Page 01
*JUYIN LAMARI*
By
*Ummu Fadeela*
DISCLAIMER: Wannan labarin da dukkan abin da ya kunsa kirkirarre ne, sunayen mutane, garuruwa, masana'antu da dukkan wani event da ya faru a labarin aikin kirkira ne. Idan ya yi kama da rayuwarki/ka to arashi ne.
*Ban yadda a canza mini labari ko a dora mini labarina a YouTube ba tare da izini na ba, yin hakan zai sa a fuskanci Shari'a. Wannan gargadi ne da babbar murya, idan kunne yaji, jiki ya tsira*
*BOOK ONE*
*Page 01*
"Na dade ina jin ana cewa rayuwa makaranta ce, amma ban taba sanin cewa wasu darussan dake cikin makarantar da hawaye ake biyan kudin karatunsu ba. Ba kowace rayuwa muke zaɓa ba, wasu lokuta kaddara ce ke zaɓar mana hanyar da za mu bi.
Wannan ita ce JUYIN LAMARI da kan riski mutum a lokacin da bai yi zato ko tsammani ba.
Rayuwa ba kullum take tafiya yadda muke so ba, amma kowace ƙaddara tana ɗauke da wani darasi da ba za a iya guje masa ba."
Cewar Dubulle tana share hawayen dake malala bisa fuskarta da bayan hannunta.
Durkushe take a tsakanin su tana rera kuka mai tsanani, irin kukan da mutum yake yi a lokacin da ya rasa wani da zai fahimce sa, ko mutum ya rasa wani madafa a cikin rayuwarsa.
Dakyar ta tattaro duk kuzarin da ya yi saura a jikinta ta rarrafa har gaban wacce ke kusa da ita. Ta dafa kafafun ta cikin gunjin kuka mai taba zuciyar mai sauraro ta ce.
"Don girman Allah ki dube ni, wallahi ban aikata ba. Ba ni na aikata abin da ake tuhumata ba, ku yi mini adalci domin Allah!"
Ta fada tana jan majina da hadiyar zuciya.
A fusace matar ta fisge kafafunta ta haure ta da kafa daya tace.
"Tirrr dake Dubulle! Tirr da hali irin naki. Tabbas kin jawa ahalin Baraya abun kunyar da kika cancanci a haka rami a binne ki da ranki.
Amma ki sani, wannan abun kunyar a kan ki da iyayenki zai kare. Ta yi ajiyar zuciya kadan ta dora da fadin, "Ko da yake me abun mamaki a wajanki Dubulle?
Da karfi na runtse idanu jin sauƙar kalamanta tamkar harbin mashi a kahon zuciyata.
Ba tare da ta bani damar cewa komai ba ta shige daki.
Sauran jama'ar dake zagaye da ni na fara bi da kallo, muka hada idanu sai na kara jan jiki zuwa gareta.
Koda ace kowa ya gaza fahimtata, na san ita zata fahimce ni. Sai dai kafin in karisa ta daga mini hannu da kyakkyawar gargadin cewa.
"Kada ki kuskura ki matso kusa dani, Allah ya wadaranki Dubulle, you really disappointed us, a yanzu ya rage naki ki aikata abin da ake so ko ki kare rayuwarki a cikin masifa da tashin hankali" tana fada itama ta shige dakinta.
Daya-bayan-daya suka fara watsewa a wajan.
Karfin kukanta yana karuwa, amma babu wanda ya kalleta. Tun tana kuka har ta koma sheshsheka sakamakon karfinta da ya kare.
Tayi yunkurin tashi dakyar tana jin hajijiya yana kokarin kada ita, tayi karfin halin daukar envelope dake gabanta ta matse shi gam a kirjinta sai ta durfafi fita daga gidan.
Hawayen da ta kasa tsayarwa suka zubo a hankali saman kuncinta, yayin da take kallon ƙofar gidan da take kallonsa a matsayin mafaka a baya. A yau kuwa, ta zamar mata kamar ƙofar shiga cikin wani sabon al'amarin da bata san abin da yake ɓoye a cikinsa ba.
Da ace na san cewa wannan rana ce da za ta JUYA LAMARIN da ke tsakanin tsohuwar rayuwata da sabuwar rayuwa, da na roƙi lokaci ya tsaya… Sai dai kash, ita kaddara ba ta jiran izinin kowa.
“Shin wannan shi ne ƙarshen farin cikina?” Ta tambayi kanta cikin raɗa. Ba tare da ta san amsan da zata samu ba, ta tare dan adaidaita da ya tunkaro ta
"Murtala Muhammad Way" tace mishi bayan ta daidaita zamanta a cikin adaidaita sahun.
Sannu a hankali take share hawayen dake gangaro mata duk bayan second.
