AMATULLAH

Chapter One

by @ameerahfarouk

Mai keke napep din da ya dauko wata  budurwa black beauty matsakaiciya yake tambayar su dai dai inda zaya sauke su ita da matar da ya daukosu atare.


 "corner ta dama zaka shiga damu" matar da take tare da yarinyar ce tabashi amsa . yashiga dasu corner ta daman . 


unguwace mai kyau , layinda suka shiga babu wata hayaniya .ga gidaje masu kyau , ga dogon titin da akaima layin tare da jera mashi security lights da akayi . 


tunda suka shiga layin mutum ukku ne kawai suka gani wata matace tare da yarinyar da ta kamama hannu suna tafiya sai kuma wani mutum da yake tafiya shi kadai .


suna cikin tafiyane yarinyar taji matar da suke tare ta cema mai keke napep din "nan yayi" nan take yatsaya da tukin suka sauka ta fiddo dari shidda tabashi ya amsa yayi godiya yajuya ya tafi. 


Wani gida mai kyau ne tagansu a gaban shi wanda duk kauda kan mutum da nuna baidamu ba idan ya ganshi sai yakara kallonshi. gate dinshi combination din gold da farine,muryar matar da suke tare ce taji ta cemata "muje koh" tadan zabura kadan jin maganarta da tayi. 

Kada mata kai tayi suka nufi gidan. mai gadin gidanne da yake zaune akan benchi ruke da radio ahannunshi yanaji sanye da yar shara ajikinshi  yatashi da saurin shi ganin alamar gidan suka nufa."Sannunku da zuwa" ya fada da fara'arshi "yauwa baba yahayya inawuni  ya aikin " matar da suke tare da yarinyar tafada ta gaisheshi cike da girmamawa . 


amsawa yayi "lafiya lau ya maigidan ya yaran?" ta amsa mashi "lafiyarsu kalau Alhamdulillah" itama yarinyar ta gaisheshi ya amsa tare da tashi ya budemasu kofar suka shiga cikin gidan. 


Shigarsu ciki ne yasa  yarinyar tagane wajen gidan ba komai bane ba a kyau  saboda cikin gidan ya linka shi kyau sosai akan wajen. 


gidane mai girma, part biyu ne acikinshi sai wani gini da yake facing din gate, sai kuma parking space wanda aka ajiye motoci guda hudu acikinshi . 


suna kokarin karasa shigane wata bakar mota tazo ta wucesu ahankali tayima mai gadi horn zata fita ,dan kallon motar kadan tayi tacigaba da kalle kallen da take yima gidan. 


Part din hagu suka nufa . knocking din kofar shiga matar tayi , wata muryace tace "su waye ku shigo abude kofar take" suka shiga tana biye abayan matar . 


wata matashiyar yarinya ce gajera baka suka iske tsaye abakin kitchen . "sannunku da zuwa" tafada masu suka amsa mata da "yawwa kice ma hajiya salma ce tazo tare da yarinyar da zata ruka yimata aikin" matar tafada "toh" yarinyar ta amsa mata . 


parlo ne mai dan girma mai kyau sosai ta haura  upstairs andan jima sai tasauko "hajiya tace ku haura kusame ta", tashi sukayi suka  haura upstairs din suna biye abayanta. wani parlon suka kara gani wanda bai kai wancen girma ba but ya fishi kyau sosai. Kofar da take facing dinsu ce tanufa ta tsaya abakin kofar tayi knocking sukuma suka zauna akan kujera suna jiranta . shiga tayi ciki bata wani jima ba tafito tare da cewa "hajiya tace ku shiga" suka tashi dukansu mai aikin kuma ta sauka kasa  itadai yarinyar tana biye abayan matar.  


knocking kofar matar tayi wata muryace ce sukaji tace "zaku iya shigowa" shiga sukayi tare da yin sallama amman abun mamaki kuma sai taji bata amsa sallamar ba . 


