Chapter 5
Dandanan nafara KuKa tun Kafin inna Kande tayimani hukuncin da zata yimani saboda tunanin irin azabar da zani sha aranar . shi Kuwa baba banda hakuri babu abunda yaKe bata ,naKasa Kunnena inji mi taKe cewa sai Kuma naji tayi shiru batace Komai ba dandanan hankalina yakara tashi saboda ni Kaina nasan shirun inna Kande ba abanza tayishi ba shirunta ba alKhairi bane ba dan wani loKacin ma har gwarama tayi masifar ta da tayi shirunnan mataKin da zata dauKa bazaiyi Kyau ba .haKa baba yagaji da ban hakurin shi ya shiga daKin jiKinshi asanyaye . isKeni yayi inata uban KuKa Kamar raina zaya fita "Amatullah Kiyi haKuri Kiyi shiru in sha Allah zuwa gobe in Kin bata haKuri zata sauKo"
atsorace nace "wlh baba nasan inna bazata taba hakura ba dan Allah Kazo muje inbata hakuri atare idan ni Kadai ce bazata hakura ba!" Kallona baba yacigaba dayi bai cemani Komai ba sai chan Kuma yace mani "Ki Kwanta Kiyi bacci itama naga Kamar baccin taKeyi Kinga in muKa samu tayi baccin zuwa gobe in sha Allah nasan ta yanda zani billoma al'amarin" nadaga mashi Kai nayi atsorace shiKuma yafice ya shiga daKinshi yabarni inata tunani da fargabar huKuncin da inna Kande zata yimani .Baccin wahala ne yadauKeni ba tare da nasani ba . aciKin baccin ne naji sauKar bulala ajiKina natashi atsorace inna Kande ce nagani tsaye agabana ruke da dorunar da taKe buguna da ita "munafuKa yau sai Kin gane Allah dayane ba dai ubanKi ya boyeKi ba yabaKi abinci aboye bayan asarar da KiKa yimani ?"nidai sauraronta na cigaba dayi agigice, takara da cewa "Allah yaKai mu dasafe duKanKu zaKuyi bayani ne daga Ke har uban naKi " Ko tsayawa batayi ba tana fadamani maganar ta fita tabar dakin . Shigar inna Kande da tafiyar ta ne da tayi adaKin yasa duK baccin yafita a idona na neme shi na rasa daman saceni yayi ba da niyyar inyishi ba na Kwanta .abun duniya duK ya isheni nayita tunane tunane na da fargaba har gari yawaye bansani ba . dan Ko Kiran sallah banji ba tsabar tashin hanKalin da nashiga . Abunda yabani mamaKi shine batazo ta tadani da asuba ba inyi aiKi Kamar yanda taKe tadani Kullum . sai Kuma nayi tunanin toh Ko tadin da tayimani na dazu ne ?" Dandanan hanKalina yakara mugun tashi saboda nasan bazanji dadi ba inna Kande tazo ta tadani inki tashi , ga Kuma laifin amsar awarar da baba yasawo mani da nayi naci . daura hannuwana biyu nayi asaman Kaina nacigaba da rusar Kuka . instead of infita in cigaba da ayyuKana da naKeyi Kullum sai na zauna na cigaba da KuKana na koshi , aciKin KuKan ne wani baccin yakara dauKeni ba tare da nasani ba . wani irin kyakkyawan marin da naji sauKar shi aKumatuna ne yasa na tashi namike tsaye azabure "Amatullah yau sai na KasheKi aciKin gidannan na lura lalaci KiKa Koya Koh !? Ko dayaKe ba laifin Ki bane ba ai Kinci awara Kin koshi dole Ki Kwanta Kiyi baccin Ki yanda ranKi yaKeso " inna Kande tacemani tare da jinjina Kanta da tayi cike da mugunta . baba ne yafito da saurin shi daga daKin shi cike da tashin hankali jin maganar da inna kande tafada , akufule tace mashi " wlh malam idan baKa Koma ciKin daKinnan ba ranKa zaiyi mugun baci! "ta runtse idonta da ciKe da masifa .
tun Kafin inna Kande ta Kulle baKin ta baba yayi sauri yaKoma ciKin daKin shi ba tare da yakara cewa uffan ba .sabata tayi ta cigaba da dukana. Sai da tagama dukan da take yimani sannan tace " maza maza Kifara aiKi tun Kafin raina yakara baci idan Kinga dama Kigama dawuri idan Kuma Kinga dama Kitsaya saKarci"rudewa nayi sosai jin "Kada ranta yabacinnan" da tacemani . dauKar tsintsiya nayi tsabar rudewa sai Kuma na yadata akasa na nufi daKi da sunan zani gyara shi shima nafito na nufi Kayan wanKe wanKe shima har nadaga Kwano shima na ajiyeshi . tsaye inna Kande tayi taKama kugu tana Kallona ciKe da mamaKi da kuma haushina da tajeji at the same time, nufata da nayine yasa jiKina yafara rawa , nakara nufar tsintsiyar da niyyar in dauKeta inyi sharar .inna kande ta finciKoni tare da cewa " namaKi Kama da abokiyar wasanKi Koh Amatullah ?