"Hajiya sai hakuri, gabadaya rayuwar haka ake lallabata yanzu" muryar mai adaidaita ya dawar da ita daga duniyar tunanin da ta afka.
Bata ce mishi komai ba, ya ci gaba da sharara gudu bisa kwalta.
Dari biyar ta fitar daga cikin envelop dake hannunta ta mika masa bayan sun iso, yaja babur dinsa yayi gaba.
Saisaita nutsuwarta ta yi duk da kallo daya zaka mata fuskarta ta fallasa asirin halin da take ciki. Ta tunkari shiga babban ginin dake gabanta. Mai dauke da wani babban tambarin da aka yi rubutu ruwan gold mai walkiya a jikinsa.
*MALABU HOLDINGS COMPANY*
Shine rubuce a jiki.
"Barkanku da aiki" daya daga cikin securities na wajan ya kalleta kallon tuhuma ba tare da ya amsa gaisuwar ba cikin harshen turanci ya ce, "Me kike bukata a nan"
Ta kara tattaro duka jarumtarta, ta zaro karamar kati cikin envelop din ta mika masa.
Kallon sakan biyar ya yiwa katin ya dago kafin yace komai, wasu jerin gwanon motoci bakake wuluk suka durfafo ginin da mugun gudu kai kace su kadai ne a hanyar.
Babu shiri muka ja gefe wasu daga cikin securities din suka wangale wawakeken get na shiga wajan motocin suka wuce tamkar walkiya.
*WANI LOKACI KAFIN YANZU*
Miller road Kano.
Wayarta da ke makale a bakin siket ne ta dauki vibrating.
Da sauri ta fitar tana makalashi a kunnenta. Kasa-kasa tace,
"Haba Ya Abdul, ya kake neman dora mini jakar tsaba ne, wannan kwarzaba har ina?
Bani nace ina zuwa ba, to idan an takura mini yasin sai inyi zamana" Ta karisa fada da kashe wayar tana jan wani dogon tsaki.
Karo na biyu ta kuma dage labulen window tana leka waje, yana zaune a wajan da aka tanada musamman don yin alwala amma yanzu ya kammala, addu'ar bayan alwala yake yi.
"Alhamdulillahi" Ta fada da sakin labulen. Bata da matsala da Umma ta san sai asuba zata kuma shigowa dubata, tunda yanzu ta tabbatar da tayi alwalar kwanciya kuma tayi addu'ar bacci.
Ajiyar zuciya ta sauke tana rufe idanunta bayan jiyo karar rufe ƙofar dakin Baba. da hanzari ta debi takalmanta a hannu.
A hankali ta bude ƙofar ba tare da yayi kara ba, cikin sanda take bin bango har tayi nasarar bude karamin kofar da ke tsakanin gidansu da asalin main house din.
Babban compound ne sosai mai dauke da dogayen gine gine bangare bangare, wanda ke nuna gidan yawa ne.
Duk da dare ne zaka fahimci mai gidan hamshakin attajiri ne, ma'ana dai duka gida daya ne amma akwai dogon gini da ya raba tsakani da karamar kofa da ake bi a shiga gidan da ta fito.
Dallare ta da fitilar mota yayi yana danne horn ta karisa wajan motar da hanzari ta bude front seat ta shiga.
"Wallahi da kin kara minti biyu idan kin fito ko kurar motata baza ki gani ba"
Ya fada yana danna horn mai gadi ya bude masa get suka bar gidan.
"To dan neman jaraba gani na fito ai, kai kullum bakin ka bai fadin alheri, ka ma san ta yadda akayi na fito yanzu?
Sittin ta Qur'ani idan ka mini abin da bai gamshe ni ba sai in sauka a motar nan".
Ta fada tana jan kwafa da juya kai gefe.
"Allah ya huci zuciyarki Dubulle, a huce haka gimbiya"
Kwafa ta kuma ja ta turo dankwalinta gaban goshi.
A bakin wani babban boutique ya tsayar da motar.
Cikin lallashi yace "plsss Dubulle kada ki jima, kinga bamu da isashshen lokaci.
Ya fada yana duban agogon hannunsa.
Bude motar tayi ta shiga boutique din da babu abin da babu na English wears kala kala masu daukar hankali.
Cikin kasa da minti goma ta fito shirye tsab cikin wasu damammun riga da wando, kayan sun matseta kamar idan tayi numfashi mai kyau zasu tsage, dakyar take iya tafiya.
Back seat ta bude ta jefa ledan asalin kayan da ta fito dashi daga gida.
"Woww kin gan ki kuwa wutaaaaa" Yau kin cinye taron nan kowa sai ya jira aradu".
Ta juya ta ganshi sai tayi wani murmushi da yin fari da idanu ta ce, "Ya Abdul bani da bukatar tuni, already na san ni mai kyau ce".
