Chapter 12
CHAPTER 12
...Karasa zaman yan bori Inna Asibi Tayi. Talatu kuwa mayafi ta ɗauka ta bi bayansu.
Inda Allah ya rufa masu asiri kafin Nadiya ta karasa gidan malam Bawa aka yi sa'a wani kato majiyin ƙarfi ya riketa gam.
"Nadiya me kike yi haka? Ki rufa mana asiri mu karasa kai ki. Kin manta cikin kiyoshi zaki je"
"Inna Sahura wannan ba damuwata bace. Ji nake kamar In bude ido in ganni cikin gidan Malam don Allah kuyi sauri ko kuma ni in karasa."
Ta karasa maganar tana waige-waige.
Hangawar da zata yi ta hango Talatu ta nufo su a guje. Bata tsaya jiran wani abu ba ta sake fizge ta antaya da gudu.
Bata bata lokaci ba ta afka cikin gidan. Kande da suwaiba dake tsaye bakin murhu suna faman dafa shinkafar tarbar amayar ganin su Nadiya a guje ya saka suka dare kowa yayi ta kansa.
Malam Bawa da ke tsaye bakin kofarsa komai a gabansa ya wakana dariyar mugunta ya yi. Wani turare mara dadin kanshi ya dauko ya bulbula a jikinsa ya yo waje.
Ba kowa sai ƙananun yara dake fama tsanyara kukan gudawa da iyayensu suka yi suka barsu.
"Kande, Jummai, Suwaiba"
Ya daka masu uwar tsawa.
A rikice kowacensu ta fito jiki na kyar tamkar wanda suka yi ma sarki karya suka zube a gabansa.
"Wane shashanci ne ya saka zaku gudu ku bar abincin amarya, salon awaki su shigo su kwashi rabonsu ko?"
"Tuba muke, mun tuba ka yafe mana. Su ne suka shigo a guje shi ne duk muka tsorata"
Kande wadda ita ce uwar gida ta karasa maganar kamar mai shirin yi masa sujada.
"Kun manta wane ne malam Bawa ko?"
A rikice cikin hade baki suka hau ba shi hakuri suna magiya.
Gargadin karshe ya yi masu ya na fadar su tabbar sun gama girki kafin ya shiga ɗakin amarya ya fito.
Nadiya kuwa tsaye take a saman gadon karfen da Malam Bawa ya saka aka kai mata saboda ya ce kada ayi mata komai.
Alamun fita da taga tanayi ya saka Talatu rirriketa.
"Nadiya! Innalillahi... Anya kuwa ke ce Nadiyar da na sani ko dai wata ce aka canza mini?"
Turo Baki Nadiya ta yi.
"Muryar Malam na jiyo tsakar gida ni ki barni in leƙa in gaida shi ko na samu hankalina ya kwanta"
Sahura da Talatu kallon juna suka yi cike da takaicin Nadiya.
Da karfin tsiya Sahura ta fizgota ta tura saman gado.
"Ta tabbata Nadiya baki da hankali. Bayan shigowa da kika saka muka yi gidan nan a guje, tamkar awaki shi ne yanzu ma za ki fita har tsakar gida a gaban abokan zamanki ki nufi wurin miji?"
"Sahura ki barni in shaƙe yarinyar nan har sai ta daina motsi. Anya kuwa Nadiya ba hada zuciyarki mutumin nan ya cinye ba? Ni kam Sahura anya gidan Malam Bawa muka shigo. Na kula da matansa ɗaya ce kadai ta manyanta. Biyun duk yaran mata ne"
"Nima haka na gani. Amma tabbas gidansa ne"
Shuru Sahura ta yi sakamakon motsin shigowar mutum da ta ji.
Washe baki ya ke yi yana kare masu kallo.
Daga Sahura har Talatu ba wadda tayi masa kallon arziki.
"Ina yininmu, fatan kunzo lafiya. Ma sha Allah"
Malam Bawa ya fada.
"Ka ga Malam ba wannan ba ce ta kawo mu. Ba dai ka tsafe mana ɗita ba? To kada ka ɗauka ka ci riba ka jira mu wannan auren babu inda zai je"
Talatu ta fada.
Dariyar da ke ƙara bayyanar masa da muni ya yi.
"Baiwar Allah da za ki yiwa kanki adalci da kinja bakinki kin tsuke. Aure dai yadauru babu wanda ya isa ya raba shi, idan kuma za ki iya ga fili ga Mai doki"
Sahura bata ce uffan ba saboda ba abin da ya kawo ta ba kenan.
Ganin Talatu ta bude baki da zummar yin magana ya saka tayi saurin tarar numfashinta.
"Malam duk bata kai mu ga haka ba. Wannan lamari dai sai dai kowa ya dauki ƙaddara, kar mu zauna mubaya'a ƙananun maganganu"
“Sahura me yasa zaki sakamin baki, ki barni inyi da wannan tsohon banzar”
Nadiya da ke durkushe gaban Malam bawa ce ta mike tamkar wadda aka zungura.
“Anti Talatu! Mijin nawa kike zagi kike cima mutumci a gabana? Ki daina domin ina ganin sauran girmanki”
Sokoko Talatu ta yi tana kallon Nadiya.
“Nadiya! Kinsan da wa kike magana kuwa? Ni ce fa Anti Talatu kanwar uwarki Asibi”
“Ina sane da ke ce shi ya sa ma ban dauki wani mataki ba. Cikin mutumci da girmanawa nake rokonki ki daina zagar mini miji domin aljanna na fito nema. In ba haka ba kin sani miji ba fin miji ya yi ba yanzu sai in rama zagin akan naki mijin”
Dafe kirji Talatu tayi cikin kaduwa.
