MASIFAFFAN NAMIJI

38

by @jamilaumarjanafty

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty💞*


HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
Contact Hijabs Corner by Janafty for all kind of Qualitative hijabs for women of class.
*** ZARIA/KADUNA Natio wide delivery.

*038*

"Har Abdullahi yakai Office yana Tunanin maganganun Barkat Abun ya Dauremai kai matuka kuma Kaso mafi yawa Daga Cikin kimarta sai yaji Ta Ragu ba saboda komai ba sai Saboda Ta Nuna Kishinta karara akan Hafsah har kuma Hakan ya saka mata Tsanarta acikin Ranta Batare da ta mata komai ba..Miye laifin Hafsah..? Itafa tazo ta isketa da Mijinta Suna Rayuwansu Ta Shigo Cikinsu Ashe kuwa indai Ita bata Bude baki Tace tana Shigar mata Hanci bai kamata ita Barkat din Tace Haka ba,Domin Shi yana da yakini kan Hafsah 100%Bata da Tunani ko Zuciyar Cutar da Barkat Tana Zaune da ita ne Tsakaninta da Allah.

Tagumi kawai ya Zuba Lokaci Daya yana Cigaba da Auna Abubuwa masu Girma Ta Bangaran Hafsah da Barkat,Ko kankani basu ma Daidai ba Domin Akowani Mizani in ya Auna sai yaga Hafsah Tayi ma Barkat Fintinkau Bata iya ma Tsara da ita,Ta Bangaran Hakuri,ta mata Zarra ta Bangaran Ladabi da Biyayyah Wlh zai bada Rantsuwa kan cewa Duk Matan Duniya Ba Mace mai Ladabi da Biyayyah Uwa Uba Hakuri Bayan Hafsah,Sai kuma Bangaran iya Mu"amala da kuma Yadda zata Tafiyar da zamantakewarta Yafi kowa sanin Wacece Hafsah bai Taba Jin wanda ya Fadi aibunta ba Kama Daga Danginta Zuwa Danginsa ba,Hakika Tayi Gadon Dattako da kuma kyawawan Halin Iyayenta,Ya sani Mama Tamkar uwa take gareshi Ammh Ita kanta tana Girmama Hafsah,Umman Sadiq ita ta Haifeshi ammh Tafi Girmama Bukatun Hafsah Fiye da nashi Bukatun Kuma Tana Fadamai koda yaushe sukayi mgana kan ya Rike Hafsah da gaskiya da Amana Domin In ya bari ya Rasata ko kuma Giyar Rudin Duniya ta Sameshi ya Wulakantata Toh Tabbas Watarana zai yi Nadama,Kuma zai yi Kuka da idanuwansa Domin bazai Taba sanun mace kamarta ba bai kara gasgasata mganar Umma ba sai yanzu Daya Auro Barkat yaga Bambamce Bambamce Halayyah Da yawa ta Bangaran Hafsah sai kuma yanzu yake Tunanin kodai mganar Nazifi gaskiya Bayan Hafsah ba Macen da zata iya Hakuri ta zauna Dashi..?

Gabadaya Ransa yana Jagule ne Dakyar ya iya yakice komai ya maida kai ga aikinsa ammh Kuma Gefe Daya na Zuciyarsa na karfafamai Gwiwan Takama Barkat din Burki Domin Bazai Lamunci ta Raina mai Mata ba gaskiya Indai Hafsah batace ta Tsare mata komai ba itama bata da Wannan Damar da zata Fadi Wata mgana kan Hafsah Domin akomai Da take ganin Hafsah Ta mata Fintikau Halayyanta ne suka Siya mata Duk Wannan Kimar Datake gani tana Kishi akanshi.

******

Baiwar Allah Hafsah bata son Wainar da Aka Toya da safe Tsakanin Abdullahi da Barkat ba Dama Jiya ita ta Fita Girki Barkat din ta karba,Da Safe kuma Abdullahi ya Shigo mata Sallama ya isketa tana Wanka Su Amira Kuma Daman Mai mashin Dinsu ya kira yakaisu so basu Hadu ba Balle Taga Cikin yanayin Daya Fita Noor kadai Dake kwance kan gado yayi ma Wasa ya Fice.

Har Wajen 12pm na Rana bata ji Motsin Barkat ta Fito ta Daura Girki ba sai Abun ya bata mamaki Ta sani da Wuri take Gama Girkinta,Sai Tayi Tunanin kila Girki Daya Zatayi ammh sai me Har Pass2 shuru bata ji Motsinta ba Duk da haka dai bata Fito ba,Tana Daki Ita da Noor Dataji yunwa Sai Ta Hada Tea tasha,Har Amira suka Dawo Makaranta Barkat bata Fito ba Suna Ta Tambayan Abinci sai ta Hada musu Complex suka Sha Suka kwanta kafin Lokacin Islamiya sai Lokacin ta Fito Tsakar gidan Abun mamaki Dakin Barkat din ma na Bude ammh Kwata kwata ba Motsinta sai Hafsah ta Fara Tunanin kodai Bata da lafiya ne..? Kamar zata Shiga sai kuma ta Fasa Tunda Daman bata Shiga Dakinta sai ta kama Kuma Daman yau din Barkat din bata Leko Ta mata gaisuwan Safe da Abdullahi ya kafa Dokar Haka ba, sai kawai Zuciyarta ta bata ba lafiya.

