AMATULLAH

Chapter 8

by @ameerahfarouk

Inna Kande bata bari na karasa aman da naKeyi ba ahaKa ta azazzale ni da masifa tare da tureni da tayi "debo ruwa Ki wanKe amannan sannan Kitafi "tace mani . 


ruwa na debo na dauKo tsintsiya na wanKe aman sannan naKama hanya zan fita " gargadina tayi tare da nunani da danyatsan ta da tayi" ai Kinji mi nacemaKi Kada KisaKe Ki bude sakonnan na gayamaKi " 


Kai nadaga mata ina hawaye na juya natafi .na anso sokon na rukeshi ahanKali gudun Kar hannuna yayi KusKuren rukeshi da Kyau inna Kande tace nabude ta huKuntani .


isa gidan nayi tare da yin sallama nashiga ciKi inna Kande tanufeni da saurin ta tafizgi ledar sakon tayi daKi dashi .takuma kara fitowa daga daKinta ruke da wata kwarya tare da cemani" ansa wannan jeki dauraye mani ita Ki Kawomani ita yanzunnan" 


da sauri na amsa naje na wanKe mata ita naKoma namika mata . kara shiga daKin tayi takara fitowa da wani abun wanda ma ni tunda naKe bantaba ganinshi ba ma sai aranar wani irin abune wanda bansan tayaya zani iya kwatantashi ba .  ta tullomani shi  shima tare da cewa inwanKe mata shi shima inbata . 


amsa nayi nadaKe na nunama inna Kande banji tsoron shi ba amman har ga Allah naji tsoron wannan abu sosai , ahaKa kuma narukeshi sai dai ban wanKe shi ba nayi sauri na sheka mashi ruwa  saboda banji zani iya wanKe shi ba tsabar tsoronshi da naji . 


Komawa nayi namika mata  shi ta amsa da saurin ta . nidai tsaye naKe ina tunanin toh saurin na miye ne da inna taKeyi haKa ? 


"Ko mizatayi dasu?"tambayar da nayima Kaina Kenan araina ban wani damu da insani ba na cigaba da yin ayyuKana da taruka saKani inayi ba kakkautawa daga wannan sai wannan. 


Ba'a wani jimaba sai ga inna barira ta shigo gidan "salamu alaiKum aminiyata taKaina daga Ke babu wata" tafada ciKin Kwaratsinta da rashin natsuwa irin nata . 


gabana yakara faduba bayan faduwar gaban da nayi dazu da naje gidanta  " Amatullah yar albarKa anananan anata aiKi Ko? sannunKi da aiKi Allah yaimaKi albarKa " tacemani tare da Kallona da taKeyi tana murmushi ciKi ciKi . 


dagamata Kai nayi nidai na cigaba da abunda naKeyi . inna Kande tace "hmm amiya Kenan mushiga daga ciKi Ko ?" 


Suka Shiga daKin sunata faman kuskus dinsu da suKa sabayi duk time din da tazo suka shiga daki . har suKa gama ni dai bansan abunda suke cewa ba . 


fitowa suKayi atare ,na hada ido da inna Kande wata muguwar harara tayimani tare da nunamani hanyar daKi inshiga . 


shiga  nayi  daKin da saurina  ba tareda ta bude baKi tayimani magana ba . ahanKali naji inna barira tacema inna Kande " gasKiya Kande Ke ba karamar muguwa bace ba duK muguntata na saramaKi Kiga yanda yarinya Ke jin tsoronki Kamar wata dodanniya tsabar tsoron da take maKi " 


inna Kande tace "ai gwara ni baniyin Kisa da hannuna " Kwashewa da wata irin dariya inna barira tayi . naji suna banKwanan su . inna Kande ta raKata baKin Kofa tadawo ciKin gida . shiga daKinta tayi ta fitomani da kullin wanKinta ta hadani dashi . dauKar wanKin nayi na ajiyeshi abaKin toilet inda nasaba yin aiKin nahado bucKets na debi ruwa ciKin robar da Kullum sai na ciKa ta dam da ruwa . 


warware wanKin nayi sabulun wanKi karami guda daya ne nagani na cigaba da gurza shi aKayan na cigaba da wanKe Kayan .


Bansamu nagama wanKin ba sai sanda baba yadawo daga kasuwa, shanya ce ta ragemani sai jin sallamar shi nayi na amsa mashi inata jin dadi na nufeshi nayimashi sannu da zuwa  


"yawwa Amatullah sannu da aiKi " na amsa mashi da " yawwa baba " maganar da muKeyi ne da baba yasa inna Kande tafito daga daKinta babu a inda idonunta suka kai sai shanyar dake ajiye agefena.