Wani irin ihu yayi yana bugun steering da hannu biyu yace, "Wannan salon ya tashi kaina Halima"
*LAGOS*
*VICTORIA ISLAND ESTATE*
Kamar yadda sautin discon ya hanata bacci, haka ya hana daukacin mutanen dake gidan har ma da makwafta bacci. Kida ne yake tashi tamkar gidan gala.
Hularta ta lalubo ta dora a kanta ta nufo falon.
Duhu ne dim dim a cikinsa, sai sautin dake tashi tamkar zai balla majiyar kunne.
Kidan ta kashe tana kunna switch na falon haske ya gauraye ko ina.
Yana kwance rigingine bisa doguwar kujera, kafafunsa suna lilo a kasa kasancewar yafi kujerar tsawo.
Ya dora throw pillow a saman kan sa sai karkada kafafu yake.
"Boy"
"Boy! Ta fada a karo na biyu tana shafa kansa a hankali cike da kulawa.
Cikin yanayin dake nuna baccinsa ya yi nisa ya motsa ciki-ciki yace.
"Mother"
Da mamaki take dubansa yadda ya iya bacci cikin wannan sautin har yana karkada kafa.
Tashi ka wuce daki dare ya yi sosai. Duba agogo kaga around 2:00pm fa amma kana falo kwance, kana bukatar hutu Boy ka san tafiyar awanni zakayi gobe daga Nigeria to England.
Tashi ka wuce bedroom kada kan ka yayi ciwo ohk" ta kuma fada a hankali tana shafa kansa tamkar jariri.
"Mother!"
Ya kuma fada cikin shagwaba da magagin bacci.
Ba ta bari yace komai ba ta kamo kafadunsa ya mike.
Yana hade hanya ya wuce bedroom din sa. Ajiyar zuciya ta yi ta tattara tarkacensa dake falon ta wuce bedroom itama.
Har ya kama handle na ƙofar, sai kuma ya sake ya juyo cikin falon ya shiga wani walkway, a hankali ya murda ƙofar dake farko ya leka.
Stepmom nashi tana kwance saman gadonta kamar mai jin sanyi. ta kudunduna waje daya wayarta na gabanta kunnenta makale da headphones.
"My Bads"
Ya fada yana bugun kansa da hannu. Ya dan shigo dakin kadan ya leka fuskarta, yace a hankali.
"Sorry Mom" Domin ya san kidan da ya cika gidan dashi ne ya tilasta mata makala headphone din. Sakin ƙofar ya yi ya fita.
Misalin karfe uku na dare, a firgice suka farka sakamakon ihunsa da ya karade gidan.
Jar karo suke yi da juna wajan shiga dakinsa.
"Mother. Mother help me. abin da yake fada ke nan yana juyi a kan gadon zufa ya mamaye masa jiki kamar bokitin ruwa aka juye masa.
Dora hannu tayi a kanta tana zagaye dakin da fadin "Ohh Yesu heal my Boy, covered him with your blood Jesus". Sai nanatawa take yi tana zagaye dakin.
"You are covered with the blood of Jesus Christ my Son"
Mother Ta fada tana zama a bakin gadon, ta kamo kansa ta dora a saman cinyarta. tana shafa mishi kai a hankali idanunta a rufe take fadin.
"Plss Jesus heal my son."
Da sauri Mother ta dago a fusace take kallon yadda ta dukufa tana karanto addu'o'i tana tofe fuskar Boy nata dashi.
Cikin rawar harshe tace.
"A'a Hawwa me wannan kike yi a kan dana, yau kuma maitar a zahiri kike aikatashi? Hawwa stay away from my Son. ki karkade hannunki a kan duk wata safgar da ta shafi dana bana so.
Dan haka ki fita ki bani waje yanzun nan."
Mother ta fada cikin tsananin fusata tana nuna kofa.
Hauwa ta kalleta cikin nutsuwa tace, "Dangana ko bakya so sai na fada miki gaskiya, idan zaki farka daga wannan baccin da ya dauke ki gwara ki farka ki bude idanunki da kyau ki san cewa wasa ki Ke yi da rayuwar dan ki". Sai ta juya ta fita.
Wani kallo Dangana ta raka bayanta dashi a fusace tace, "Dangin jaraba irin maita masu lashe kurwar mazajen mutane".
"ALEXX!" Ta Kira sunansa tana cigaba da shafa kansa. Alex plsss wake up."
Idanunsa da suka rine tamkar garwashin wuta ya bude ya zuba su cikin na uwar. Cikin muryar galabaita yana sauke numfashi a jejjere kirjinsa yana hawa da sauka yace. "Who's she Mother, tana son rabani da rayuwata kice ta daina azabtar dani haka nan ta fadi duk abin da take so."
Kuka Dangana ta fashe dashi mai sauti tana rungume fuskarshi a kan kirjinta.