Dakinta ta koma,Itama takwanta ita da Noor sai Hudu Saura Tatashi Tayi sallah tatashi Su Amira sukayi sallah sukayi Shirin zuwa islamiya,Ta rakasu Har Kofar gida kana ta Dawo Cikin Gida,Tayi Tunanin ta Kira Abdullahi sai kuma ta Tuna yana Office yana aiki bazata so ta tayar mai da Hankali ba,sai kawai ta Share acikin Ranta kuma Tayi Wani Tunani inda Barkat din Tana so ta san Tana Cikin wani hali ko bata lafiya da Ta Kirata ta sanar da ita Tunda suna Gida Daya amfanin zaman Taren kenan ammh Tunda taki Fitowa bata Bukatar wani ya sani kenan kawai sai ta Fita Batunta ta kama Harkan gabanta 

Ganin Har 5pm na yammah Tayi Shuru bata Ji Motsin Barkat ba sai kuma Zuciyarta ta kasa Natsuwa Batare da Tunanin komai ta Isa ga Kofar Dakin Barkat din Tana Doka sallama ammh kuma Shuru ba"a amsa ba,Sai kawai ta Tura labulan Dakin ta Shiga Falon ba kowa Ta kara Rangada Sallama taji ba"a amsa ba Sai Tsoro ya kamata ko Barkat din na Cikin wani Hali da Sauri Tana goye da Noor abayanta ta Tura Kofar Bedroom din ta Shiga Lokaci Daya Tana Kiran Sunan Barkat din.

Abunda ya bata mamaki yasa ta Dakata bata karisa ga Shiga Cikin Bedroom din na Barkat ba ganinta Zaune Gefen gadonta ta Kishingida da Gadonta taci Kwalliyarta Cikin Riga da wando Wadanda suka kamata kanta ba Dankwali tasaka Band ta Daure gashinta kafarta kan Daya tana Taunan Cingam gefe Daya kuma Tana ta latsa wayarta Kamar ma bata ji Hafsah ta Shigo Tana sallama ba, Tare da Kiran Sunanta ba.

Mamaki ya kara kume Hafsah ta Bita da kallo kafin tace"Ikon Allah Barkat lafiya kuwa..?kina ji ina ta sallama baki amsani ba kamar ba yar musulma ba..? Tafada tana kallon Barkat din Wacce tayi kamar bata jita ba Sai Ran Hafsah ya baci ta kada kai Tana Fadin"Allah ya baki Hakuri dana Shigo Miki Daki ..Dama Shuru naji Duk yau baki Fito ba, Sai nayi Tunanin ko lafiya Shine na Shigo na gani Saboda Hakkin zaman tare ammh Alhamdulillah Tunda kina Lafiya.."Daga Haka ta Juya Zata Fice Barkat ta Dago Tana mata wani Wulakantattacen kallo Idanuwanta sun kumbura alamun Tasha kuka Mikewa zaune Tayi Tana Fadin"Ina Jinki Kina Sallama Kawai banga Damar amsawa bane..Mganar kuma Kinjini Shuru ina Abunda ya Dameki ai ba zamanki nake ba balle Fitowata ko Rashinta ta Dameki,mganar kuma zaman tare ke kika sanshi Malama ba Wata Amana Tsakanina da Kishiya Saboda haka karki kara Shigomin Daki Daga yau Kowa Tashi kawai ta Fissheshi Malama.."Tafada tana wani Karkace kai tana Jifan Hafsah da wani kallo na, na Gama Tsanarki.

Hafsah Data Waiwayo Tana kallonta Tunda ta Fara mgana Mamaki ya Cikata ta Bude baki kawai Tana kallonta,Dakyar ta iya Rufe bakinta kafin tace"Ai Shiyasa na Fara baki Hakuri Da Farko..Mganar kuma Ba zamana kike ba Duk bai taso ba Dukkanmu muna karkashin Mutum Daya ne..Dama gani nayi ke keda Girki kuma kinki Fitowa ga yara sun Dawo makaranta Dazu suna Jin yunwa Complex na Hada musu suka Sha suka Tafi islamiya kada su Dawo kuma su sakemin kukan yunwa bana so na Shiga Hakkinki Ranar girkin ki na Shiga Kitchen ina Girkin Hakan ba Dadi Shiyasa na Shigo na gani ko Baki lafiya ne sai na Tambayi Izininki na Girka kodomin yara da kuma Abban Amira da zai Dawo Daga aiki a gajiye yana Bukatar Abinci.."

