Chapter 6
Ƙarasawar da tayi daidai inda nake tare da fizgoni da tayi ta maida gefe ne yasa nadan dago kaina cike da son ingane dalilinta nayin hakan?wani irin mugun Kallo ta yimani da yasa nayi daKi da saurina nashige ciki. shiga daKinshi baba yayi shima da saurinshi "malam fito Kazauna nan tsaKar gida Kuma abinci Kawai zaKaci yau Ka Koma, shin wai miyema yadawo daKai ne dawuri haKa ?"Inna Kande tacema baba cike da rashin jindadin dawowarshi da tayi "daman wasu ledojine da namantasu dazu nadawo dauKa "baba yaba inna Kande amsa atsorace. afusace inna kande tace " maza Ka dauKosu Kazo Kafice Kabar gidannan!" ledojin baba yadauKa yafice yabar gidan within seconds, inna kande tawani hanKada labulen daKin da naKe tare da shiga daKin a hargitse Kamar wadda aKa Korota."munafuKa Kawai maKirar yarinya baKiji Kashedin da naiyimaKi ba Koh ? toh Allah ubangiji yabaKi sa'ar yima malam maganarnan anan zaKi gane Allah dayane" zaro idanuwana nayitayi atsorace nace "wlh inna bazan gayamashi ba" ya fiye maKi " tafada tare da juyawa zata fita daga daKin sai Kuma tadawo" munafuKa Kawai zaKi ci abincinnan Ko ko ? ta cemani tare da satar kallon abincin da takeyi . da saurina nayi bismillah nafara cin abincin , tsareni inna Kande tayi har saida taga lomata ta karshe sannan tafita daga daKin . niKuma araina sai naruka tunanin toh wai miye dalilin inna Kande nayin haKan ? Ni dai nasan ba abinci mai yawa take bani ba Kuma ma har da nama ta saka mani . Ƙokarin fita nayi da niyyar inje inyi Fitsari " ina zaKije ? tambayar da inna kande tayimani Kenan . Kafin inbude baKi inbata amsa ta nunamani hanyar Komawa daKi da hannunta sum sum najuya naKoma nasamu guri na zauna inata tunanin dalilin da yasa inna Kande tahanani fita daga daKin . araina nace daKin da Kullum bani wani dadewa aciKinshi sai idan nasamu tayi bacci sannan" haKa na matse fitsarin da naKeji na hakura da yinshi na cigaba da zaman daKi duK sai naji na taKura da zaman tunda bansaba da zaman daKin ba kullum cikin aiki nake . fitsarin da naKeji sosai ne yasa nayi saurin fita na nufi toilet dagudu nashiga nayo gudun kada inyishi ajikina injama kaina.time din da nafitone na isKe inna Kande tsaye abaKin Kofar toilet din tana jirana ruke da dorunar ta , daya Kawai tayimani sai da na gigice na kwala wani irin ihu . "wuce kishiga daKi wlh idan kika kara fitowa daga daKinnan inhar ba ni naKiraKi ba wlh sai jiKinKi ya gayamaKi sai nayimaKi bulalar da tafi wannan zafi" tacemani ciKe da mugunta . rugawa nayi dagudu nayi daKi na cigaba da KuKa wani bakin ciKi ya tasoman naji wai mi nayimata ne da taKe wahalar dani ne har haKa !? Inata so inyima baba tambayar idan yadawo anjima shin ita din dai ce ta haifeni KoKo ? . inata faman zaman daKin ne naji muryar inna barira aminiyar inna Kande tashigo tayi sallama hausawa suna cewa "tauraruwa mai wutsiya ganinKi ba alKhairi ba" inna barira bata wani nunaman kiyayya afusKar ta Ko Kadan haka zani gaisheta ta amsaman faram faram har albarka take shimani . amman bansan miyasa ba duk sanda naganta Ko naji muryar ta sai gabana yafadi dandanan gabana ya yanKe."haba aminiya inKiraKi tun dazu amman sai yanzu " inna Kande tacema inna barira "Kefa tsiyarKi Kenan aminiyar Kema ai Kinsan hidimar ce bata karewa" inna barira tafada tare da wata irin dariya da tayi cike da rashin natsuwa irin nata, karar Kashewar su naji inna Kande takara tacewa "ni bama wannan ba wlh barira yau ina cikin tashin hankali."inna barira tace" ai tunda naga Kin yimani missed calls shidda nasan da walaKin goro amiya mi yafaru ne wai?" cike da damuwa inna kande tayi kasa kasa da muryarta tace"barira Amatullah taga aikina na yanzu" arikice inna barira ta tambayi inna Kande " ya aKayi haKa toh garin yaya KiKa bari tagani toh Kema dai !? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu miye abunyi toh?Kina ganin Amatullah zata iya fadamashi !?" Da saurinta inna Inna Kande ta cemata "yi ahankali kada tajiyomu, Amatullah batada magana sosai amman wannan abun da tagani ina tunanin zata iya fadamashi tunda ba abunda ta saba gani inayi bane" ahanKali suKeyin maganar amman ni dayake Allah ya yoni da Kunnen ji sai da najiyosu abunda suKe cewa Kadan Kadan . tambayar inna kande inna barira tayi" toh yanzu minene abunyi Ko itama irin yanda aKa yima uwarta za'a yimata ne ? Kinsan fa malam na tsanni akwaishi akwai ciKa aiKi yanda Ka bukace shi " inna Kande ta girgiza kanta tare da cemata "Aah tayaya zani yimata haKa ai Kuma baKisan wani abu ba idan aKayi haKa abun bazai tafi dai dai ba"
dariyar mugunta naji inna barira tawani kyalkyale da ita , alamun tashin su da naji sun nufi daKin inna Kande sun shiga ciKine yasa nadena jin abunda suKe fada ina jinsu suKa gama kus kus dinsu da bazan iya fadin takamaimai abunda suke cewa ba, suKa fito daga daKin inna Kande ta raKata baKin kofa suKayi banKwana ta tafi .araina nace "abunda naKe zato dagasKe ne Kenan Kodai banji dakyau bane ba Kunnena ne ya jiye mani haKa?
