1
💕NUFIN ALLAH💕
By
Anisa Muhammad
Allahumma salli ala Muhammad wa ala Ali Muhammad kama sallaita ala Ibrahim wa ala Ali Ibrahim inna ka hamidum Majid Allahumma bareek ala Muhammad wa ala Ali Muhammad kama Barak ta ala Ibrahim wa ala Ali Ibrahim inna ka hamidum Majid
I hope zamu ilimantu kuma munishaɗantu dashi, idan akwai mistake din da nayi feel Free to advise me, saboda wannan ne novel dina na farko da na fara rubutawa
Page 1️⃣
Ɗaki ne me rangwamen haske saka makon duk wutan dakin a kashe suke,
Saidai hasken dayake shigowa ta window yasa ake dan ganin cikin dakin, kana Jin karar iska mai karfi alamun nan bada jima wa ba zaa iya tsugewa da ruwa mai ƙarfi, sai walkiya ake tayi.
wani walƙiyar aka kara yi, a lokacin ne kuma na hango wata yarinya a gefen gado ta hade kai da cinya, saboda rashin haske bana ce ga kaman nin ta ba Amman dai zan iya cewa Allah yayi mata baiwar gashi, ba Dan kwali akanta gashin nata har gadon bayanta mashallah abun gwanin ban Shaawa.
Wani tsawan aka karayi sai Kuma ruwa ya tsuge shaaaa kamar da bakin kwarya, ita Kuma yarinyar sai kara duƙunƙune jikinta take tana kara tura fuskanta cikin cinyar ta tana sake fashewa da kuka.
kofar dakin nata aka bude aka shigo, sai aka kunna wutan dakin, wata dattijuwar mata naga ni tsaye, yar baƙa Amman baƙi mai kyau kana ganinta kaga black beauty, tanada kiba Amman dayake tana da tsawo sai tsawon ya shanye kiban ga dogon hanci da idanu masu kyau mashaallah.
Dan dariya ta saki kadan tace ''habibty taso muje dakina mu kwanta ko tunda dai baa dena tsawar ba"
Sai a yanzu ne budurwar ta dago na ganta da kyau, ya subhanallah, kai Allah yayi halitta afuskar baiwar allah nan, ita baza'a ce mata baƙa ba Kuma ba fara ba, wanka tarwada.
ga ido mashallah, cikin idon nata fari tasss harwani shining yake, ga hanci, Dan hancinta yafi na dattijuwar matan tsawo, ga lips dinta Dan karami pink colour.
Tana bude baki dan tai magana naga teeths dinta farare sol gasu en kanana ajere tace
"Ni dai hayaty kibarni na kwana a dakina, nafison kwana anan, baso nake ina kwana adakin mutane ba" ta faɗi a shagwaɓe,
Tana magana dimples dinta suna lomawa.
Haɓan ta takama tace "ahh ni naga ikon Allah agurin wannan jairar yarinya, nice ma waansu mutanen kenan koh"
Ido ta zaro tace "hayati bafa haka nace ba kwai nafison kwana anan ne"
"Kinci gidanku, tashi kiwuce mutafi, nagaji da tsayuwa bacci Nike ji, kalli yanda kika duƙunƙune a gefe kina wani mazarine tsoro, shine kike so in barki ki kwana anan, tashi maza mutafi"
Haka ta tusata gaba suka tafi badan ranta Yana soba.
Ita Kuma tayi hakan ne saboda tasan In tabarta ba bacci zatayi ba, dan shegen tsoro gare ta kamar farar kura, shiyasa gwara ma suje dakin nata koda ba suyi baccin ba ko karatu ko hirane ma suyi.
Da asuba suna tashi sallah sukayi, zata koma bacci ammi tace tayi karatu koda izu dayane kafin ta kwanta.
Nan fa ta hade rai tafara ƙunƙuni kasa kasa.
Abu ɗaya da Anisa shine gashi dai bata wasa da sallah Kuma tana azkhar safe da yamma amman Banda wannan sai ammi ta sata gaba kafin tayi addua ko karatun qurani, har gwarama karatun qurani yanzu ta farayi idan ta idar da sallahn magriba. Shiyasa ammi ke fatan Allah sa hakan ya daure.
da badan ammi jajirtacciya bace ai da ba hakan bama.
Duk yanda suke wasa da dariya datayi ba daidai ba take kwabar ta, in na nasihane tayi mata.
ga shaƙuwarsu kamar ta ƙawaye, Dan duk wani sirrin Anisa ammi kawai take fada ma, kokuma pickles wani lokacin, saboda tanada zurfin ciki, bata yadda wani yasan sirrin ta ba; ammi kawai tayarda tasan halin da take ciki.