Har tagama Bayaninta Hararanta Barkat take sai da ta ida kana ta Mike tana Tafa Hannuwanta  Lokaci Daya Tana Fadin"Wow..Bravo..Hajiya Hafsah...kinyi iya Tsara kalamai ba Shakka sai dai kuma kin makara bazasu Taba Tasiri a kaina ba Munafuka mai Fuska Biyu,Dama tun Shigowata Gidanan nasan Sai kin kawomin Mtsala azamana da Mijina gashi kuma kin Fara Tunda komai nayi mai baya gani sai ya ambaci Sunanki kamar don ke kadai akayi Shi Bazan Boye miki Na Tsaneki Kuma Allah ya isa Tsakanina Dake Tunda kina son Rabani da Mijina.."Tafada Idanuwanta sun kawo Kwallah baki Hafsah ta Bude tana Bin Barkat da kallo kafin tace"Ban..Bangane ba Ni..."Dillah Rufemin baki Karya nayi Ke ba Munafukar bace..? Har kina wani kokarin cewa baki gane inda na Dosa ba da anyi mgana sai ace ke mai Hakuri Hafsah mai Hakuri Hafsah me kaza..! Kan me nima ai mace ce ki barni nasamu Sakewa mana Nida Mijina Don Allah ki kyalemmu hakanan Bana kaunar ina Tare dashi naji yana Ambatan Sunanki Raina na kuna Kamar zan Mutu nake ji..Na Rokeki ki barni da Mijina Don Allah mganar Girki kuma in kin matsu ki Girki kici Keda ya"yanki kuma In kika Kuskura kika bama Mijina Wlh Allah ya isa ban yafe ba kuma sai Allah ya Kamaki da Cin Amanata Ranar Girkina.."Tafada Lokaci Daya Tana Haki Da Share Zufan Dake Digo mata Daga saman Goshinta.

Harta gama Mganarta Hafsah na Tsaye Tana kallonta Zuciyarta na kuna Idanuwanta Suka Cika da kwallah sai Tayi Saurin Dannewa ta Dago Tana Mirmishin Dayafi kuka Ciwo kafin tace'Naji Duka maganganuki..Sai dai ban isa na Sauya Miki Abunda ke Ranki game Dani ba.Ammh ina so ki sani ko ki yarda ko karki yarda Wlh Tallahi Ni Hafsah da Zuciya Daya Nake Zaune da kowa bama ke ba..Mganar kuma na barki da Mijinki Dama ni Ina Ruwana..? Inace Girki Arabe yake kuma kowa baya Shiga Hakkin kowa..?mganar abinci kuma zan Dafa kodon Ya"yana kuma nayi Miki alkawarin Insha Allahu Bazan Bama Abban Amira ba ballatana Allah ya kamani da laifin Cin Amana Daga karshe ina mai Baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba.."Ta karishe Fada tana jin wani Daci akasan Ranta lokaci Daya ta Juya ta Fita Daga Cikin Bedroom din Barkat din ta Rakata da Dogon Tsaki Lokaci Daya Tana Fadin"Stupit kawai.."Kafin ta koma ta kwanta tana kwafa Tana jin kaso Mafi yawa Daga Cikin bacin Ranta ya Ragu Tunda ta gayama Hafsah Abunda ke Ranta ammh Duk da Haka bata Huce ba tana ji kamar ta kasheta saboda Kishi da Haushi.

Hafsah kuwa koda takai Dakinta bata gani saboda Hawayen Daya wankemata ido kan kujera ta samu ta Zauna tana Kuka,tana Tunanin yau ita Barkat ke Kira Munafuka..me tayi mata..? Bata son komai ba Tsakaninta da Mijinta ba..In Hakane toh sai tace me.? Wani irin Abu ne Abdullahi baya mata Tataba Dora laifin kan wani..? Kodon mai Kishiya bai Mutuwar Allah me yasa take Zarginta..? Ta kasa gane komai sai Tayi kukanta ya isheta kana ta Share Hawayenta Ta kuma yi kokarin Cire Abun Acikin Ranta da Tunanin kirkiro ma kanta aikin Dazatayi wanda zai Dauke mata Hankali.


Wankin Noor da Uniforms dinsu Amira ta fito dashi ta wanke,Ta Share Dakinta Ta gyara Ko"ina Tayi ma Noor wanka ta goyata Gabda mangariba su Amira suka Dawo Daga makaranta Ta umarcesu da suyi alwala suka yi Sallah Tare bayan sun gama Ta Dauko Qur"ani suma tace su Dauko ta Shiga yi musu karatu Noor na Goye abayanta tayi Barci

Sun Dade suna karatun Kafin tace su Maida Qur"anan Su Dauko Littafan Bokonsu su yi Aikin da aka basu,Suka tashi Suka Dauko Ita kuma ta Mike tana Tunanin gwara ta nemi Abunda Zata ci ita da ya"yanta Shayarwa Take tana Bukatar Abinci Sosai Wuni kawai tayi Shan Ruwan Tea,su kansu su Amira yunwa Sukeci Karamin Hijabinta ta Sanya ta Dauki karamar Fitila mai Batir Dayake Sun Dauke Wuta ta Shiga Kitchen tana Goye da Noor ta Fara Jajjaga kayan Miya kafin ta Kunna Gas Dinta Wanda Abdullahi ya gaji ya Siya mata ta Dora Jallop din Taliya.

