Chapter 4
by @umsar
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
AREWAPEN: umma mustapha
WATTPAD:umma mustapha
PAGE 4
GIDAN ALHAJI IBRAHIM KWALLI, DAKE JIHAR KANO
Babban gida ne wanda ya shahara a cikin Jihar Kano. Mutum ne da mutane suke ba shi girma da daraja sosai, kasancewarsa dattijo mai sanin ya kamata, kuma malami mai kiyaye dokokin Allah.
Alhaji Ibrahim mutum ne mai taka-tsantsan, mai tsananin ƙin abin duniya. Bai kasance mai son tara dukiya ko nuna abin da yake da shi ba. A gare shi, abin da ya fi komai muhimmanci shi ne tsoron Allah da kyautata wa mutane.
Ya kasance mutum ne da jama'a suke mutuntawa saboda kyawawan halayensa da yadda yake tafiyar da rayuwarsa bisa koyarwar addini.
Alhaji Ibrahim tsohon malamine a jami'ar Bayero university.
Alhaji Ibrahim ya rasu, ya bar mata biyu da 'ya'ya goma sha daya.
Daga cikin matansa akwai Hajiya Aisha, wadda yaran gidan suke Kira da Hajiya Babba. Tana da 'ya'ya bakwai.
Daga cikinsu akwai Abubakar, shi ne babba. Sai Umar, wanda yake bi masa, sai Usman, Aliyu, Jafar, Asiya,sai autarsu wato Hafsah, wadda ta ci sunan kakarsu,mahaifiyar mahaifinsu. Saboda haka suke mata laƙabi da Nihla.
Sai kuma ɓangaren matarsa ta biyu mai suna Khadija, wadda suke kira Hajiya Mama. Tana da 'ya'ya huɗu, dukansu maza: Abdul Rahman, Aminu, Hafiz,da Fa'iz.
Hajiya Babba ta rasu a lokacin da ta haifi autarta, Nihla. Alhaji Ibrahim ya riga Hajiya Babba rasuwa da watanni takwas. Daga baya Hajiya Babba ta bi shi. Wannan dalilin ne ya sa Nihla ta tashi a marainiya.
Ba ta san mahaifinta da mahaifiyarta ba, sai dai ta san su ta hanyar hotunansu.
Hajiya Mama ce ta karɓi Nihla, ta shayar da ita, domin a lokacin ita ma tana shayar da Fa'iz, wanda yake da shekara ɗaya da rabi.
Duk Wanda ya Kalli iyalan Gidan Alhaji Ibrahim, yasan cewa suna zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan Kuma Yaran Gidan sun koshi da tarbiyya. Alhaji Ibrahim ya tsaya tsayin Daka wajen tabbatar da zaman lafiya da Kuma hadin kan iyalansa kafin ya koma ga uban gijinsa.
Bangaren matansa ma sun Zauna cikin Aminci da kaunar juna, har zuwa lokacin da me rabawa ta raba.
Nihla ta fi sabawa da Fa'iz a cikin yaran gidan. Tare suka taso, duk da cewa akwai kusan shekara ɗaya da rabi a tsakaninsu Amma akwai shakuwa a tsakanin su.
Nihla ta taso cikin gata gaba da baya. 'Yan uwanta ba sa barinta ta shiga damuwa. Kowa yana sonta, kuma kowa yana son ya kyautata mata. Ga Hajiya Mama kuma wadda ta tsaya mata shi yasa Bata da damuwar komai.
Nihla ba ta san ma'anar maraici ba, domin duk abin da ta nema tana samu. Sai dai kawai irin maraicin da ke tattare da rashin sanin iyayenta. Amma Hajiya Mama ta cike mata wannan gurbin.
Abubakar mutum ne mai zafin zuciya kuma mai ra'ayin rikau. Idan ya ƙuduri aniyar yin abu, babu wanda yake iya sauya masa ra'ayi.
