Chapter 45&46
by @deeyamerh10
💖💖 SOYAYYAR ZUCI 💖💖
(Love and Romantic story)
Written
By
Deeyamerh
07070647236
Page 45&46
Washi gari gida fa ya hargitsewa da kamshi ta ko ina domin a yau za'a tafi kai amare gidajensu domin ko wacce tana da nisa,tunda Fatima Abuja zata zauna ita kuma Suhaima za'abiya da ita domin babu jirgi daga kano zuwa JEMETA direct.
An shirya komai tun da wuri. Motoci sun kasance a harabar gidan, kayayyakin Amare daman ko wacce a inda zata zauna aka siya mata ,domin kaukar kaya daga nan zuwa can ba abu bane mai sauki, wasu suna ɗaukar kaya, wasu kuma suna tabbatar da cewa babu abin da aka bari a baya.
Sosai Ammey da Mama suka hadu su sukai Masu fada mai tsayawa a zuciya,haka wasu daga cikin dangiie sukai musu,tunda gari ya waye suke kuka har yanzu da kowacce tayi wanka domin tafiya.
Haka aka fito dasu suna kuka akasu a mota,ba wanda basu bawa tausayi ba domin kukan me taba zuwaciya ne.
Da suka isa filin jirgin Kano, Suhaima ta tsaya kusa da Fatima,hannunsu rike da na juna kamar karsu rabu.cikin sanyi murya suhaima tace"Fatima, ki kula da kanki sosai zanyi kewarku,Suhaima ta ce cikin damuwa.
Fatima ta damki hannunta cikin kwalla yace"inshallah Ke ma ki kula da kanki. Kuma da zarar kin isa Jimeta, ki kira ni.”
Suhaima ta gyada kai "Zan kira ki inshallah".Bayan sun shiga jirgi,mutanen da za su raka su suka zauna a gaba, yayin da Suhaima da Fatima suka samu kujera kusa da taga suka zauna.
Jirgin ya tashi daga Kano, kuma bayan tafiya na ɗan lokaci suka isa Abuja. Abuja aka jiye Fatima domin wanda zasu raka Fatima da ban wanda su Suhaima da ban ,Fatima ta sauka tare da mutanen da za su raka ka ta.Kafin su rabu, Fatima ta rungume Suhaima sosai tana kuka,haka suka saka mutane a gaba da kuka..
“Allah Ya kai ki lafiya yabamu hakuri da juna a gaida mun da SH Kuma don Allah, da zarar kin isa Jimeta ki sanar da ni.”
Suhaima ta amsa da murmushi mai cike da damuwa ki kula da Yayana Sannann keman ki kula da kanki.”
Fatima ta ɗaga mata hannu yayin da take tafiya Suhaima ta tana kallonta har sai da ta shiga cikin mota sanna ta dauke idanunta daga kanta.
Haka ta zauna acikin jirgin ita kadai sai Zuciyarta cike take da tunanin Ammey.
Bayan ɗan lokaci, aka sanar da fasinjoji cewa jirgin Abuja zuwa Yola zai tashi da jirgin ya fara tashi, ta kalli Abuja daga sama, sannan ta mayar da idanunta ƙasa bin da take tunani ɗaya ne kawai Ammey da Abba shikenan rayuwa agidansu ta kare sai kuma ta gidan miji.
Sunyi tafiya sosai ,Bayan kusan awa ɗaya, aka sanar da cewa kowa ya shirya jirgin zai sauka a yola.
Da Suhaima ta leƙa ta taga, ta hango garin Yola daga sama. Zuciyarta ta buga da ƙarfi.
“Ya Allah…”
Jirgin ya sauka lafiya,saukowa tayi daga cikin jirgin a hankali tana mai Addu'ar Allah yasa ya shigo ga cikin garin yola a sa'a.
Motocine a jere guda biyar domin daukar amarya da ita da Mutanan ta, sosai hakan yayi wa famliy suhiama dadi ko daganan sun san zasu kawo yar su cikin mutunci.
Driver ɗin ya ɗauki kayan da suka taho da su raguwa yasa saka cikin motar,duk shiga cikin mota sukai aka dau hanya sai JUMETA.
A cikin motar, ta kasa daina kallon hanya, tunani kawai take yadda Zata sake wata sabuwar rayuwa da sababbin mutane.
Isar su gidan su SH sosai gidan ya cika da motoci sun cika harabar gidan. Matan gida da ’yan uwa sun fito suna jiran zuwan Amarya.
ana cewa amarya ta iso gidan ya kaure da buda sosai irin me kayatarwa.
Da motar Amarya ta tsaya, aka fara tafi da murna hankali aka buɗe ƙofar motar, aka taimaka wa Amarya ta fito. Cikin kunya da nutsuwa ta sunkuyar da kanta, yayin da wasu daga cikin matan suka kewaye ta suka shigar da ita cikin gidan.