Ta Zuba Taliyan kenan Taji an kwala Kiran Sallar Isha"i yasa ta koma Daki Tayi sallah taso ta Shinfide Noor Daga Bayanta Ganin tayi Barci Ashe barcinta bai yi Nisa ba ta Farka ta Fara kuka Dole ta zauna ta bata Nono Ta mikama Amira ita,ta koma Kitchen tana Duba Girkin nata,Ita kuma Noor an Tsigeta Daga Nono bata Koshi ba ta Fara Kuka Hafsah kuma na kokarin Sauke Taliyan ta kashe gas ta Zuba musu sai ta Shigo Gabadaya Taji Karan Mashin Din Abdullahi da Shigowarsa.

Da kukan Noor ya Fara Cin karo Tun kafin ya kafe mashin Din ya sauka ya Fara Fadin"Kukan wa nake ji haka..? Noor ce ina Hafsah din take ne kika bar yarinya nata Tsala kuka..? Ya fada yana Sauka Daga kan Mashin Din Lokaci Daya yana Saba karamar jakarsa,Hafsah Data kashe gas ta Leko Daga Kitchen Tana Fadin"Ga ni nan Abban Amira Ina Kitchen ina Kokarin sauke abinci karya Kone..Kuma ma fa yanzu nagama Bata Nono da zan Fito na bama Amira ita ta Riketa Haushin na Cireta anono bata koshi ba yasa kaji tana yanka wannan Ihun kamar wacce ake yankata.."Tafada Tana kallonsa Cikin mamaki Abdullahi yace"Abinci kuma..? Ina ita Barkat Din Da bata Girka ba ko ba ita keda girki ba yau..?

Hafsah Cikin Halin ko In kula ta Juya Zuwa Kicthen din Tana Fadin"ita keda shi mana..Bata Girka bane.."Cikin Kakkausan Murya yace"Saboda mene..? Hafsah ta Fito Dauke da kulan Abinci da Filet Filet na Zubawa Tana Fadin"Bansani ba Abban Amira.."Tafada Tana kokarin Daidaita kanta Ta gabansa ta Wuce tana mai sannu da zuwa Bayanta yabi Zuwa Cikin Daki Acikin Ranshi yana Tunanin Lalle Barkat ta Rainashi ya kuma Zama Dole ya nuna mata kalansa.

Yana Shiga Amir ya taso yana mai oyoyo,Ya daukesa Lokaci Daya ya karisa kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ya zauna Kafin ya Sauke Amir Noor ya karba Hannun Amira yana Lallashinta Lokaci Daya yana Kallon Hafsah wacce ke kokarin Zuba ma su Amira Abinci yace"Kinga Bar Zuba abincinan zo ki karbeta ki bata Nono Tana ta kuka Fa.."Tana Zuba Abincin Tace"Rigimarta ce kawai fa Abban Amira bata da yunwa.."Cikin Daga Murya yace"Wani irin Rigima yarinya na Kuka kina Gayamin Rigima..? Kizo ki Amsheta nace bana son Gaddama Kin sani kuma.."Ya fada muryansa Tana Bayyana yadda Ya Hassala Jin haka yasa Bata kara mgana ba ta Tura ma Su Amira Filet din data Zuba Musu Taliyan Tana Fadin"Oya kuje Tiolet ku wanko Hannuwanku ga abinci kuzo kuci ku kwanta Gobe akwai School."Suka Mike Tare Amira tana Fadin"To Mommy.."kafin su wuce Zuwa Cikin Bedroom Din Abdullahi ya bisu da kallon Sha"awa gefe Daya kuma yana Jinjina Hafsah Domin Bata wasa Wajen Tarbiyansu Shiyasa koda yaushe zaka gansu Cikin Natsuwa da kalama.

Karisowa Tayi kusa dashi ta Zauna ta mika Hannu ya Bata Noor ,Shi ya zage mata Zif din Rigarta ta baya Ta Ciro Nonon ta mika ma Noor ta karba da Sauri  ta Fara tsotsa lokaci Daya Tana Sauke ajiyar Zuciya Abdullahi ta kallah ya bankamata Harara yana Fadin"Ji yadda yarinya ke Sauke Numfashin Wahala ammh Ana mgana kina Fadin wai Rigimartace.."Ko mgana Hafsah batamai ba Shima bai Damu ba ya Mike Kawai ya Fice Batare Daya kara mata mgana da kallo Ta Bishi Tana wani Tunani acikinta ranta Su Amira ne suka katseta da suka Dawo Falon.

