AMATULLAH

Chapter 4

by @ameerahfarouk

Rigata ta daga sama ta cigaba da zabgata da dorunar da ke hannun ta iya karfin ta tana dukana tana marina ta Ko ina . 


KuKa Kawai naKeyi wanda idan mai imani yaji ina yinshi dole zaya tausaya mani .amman inna Kande Ko ajiKinta Kamar ma kara zugata naKeyi da ta dakeni , ta cigaba da dukana har saida tagaji sannan tayada dorunar akasa taKoma tasamu guri ta zauna tanata faman nishin gajiyar dukana da tayi .ni Kuwa naci KuKana Kamar Allah ya aiKoni . 


"munafuKa zaKiga wanda zaya baKi abinci yau badai ni KiKa yima asara ba!?" Inna Kande ta cemani tare da shiga daKin ta da tayi tafito da kullin wanKin da ta daureshi da zani da dari biyun da ta tullomani su ta cemani " wuce Kitafi Ki siyo omo Ki wanKe mani Kayannan yanzunnan Kafin Kuda ya rugaKi " 


juyawa nayi inata Kuka Kamar Allah ya aiKo ni na fice nabar gidan .  cike da takaicina da takeji inna Kande takara da cewa "bakar munafuKa Kawai yau Kin yimani asara baKi ba Kwanciyar hanKali agidannan! "  


Babu yanda na iyahaKa naKama hanya natafi nasawo omon ina tafe ina Kuka ahanya ga yunwa da kishirwa da Kuma gajiyar yawon da nayi . 


naKuma Koma gidan da niyyar indan huta Kafin infara wanKin ta hanani tareda tadani tsaye da bulalar da tawani zabgamani ita ,mikewa nayi da sauri na nufi Kayan wanKin ba tare da inna Kande ta cemani Komai ba saboda bulalar da ta zabga mani ce yasa nagane abunda take nufi.

Gama shanyar wanKin da nayi Kenan sai ganinta nayi agabana da tsintsiya ahannun ta "maza amsa Ki share mani gida" tacemani tare da wani mugun Kallo da tayimani . 


dafe bayana nayi saboda tsabar gajiyar da nayi naji kafafuwana sun Kasa dauKata , ga yunwar da kara jinta Kawai naKeyi .tambayar ta nayi awahale " inna dan Allah ki taimaKa Kibani abinci inci yunwa naKeji" muryata ciKi ciKi Ko fitowa batayi sosai aloKacin .


Wani wawan mari ta Kwashe ni dashi ta cemani "Kece zaKi fadamani abunda yaKamata inyi ? Toh anki baKi abincin nafiKi sanin yunwa KiKeji ba dai ni KiKa yima asarar ciniKi ba ? Zanga wanda ya isa ya saKani inbaKi abinci yau agidannan " 


hawaye Kawai suKa ruka bin afusKata dan karfin yin KuKan ma tuni na nemeshi na rasa. 


Adudduke nasamu na karasa sharar da nakeyi tashin da zaniyi ne in zubar da sharar naji ciKina yafara kullewa da kyar nasamu naje na zubar da ita . na nufi daKi adaddafe da bango , ahaKa nasamu na shiga na Kwanta inata juye juye ina magowar ciwo ,inna Kande na jiyoni tayi banza ta kyaleni .


Sallamar baba da yadawo daga masallaci naji ban iya in amsa mashi sallamar ba .


dakin yanufa jin alamar Kamar Kuka naKeyi .yashiga ciki tare da yin sallama ya isKeni inata juye juye "subhanallah Amatullah lafiya!?" baba ya tambaye ni hanKalinshi atashe . 


ban iya yimashi magana ba sai ciKina da nayi pointing mashi da hannuna daya shima da kyar nasamu na nunamashi shi "sannu sannu Kinji !" yafada yana Kallona ciKe da tausayi "bari inje infadama Kande zani KaiKi asibiti Kada mudawo tayi fada tace banfada mata ba " baba yacemani tare da fita daKin da saurin shi . 


Hargagin inna Kande na ruka jiyowa "ni zaKa rainama wayau Kawani ce zaKa Kaita asibiti saboda ni bansan dai dai ba Koh !? toh babu inda zaKuje Ka jika mata Kanwa intaga dama ta sha idan bata ga damaba ba Kada tasha matsalarta ce ba tawa ba , babu asibitin da zaKuje ni banma yarda ciwon ciKin gasKe taKeyi bama wlh dan yarinyarnan ba karamar munafuKa bace ba! bacemani da gani  Kaima Kafin ranKa yabaci yanzunnan " taja dogon tsaKi  tare da cewa " aiKin banza ni za'a rainama hanKali da wani karyar ciwon ciKi tabari inzo insameta adaKinnan aKwance zata yabama aya zakinta ne ta fada da karfi ta yanda zaniji da Kyau"



baba yadawo jikinshi asanyaye yana Kallona ciKe da tausayi"baba yunwa naKeji " nacema baba ahanKali .


fita baba yakarayi daga daKin niKuma sai nazaci Kanwar yaje jikomani ashe gurin inna Kande yaKoma . bankara jin muryar baba ba sai ta inna Kande da taKe ta faman masifa "wlh bari ingama abunda naKeyi insame Ki adaKinnan zaKiga iKon Allah yau! Kai Kuma malam Komi yarinyar tace maKa sai Kahau Kazauna , Kaima ranKa baci zaiyi nazo nasame Ka adaKinnan Kudai bari ingama abunda naKeyi insame Ku!" 


nidai ta Kaina naKeyi inata murkushe murkushe baba dai naji shiru bai ce Komai ba dan nayi expecting zaya leko ya lallasheni yace inyi shiru gudun Kar inna Kande tazo ta sameni ahaKa . 



Shirun naji yayi yawa sai chan anjima naga baba yashigo mani da magani yana ta yimani sannu yabude Kwalbar maganin yazuba amarfi yabani nasha yaKuma debo ruwa yabani nasha shima, dandanan ahanKali nafara jin kullewar ciKin tana warwarewa . Baba ya mikomani bakar leda na amsa, bude ledar nayi naga awara ce aciKi . 


nafara cin awarar  nacigaba da ci da sauri kamar za'a kwacemani ita daga hannuna tsabar yunwar da naKeji har sai da naKusa cinyeta tas . baba daman yatsare ni yace sai nacinyeta aciKin maganar da muKeyi dashi ahanKali dan Ko sallama baiyi ba sanda yadawo daga sayen awarar gudun Kar inna Kande tagane yasayo mani wani abu . 

Awarata na cigaba daci ina jindadin ta , labulen daKin muKaga andaga muKa juya duKanmu daga ni har baba arude dan zaton mu inna Kande tayi bacci aloKacin ashe idonta biyu shiru Kawai tayi . Kanta ta girgiza tare da saKin labulen daKin da tayi tafice abunta na kalli baba ciKin tashin hanKali shiKuma yayi waje yabi inna Kande.