Bayan an zaunar da ita, aka kira SH domin duk hadasu za'ayi ai musu fada duk da ba'a gidansu zata zauna ba,an dai kawuta ne kamar yadda al'ada take wajan kai amarya gidan mijinta domin tana karkashin kafar mijinki ,Zai iya kuskure, ke ma za ki yi kuskure. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne kada ku bari ƙaramin abu ya zama babban rikici a rayuwar Auranku,kizama mai hakuri da duk wani sauyi da zaki gani,domin baki da inda yafi miki irin daki Mijinki,tsafta,kwalliya,iya girki shine yake kara daga darajar macce a cikin gidan mijinta har ma da yan uwansa sosai suhiama take kuka,inda SH yake jin kamar ya rungumeta yabata hakuri.
Juyawa tayi kan SH" ka tuna cewa matar da aka kawo maka amana ce. Kada ka wulakanta ta, kada ka ci zarafinta, kuma idan ta yi kuskure ka gyara ta cikin hikima domin su mata ababen lallabawa ne, ki girmama mijinki. Idan akwai abin da ya dame ki, kada ki tara fushi a zuciyar Ki yi magana cikin ladabi, ki saurare shi, shi ma ya saurare ki.
Hajjiya ta ƙara da cewa“Haƙuri shi ne ginshiƙin aure. Ba za a yi aure ba a ce komai zai tafi yadda ake so. Wata rana za ki yi fushi, wata rana shi zai yi fushi. Amma kada ku bari fushin ya fi soyayyar da ke tsakaninku.”
Sosai Suhaima tasha kuka ta sunkuyar da kanta,cikin sanyi SH ya kalleta"
“In sha Allah, zan yi iya ƙoƙarina in zama mijin da za ta ji daɗin rayuwa tare da shi,wanda zatayi Alfahari dashi a cikin kawaye da yan uwa.
Sai murmushi ya bayyana a fuskar manyan.
Kanwar hajjjiya tayi dariya tace “Allah Ya sa haka. Kuma ke Amarya, ki tuna cewa ba kullum mace ce za ta yi haƙuri ba. Miji ma yana da nasa haƙurin. Idan kun koyi yafiya, kun koyi rabin sirrin zaman aure.”
Daga nan aka yi musu addu’a.
“Allah Ya sanya albarka a aurenku. Ya sanya soyayya da rahama tsakaninku. Ya kare ku daga fitina, ya ba ku zuri’a ta gari, ya kuma sa gidanku ya zama gidan salama.”Kowa ya amsa da “Amin.”
Suhaiam ta ɗago kanta ta kalli SH ta cikin mayafain da ka rufe mata fuska da shi amma kallon ne da ya nuna cewa sabon babi na rayuwarsu ya fara.
Daga haka aka dauke ta domin kararsa da ita Gidanta inda kana barin gidansu SH gida biyu ne ya bata da Gidan nasu.sosai gida yayi kyau dan kowanne daki da irin Adonsa da kwaliyarsa,
Sosai Abba ya kashe kudi a gidan suhaima komai biyu akai mata,dan har ta extra kitchen da aka sake zuba mata wasu kayan ko da nan gaba zata bukata.
Famliy su Suhaima basu suka bar gidan ba sai 9:40 na dare suka koma gidan hajjiya domin kwana idan Allah ya kai mu gobe su dau hanyar komawa kano,tana kuka tana komai suka wuce inda Allah ya tai make fa su Nihal sun tsaya a gidan idan SH yazo sai suewuce gida,wannan dalili ne yasa tasake dasu domin sai labari SH ake bata hakan yayi mata dadi domin a cikin hirar taji abubuwa da yawa da batasani ba game dashi,tunda kan abunda yake so,me yake sashi fushi,irin abincin da yake so duk a yanzu tasani tunda basu wani dadewa tayi da shi sosai ba.
Suna zaune suka ji karkar bude get din gidan nan fa duk suka dau mayafi domin yana shigowa suka su fita,tun kan ya karaso kamshinsa ya isar da zuwansa,sosai Zuciyar suhaima tafara bugawa da karfi,Da Sallama yashigo,amsawa tayi cikin sanyin da jikinta yayi,raga regen gaishi sukai inda suka kalleta suka ce mata sai da safe,sakon gaisuwa tabayar a bawa hajjiya da yan uwa.
Sosai hakan yayiwa SH dadi domin tun anan ta nuna tana san nashi,Tunda ya shigo yake mata kallon kasan ido sosai tayi tayi Miki kyau.
Gidan ya rage dashi sai ita,cikin kunya tayi masa sannu da zuwa kanta akasa,jin shiru bai amsaba yasa ta dago da kanta,kallonta kawai yake irin kallon da takasa gane manufarsa,"wanna sannu da zuwan batai mun ba,idan har Ni zaki tabar to bari kiga irin wacce nake so,kai tsaye inda take a zaune na nufa bai ba damar tantace mezaiyi ba yadagota daga zaunan da take kawai ya rungume ta,iska yahau hura mata a kunne kafin yace"irin wanna sannu da zuwan nafi bukata,dago da kanta yayi ya hade bakinsu guri guda sosai yafara sotsar bakin ganin zai iya zarcewa a parlon yasa ya dawo cikin muryarsa da tafara shigewa ciki yace"wanna gaisuwar nafi bukata safiya,rana,dare.