Afalo ya Iske Barkat tana Zaune tana Kallo ta Dora kafa Daya kan Daya Ta sauya Shiga Tunda yanzu Atamfa ce ajikinta Riga da zani tayi wani Daurin Dankwali na Ture kaga Tsiya,Sallamansa ma Dakyar ta amsa Tunda ya Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa Kafin ya Karisa Cikin bedroom dinta ta Rakashi da Harara.

Yana Shiga Jakarsa kadai ya ijiye ya Sabule kayan Jikinsa ya Fada Tiolet yayi wanka Ya Fito ya Shafa mai ya Fesa Turare ya saka Wata bakar Jallabiya ya Fito Falon Hannunsa Rike da wayarsa Inda ya barta nan ya isketa ammh wannam karon Wayarta na Hannunta tana Dannawa Kanta ya Tsaya Lokaci Daya yana Nazarinta kafin yayi gyaran Murya yana Fadin"Ina Abincina..? Naga har na Fito wanka baki kawomin ba..? Ko sai na Roka..?

Yafada yana mata wani kallon in kikace zaki kawomin wani Raini Zaki gane baki da wayau,Banzar iska tamai ko tama san yana kanta yana mata mgana Ran Abdullahi ya baci Cikin Mamaki yake Binta da kallo kafin ya saka hannu ya Fizge wayar Hannunta yana sakin Huci Jin am Fizge wayar yasa ta Dago a Zafafe Tana kallonshi Cikin Fushi yace"Ke Bada ke nake mgana ba..? Tambayanki nake ina Abincina..?

Kai Tsaye tace"Abinci..? Ta kada kai kafin tace"Ban Girka ba..Kuma ban ga Damar girkawa ba Sai yaya..? Ta fada Lokaci Daya Tana mikewa,Wani Sororo Abdullahi yayi yana kallonta kafin ya nuna kansa yana Fadin"Ni..Ni kike cema Baki Girka ba kuma baki ga Daman girkawa ba Barkat..? Yafada yana Nuna kansa Wani Rausayar dakai Tayi Tana Fadin"Eh kaifa..Ban girka ba nace zan maka karya ne..?Dama na bari ne sai Ranar da na koyi Hakuri da Biyayyah irin na Hafsah sai na Cigaba da girkin..!

Tafada tana wani Girgiza kai Abdullahi da Zuciyarsa ta Fara Tafarfasa yaji Ta kawo mai Wuya Yana Tunanin wani irin Raini ya auro ma kansa,Tunda yake ba Macen da tataba mai irin Wannan Salon Rainin da Barkat tamai,Tuni Idanuwansa Suka Sauya launi Jijiyoyin kansa Suka Tashi Radau Kallonta yayi ido Cikin Ido kafin yace"Kin san kuwa wa kike gayama Mgana Haka..? Nifa Mijinki ne ko kin manta ne..?

Ta Koma ta Zauna Tana Fadin"Nasani mana..Ba Abdullahi bane Mijin Hafsah ba.."Tafada tana Sakarmai ido,Wani Irin Zafi yaji Ransa na masa kamar ya Daga Hannu ya Zabga mata mari sai wata Zuciyar ta kwabeshi,ganin in ya Cigaba da Tsayuwa Wlh sai Barkat taci Ubanta  kawai sai ya Wurgamata Wayarta ya kada kai ya Fice ta Rakashi da Mirmishi kafin ta Mike ta Dauki Wayarta Tana Fadin"Dama Ashe ni na bada Dama ake min Abunda aka ga Dama.."

Yana Fita Fuu sai Dakin Hafsah Tana Zaune tana Cin Abinci Noor na kan Cinyarta,su Amira sun Shiga Ciki sun kwanta, ya Fado Dakin Har sai da ta Tsorata Kusa da ita ya zauna kan kujera Yana Kallon Hafsah Wacce ta Dakata da cin Abinci Tana Fadin"Abban Amira lafiya kuwa..? Muryansa Cikin Kaushi yace"Tashi ki Sawo min Abinci.."Kawai ya iya Fada yana Sakin Huci Sama sama Galala ta Bisa da kallo Bata samu Zarafin mgana Ya Daga Murya yana Fadin"Ki tashi ki bani Abinci nace ko..?

Ya fada Cikin Fushi yana Tsareta da ido ajiyar Zuciya ta Sauke Data gano Dalilin Masifar Cikin kwantar dakai Tace"Sai dai kayi Hakuri Abban Amira na Riga nayi alkawarin Bazan baka Abincin nan ba..? Ido ya sakar mata Yana Fadin"What.? Saboda mene..?

Kai Tsaye tace"Saboda bana son Amanar Barkat ta kamani...Tunda ba Ranar girki na bane bani da Hakkin baka abinci."Bata gama mgana ya Mike a Fusace yana Fadin"Wannan ai Zencen banza ne..? Kina matata kuma a kawomin wani iskancin banza acikin Gidana Uban waye kuma yace miki haka.? Ehe nace waye yace zaki ci amanar barkat...? Tunda ita bata Girka ba Hakkinki ne ki Girka ki bama Ya"yana Nima ki Bani Tunda zama na Kike ba zaman wani ba Malama.."Ya Fada yana wani Sakin Nishi na Masifa Kai kawai ta Girgiza Tana Fadin"Kayi Hakuri Abban Amira ban Taba saba Umarninka ba ammh yau zan saba Bazan iya baka abinci ba alhalin Barkat tamin Allah ya isa bata yafemin ba matukar na Baka abinci Ranar girkinta.."

