki faɗi na biyar ɗin ba mai muhimmancin daga ciki". "Ai shi wannan ba sai an faɗa ba, kawai aiwatar wa ake yi". Ta na faɗa ya jawo ta, ta faɗa jikinsa, ya haɗe bakinsu guri guda. Kusan minti ɗaya kafin ya sake ta yana cigaba da kallonta. Ta ce "Kallon fa, ko na sauya maka ne?" Ta faɗa tana ɗaga masa gira. Ya ce "Eh, kullum ma sauyawa kikeyi, wai meye sirrin ne Amali?" Tayi far da ido domin tana so ya kirata da wannan sunan. ta ce "Kaine sirrin mijina, kana bani ci da sha da kulawa da soyayya, ai kaga dole na sauya". Ta na faɗa tana kokarin cire masa riga. Har ta cire sannan ta fara zame masa dogon wando. Ta cigaba da cewa "Duk macen da ta samu miji irinka to ba ma iya sauyawa ba, har natsuwa da hankali sai ta kara". Tana faɗa ta kamo hannunsa suka shiga cikin toilet ɗin da yake uwar ɗaka. Itama ta cire kayanta, dama tun tuni ta kai ruwa bayi, da yake lokacin zafi ne yasa bata buƙaci na zafi ba. Kafin a fara wankan sai da aka sha love kamar ba za'a bari ba, sannan ta shiga wanke abunta tass, shima ya wanke kayarsa suka fito. Ta dauko masa wata bakar jallabiya ta saka masa, itama ta saka tata, kasancewar duk kayan da ya saya to itama tana da irinta, ko taƙalmi ne to dole sai ya sayo mata irinta. Bayan sun saka ya ce "Kin saka komai a chaji dai ko? Kin san yau wasanmu mai zafi ne muda yaran nan Evarton, suna bamu ciwon kai wallahi, kar sai muna kallo nefa su ɗauke wuta?" Ta ce Ai ana kawo wuta abun da na fara yi kenan". Ta amsa masa suna zama a kasan Palon kamar yadda suke yi duk lokacin da zasu ci abinci. 

Ta ɗauko kular abincin ta ajiye a tsakiyar su, ta ɗauko plet guda ɗaya, taje firiza ta dauko ruwa guda biyu. Ya ce "Wai me kika dafa ne haka tun kafin a buɗe ƙamshi ke min maraba?" Ta ce "Idanunka zasu gane maka yanzu ai". Ta na zama suka ji ana buga ƙofar gidan nasu. Suka kalli juna, gaban ta ya faɗi domin tunanin ko Mama ce ta dawo, shi kuma yana tunanin ko Maryam ce matar Yay Salim da yace zai aiko ko kuma Ali ne ya biyo bayansa. Har ta tashi zata nufi gurin ya ce "No dawo, shiga ciki bari na ga waye tukunna". Ta miƙe ta shige ciki shi kuma ya nufi Kofar ya buɗe yana kallon ta. Ya ɗan sakar mata murmushi itama haka ya bata hanya ta shigo. Ya shiga cikin ɗakin ya ce ta fito Hafsa ce. Sai lokacin ma ta tuna ashe fa ta ce mata tana hanya. Ta ce "Shet na manta ne fa, dama tace min tana hanya, amma duk shigowarka gidan ka mantar dani komai". Ya ce "Ai nima ina da abun da zan faɗa miki amma duk kin sa na manta da komai". "Ai kuwa sai ka tuna ka faɗa min". "Bayan na manta ɗin ai ba zan iya tunawa ba muddin ina tare da ke, domin bana ji bana gani a lokacin da muke guri ɗaya". "Tom yanzu idan na mutu yaya za..." Ai kafin ta karasa ya sa hannu da karfi ya toshe mata baki gami da matse bakin har sai da numfashi ya gagare ta shaƙa. Ya sakar mata har idanunsa da nata sunyi ja. Ya ce "Bana son jin wannan maganar daga bakinki, kar ki ƙara". Yana faɗa yayi waje ya barta tana tari. Ta ja numfashi da karfi tana jinta kamr taje wata duniyar ta dawo. Ta bi bayansa ta same shi zaune suna gaisawa da ita. Ta kalleshi a sace taga ya dawo yadda yake. Ta koma kiching ta ɗauko wani plet ɗin. Ta fara zuba nasu ita da shi. Kafin ta zubawa Hafsa tana kallon shi. Hafsa ta ce "Kin dai fi kowa sanin taliya ba abinci na bace ko?" "To wannan ai ba taliya bace, wannan sunanta jalof ɗin taliya da wake". Ta faɗa tana ci gaba da zuba mata duk da kuwa ta fi kowa sanin bata ci ɗin. "Ba cinyar ba ƙafar baya iji ɗan Gwari". Ta turo mata, sai ta yi tsaki tana faɗin "ko da ina jin yunwa ma ba zanci ba bare a koshe nake, kin dai san abin da ya kawo ni". Yasir ya ce "Ko dai saboda ba kifi ko nama ne yasa?" Ta ce "A'a wallahi, ita ai tasan bana ci". "To bari mu gama ci sai na baku guri ko?" Ya faɗa daidai sun fara cin abincin. Amal ta ce "Ai gurinka ta zo". Ya ce "Ni Yasir?" "Eh kai mijin Amal". Ta bashi amsa suna dariya gaba dayansu. 

