Chapter 2
Shekaruna ashirin, ni yarnan garin Katsina ce. muna zama asabuwar unguwa layin central market, ana kiran Babana da malam jamilu, kannena su biyu ne hafsat da kuma zainab. Natashi ahannun matar babana inna Kande.
Bansan jindadin rayuwa ba kullum cikin kunci da bakin ciki nake .
babu abunda yake hadani da inna Kande sai duka da hantara dakuma zagi . babanmu yanasona sosai kuma yana kokarin nunamani kulawar shi sai dai babu yanda ya iya da inna Kande . bai isa ya hanata yimani duk abunda tayi niyya ba saboda bashi da say acikin gidan duk yanda inna Kande tace shi akeyi . bishiyar da ke tsakar gidanmu ma tafishi daraja agurinta .bata darattashi ko Kadan sai ma mulka shi da takeyi .
Kullum cikin wahala nake. Bani da hutu sai idan nasamu tayi bacci sannan . shima baccin na darene kadai takeyi bata baccin rana .
Tun inada shekara biyar tafara daura mani tallar fanke ina kaiwa bakin Kasuwa . ga dibar ruwa da nakeyi , ga shara ga wanke wanke ga kuma gyaran daki da wanki . abinci ne kadai bana dafawa .
tun ban iya ayyukan gida ba har sai da nakoyesu da tsiya . idan tasakani shara banyi da kyau sai tabari nagama sannan ta samo bulala ta jawoni ta zane mani jikina da ita , ta kumace insake yin wata sabuwar sharar . haka zatayita mani har sai nasamu nayita da kyau . fanke kuwa idan ban saidoshi ba shima wata bulalarce zani kara sha ,iya adadin fanken da na maido iya adadin bulalar da zata yimani .
agurin wani masallacin layinmu ne nake zama in sha kukana duk sanda ban saido shi duka ba .haka inna kande tayita yimani azaba har nafara sabawa da wahala.
Bazan taba mantawa ba lokacin inada shekara shidda ne baba yadawo inata sharaar tsakar gida na yimashi sannu da zuwa ya amsa yana ruke da farar takarda ahannunshi inna Kande dake dafe da Kofar dakinta ce ta tambayeshi " wannan takardar fa ta micece?"
"Eh daman inaso intambayeki ne toh daman.. da yake munyi magana da Alhaji isa ne daman ... daman Admission din Amatullah ne " baba yabata amsa cikin dabur dabur .
Katse shi tayi da sauri cikin fushi tareda cewa "shine bakayi shawara dani ba baka tambayeni ba zakaje kayi gaban Kanka koh ? toh sai inga wanda ya isa yasa Amatullah maKaranta ba da izinina ba !"
agaban idona naga baba ya durkusa yanaba inna Kande hakuri akan tabarni infara zuwa makaranta , sai da yahada da magiya har da yar kwallarshi . da naga ban iya ganin yana hawaye agabana ne yasa na ajiye tsintsiyar nayi waje na tsaya akofar gida nima ina matse nawa hawayen .
sai da nadau yan mintina sannan nakoma cikin gidan . sai kuma na tarar da anyi sa'a baba yasamu ya shawo Kan inna Kande yanata yimata godiya cike da farincikin barina da tayi inruka zuwa
"zonan munafuka" ta cemani afusace tareda kwatsa mani wata tsawa da tayi" WA YA BAKI IZININ FITA DAGA GIDANNAN!?" ta karasa dai dai inda nake afusace nikuwa har nafara Kuka tun kafin tafara yimani abunda zata yimani, hannunta daya tasa ta fizgoni ta cigaba da dukana tana mari nikuwa banda kuka babu abunda nakeyi .
baba yana ganin alamar dukana inna Kande zatayi yayi sauri yabar gidan yacema ta yatafi zaya koma kasuwa ne . daman haka yakeyi duk sanda yaga alamun zata duke ni.
Baba yana da burin inyi Karatu mai zurfi nima kuma inason Karatun sosai dan kusan kullum ina damun shi da yasaka ni amakaranta .
dandanan washe gari sai gashi tunda sassafe ya shigo da leda ahannunshi inata faman hura wuta agaban murhu . mikama inna Kande ledar yayi tare da cewa "gashi Kande kiduba kigani kayan Karatun Amatullah ne "
cike da kulewa kamar daman inna Kande jiran baba takeyi tace "sanda zaka sawo ka tambayeni ne ko Kayi shawara dani ne!"?