Tafada Cikin kwantar da Murya Sai Abdullahi yaji kamar Jiri na Neman kadashi Saboda kalaman Hafsah Cikin Wani Fushi mai Tsanani yace"Ita tace Haka..? Kai Hafsah ta Sunkuyar kafin ta Ture Filet din gabanta ta Mike Sai da ta Shimfidar da Noor kan kujera ta Dago Tana Fadin"Nidai ina kara baka Hakuri Abb..."Bata idasa ba Taji ya Damki Dankon Hannayenta Da karfi ya Girgizata yana Fadin"Tambayanki nake ki gayamin ita tace haka..? Yafada Cikin Tsanani Fushi sai da Hafsah ta Tsorata Domin Duk Fushin Abdullahi bata taba ganinsa Cikin wannan Fushin ba.

Cikin Rawan Murya tace"E..eh ita tace min haka.."Ido ya Runtse kafin yace"Wani Abu ya Faru bayan Bana nan ko..? Yafada yana kureta da ido Girgizamai kai Tayi Tana Fadin"Bafa Abunda ya Faru Abban Amira.."Karya kike..Wani Abu ya Faru..? Ya katseta Cikin Daka mata Tsawa kafin ya Cigaba da Fadin"Zaki Fadamin Abunda ya Faru ko kema sai Ranki ya baci..?

Yafada yana Sakarmata Jajayen Idanuwansa Numfashi ta Sauke ta karya Wuya tana Fadin"Abban Ami.."Ashe ke ba Wakiliya ta bace in bana gida..? Kice makwafina in bana Gida Hafsah Saboda Haka ki Fadamin Abunda ya Faru yanzu Ina Jiranki.."

Hafsah ta Runtse ido ta Bude Zatayi mgana kawai ya saketa yana Fadin"In baki Fadamin ba.Ban yafe miki ba Hafsah kuma bazan Taba yafe miki ba indai baki Sanar dani Abunda ya Faru ba bayan bana nan.."Yafada yana Kokarin Controlling Din Fushinsa Ido Hafsah ta Zaro Tana Fadin"Baka yafemin ba Abban Amira..?

Cikin kakkausan Murya yace"EH BAN YAFE MIKI BA HAFSAH MATUKAR BAKI SANAR DANI BA.."jin haka yasa Hafsah bata da Zabi Tiryan Tiryan ta Shiga Zayyanamai komai Har karshe ta Karishe da Fadin"Plz Abban Amira karka ce zaka yi wani Abu..Ka bari ka wuce yanzu kana Cikin Fushi ne plz.."Ko Sauraranta bai yi ba ya saka kai zai Fice ta Bishi Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"A"a Abban Amira ina zaka..? In kayi mata wani Zarginta zai Tabbata akaina tace na Hada mata Gulma Na Shiga Tsakaninta da Mijinta Don Allah ka kyaleta Ni Tayi mawa kuma Wlh komai ya wuce..'"

Fizge Hannunsa yayi yana Haki yake Fadin"Wlh karya take Hafsah..Ita Wacece..? Ita din Banza da Wofi Ita Har ta isa ina Auranta Tana Karkashina tace zata zo Gidana ta Raina ni ta kuma Raina min mata..? Me take Takama dashi...? Wlh sai ta gane bata da wayau matukar bazata Darajani ba Kuma bazata Girmamaki kamar yadda Ni da Sauran yan"uwana muke Girmamiki ba Wlh sai dai ta bar Min Gida Bazan Dau iskanci ba Kinjima na Rantse.."Hankalin Hafsah ya Tashi ta Dafe Kirji ko kafin tayi wani yunkuri ya fice ta Bishi da Gudu Tana Fadin"A"a Abban Amira karkayi haka.."

Waigowa yayi yana Fadin"Ki koma Daki Hafsah.."Taki komawa tsawa ya Dakamata wanda Harta Barkat Dake Dakinta sai da tajita Cikin Kakkausan Murya yana Nuna mata Hanyar Dakinta yana Fadin"Ki koma Dakinki ki Zauna...Babu Abunda zaki iya yi, awannan al"amarin saboda Haka Babu Ruwanki.."Daga haka ya Barta nan tsaye ya Banga Labulan Dakin Barkat ya Shiga Cikin Fusata.

Baya Hafsah taja ta Dafe Kirji Tana Fadin"Innalillahi Wa'inna illaihirraju"un.."Domin a yanayin Abdullahi kadai ta Tabbarta da kalamsa Tsoronta kuma Tasan baza"ayi mai kyau ba kasa komawa Daki Tayi Taja ta Tsaya Cikin Zullumi.