zaune take akan sofa tana kallon tv ta daura kafa daya akan daya tana karkada ta ruke da remote ahannun ta, sanye da baby pink lace wanda akayima dinkin buba da shi ga sarka da dankunne gold da tasha ta kashe daurin dankwali tayo gaba da shi. farace amman ba sosai ba mai kiba marar tsayi. tayi kyau abunta tasha kwalliya kamar zata gidan biki amman sai dai fuskarta babu annuri ko kadan. 


sudai suna durkushe sun zubama sarautar Allah ido. gaisheta sukayi atare "lafiya lau" ta amsa masu ciki ciki tare da yatsina fuskarta da tayi "sai yanzu kenan koh salma ni da nace karfe 12:00 ta yimaku agidannan amman sai yanzu kuke zuwa?" tambayar da tayima mata kenan.


cike da girmamawa ta amsa mata da "hajiya kiyi hakuri wlh yanzu ma da kyar muka samu muka fito gidan" 


hajiyar ta ajiye remote din da taruke tajuyo tana yima yarinyar wani irin kallo awulakance. tunda hajiya ta juya yarinyar ta lura da tanata kare mata kallo . da taga kallon yayi yawane yasa ta dan dago kanta kadan ta kalleta, hada ido sukayi da ita wata irin muguwar harara tayimata wadda tunda take rayuwarta ba'a taba yimata irinta ba. tayi sauri ta sauke idon ta kasa ba tare da taji tsoro ba ko kadan.



Wa yacemaki ana hada ido dani "? Hajiya ta tambayeta . shiru tayi ba tare da ta cemata komai ba "BA DAKE NAKE MAGANA BA?" ta kara tamabayar ta tare da kwatsa mata wata irin tsawa . ita dai babu tsoron da taji sai dai taji babu dadi arata. hajiyar takara cema matar da suke tare da ita "da ke salma baki gayamata dokoki na bane ba? Toh sai ki maida ita inda kika daukota tunda naga alamar bata shirya yin aiki ba sanda ta shirya ta dawo" tafada cikin hargagi. 


cikin tattausar murya kasa kasa matar tace "hajia kiyi hakuri Allah ya huci zuciyarki ban gayamata ba amman in sha Allah yanzu zani gayamata" hannun yarinyar matar  takama tajata suka fita waje. 


tsayawa sukayi achan gefen bakin wata kofa da take a parlon "Calmly, kiyi hakuri kinji ita haka take sai kin kara hakuri" matar ta fadama yarinyar ahankali tana kasa kasa da muryarta tanayi tana waigen kofar da suka shiga gurin hajiyar "babu komai Anty salma" tafada tare da kokarin tattaro smiling din da batayi niyya ba. 


"Good girl" tafada mata itama tare da yimata smiling. hannunta takara kamawa suka kara nufar kofar suka karayin knocking. instead of yarinyar taga sun shiga kawai sai taga sun tsaya chak abakin kofar.


 "anyi knocking what next ba sai ashiga ba?" tambayar da tayima kanta kenan aranta . sai da suka kusa kai 15 munites sannan taji hajiya tace "zaku iya shigowa." 


cike da mamaki tabi bayan matar da take ruke da hannunta suka shiga. sallama suka karayi atare still hajiyar bata amsa sallamar ba. su dai suna durkushe akasa suna jiran ikon Allah. hajiya ko kallon inda suke batayi ba sai da aka kusan kai 30 munites tajuyo fuskarta amurtuke tare da tambayar ta da tayi "kin shirya yin aikin kenan yanzu?" 


ita dai kanta akasa ta amsamata da cewa "Eh hajiya kuma in sha Allah zani ruka yimaki aiki da kyau yanda kika bukaci in yimaki" dauke kanta hajiyar tayi bata kara cemata komai ba sai chan kuma tafara kwala kira "Hassana hassana!" alamun rugowa dagudu sukaji tare da knocking kofar da akayi. 