Ita dai Hafsa tana mamakin irin son da Yasir yake wa Amal. Tun tana jin kunyar wani abun idan tazo gidan har ma ta daina. Ita kanta saboda abotar dake tsakanin su ba karamin mutuncinta Yasir ɗin yake gani ba. Kuma yana daga cikin dalilan da yasa take son Ali saboda abokin sa ne, tasan ko ba komai dai ba zai rasa wasu daga cikin halayyar sa ba. Dama kuma masu iya magana sukance idan kana so ka gane waye mutum to ka kalli abokansa. Yasir ya ce "Tom Allah yasa dai ba laifi nayi ba". Hafsa tayi murmushi ta ce "Za dai kayi ɗin idan baka bada goyon baya ba". "Tofa!" ya faɗa yana mamakin abun da zai sa ta neme shi. Nan suka fara cin abincin da chokali ɗaya idan yaci ya bata taci, har suka cinye. Ta bashi ruwa ya fara sha kafin itama ta sha. Ta kwashe kwanukan shima ya tashi zai tayata Hafsa ta ce "A'a bari na je mu gyara sai mu dawo". Ya kalli Amal ya ce "Zata hana ni ladan yau". Ta ce "Nima dai yau na hutar da kai tunda ga ta tazo". 

Suna shiga kiching  ta ce "Kina ganin kuwa zai taimaka min?" "Mai zai hana, ke dai bari muje, ai bama iya taimakawa ba, har dole sai ya masa muddin kin faɗa masa". Nan suka gyra komai, sosai Amal ke son faɗawa Hafsa halin da take ciki na kwashe abincin da Mama tayi, wanda kuma abincin da zasu ci gobe da jibi kenan. Sai dai kuma Yasir ɗin ya hana ta shering ɗin matsalar gidan su da kowa sai shi, kuma tasan idan tai mata maganar zata samu ko 2k ne a gurinta, amma dai tayi shiru ta daure duk yadda maganar ke cinta a rai. Ta bari akan Allah zai kawo mata mafita. Lokacin da suka fito sun samu ya ɗora laptop din sa a cinya yana dannawa. Yana ganinsu kuwa ya ajiye ya basu hankalinsa. 

Bayan ya gama jin abun da ke tafe dasu. Sai ya ɗan yi jim kaɗan. Ya ce "Ali dai abokina?" Ta ɗaga masa kai. Ta ce "Wallahi ba ina sonsa dan komai nasa bane, saboda Allah nake sonsa, kuma ba zan iya zuwa na faɗa masa ba, shi yasa na biyo ta gurinka". Ya kalleta, sai yayi murmushi ya ce "Amma kin san yana da mata ko?" "Eh harda yara biyu, duk na sani". Ta ƙarasa masa tana kallonsa. Ya kalli Amal ya ce "This is seriously,". Sai ya fara tunanin abun yi. Hafsa dai kam ko shi zaiyi shedar ta wajen natsuwa, amma Ali fa, ina sam bama zai bari hakan ya faru ba. Ya ce "Okay tom karki damu, in sha Allah zan masa bayani, zaki ji komai a gurin Madam". Ta amsa da godiya ta tashi zata tafi. Amal ta rakata har ƙofar gida. Bayan ta dawo ta samu ya cigaba da abun da ya keyi a laptop. Ta dawo kusa da shi ta ce "Dama dai abun bai ɓata maka rai ba ko?" Ya ce "Bai ɓata min ba, sai ma murna da na taya Ali. Amma bari nai miki wata tambaya?" Ya faɗa yana ajiye laptop ɗin. Ta ce "Ina jinka". Ya ce "Mai yasa sai nine zan faɗa masa, idan har da gaske tana sonsa ai gara taje ta faɗa masa ba tare da ma na sani ba, kin san kuwa yadda Aisha take ganina da mutunci (Wato matar Ali) sai kawai taji labarin nine na kawo wacce za'a mata kishiya da ita". Amal ta ce "To ai bazata sani ba, kawai fa faɗa masa zakayi sai kawai ka barsu da kansu". Ya ɗan yi dariya ya na sake rugumeta ya ce "Amali kenan mai tunani irin na yara, kin san kuwa tsakanin mata da miji, to ki ɗauka ko wasu ma'aurata kamar yadda muke, suma basa ɓoyewa juna komai, dole watarana zai faɗa mata, kuma ba zata ji dadi ba, kuma fa Kamar kece yanzu da kike ganin Ali da mutunci sai kawai nazo nace miki Amal ai yanzu zuwa na shagon Ali wata ya nuna min wai tana sona kuma na aureta. Dan Allah yaya zaki ji". Ya na faɗa gabanta ya bada wani irin sauti kamar tsawa a lokacin ruwan sama, wallahi idan batayi karya ba har wani abu mai kamar yaji-yaji taji a cikin zuciyarta na tsoro...📝 



Duk mai son karanta complete su shiga Channel dina a sama.