Barkat na Tsaye Tun Bayan Jin Tsawan da Abdullahi yayi ta Mike Tana Tunanin ko lafiya..? Bata gama Tunani ba taga ya Fado gabanta kamar wani Zaki Cikin Hargowa ya Nuna ta da yatsa yana Fadin"Me kika Fadama Hafsah dazu..? Wasu irin mganganu kika Fadamata Dazu Data Shigo Dakinki ta Dubaki ko kina lafiya...?ya fada yana Huci kamar wani mayunwancin zaki.

Barkat Ta saki baki tana kallonshi kafin tayi wani Munafukin Mirmishi Tana Fadin"Ba Shakka ashe harta Gaya maka..? Oho na gane ta Zugo ka ne kazo kamin Tijara Saboda an Taba yar gwal..? toh bude kunninka Ba komai nace mata sai Munafuka mai Fuska biyu mai kuma Kokarin Raba mata da Miji..."Bam..! Abdullahi ya saka Hannu ya make mata baki yana Huci Cikin mamaki ta Dafe bakinta Tana Bin Abdullahi da kallo kafin tabi Hannunta da kallo ganin Jini yasa ta Saki Kuka Tana Fadin"Kambu kan Na Fadi gaskiya ka Fasa  min baki..?

Abdullahi yace"Kadan kika gani..In kika kara Zagin Hafsah sai Na zabga miki mari Wlh Sakarya kawai mara Tunani.Karya akayi bata Fiki komai bane..? Ke Uban me kika iya..? Ina ce a zaman Aure Ginshiki Shine Hakuri ladabi da Biyayyah ga Abokin Rayuwarka ke ki Fadamin in kina Kare Guda Daya Baki iya komai ba sai Girman kai kishi mara amfani Kina Kishi da wacce tafiki Komai..na fada na kara fada Hafsah Tafiki Komai Barkat maimaikon Kiyi Kishi Da ita wajen kwaikwayom kyawawan Hallayarta sai kike kishi da ita Wajen Kokarin ki Wargazamin Zaman Gidana kina zagin Uwar ya"yana mata ta Farko matar Rufin Asiri na ko..? Toh baki isa ba Wlh Kin kuma yi karya Wlh ni Abdullahi komun son da nake ma mace bata isa tazo gidana ta kawomin wani iskanci ba Cikin biyu za"ayi Daya ko Ta Sauya Halinta mu zauna Daya ko kuma ga Hanya nan ta kama Gabanta ba Lalle ba Dole.."Ya karishe Fada yana nuna mata Hanyar Fita.

Barkat da Kuka yaci karfinta ta Dage iya karfinta ta kurman Ihu wanda ya Tsorata Hafsah ta Fada Dakin da Gudu a Tunaninta Abunda Abdullahi bai Saba bane yake yi wato Duka,Sai kuma Taga sabanin haka Tsayawa kawai Tayi Cikin Damuwa,Barkat kuwa Data ganta sai Tayi kukan kura tayi kanta Abdullahi ya Shiga Tsakani Ya Daga Hannu zai mareta Hafsah ta Tare tana Fadin"A"a karka Fara Abunda ka kyamata Abban Amira.."Fadin Haka yasa ya maida Hannunsa yana Jifan Barkat din da wani banzan kallo.

Ita kuwa Baya Taja Cikin kuka Tana Fadin"Lalle kin Ciru Tuta..Tunda kika yi Sanadiyar da Aurena ko Wata uku bai Cika ba,Ammh kin Saka Mijina yana Cemin zan iya karawa gaba bai Damu ba..Zan Tafi Domin Shi ya Bukaci Haka ammh Ki sani yadda kikayi Sanadiyar Wannan rashin Jituwar da mijina kema.."Bata karisa ba Abdullahi yaja hannunta keeee.sai Kofar Dakinta ya Wurgata sai gata Waje tama kusa Fadi Nuna Mata yatsa yayi yana Fadin"Na baki Minti Goma kachal ki Kama gabanki..Gidan Abdullahi ba wajen zaman irinku bane...Kije Gida Akara baki Tarbiya Domin kwata kwata baki Dashi Sannan Abu na karshe ina kara gargadanki Kada ki kara kuskura Bakinki ya Bude ki kara aibata matata Im kuma kika ji Wlh bakya ki gani ba...Wawiya kawai Jahila wacce iliminta bai amfaneta da komai ba.."Daga Haka yaja Hannun Hafsah Datake ta Faman bashi Hakuri Suka Shige Dakinta Lokaci Daya da Bango kofa.