chan sai sukaji hajiyar tace "zaki iya shigowa" aranta yarinyar tace "ni wlh harma na manta da ta kirata" 


shiga tayi tare da yin sallama yarinyar suka amsa sallamar ita da dayar matar da suke atare, hajiyar kuwa tana zamanta bata da niyyar amsa sallamar ta. yarinyar da tayimasu jagorar shiga gurin hajiyar ce suka gani karasa shiga tayi ta durkusa ta saddar da kanta idanuwan ta na kallon kasa tana jiran abunda hajiyar zata cemata.

saida hajiya ta mula tasha iska sannan ta cemata "kije ki nunamata masaukinta, ki fadamata sharuddana da kaidojina sannan ki kwatanta mata yanda zatayi aiki, ki kuma gwada mata ko ina" sannan takara da cewa "zaku iya tafiya." 


aranta yarinyar takara cewa "ikon Allah ankira mutum anbashi sako tafiyar ma sai anbashi izini sannan ya tafi!?" Mikewa tayi itama tabita abaya. 


Har sunjuya suna kokarin tafiya hajiyar hajiyar ta dakatar dasu "ku dakata." cirko cirko sukayi dukan su. juyawa tayi ta kalli matar da sukazo gidan awulakance tare da cemata "ke kuma kuyi bankwana da ita ayanzu." 


"Allah ya taimaka ya bamu alkhairi ki kara kwazo ki natsu kiyi aikinki da kyau kinji ko sai munyi waya" matar tacema yarinyar  

"Ameen Anty salma nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" yarinyar tafada, sai kuma taji batasan rabuwa da ita but sai ta tuna da kaddara ce ta hadata da ita yanzu ma itace zata rabasu da ita. 


cike da izza  hajiyar tace "zaku iya tafiya" cigaba sukayi da tafiya tana biye abayan dayar yarinyar dake yimata jagorar ganin yanayin gidan. 


Hajiyar kuwa sai faman fada da hargagi taketa yi. ita dai matar da takawo yarinyar hakuri kawai taketa bata "wlh zakiji dadin aikin yarinyarnan hajiya akwai ta akwai hazaka da juriyar yin aiki, ko ni kaina da ba wani dadewa nayi da ita ba nadan huta zaman da nayi da ita in sha Allah zakice nafada maki hajiya" matar tafada takara da cewa "yarinyarnan yarinya ce mai dadin zama wlh" 


ita dai tana ta jiyosu aranta tace "ni mi za'a yimani yanzu inji tsoro arayuwarnan ni kuwa? ai banganshi ba. 

 
Sauka kasa sukayi ta gwada mata ko ina a bangaren sannan tace "na gwadamaki ko ina banda saman da muka baro koh?" "Saman da muka baro shine bangaren hajiya da kuma yayanta asannu zakisan ko ina in kika saba da gidan kika gane kanshi" 


"wai daman hajiya tana da yayane naga tunda mukazo banga kowa ba sai ita dake?" tambayarta tayi cike da mamaki . amsama ta dayar mai aikin hajiyar tayi tare da cewa "Eh tana da yaya su ukku ne Asiya , salim da kuma Ahmad "  takara da cewa "Asiya itace babba tana aure ne a kaduna itama yayanta guda ukku ne intisar , siyama da kuma Amir suna zuwa nan ita dasu duk karshen shekara suyi hutunsu anan. salim kuma yana Qatar achan yake aiki yana zuwa amman ba sosai ba gaskiya koma yazo baya wani dadewa yake komawa chan, shikuma Ahmad a umaru musa yaradu'a (UMYUK) yake yin karatunshi shi kadai ne yake zaune da hajiya yanzu Amman yanzu baya zama gidan saboda exams da sukeyi ya koma hostel da zama sai idan sungama zaya dawo. yanzunnan ma babu dadewa yabar gidan yazo ya dauki kaya yakoma" ahankali takara da cewa "danwahala shine yabiyo uwarshi rashin ganin  darajar mutane da rashin mutunci" 


dan zaro idonta yarinyar da aka kawo tayi tare da cewa "kinga kirufa mana asiri" dariya dayar yarinyar tayi tare da cewa "kuma fa" tadan toshe bakin ta "gaskiya hassana na jinjina maki da surutu tambaya daya nayimaki amman da kika tashi bani amsa sai kika bani ita hadama kari da wanda ban tambayeki ba" tace mata tanata mamakin surutu irin nata. 