Nikuwa Allah Allah nakeyi baba yadawo in tambayeshi in Kuma tabbata da abunda inna barira ta fada hakanne ko kuwa? kwalla taruka zubo mani nafara tunanin toh idanma haKan ne mi aKa yima tawa uwar ?
Ranar Kwata Kwata inna Kande bata bari na zauna da baba ba dan tare ma muKa Kwana adaKin ta ni da ita tana aKan gado niKuma ina akasa ahaKa muKa Kwana har gari yawaye.the next day nazaci zata chanza ra'ayinta sai kuma naga takara turani dakinta nakara kwana achan . sai da aKa Kusan yin sati biyu tana mani haKa, gaisawa Kawai muKa rukayi tsaKanina da baba muKa zama Kamar wasu aboKanan gaba tsabar hanamu muzauna tare da inna Kande tayi . ayyuKana dai ban fasa yinsu ba amman ina gamasu zata dannani adaKi ta maida ta rufe shima baba haKa idan yadawo daga Kasuwa zata ce mashi yafito tsaKar gida su zauna atare, haKa zaya hakura yayita zama anan din Ko yaso Ko baiso ba . Tallar fanke Kuma idan na dade bandawo ba sai inna Kande tayita dukana tana cewa wai "gurin baba na tsaya akasuwa" ni da Ko inda yaKe saida Kayan miyan ma bansani ba . har sai nayita yimata rantsuwa ina KuKa sannan zata yarda tayita duraman ashar tana Kirana da sunan da tasaba Kirana dashi Kullum . A school Kuma inayin kokari sosai amman matsalata daya abincin da bani zuwa dashi sai dai inga yara Kowa da lunch box dinshi wasu da sauran KayayyaKin yara naci da drinKs wasu ma har dan Kudinsu amman ni bani zuwa da Komai . yara Kuma suKa samu damar samun yimani gori da tsoKanata fada . ni dai sai dai inta yin KuKa bani da baKin ramawa har teacher n mu tafara lura da haKan . taKuma Kirani ta tambayeni "minene dalilin kin zuwa da abinci da naKeyi ?" Nabata amsar cewa " innata ce bata bani abincin ina zuwa dashi Kuma idan babana yazo zaya bani Kudin maKaranta sai ta hanashi Kuma tace sai naje maKaranta akasa Kullum" Kallona teacher ta cigaba dayi cike da mamaki tare da tambayata da tayi "daman Kullum akasa KiKe zuwa school !?" Daga mata Kai nayi alamar "Eh" tambayata takarayi wace unguwa naKe nabata amsa da cewa " anan sabuwar unguwar naKe amman layin Kasuwa, ta jinjina Kanta ciKe da al'ajabi tare da cemani" zani baKi sako"paper tayago ta rubuta phone number n ta aciKin ta linKeta tabani "idan Kinje gida Kiba babanKi Ki fadamashi number ta ce yaKirani inaso muyi magana dashi Kinji Koh?" Na amsa mata da "toh" sannan tabude handbag dinta ta fiddo dari biyu tabani tace inje insawo Ko biscuit ne Ko wainar fulawa inci . Karbar kudin nayi nayimata godiya inata jin dadi nayi waje na nufi shop din school din na sawo ruwa na isKe mai wainar fulawa na saya naKoma class nasamu guri na zauna naci . Classmates ɗina Kuma sai suKa kara samun chance din yimani gorin da suKe yimani na bani zuwa da abinci . suKa ruka bi suna cewa wai "mu talaKawa ne ina zuwa school da datti ba'a yimani wanKin uniform , Kuma bani da abinci teacher ce Ke sai mani abinci" irin dai abunnan na yara.akwai wata fatima sagir aciKin classmates dina itace tayi nadamar abunda suka ruka yimani ta ruka tausayina tun daga ranar taruka cema sauran su daina tsokanata fada saboda ita agabanta aKayi Komai time din da teacher taKe tambayata dalilin kin zuwana da abinci na bata amsa .