"inna kiyi hakuri dan Allah wlh bazan karaba !" nafada ina KuKa hanKalina atashe . marina takarayi na dafe gefen Kumatun da tamara nafadi na cigaba da KuKa . wani marin da takara yimani ne yasa namike tsaye na hadiye KuKan da naKeyi sai dai hawaye da Kuma ajiyar zuciyar da naKeyi. "zaKi cigaba da aiKi Ko Ko sai naci mutuncinki ? MunafuKar yarinya Kawai, idan ma Kinyi ne saboda ubanKi yaji Kinsan shi Kanshi bai isa ba ballantana Ke Ko ?" tawani Murda mani Kunnena cike da warning din da ta yimani " daga yau sai yau duK sanda malam ya kara sawomaKi abinci KiKa ansa KiKaci Kisan ranar ranar mutuwarKi ce" ta daKa mani tsawa tare da tambayata " KINA JINA!?" Kai na daga mata ciKe da tsoro ta saKina tayi taKuma tureni tare da cema baba " KaiKuma malam zan dawo KanKa zaKa yimani bayanin ta yanda Kafita gidannan ba da izinina ba "tayi kutta sannan tawuce ta daga labule tashiga daKinta .Aikina na cigaba da yi ina hawaye shi dai baba bai yarda yafito ba sai dai faman daga side daya na labulen da yaKe jikin kofar daKin shine yakeyi yana lekoni ahanKali . haKa nasamu na gama aiKin gidan sannan na dauKi bucket din dibar ruwa nagama cin uban layi nasamu na debo shi da kyar . naKoma gida na wanKe fusKata na cigaba da tunane tunane na . HaKa zaman mu ni da inna Kande yaruka tafiya. Kullum abun kara ta'azzara yaKeyi , Kullum Kamar kara Koyamata sabon course din mugunta aKeyi . MaKaranta Kuwa Kullum sai najeta amaKare tunda nashige ta . akwai sanda naje dibar ruwa na tarar da layi yayi yawa ga sauran fomfunan duK sun lalace wasu Kuma sun Karye . ganin layin da yayi yawane yasa nabada ajiyar bucKet dina naKoma gida . inna Kande da taKe daKinta ce nayimata sallamar zani tafi maKaranta "Allah yaraKa taKi gona" ta cemani Kamar yanda taKe cemani Kullum . fita nayi daga gidan naKama hanyar tafiya maKaranta . baba daman shi tun da sassafe yaKe shiga Kasuwa . sai na manta ban fadama inna Kande ba yanda na isKe gurin dibar ruwan . Komawa nayi gidan saboda infada mata dalilin kin dibar ruwan da nayi sai isKeta nayi atsaKar gida ruke da kadangare ahannun ta tana kullemashi wuya da wani abu da bansan minene shi ba ba kuma zani iya kwatanta yayake ba . toshe baKina nayi na zabura sosai saboda tsoron da naji gashi banyi expecting ganin abunda nagani ba. Zabura inna Kande tayi itama saboda ganina da tayi aloKacin da batayi expecting ganina ba"ubanmi KiKa dawoyi !?" tambayar da tayimani Kenan tare da nufata da tayi gadan gadan" ba magana naKe yimaKi ba !?" Inna Kande ta tambaye ni afusace" daman... dawowa nayi infada ...maki" lips dina na rawa nafada inata inda inda . karasowa tayi ba tare da ta saurari abunda naKe kokarin fadamata ba ta kwasa mani wani irin wawan mari wanda yasa sai da nafadi "wuce Ki Koma maKaranta munafuKa Kawai " tarada nuna mani hanyar kofar fita gidan mu da tayi natashi na dafe Kumatu na daidai side din da tamare ni nafita daga gidan inata uban KuKa naKama hanyar maKaranta ina tafe ina KuKa ban dena KuKan ba har sai da naKusa shiga maKaranta sannan .Classmates dina Kuma suna nan aKan baKar su na tsanar da suKa daurama Kansu aKaina . shiga nayi class naga teacher nata Koyar da mathematics har anyi nisa da lesson din .na gaisheta ta amsa tare da duba agogon daKe makale abangon ajinmu tayi ciKe da mamaKi tace "Amatullah again , you're always late! why now !? and what happened to your face ?" Sawun marin da inna Kande tayimani tagani , na sunKuyar da Kaina kasa ba tareda nabata amsa ba . girgiza Kanta tayi tadanyi murmushi tace inje inzauna naje nazauna takara Kallona