Da kallo Barkat ta Bisu kafin ta Sulale nan tana kuka mai Cin Rai kamar zatayi Hauka,Gefe Daya tsanar Hafsah na kara Shiga Ranta Tuna kalaman Abdullahi yasa ta Mike ta Share Hawayenta ta koma Cikin Dakinta ta Hada kayanta Cikin karamin akwati ta Dauki Wayarta da karamar Jakarta sai Littafan karatunta na makaranta Domin sun kusa komawa makaranta tafito ta Rufe Kofarta da Makulli lokaci Daya Tana Duba agogon  wayarta 10:10pm na Dare  ba ta kara kallon Barayin Dakin Hafsah ba ta Ja akwatinta taje ta Bude Gida ta Fice tana Tsiyayan Hawaye.

Hafsah Dake Zaune gefen gado Ta kalli Abdullahi Dake kwance ya Juya mata baya tace"Abban Amira ta Fita fa..? Don Allah kaje ka Dakatar da ita ka dawo da ita Don Allah.."

Ta Fada kamar tayi kuka,Cikin Fushi Abdullahi ya juyo Lokaci Daya da mikewa yana Fadin"Bazan Dakatar da ita ba Hafsah ammh in kin Damu da ita kije ke ki Dakatar da ita.."Yafada yana sakarmata ido Mikewa tayi Cikin Farinciki Zata Fita Taji ya kira Sunanta ta waigo Tana kallonsa Cikin kakkkausan murya yace"ammh da Sharadi..Sai dai indan kin Fita kin Dawo da ita Badai Gidana ba kema ki bita ku Tafi Gidanku Gabadaya.."Ya fada yana Kallonta Lokaci Daya yana mikewa ya Tura Kofar Tailet ya Shiga Cikin Fushi.

Ajiyar Zuciya Hafsah ta Sauke ta Dawo ta ZAUNA gefen gado kusa da Noor Tana Fadin"Ya illahi..Allah ka saussauta Wannan Zuciyar ta Abban Amira..Allah ya Daidaita tsakaninsa da Matarsa kada Auran nan ya kare  kowa ya Doramin laifi.."Tafada tana Share Hawayen idanuwanta.

_Assalamu Alaikum Masoyana Na nesa Dana kusa ku dan bani aron Hankalinku anan Kadan Da Farko ban so nace wani Abu ba sai Sakonninku yayi yawa Tsakanin posting din Jiya da wanda akayi kafin shi na Farko akwai masu Korafin Abdullahi ya cika Masifa gashi Hatta iyayensa Suma Binsa suke bamai iya mai Gaddama ko..? Toh Misali Abdullahi ya Dauki Girman da wani Babban magidanci bai Dauka ba a karamin aikinsa yake Iya Rike da Gidansu da kannensa Duka ya Biya musu kudin makaranta yayi Duka laluransu Dasu da Mama,gefe Daya kuma ga tashi Laluran gata matarsa gata yayansa..? Baba wada matsayin Uba yake gareshi yana kokarin bashi Girmanshi Tunda baya Zartar da wani Abu sai dashi da kuma Shawaransa kusan meyasa Suke Girmamasa..? Yana da kwarjini kuma yana Son Girman kuma sai Allah ya bashi,Duk Abunda zai Zartan kan gaskiya ne Taya zasu Dakatar Dashi..? Duk Abunda Abdullahi yake baya kan kuskure bane Taya ya Zasu Dakatar dashi..? Su kansu suna Girmamashi Saboda matashi ne mai Zuciya da kuma Halin Dattako Ya kamata kuma masu karatu ku Tayasu Girmama Abdullahi Domin na Tabbata awannan Rayuwar da muke Ciki samun Jajirtattacen Yaya irin Abdullahi sai Antona..Sai mgana ta Biyu kan wasu Suna Fadin bai dace akomai Abdullahi ya Dinga Kiran Hafsah ba..? In bai kirata ba wazai Kira..? Kuyi adalci Barkat fa Da Shigowarta gidan Wata uku fa kenan..? Ammh saboda Rashin ta ido sai ki Fito da Tsirfan Fara nuna Tsana da kishi ga uwargidanta da kikazo kika Tarar tayi Shekaru da Shekaru da mijinta..? Wa yan"uwansa suka sani kafin ke..? Ita tace komai nashi ita ta gyarashi Har ta ganshi tace tana sonsa kuma bai ce bayason Hafsah ba karin Auransa wani Nau'i ne Daga cikim kaddaransa bashi da yarda zai yi..ko Shekara baki Rufe agida ba kina Complain kaza Taya zaki iya Hakurin da Ita Uwargidanta tayi..? Komai da sannu ake bi kema sai ki natsu ki Fahimci me Uwargidan take yi ne ta samu wannam Kimar sai kiyi kishi irin na wayewa kema ki koyi da ita Wlh with Tym kema za"a Fara yabonki Kuma Mijin zai Dinga kama Sunanki yana Tunanin yafi kowa Dacewa ammh kuma Sakarci Barkat ya Chanchanci koma miye ya Faru da ita Ballatana Miji irin Abdullahi Yana da kyau ka nuna Ma Duniya matarka tana da kima awajenka bawai saboda ka kara Aure ka Nuna ma Amarya cewa Uwargida ita da Banza Duk Daya ba.._




*Janafty*