Mutum biyu ne kawai a duniya suke iya taka masa birki: Hajiya Mama da kuma wan babansu, Baba Malam.
Abubakar mutum ne mai wahalar sha'ani, ba shi da sakin fuska. Wannan ya sa yaran gidan suke tsananin tsoronsa. Idan suka gan shi, sai su ji tsoro tamkar sun ga mala'ikan mutuwa.
Har Nihla ma, duk da abin da take yi, idan ta ji an kira sunansa sai ta nutsu. Tana tsoron Yaya Babba, sunan da yaran gidan suke kiransa da shi.
Za mu iya cewa Abubakar ya gaji mahaifinsu, domin kuwa malami ne a Jami'ar Bayero da ke Kano. Bayan nan kuma yana taimakawa wajen tafiyar da harkokin kasuwancin gidan.
Suna da babban shago a Kasuwar Kwari, inda suke sayar da shaddoji da yadikan maza. Sannan suna da wani babban shago a Kasuwar Singa, inda suke sayar da kayan masarufi.
Umar kuwa yana Abuja tare da iyalinsa. Matukin jirgin sama ne. Umar yana da miskilanci, amma bai kai Abubakar zafi ba.
Usman yana Lagos, inda yake aiki a kamfanin Dangote. Yana da mata ɗaya da yara biyu.
Abdulrahman kuwa yana Ilorin. Shi ma koyarwa yake a Jami'ar Ilorin.
Anty Asiya tana Gombe, tana aure.
Hafiz yana aiki da wani kamfanin tafiye-tafiye.
Aliyu yana Kasuwar Singa.
Aminu yana Kasuwar Kwari.
Fa'iz kuwa yana ƙasar Saudiyya, a Madina, inda yake karatu.
Fa'iz,Jafar,Hafiz,Aminu,Aliyu sune suka rage Basu Yi Aure ba da kuma Yar Auta NIHLA, Amma ragowar duk sunyi aure.
Fa'iz ne ƙarami a cikin 'ya'yan Hajiya Mama, kuma shi ne wanda Nihla ta fi kusanci da shi. Duk da cewa yanzu yana Madina yana karatu, har yanzu suna yawan magana ta waya.
Fa'iz yana matuƙar ƙaunar kanwarsa Nihla. Duk da cewa idan suna tare kullum cikin faɗa suke, idan ya shigo gida babu wadda yake fara nema sai ita. Idan ba ta da lafiya kuwa, shi ne mai zaman jinya da ita.
Tafiyarsa karatu ce ta sa Nihla jin gidan ya mata shiru. Dama Fa'iz ne abokin hirarta.
Shekaru biyu kenan da tafiyarsa. Sai dai su yi waya ko video call, kafin su gama wayar kuma sai sun taɓa halin juna.
Rayuwar gidan Alhaji Ibrahim Kwalli rayuwa ce mai tsafta. Yaran gidan suna da tarbiyya da nutsuwa, kuma suna da ilimi, daga na addini har na boko.Duk kansu Babu Wanda be sauke alkur'ani me girma ba. A bangaren karatun boko Kuwa daga masu degree sai masu PhD. NIHLA ce kawai Mai secondary a cikinsu.
Gidansu babban gida ne wanda za a iya kiransa da family house. Sai dai yanzu babu kowa a cikinsa daga Hajiya Mama sai Nihla, wadda take kwance a ɗakin Hajiya Mama. Sai kuma masu aiki da suke kai-komo: mai girki, mai shara da kuma wadda take mopping.
Hajiya Mama ce ta kalli Baba Jummai, mai aikinsu, ta ce mata:
"Har yanzu Auta ba ta tashi ba?"
Baba Jummai ta amsa wa Hajiya Mama:
"Wallahi, har yanzu ba ta tashi ba."
Hajiya Mama ba ta ƙara magana ba. Ta miƙe ta nufi cikin bedroom ɗinta. Ta san Nihla tana ciki, tunda a nan take kwana. Idan ka ga Nihla ta je ɗakinta, to kaya kawai za ta ɗauka, amma a ɗakin Hajiya Mama take kwana, a nan take yin komai.