 "daman baKi gama shanyar ba KiKa Kama wani uzurin ? maza Kafin raina yabaci Kitashi Ki fara yin shanyarnan yanzunnan " na dauka  atsorace na cigaba dayi.


 " Kaikuma malam ina abunda nace Ka sawomani ? Inna Kande ta tambayi baba . 


tsintsiyar KwaKwar da yaKe ruke da itace ya mika mata ta amsa tashiga daKi da ita  tafito da Kwaryar da tabani  nawanKe mata ciKe da wani ruwa aciKinta . 


nufar inda baba yake tsaye tayi takarasa har inda yaKe ta tsaya agabanshi tare da mika mashi kwaryar  "ansa Ka sha " baba ya amsa ba tare da yayima Inna Kande gardama ba ya sha . takuma ce mashi  yakara sha yaKuma kara shan ruwan . ta amsa kwaryar taKoma ciKin daKin, 


kara fitowa daga daKin tayi tare da cema baba " wuce Kashiga daKinKa Kada Ka kara fitowa ba tare da na baKa izini ba"shiga daKinshi baba yayi tun Kafin inna Kande ta karasa maganar da taKe yimashi ni dai inata shanya inata Kallon iKon Allah .

 
Jin shirun inna Kande yayi yawane yasa nagane tayi bacci saboda Kullum ciKin sani aiKi taKe daga wannan sai wannan .nashiga dakin baba tare da yin sallama ahankali ya amsa mani  tambayata yayi " lafiya Amatullah ?" na amsa mashi da "lafiya lau baba daman magana ce naKeso inyi daKai" 


da saurin shi  baba ya tambayeni da cewa" magana Kuma Amatullah miyasa KiKa shigo ? ai da Kinbari sai gobe sai muyi maganar Ko" dan smiling nayi kadan nace "baba nifa tambayarKa Kawai zaniyi" baba yayi dan jimm sannan yace "toh Allah yasa nasani Amatullah yi sauri Kiyi tambayarKi Kafin Kande tazo ta sameki adaKinnan.


 " tayi bacci fa baba"na cemashi ina dan yin dariya Kadan baba yace " toh shikenan ina jinKi minene tambayarKi ?" baba wai dagaske inna ba itace ta haifeni ba ?" 


Dandanan naga baba ya dago Kanshi da saurin shi ya Kalleni da Kyau sannan yace "miyasa KiKa yimani wannan tambayar ne Amatullah ?" 


amsa naba baba da cewa " ji nayi ranarnan inna barira tafada" baba yayi shiru yayi suKuKu sannan yace mani "Eh Amatullah amman KidauKa Kamar itace ta haifeKi saboda itace tarukeKi har yanzu, kinji Koh ?" 


nace "toh baba " kara tambayar baba nayi "ina mamata taKe baba ?" Kallona baba yakarayi dandanan idanuwanshi suka ciKa da Kwalla yabani amsa da cewa " nima bansani ba bansan inda taKe ba , tun Kina da wata shadaya aka nemeta aka rasa  nayi neman nayi cigiyar har nagaji Kullum ciKin tunanin ina zanga mamarKi nake har yanzu Kuma ban fidda ran ganinta ba duK da sheKarun dayawa" yafada  tare da goge hawayen shi da yayi .


nima Kaina KuKan naKeyi , muryata na rawa nakara tambayar baba" ina danginta!?" yabani amsa da cewa  "iyayenta sun rasu"



kara tambayar shi cikin muryar kuka  "to baba Kai yanuwanKa fa ?" Dandanan naga yanayin fuskarshi ta sauya ya daureta sannan yakara Kallona yana zare mani idanuwanshi tare da cemani da yayi "tashi Kibani guri!" tunda naKe da baba bai taba nunaman bacin ranshi ba sai ranar . har namike ina kokarin fita daga dakin ya dakatar dani tareda cemani "kada Ki kara yimani wannan tambayar daga yau" 


Kai nakada mashi atsorace na fita daKin nashige daKina na Kwanta inata tunanin miye nafada atambayar da nayi har yabata ma baba rai sosai har haKa ? Ko nafadi wani abunda bai dace bane ba ?" 


HaKa nayita yima Kaina tambayoyin da ni Kaina bansan amsarsu ba ahaKa na Kwana da tunanin abun araina inata mamaki.