Cikin kasalar da ya saukar mata tadege masa kai domin bakin bada amsa ya mutu.
hanunta yahau ja ya nufi dakin da yzaba a matsayin nasa,sosai kamshi ke tashi ta ko ina kai tsaye Toilet ya kaita yace tayo alwala yana jiranta.
Wajan 2mins tana tsaye tana kallon Toilet kafin takarfa fawa jikinta yo alwalar ta fito,tana fitowa ta tarar ya shimfida musu danduma shi kuma yana kan tashi alamun ita yake jira,Cikin nutsuwa ta hau kai.
Kabbar Sallah ya tayar,kafin cikin murya me dadi ya hau karatun Sallah,sun dau lokaci kafin ya idar,alamu yayi ta da tamatso kusa dashi hakan tayi ya kama kanta ya sake karatu addu'a tsari da zaman lafiya a rayuwar auransu,sosai SH ya burgeta domin a rayuwar Aure ilimin addini yana da matukar muhimmanci a rayuwar ma'aurata.
Mekewa yayi ya fita a dakin bai jima ba yadawo hannunsa dauke da ledoje da flat,duk abinda ya shigo dashi ya hau budewa,komai sai da yazu a flat Dan so yake taci ta koshi dan daga ninta bata da nutsuwar da tasamu taci.
Wanke hannunsa yayi komai shi yabata tun tana kunyar ci har tasaki jiki taci dan wllh yunwar take ji sosai, ga fargabar abinda zai wakana a yau din,haka yasa ta ita ta ciyar dashi da hannunta kafin yace ya koshi tare suka kwashe komai suka mai da ma ajinsu,a hanyar dawowa ya lura da yadda duk ta wani takura kanta murmushi yayi dan yasan me takewa shi kuwa yayi alkawari yau dai zai daga mata kafa har bakin su wacce kafin yazo gareta.
Daki ya kaita domin tayi wanka ta huta dan takwaso gajiya ta samu tayi bacci ko taji dadin jikinta,sai da tadago ta kalleshi jin abinda yace, Murmushi yayi ma wanda yake bada tabbacin abinda yace kafin yasa kai yayi ficewarsa.
Wayarta ta dauko ganin 11 tayi yasa bata kira Fatima ta barshi sai zuwa gobe da safe ta kirata,da haka tashige Toilet Dan gani take kamar SH zai iya shigowa ciki.
Nace ummm duk wayan Amarya dai dai ansha manta,suhaima kigama guje gujenki zaki kawo kanki ne ah to😂😂
Wage gari da sassafe ta tashi tahau gyaran gidan,ta karasa turaruka masu kamshi dadi,wajan 7 ya fito da kayan bacci a jikinsa ganin nata Parlon yasa yayi kitchen kai tsaye dan nan yajiyo motsinta,jingina yayi da kofar yana kallonta yadda take ta aikin yi musu abin karya wa,cikin takun sanda ya tsaya abayanta hannunsa yasa ya kama ugunta ya dora habarsa akan kafadarta,cikin sweet voice dinsa yace"umm Wife haka Hajjiya ta baki Amana dan Allah ace daga tashi kin kihau aiki ko kixo kiga ya ina da rai ko na wuce tsabar farinckin mallakarki.
Cikin kunyar da ko wacce ya macce take kasancewa a ranar da ta wayi gari a gidan mijinta"tace Umm nazofa naga kana bacci nasu sa kusane kuma kagaji da yawa shiyasa ya Barka katashi da kanka fa,gashi har ina kokarin gama abin karyawa"umm nagani yafada yana mai shinshiniyar wuyanta domin kamshin ya tafi da shi,sosai yake yamutsa dan wllh jiya dauriya yayi shiysa ma baizo dakin sun kwanaba dan bazai iya kauda kai ba,bata hanashi ba domin tasan hakkinsa ne,yana kokarin juyo da ita ne suka ji alamun ana kwankwasa kofar parlon ba dan yaso ba yasake dan may be yan uwanta da zasu wuce.
Ai kuwa sune,sosai suka ji dadin ganinta haka,duk da sauri suka haka suka zauna akadan taba hira tare da kara bata hakuri da nasiha kafin suyi mata sallama su tafi,shatara ta arziki haka SH ya hadasu da shi domin a cewarsa komai zaiyiwa dangi Wife sun kai ayi musu tunda sun wanke sun bashi.
Haka ya zauna rarrashi har tare,takawo musu abinci suka ci kafin yasata a gaba suka zaga gidan gaba daya,sosai ta jinjinawa Abba da Ammey Domin sunyi abin ko wacce 'ya'zatayi alfahari dasu.
A parlon suka yada zango inda ya zauna ya hau bata labarai kala kala domin a cikin idanuwanta yake hango tsoro shi kuma zayi duk yadda zaiyi ta sake dashi kafin yace zayi wani abu da ita.
Ai kuwa sai ga suhaima har da rike ciki dan dariya Domin yadda yake bata labarin yan matan suke sonshi a ciki ya hadu da wata wai a cewarsa yar bariki ce lalatashi zayi ta karbe masa budurcinsa,wannan labari yasa suhaima har da hawaye dan dariya.