tare da cemani" but don't be late next time " dagamata Kai nayi alamar "toh" Nasan dalilin da yasa teacher ta ragamani saboda ban dade da shiga maKarantar ba shiyasa ga Kuma answer n da naKe bata Kullum idan tayi questions a class. Classmates dina duKan su suKa bini da harara cike da haushina da sukeji , takara maido da lesson din baya saboda ni. dandanan classmates dina suka kara kulewa suKa cigaba da hararata . ji nayi damuwar tsanar da suKe yimani tafara raguwa gradually . tagama Koyawa tabada class worK muKa gama Kowa yayi submiting tayi marKing taKuma maidama Kowa littafin shi time din break yayi aKa shiga yin breaK . tagumi nayi inata Kallon sauran classmates dina Kowa da abincin shi amman banda ni Kowa nahada ido dashi ciKinsu sai su harare ni . time din break yawuce wani period din yashiga aKa Koya Nursery rhyme, time din tashi yayi aKa tashemu . dandanan Kuma wani bakin ciki yakara dawomani da natuna da gida zani Koma yanzu . juyawa nayi naKalli Kowane yaro yanata jin dadin zaya Koma gida amman banda ni . aloKacin ne wani tunani yafara fadomani anya inna Kande ce tahaifeni Kuwa ? tafiya naKeyi aKan hanyar Komawata gida inata tuna duK abunda suKayita faruwa tsaKanina da inna Kande da duK abunda taKe yimani . sai nayanKe huKuncin idan baba yadawo daga kasu zani tambayeshi shin dagasKe ita din ce ta haifeni KoKo? Gida na isa agajiye ga yunwar da naKeji da Kullum ita naKe komawa acikina bucket din fanKen da Kullum dashi naKe cin Karo idan nadawo daga maKaranta yana jirana abaKin kofa daga cikin gida nafara haduwa dashi .
inna Kande ce na tarar atsaKar gida tabuga uban tagumi . nayi sallama tareda karasa shiga ciki da nayi ,inna Kande batama san nashiga cikin gidan ba tunani Kawai taKeyi . zabura tayi ganina da tayi tayi sauri ta karaso inda naKe afijajan tare da cemani" sa idanunKi ciKin nawa "Kallonta na cigaba dayi atsorace nidai "Amatullah idan nasaKe naji Kinba malam labarin Kinga kadangare ahannnu na wlh Amatullah Kwanan Ki agidannan yakare "tare da tsawar da tayi mani ta tambaye ni " KINA JINA!?" na dagamata Kai atsorace alamar "Eh" tare da dauKe numfashi na da nayi cike da tsoro."wuce Ki ajiye Kayannan Kije mani talla maza maza "inna kande tafada mani tare da watsa mani wata irin harara maisa jiki yayi sanyi , wucewa nayi daki nacire uniform din jiKina na saKa wasu Kayan nadauKi bucket din fanKen na fice .Nagama saido fanKen da wuri naKoma gida nakara tarar da inna Kande atsaKar gida still ta karayin tagumi da Kaganta Kasan tunani taKeyi . sallama nakarayi tare da karasa shiga ciKin gidan da nayi . Kallona inna Kande tayi takara watsa mani harara "bani Kudin ciniKin" tafada na mikamata sannan takara da cemani "wuce Kishiga daKi abincin Ki nanan KidauKa Kici " dadi naji sosai araina na dagamata Kai ina murmushin jin dadi nawuceta da sauri nashige zani dauKi abincin infara ci , budeshin da nayine naganshi dayawa hada nama aciKi . mamaKi ne yaKamani saboda nasan inna Kande bata bani abincin da zani ci inkoshi dayawa kamarshi ba, gudun Kada inkara yimata wani laifinne yasa nafita daga daKin dan intambayo ta abincin nawane KoKo ?" inna abincin nawane ni Kadai ?" Na tambayi inna Kande ina dari dari . bani amsa tayi ba tare da tacemani Komai ba sai dai hararar da takara watsamani , hakanne yasa nakoma ciki da saurina nagane tabbas abincin nawane na zauna na tasashi gaba zani faraci sai jin sallamar baba nayi, nafita daga dakin naruga dagudu na tunKare shi inata murna da niyyar in yimashi sannu dazuwa inna kande ta mike ta nufeni da saurin ta.