Hajiya Mama ta buɗe ƙofar bedroom ɗin ta shiga. Can ta hango Nihla a kan gado, a nade cikin bargo. Ta ƙarasa gaban gadon, sannan ta saka hannu tana yaye bargon da ta lulluba da shi, tare da kiran sunanta.
"Nihla! Nihla! Ya kamata ki tashi daga wannan baccin haka."
Hajiya ta ci gaba da cewa:
"Sha biyu rana ta yi. Ko wani dare za a sake miki?"
Mika Nihla ta yi, bakinta yana ɗauke da salati. Sannan ta sake juyawa daga farkon gadon zuwa ƙarshen gadon, gaba ɗaya gashin kanta ya barbazu a kan gadon.
Hajiya ta miƙe ta nufi bakin window tana buɗe shi, sannan ta kunna hasken da ke ɗakin.
Nihla har yanzu tana kan gadon. Sai lumshe ido take tana buɗewa, alamar baccin bai ishe ta ba.
"Wai ba za ki tashi ba sai na zo na same ki a wurin nan?"
Da ƙyar Nihla ta samu ta miƙe. Toilet ɗin da ke cikin ɗakin Hajiya Mama ta shiga, sannan ta rufe ƙofar.
Ganin haka ya sa Hajiya Mama ta koma falo ta zauna tana kallon TV.
Nihla kuwa bayan ta shiga toilet, brush ta fara yi, sannan ta yi wanka. Sai ga ta fito daure da tawul a jikinta, sannan da wani a hannu tana goge jikinta. Daga nan ta kunna fan, ko za ta samu ta bushe da wuri.
Bayan ta bushe, sai ta fara shafa mai a jikinta. Sannan ta miƙe ta buɗe wardrobe ɗin da ke ɗakin Hajiya Mama, ta ɗauko doguwar riga ta material mara nauyi ta saka.
Ta ɗauki turare ta shafa, sannan ta saka hannu ta tattara gashin kanta ta ɗaure shi a baya. Daga nan ta ɗauki hula ta saka a kanta, ta nufi falo inda take jin hirar Hajiya Mama da baba Jummai.
"Ah-ah, Auta, an fito kenan?"
Baba Jummai ta faɗa, fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Nihla.
Murmushi Nihla ta yi, tana yi wa Baba Jummai da Baba Asabe Ina kwana Suka amsa mata cikin fara'a.
Wucewa ta yi ta barsu, ta nufi dining ɗin da ke cikin falon. Ta fara buɗe fulasan da ke wurin, ta janyo kofi ta zuba kunun gyada a ciki. Sannan ta samu plate ta zuba dafaffiyar farar doya da miyar ƙwai.
Ta dawo falo kusa da Hajiya Mama ta zauna. Ta yi Bismillah ta fara cin abincin.
Baba Asabe tana ba Hajiya Mama labarin wata mata a unguwarsu da ta yanke wa mijinta mazakuta.
Ita dai Nihla ba ta saka musu baki a hirar ba. Abincinta kawai take ci, hankalinta kwance. Ta gama cin abincin, ta ɗauke kwanukan ta kai kitchen.
Sannan ta dawo ta zauna. Hajiya Mama ta kalleta ta ce:
"Ki zauna cikin shiri. Dazu yayanku ya faɗa min zai turo Jafar ya ɗauke ki. Za ki yi registration na JAMB. Ki shirya da wuri. Kin san halin jafar da azalzalar masifa."
"Da to," Nihla ta amsa, tana jingina kanta a kan cinyar Hajiya Mama.
Wannan ne karo na biyu da Nihla za ta rubuta jarabawar JAMB. Ta rubuta ta farko, amma makarantar da ta nema ba su ba ta admission ba. Shi ya sa za ta sake rubuta wata.
Umsar ✍️
***