AMATULLAH

Chapter 7

by @ameerahfarouk

Hawaye ne suKa fara taruwa a idanuwana dandanan nafara KuKa  "zonan munafuka" inna Kande tacemani . inda taKe na nufa atsorace inata faman KuKa Kamar raina zaya fita. "yimani shiru munafuka Kawai yau sai Kingane Allah dayane sai Kin kwammace baki sanni ba badai ni KiKa yima asara ba ? Sai nayimaki huKuncin da daga yau Ko hanyar gidansu yarinyarnan bazaKi so Kigani ba ballantana Kije Ki dade" ni dai ina tsaye agaban ta inata faman KuKa. tafiyar ta tayi tashige daKin ta tabarni anan tsaye inata na cigaba da Kukan da nakeyi. sai da taKai yan mintina sannan tafito daga daKin Ko Kallona batayi ba sai ganin ta nayi ta nufi gurin murhun wutar da ta daura girKi tare da zaro icce kwara daya da yaKe amurhun wutar tayi tana  nufar inda naKe atsaye dashi ,kokarin rugawa nayi ganin alamar ni take kokarin tunkara dashi. Da saurinta karaso inda naKe ni dai atsorace naKe har numfashina sai da ya dauKe saboda tsoron da naji, Kafin na ankara inna Kande har tayi sauri ta karaso inda nake iccen da yakeci da wuta ta  daidaici bayan kafata ta bugamani shi. 
wani irin ihu nayi wanda tunda nazo duniyarnan ban taba yin shi ba sai ranar, Kasa tsayuwa nayi naji Kamar rayuwata ta kare .Jin alamun surutun mutane da suKe kokarin shiga gidanmu dan so suji ba'asin miKe faruwa ne inna Kande tayi sauri ta samesu akofar gida "ihu KuKaji KO ? Wlh kadangare ne ya tsoratamu "ta cemasu cikin hanzari dan ko bari suyi magana batayi ba ta tari numfashin su.
wani daga cKinsu yace "Kai mata da tsoron kadangare Ko miye abunyin  ihu dan anga kadangare ? Ko shiga zamuyi mu KoramaKu shi ne ?"Inna Kande tayi saurin Katse shi da cewa "Kada Kudamu shima ai tsorata yayi ya hau sama yaruga tafi. "ok toh shikenan Allah yakara tsarewa" mutumin yafada suKa juya suKa tafi sunata dariya . sai Kuma ya dakata yakara juyowa tare da tambayar inna Kande "itama waccen duK tsoron kadangaren ne yasa ta ta tsugunna tana KuKa ?" Inna Kande tabashi amsa da "Eh mungode sosai" suKa juya suKa tafiyarsu . shiga tayi ciKin gidan ta karasa inda naKe tacigaba da dukana  tace cike da mugunta tace mani "baKiga Komai ba ma azaba yanzu KiKa fara ganinta wlh" tashige daKinta tamaida kofa ta rufe tabarni anan tsaye dafe da kafa inata KuKa . 
Dare yayi baba yadawo yajini shiru loKacin ina adaKi azaba duK ta ishe ni inna Kande Kuma tana daKinta tanata shekar bacci abunta dan har nunsharinta inaji daga inda naKe. shigowa baba yayi adaKin da naKe tare da yin sallama . bansamu na amsa sallamarshi ba saboda azabar kunar da naKeji sai dai Kallonshi da nayi idanuwana duk sunyi jajir saboda KuKan da nasha  "Amatullah baKi da lafiya ne!?" tambayar da baba yayimani Kenan cike da damuwar ganina da yayi ahakan duk da yasan ba walwala nacikayi agidan ba ,girgiza mashi Kai nayi yakaraso inda naKe yana yimani Kallon son yasan miKe faruwa sai chan idanunshi suka sauka aKan kunar da yagani akafata. "daman konewa KiKa yi har haKa ? yaushe kika kone!?" ya tambayeni ciKe da tausayi hanKalinshi atashe , bansamu nabashi amsar tambayar da ya yimani ba na cigaba da jiyyar kafata da tasha kuna.