dariya mai aikin tayi tare da cemata "Au namanta ban fadamaki abunda hajiya keso da wanda bataso ba" "na lura da guda daya" yarinyar tafada.


mai aikin tace "ai dazu naji anata balbaleki da masifa" hada baki sukayi dukansu tare da cewa "hada ido da ita" sukayi dariya dayar mai aikin ta cigaba da cewa "ba'a amsa kira idan hajiya ta kira ki, ba'a shiga gurin ta azauna durkusawa akeyi, ba'a hada ido da hajiya dukar da kai akeyi, ba'a shiga gurinta sai anyi knocking kofar sannan kuma knocking din sau daya ne kawai zakiyi idan kika wuce dayannan sai ta hukuntaki, bataso aje gurin ta inba bakine sukazo ba ko ita takira ki, bataso kizauna a parlo ko nasama ko nakasa idan babu aikin da kikeyi bataso taganki awaje tafiso kizauna adaki, bataso atambaye ta mi za'a dafa, idan hajiya ta kira ki toh kiyi kokari ki ajiye ko mi kikeyi kitafi kiranta idan bahaka ba kika wuce minti biyar bakije ba shima sai ta hukuntaki" takara da cemata "hajiya zubaida macece mai izza da isa da so abita sau da kafa shawarar da zani baki kawai ki dauki hajiya amatsayin sarauniya ta hakane zaki danji saukin zama da ita dan wata sarauniyar ma ba'amata irin yanda ake yima hajiya. kuma kisama ranki hakuri dan zama da ita sai mai hakurin gaske zaya iya zama da ita gaskiya." 


daga mata kai tayi tare da cewa "nagode in sha Allah" "kada kidamu asannu zaki saba da halinta" dayar mai aikin tafada tambayar yarinyar tayi "ina kayanki suke?" ta gwadama ta su da suke jingine da bango akasa cikin bakar ledar da ta sakasu. 


wata kofa mai aikin ta nufa dake gefen kitchen tabi ta abaya tabude kofar suka shiga ciki "kinga dakinmu nan shine dakinmu" dakine hade da toilet wanda ba za'ayi expecting ganin irin shi agida mai kyau irin gidan ba! ta kalla takara kallonshi tana ta mamaki. gadone medium sized wanda dagashi sai katifar da babu ko bedsheet akanta sai kuma labulen da akasa aka rufe window dashi, sai kuma kullin kayan mai aikin da suke agefen gadon.


Ajiye kayan dayar mai aikin tayi da suke hannunta adayan side din gefen gadon tareda kallonta da tayi "ki zauna mana ai keda dakinnan kuma kun daura auren zama dashi har sai kin gaji inba aiki kikeyi ba." dan murmushi yarinyar tayi ta zauna abakin gadon.



Dayar mai aikin takara cemata "ni koma sunanki baki fadamani ba nasan dai ke kin ruke nawa sunanan amman ke bansan nakiba gashi inata yimaki surutu ke kuma kinki kiyimani magana sosai" 


har tabude baki zata fadamata sunanta ta katse ta da cewa "yawwa kinsan mi zamuyi yanzu? Zaki bani labarinki da labarin yan gidanku da labarin garin da kike nima zan baki nawa labarin haka yayi maki koh?" magana mai aikin ta cigaba da  yimata ba comma ba full stop .
Tunda ta yimata wannan tambayar taji duniya takara fita aranta taji wani abu ya tsayamata a makogoron ta, dandanan kwalla ta cikamata idanuwan ta , hawaye suka ruka bin fuskar ta, hankalin dayar mai aikin duk sai yatashi.  Dago kanta tayi ta kalleta da idanuwan ta da sukayi red sosai kamar an samasu barkono tare da cemata "sunana Amatullah yanzu zakiji labarina!"