Tun daga ranar fatima sagir tazama kawata muKa rukayin Komai atare har sai da tabata da Kowa a class din saboda abunda suke yimani. Washegari sai gashi na shiga class dinmu na isKe teacher adai dai loKacin da taKe duba wayarta "Amatullah zo kiji" Kirana tayi ta nunaman wani message din da ni bama iya geneshi nayi ba baKi gane miye ba Koh ? ta tambayeni, na kada mata kai alamar "Eh" sannan takara da cewa "credit alert ne munyi magana da babanKi ya turomani Kudi yanzunnan ba dadewa ciKinsu zani ruka baKi su Kina sayen abunda zaKiyi breaK dashi" Kai nadaga mata naji dadi sosai aloKacin .
haKa rayuwata ta ruka tafiya Kwata adan jin dadi Kadan, rabi da Kwata afargaba da kunci da tashin hanKali da zullumi da Kuma tsoro . idan naje school aloKacin ne zani samu dan relief amman da zarar naKoma gidanmu loKacin ne Kuma abun zaya juya inji babu dadi. Kowane yaro burinshi loKacin tashi daga maKaranta yayi yaKoma gida amman banda ni. tambayar da nayi niyyar yima baba ban manta da ita ba , na ruketa araina sai nazo yimashi ita sai inKasa Kamar ana hanani yimashi ita .HaKa rayuwata taruka tafiya , har muKa gama Nursery section duKa nazo nafi Kowa kokari a class dinmu na ruka zuwa a 1st position duK karshen term . aKa Kuma ruka saKani agaba gaba idan za'ayi competiton Ko ciKin school Ko awajen school haKa nayita cigaba a Karatuna duk sanda aKa bani Kyauta naje da ita gida sai inna Kande ta anshe ta bayar dasu .Wata ranar tuesday antashi daga school fatima sagir tace mani in raKata gidansu inga gidan niKuwa nabita muKa tafi . sai chan ana ciKin wasa sai intuna incema fatima sagir "ni gida zani Koma" ita Kuma sai tayita cemani "Aah inbari dan anjima Kadan sai taraKani mutafi tare" wasan da muKeyine ya shagalar dani Kwata Kwata yasa har na manta da fanKen da naKe siyarwa haKa muKa cigaba da wasannin ni da fatima har aKa Kira sallar magrib mamarsu tafito tayimana magana tace "mu tattara Kayan wasan muKaisu ciKi niKuma muyi sallah inKoma gidanmu"bayan mungama sallar ne mamarsu fatima ta zuba mana abinci mun fara ci Kenan natuna da aika aikan da nayima kaina salati na cigaba dayi cike da tashin hankalin da nake hangoma kaina "innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uKku fatima yau inna sai taKusa Kasheni!" daura hannuwana nayi asaman Kai na cigaba da rusa KuKa . mamarsu fatima ce ta tambayi fatima" ba Kin cemani Kun tambaya gidansu ba kukan mi takeyi kuma?" tajuyo tana tambayata "daman baKi tambaya gida ba ? Fatima tacemani Kun biya ta gidanKu Kun tambaya?" Kaina na girgiza mata alamar "Aah" ita kuwa fatima sagir sai dai aikin zara idanuwa, fizgo fatima tayi tafara dukanta "fatima ni zaKi yima karya Saboda kiyi wasa? aiKo sai nabaKi Kashin tsiya "tayima fatima sagir duka sannan tadawo Kaina nima tayita yimani fada .Sai da tagama yimani fadan ne suka rakoni inata KuKa hankalina in yayi dubu yatashi ina nunamasu hanya na labe bayansu tun Kafin mu isa gidan.shiga muKayi ciKi suKayi sallama inna Kande ta amsa masu sallamar su dan ita batayi zaton tare suKe dani ba chan sai taga nabiyo bayansu ina labe labe inata cin yatsa hanKalina tashe. "ina KuKa samu yarinyarnan ?" tambayar da inna Kande tayimasu Kenan tare da nunani da yatsanta . mamarsu fatima duK tayima inna Kande bayanin abunda yafaru takara da cewa "ayimata hakuri dan Allah Kada adaketa , nima nayimasu fada sosai nace bata Kyauta ba yaro sai hakuri mumanan duK hakurin muKeta yi dasu akara hakuri sai anjima" "mungode in sha Allah " inna Kande tacemata tare da yaken dolen da tayi suKa juya suKa tafi.