fita waje baba yayi ya shiga daKin inna Kande da taKe ta faman sheka baccinta tare da tadata da yayi afirgice "Kande Amatullah ta kone Kitashi mu Kaita asibiti!" yafada cike da tashin hanKali . inna Kande taja dogon tsaKi tare da cewa "daman saboda haka Ka tasheni !? ai sai Ka Kaita Kai Kadai ni dai malam gaskiya Kadena yimani wannan abun banaso gaskiya! mutum na baccin shi Kawai awani ruka tadashi haba ni ficemani daga daKi dalla chan!"tafada cike da masifa ranta bace , dan ba karamin takaici tajiba tadata baccin da baba yayi. Komawa daKin da naKe baba yayi yashiga dagudu ya dauKeni ahanunshi muKaje chemist din layinmu aKa yimani dressing sannan aKa bani magunguna muKa Koma gida . The next day bansamu naje school ba saboda zazzabin wahalar da yaKamani. inna Kande Kuwa Ko ajiKinta ahaKa ta ruka sani aiKi ba tare da nadama Ko tausayina ba . sai dai ma inayin aiKin ahanKali tana faman yimani masifa tana dukana . da Kuma konanniyar kafar mai ciwon haKa zani doshi hanya inje talla da ita haKa nayitayi har Allah ya taimaKeni naji sauki na warKe Kunar. bata damu da zuwana maKaranta ba Ko rashin zuwa maKarantana ba Ko Kadan . ita dai burinta Kawai Kada inji dadi inhuta .haKa inna Kande tayita chutamani shi Kuma baba bayada baKin yin magana .Lokacin da nawarke nakoma school ne teacher ta tambayeni dalilin rashin zuwana kwana biyu . nabata amsar cewa "konewa nayi akafa amman yanzu na warKe."Ayyah sorry Allah yakara sauKi ina Kiran babanKi baya dagawa" teacher tacemani daga mata Kai Kawai  nayi nidai ba tare da na cemata komai ba, sannan tace inje inzauna . fatima sagir tayi murnar ganina tarugo dagudu ta rungumeni tanata jin dadi . dawowa da lesson din baya teacher tayi saboda ni Classmates dina Kullum kara jin haushina suKeyi. ahaKa muKaita tafiya dasu a aji daya suna yimani hassada. har muKa gama primary section nakuma kara zuwa 1st position aKa bani Kyauta . naKuma kara Komawa da ita gida inna Kande takara anshewa ta Kyautar da ita. tunda take amsar Kyautata tana bayarwa ban taba jin taKaici ba  irin na loKacin dan Kyauta ce sosai aKa yimani aloKacin naKuma ji nafi sansu duK ciKin KyaututtuKan da aKe bani . ranar ciKin KuKa na Kwana baba yayi rarrashin ya gaji , inna Kande tayi dukan tayi marin tayi hantar  itama har tagaji nakiyin shiru har saida nagama kukana mai isata sannan . baba shima baiji dadin abun da yafaru ba Ko Kadan . Tunda inna Kande taKe amsar Kyautata baba bai taba sani ba saboda ba agabanshi take karba ba  sai loKacinne da nayi kuka sannan shima daliline yasa yasani . The next morning idanuwana duK sun Kumbura na tashi na cigaba da ayyuKan da nasaba yi sannan naKama hanya nagama bin uban layin da naKe binshi Kullum gurin dibar ruwa .na debo na Kuma Koma gidan . girman da nakara ne yasa tadena Kwabamani fanKe ta dena soyawa sai dai ni naruka yin Komai . aiKin da naKeyi sai yakaru. Kasuwa naje na sawo Kayan hada fanKen na Kwabashi na soya sannan naKama hanya na tafi talla .na  saido fanKen naKoma gida. DuK sai nakara ramewa damuwata ta karu saboda hutun maKarantar da aKayi . ji nayi daman ba'a bamu hutun ba saboda haka naKeji duK sanda aKa  bamu hutun maKaranta saboda ni nasan wahalar da nake sha karuwa takeyi a time din . Icce   naje  nasawo na tsinci ledoji na hura wuta na daura abinci nagama . zamana inhuta Kenan sai ga inna Kande tafito daga toilet ta nufeni tayimani wani dundun da har saida nayi aman da ban shiryama yinshi ba "wuce Kitafi Ki ansomani saKo gidan barira saura Kuma Ki Kwance Ki duba wlh Kidawo inyimaKi dukan tsiya !" ta cemani afusace.