NUFIN ALLAH

2

by @anisamuhammadyah897

💕NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


Page 2️⃣


Tana cikin kallon ne taji an ɗaka mata duka a baya, dayake a rigingine take, a zabure ta tashi tana susa baya, ta kwabe fuska danta san wanda ya dake ta.

"Kaiiiiii Wallahi Allah ya isa pickles, kin dau hakki na" tana magana tana hararar ta.
Itako wadda aka kira da pickles din dariya take me sauti tace "wai wani film kike kallo haka har na shigo baki ji ba"

"Bansani ba kije kiyi downloading naki, baza akalla awaya ta bayau, tunda ba abunda kika sani sai cin zali, muguwa kawai" tafadi tana kara ɓalla mata harara.
"Ke wallah sai na gani muga sunan film din kawai"
"Tunda kina da ƙarfi sai ki kwata mu gani ai, tare da Amma kuka zo???"
"Eh tare muk....."
Bata gama rufe baki ba Anisa ta diba da gudu sai parlour, tana zuwa taci burki ganin ya Ahmad, kawai sai ta kalli kanta ta ɗago ta kalli inda yake, shima idon shi akanta yake saboda yanda tashigo parlourn da gudu. kawai ta Kara kwasa ta koma daki.
Shikuma murmushi ne ya kubce masa yana girgiza kai.

Itama Amma murmushi tai tana cewa "ko yaushe Anisa zata girma oho"
Ammi ce tace "kedai kibar wannan ƴar taki da sokanci" ta ɗanyi tsaki tana Kiran "Allah kyauta".
Tana komawa daki ta samu jalila kwance ta bararraje tana kallon film din da tabari, 

Itama dagewa tayi takaimata duka a cinyarta, tace "shine baki ce da ya Ahmad kuke ba" tafada tana kwabe fuska Dan Allah yayi ta da shegen shagwaba.

Jalilace ta kalle ta tace "dazan fada miki ba fita kikai a guje ba, to ni ban iya wahalan binki abaya shiyasa"

"Amman nagode pickles da wulakanci" ta fada tana hararar ta tace "jibi fa yanda nake"

Kallon ta tayi ta kwashe da dariya, rigane ajikinta na bacci shape din ta ya fito aciki mashallah in kaganta kamar ita tai kanta. 
Rigar ko guiwa bai karasa ba Kuma ba dankwali akanta.

Sai ta Kara kwashewa da dariya tace
"To meye aciki ai yayanki ne kika sani ma nakoma kanwar ki instead of yayarki"

Duka ta Kara kaimata tana Kiran "kefah wallahi you are not serious, Allah kin iya fadin rubbish, yah Ahmad din, to bada ni ba so kike zulaiha ta cinye ni danye dan kinsan yanda take son ya Ahmad"
Hade rai jalila tai tace "Wallahi pixie kin ɓata mun rai me ya kawo maganar waccan mara head din, ai koda ace ke bakyason ya Ahmad ban fata ya auri zulaiha Dan karasa tarwatsa family kawai zaayi, har gwara ma ahada shi da nabila wallahi dan na lura kamar dai akwai wani abu tsakanin su''
Ta fada tana wani shan mur.
"To masu Yaya" kawai abinda tace kenan tasa hijab tayi parlour.

Ita Kuma ta cigaba da kallon perfect crown dinta, Korean film din ya mata, da tasan haka yayi kyau da tun Yana fitowa zata kalla, Amman yanzu ma bai ɓaci ba tana komawa zatai downloading ragowan ta kalla.

A parlour tana fitowa Ammah tace "kin gama gudun" kai kawai taduƙar taje gabanta tabata side hug, tana cewa "Ammah nayi missing naki sosai fah"
Dan tureta tai tana hararar ta tace "kika ce zaki zo last week ai na ganki" 
Kunne ta kama tace "sorry Ammah ta takaina" tadan yi pecking kumatunta.
Dariya kawai Ammah tai tace "Allah shiryamun baby na"

Ya Ahmad ne yayi gyaran murya yace "ni ba'a sanni ba kenan bare a gaida ni" dariya ammi tayi takalli family dinta abun Sha'awa tana tuna yadda rayuwar su ta gabata ada'.

Zuwa tayi ta gaida ya Ahmad Yana amsawa sai tace "ya yayarmu zulaiii" tsaki yaja Yana hararar ta Dan daman sun saba 
"Wallahi so kike in bige ki wuce kibani guri, banson gaisuwar taki ki rike kayanki"
Murmushi tayi tace "Nina tafi gurin pickles, na barta ita kadai" tayi waving mai hannu alamun bye
"Yace kedai kika kasani".
Tana komawa tace "keeee wai ya maganar shirye shiryen da abubuwan da zamuyi na grad din mu, ki ijje waya muyi magana"

Juyowa jalila tayi ta ja mata tsaki tana cewa "to sannu ƴar rainin wayo tun yaushe nake jiranki kizo gida muyi magana Saida nagaji, daga cewa bara ki dawo ki ɗauki abu sai yau dana gaji nace bara in biyo Ammah da ya Ahmad tukuna zaki tuna"
"To naji naji sorry yanzu dai muyi magana"

"Ina ganin musa vage colour material da light din Jersey veil koh??"
"Aa Gaskiya dark blue din material d sky blue din veil"
Haka sukai ta discussing irin shigan da zasuyi da sanda zasu bada dinkin material din.

 Ammah ce ta shigo ɗakin tace su fito a daura launch. fitowa sukai suka daura.

Har sun dora ruwan rice ne da stew ya Ahmad yace "ni wallahi danwake nake craving na kwana biyu banci ba"
"Kai yaya yaushe muka ci danwake ko 3 days baayi ba, kawai dai kace ayi best abinda kafiso"
 Bayan sun gama ɗanwaken ne suka koma suka yi sallah suka cigaba da kallon Film din su.

 Basu suka Ammah suka tafi ba sai after magriba.



___________________
By 
Anisa Muhammad yahaya 🌺