"Aah" baba yace atsorace tare da sunnar da kanshi da yayi yakara da cewa " ai Alhaji isa ne yabada yace inbata shine yasiya mata bani na shiyaba banisan dasu ba wlh nima kaina"
nikuma jin ance Kayan Karatuna ne yasa nayita jin dadi nafara tsalle da murna . wata muguwar harara inna Kande ta watsamani . nakoma gefe guda nazauna tsabar rudewar hararar da tayi mani tasa nayi.
"Kallarta munafuka zaki tashi ki cigaba da abunda Kikeyi Koko sai na farfasa maki jiki?" Inna Kande tafada mani tare da cije bakinta da takeyi cike da salon mugunta .
mikewa nayi da sauri dan nasan Kadan daga cikin aikin inna Kande kenan , bama farfasa mani jiki ba har abunda yafi haka ma zata iya yimani shi .
Daki baba yashiga da saurin shi gudun Kada shima ta dawo Kanshi ta hanashi bani Kayan .
"Kai kuma malam maza maza Ka fito daga dakinnan Ka Koma wajen Kayan miyanka Koma wa Kabarma ajiyarsu ma oho? haka kawai saboda wasu Kayan makaranta chan Kabaro sana'arka Kazonan salon Ka jamana asara ,idan naga dama ma makarantar bazata jeta ba babu ruwana baa Admission ba Koma minene tasamu sai inhana !"
Allah ya huci zuciyar ki" baba yafada tareda fitowa daga dakinshi yayi waje da saurin shi yabar gidan .
Nikuwa Allah Allah nakeyi baba yadawo daga Kasuwa ya gwadamani Kayan makaranta na .
dawowarshi ne da daddare yasa murnata takaru sai dai unfortunately , bai gwadamani su ba . da naji shirun yayi yawane yasa na fidda rai da makarantar zatona Ko inna Kande ta chanza ra'ayi ta hanani fara zuwa makarantar . ashe shi baba target dinshi yakeso ya cimmawa . niyyar shi daman inna Kande ta tafi bacci shikuma alokacinne zaya kirani ya gwadamani Kayan.
Sai gashi kuwa yakirani bayan ta shiga dakinta ta Kwanta . ledar yakara daukowa tare da budeta da yayi yafiddo mani komai ya ajiye agabana yana gwaggwada mani su cike da farincikin da yakeji aranshi shima yana fada ahankali " Kinga wannan jakka ce , ga kuma takalmi da safa , gakuma pencil ga littattafai uniform Kuma sai chan makarantar sun ganki sun gwadaki sannan su dinka subaki!"
dadi nayitaji na amsa nayimashi godiya inata murna ciki ciki dan Kar inna Kande taji alamun wani abun tafito takara damkata Ko taji haushin na tadata daga baccin ta chanza shawara ta hana zuwa makarantar , nashiga daki na aje Kayan inata jindadi araina .
Gari na wayewa nayi sauri nafara ayyuKan da nasabayi Kullum nayi Komai na samu nagama dawuri daman ba jiran abinci naKeyi ba saboda nasan ma ba samunshi zanyi dawuri ba sai sanda na saido fanke duKa sannan .
inna Kande kuma daman wani loKacin bata ma tashi ta dafa abincin sai tagama sharbar baccinta sannan . shiryawa nayi tsaf na cigaba da jiran baba yazo yakaini makarantar .
inna Kande ta tashi taga nagama duK abunda yaKamata inyi haKan ne yasa taruka creating wani aikin tana bani inayi. Banda tsaki da hararata babu abunda takeyi "mayya Kawai mai nacin tsiya Ko miye nakima na son karatu abunda Kwalwar takima ta dussace bata dauKar Komai!"sai kuma chan takara da cewa "gwarama Kitafi maKarantar Ko narage ganin wannan fuskar taKi marar dadin gani"
tana cikin yin maganar ne baba yayi sallama instead of ta amsa sai ma harara da tabishi da ita . amsa sallamar baba nayi . smiling Kawai yayi yawuce daKinshi ya fito da makullin machine .
wani mugun murmushin mugunta inna Kande tayi tareda cewa " Au da Kai atunanin Ka zan barKu kutafi amachine ne ? Lallai har yau baKasan wacece Kande ba bani maKullin machine din Kutafi akafa ai Kai Ka Kwallafa zaka sakata amaKaranta tunda naci gareKu duKanKu sai Kutafi aKafa in ita batasan hanyar maKarantar ba ai Kai Kasani sai Ka nuna mata kuyita tafiya " takuma kara juyowa ta kalkeni Kekuma Amatullah Kisama ranKi Kin dunga tafiya makaranta akasa kenan " tafada mani tareda yin wata dariya ita ba murmushi ba ita ba yake ba .