Haka takaranta baqara izu biyu ta koma ta kwanta, abun mamakin da kai ta karanta bada qurani ba, ashe hafiza ce Amman take wasa da karatunta, Kuma ammi na yawan fada mata ta Daina wasa da karatun qurani sbd tsari ne daga duk wani sharri kuma taringa addu'ah, sbd duniyar nan kayi ma ya aka kare bare Kuma baa yi, baka san masu binka da sharri ba,
A wasu lokutan karatun qurani shike ƙara kare mu tare da addu'a koda wani abu ya so ya same bawa bazai yi tsanani kamar idan baya addu'a ba, kuma addu'a na ɗaya daga cikin abinda ke ƙara kare bawa a kowani lokaci dan haka mu ringa kiyaye addu'a da karatun qurani
Barin ma mahaddata, zunubi ne ga mutum yayi hadda ya barshi ya tafi a banza, gyaran hadda yafi yin sabo wuya
duk wanda ya bar Qur'ani da kwana ɗaya zai barki da sati, in kin barshi da sati zai barki da wata, inkin barshi da wata zai barki da shekara, dan haka ya kamata mu kula,
Sai tace "hayatyyyy" Ta marairaice fuska "ai zan gyara kidaina fada danallah zan nayi"
Ita ko sai tace "ahto karma kiyi kanki, in bana nan zanga waye zai dinga fada miki"
"hayaty Banda ma abunki, karama Dani waye zai bini da wani sharri, me nama wani"
"Sai kin ma wani wani abu aka cemiki?? Wanda baya sonka wani ai ba wani abun ake mai ba yake nufar mutane da sharri"
"Toh naji nidai hayaty abar zancen bacci" ta fada tana lumshe ido.
Da safe da tashi tana fitowa parlour taga ammi na mopping, sai kawai taje ta baya ta rungume ta
"Kee sokike ki kada ni halan?" zagayowa tayi gaban ta amma bata sake ta ba tace
"Hayaty na sorry na barki kina ta aiki ban tashi ba, mezan tayaki?"
"Mtswww ni sake ni kafin ki fadar dani ki wuce kiyi wancan wanke wanken ki daura breakfast"
Zaro ido tai waje tace "ammi bakiyi breakfast ba wallahi Dana ga kina mopping, nayi tunanin kin gama komai"
"Ai dayake baiwar kika ajje da zan gama miki aiki in miki breakfast, kina bacci in yi serving naki breakfast on bed right "
Girgiza kai tayi tana Danne dariyan ta saboda yanda ammi tai kicinkicin da fuska
Sai tace "haba dai hayaty yanzu zanje inyi karki damu, ke zanyi serving breakfast in bed, kije ki huta" tafada tana amsan mopern hannun ta tacigaba da mopping din.
Murmushi ammi kawai tayi tana adduar Allah ya cigaba da dauwamar dasu cikin farin ciki aranta,
Tasha wahala arayuwa, amma it's worth it, tunsa a sanadin haka Allah ya haɗa ta da mijn da har ya koma ga Allah tana alfahari dashi, Anisa bata taɓa ganin mahaifin taba dan tun kafin a haife ta yarasu,
Indai zata kalla ɗiyar tata da mahaifinta take tunawa.
"Allah dai yajikan abhi" tafadi tana share kwalla
"Ameen" sai tajuyo ta kalli inda Anisa take sai ita Kuma tamata murmushi tana kokarin danne nata hawayen
Sai lokaci ta San cewa afilli tai adduan kawai tasake kallon tilon ƴar tata ta koma daki.
Morping din ta cigaba tana tunanin burinta nason zama doctor, saboda ceton waanda basuda ƙarfi, in ta tuna yanda talaka ke shan wahala da fuskantar wulaƙanci a wasu asibitin gwamnati yasa sai taji zuciyar ta tayi nauyi.
tana son ammin ta Kuma zata iya sadaukar da komai akan tilon mahaifiyar ta, ɗaɗɗai kun al'umma ne masu iya taimakon ƴanuwansu da waɗansu marasa ƙarfin amman dayawa wasu masu kudin iya nasu suka sani
Wasu ma iya kansu da yaran su basa taimakon dangi da ƴanuwa sai wanda sukaga dama, Kodayake zumunci yanzu ne ya koma haka sai wanda ke dashi za'ayi tarayya dashi.
In ta tuna wannan sai taji aranta dole ta jajirce tai karatu ta zama wata yanda zata tallafawa talakawa da mabukata
Duk wannan abun ynx Anisa a SS3 sune zasuyi SSCE wannan year din, gaba daya 17 take Kuma burinta ta zama babbar medical doctor. sbd taringa taimakon waanda basuda ƙarfi.
Cigaba tai da aikin ta har tagama tai musu preparing toasted bread da tea takai musu dakin ammi suka ci.
Suna gamawa taje tai wanka ta dau wayanta tafara kallon Korean dramas dinta
___________________
By
Anisa Muhammad yahaya🌺