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!”
Da sauri Sahura ta rike hannun Nadiya.
“Ki nutsu ba zata kara ba kinji”
Dariya mai dan sauti Malam Bawa ya yi.
“Shi ya sa na ce kowa ya kwantar da hankalinsa duk karta kai mu ga haka. Ke kuma kina kokarin zo mana da taurin kai, kinga wannan”
Ya karasa maganar ya na nuna mata Nadiya.
“Ko kanki na ce ta ciro mini kafin in rufe baki ta aikata. Don haka ki bari mu rabu lafiya da ke kafin kema ki amshi rabonki, domin tun farko arzikin Nadiya kika ci saboda kaunar da nake mata ya saka n kyake ki”
Wasu yawu masu daci Takatu ta hadiye ji kaje kut.
Tsoron Malam Bawa ya cika mata ciki musamman da ta ga matansa duka uku sun shigo dakin sun zube a gabansa tare da kular abincin.
“Gata an gama ranka shi dade”
Suka furta a tare.
“Ba ku ga baki bane da ba zaku gaida su ba”
Jiki na kyarma suka hau gaushesu har sai da ya ce masu ya isa sannan suka fita.
“Bari in baku wuri tunda amarya kuka kawo ga magriba ta kawo kai, idan kuka gama ayi mini magana sai in sallameku wannan zukekiyar amarya sallamarku daban take”
Juyawar da yayi wuff Nadiya ta take masa baya.
Murmushi ya yi.
“Koma ki zauna cikin danginki da kaina zan dawo”
“To Malam”
Nadiya ta furta tare da komawa ta zauna tana rarraba ido.
“Sahura mun shiga uku mun lalace. Wane irin gida ne muka kawo kanmu?”
Talatu ta karasa maganar tana sharbar kuka.
Sahura kanta nannauyar ajiyar zuciya ta sauke.
“Ni kaina nayi mamaki wannan bawan Allah. Ban taba tunanin hatsabibancinsa ya kai haka, ki duba ki ga yadda Nadiya ke bin unarninsa tamkar tayi masa sujada. Wannan lamarin fa sai an dage da addu’a “
Shuru ya gifta na dan lokaci. “Ke Nadiya! Ki matso kusa ki ci abincin nan ni dai wallahi bazanci ba, haka kawai bansan me ya saka a ciki ba nima kada ya mallake ni duk da yasan aure gareni”
Talatu ta karasa maganar tana mai ja da baya.
“Aa bazan ci ba. Har sai Malam ya umurceni”
Kallon juna Sahura da Talatu suka sake yi a dan rikice.
Sallamar abokan tafiyarsu ce ta saka su jin hankalinsu ta dan kwanta, saboda mutuwar yawa kaka…
KATSINA STATE
GRA (government residentel area)
A get din wani rantsatstsen gida daya gaji da haduwa aka yi parking.
Mai gadi ne ya bude kofa motocin suka hau shigewa ciki.
Duk da a cikin alkyabba take tana iya hango yadda haduwar gidan ta bayyana a fili.
Bangarenta aka nufa da ita a shirye suka taras da komai an ajiye masu.
Wanka Wasila ta fara shiga tana fitowa ta feshe jikinta da turaren da Umma ta umurceta. Antinta ce ta matso kusa da ita tayi mata rada a kunne.
Tuntsurewa da dariya suka yi cikin farin ciki.
Yan mata su biyu suka shiga shigowa da kayan abinci masu yawa, suna diresu a gaban su Wasila wadda tuni ta hau watse hakora domin wani abun ma bata san sunansa ba.
Safiya kawar Wasila kuma yar uwarta ce ta fara magana.
“Wasila kinyi dace wannan aljannar duniyar duk ke daya?”
Lemun data kai baki ta yi saurin fiddowa.
“Ban gane ni daya ba, to da ni da ke ne zamu zauna?”
“Mayar da wukar kawata. Ni na isa ai sai dai in raba a wurinki in dangwali arziki”
Shewa aka kwashe da ita.
“Wasila! Kin kula da matar da na gani ta fito daga cikin daya daga dakunan part dinki kuwa? Wata kyakykyawa mai ciki”
Anti Nafisa ta karasa maganar tana kallon Wasila.
“Ni ma na kula da ita lokacin da zamu shigo. Wata kila dangin Kasim ce”
Wasila ta fada cikin ko in kula.
Sallamar da suka ji anyi masu ce ta saka su kallon kofa.
Da mamakinsu matar nan ce mai ciki sai faman fara’a take yi masu.
“Sama cewa na yi bari in zo in tanbaye ku akwai wani abu da kuke bukata?”
Murmushi anti Nafisa tayi “Aa wallahi bamu bukatar komai wannan tarna da kuka yi mana ai munji dadi kun gama mana komai”
Tsayuwa matar ta gyara tare da dafe cikinta tana murmushi.
“To Alhamdulillah! Amarya sannu da shigowa wannan gida me albarka”
“Sannunmu dai sai dai baki fada mana sunanki ba”
Cewar Anti Nafisa.
“Suna na Zainab. Ni matar Kasim ce”
Lemun da Wasila ta kurba ba shiri ya dawo mata har ta hanci. Sauran jama’ar dake dakin baki bude cike da mamaki suke kallon matar…
Meenat