Chapter 9
HaKa nacigaba da tunane tunane na har bacci ya daukeni .
loKacin tashina yayi inna Kande tazo ta tasheni Kamar Kullum . ta ficewarta tayi waje na bita abaya na shiga toilet nayo alwallah na tada sallah na idar da sallar na Kuma fita tsaKar gida na cigaba da yin ayyukan da nasabayi Kullum tsakar dare kamar aljana .
baba nagani yafito daga daKinshi lokacin da ake Kiran sallar asuba "baba inakwana na gaisheshi" nayi tunanin ma baba bazai amsa gaisuwata ba saboda bacin ran da nasa shi jiya . " lafiya lau Amatullah anyi sallah Koh ?" yacemani .
dadi naji araina da baba baiyi fushi dani ba . na amsa mashi da "Eh baba" yakara da cewa "toh madallah Allah ya taimaKa "tare da nufar Kofar fita da yayi " Allah yatsare sai Kadawo"nafada baba ya amsa mani da " Ameen "yafita daga gidan .
Cigaba da sharar da naKeyi nayi inata tunanin abunda yafaru jiya . natuna da aiKen da inna Kande tayimani gurin kawarta inna barira , naKuma tuna da ruwan kwaryar da taba baba yasha sannan warning din da baba yayimani sosai akan tambayar yanuwanshi da iyayenshi da nayi . gashi banga alamun unseriousness afusKar shi ba loKacin da yaKe yimani warning din bare ma indauKa wasa yaKe yimani . araina nace" ai bama muyin irin wasannan da baba "
Abun duniya duk sai yabi ya isheni gashi inaso inga yanuwana da yanuwan babana Koda mutum daya ne ciKinsu nima insan inada dangin iyaye Kamar Kowa .
gashi tunda baba ya fadamani mani cewa "mamata ta bace sai naji inaso inganta aKowane hali taKe burina Kawai ni dai inganta . naKuma yi fatan Allah yasa tana raye aduK inda take . gashi ya cemani iyayenta suma sun mutu . jiKina naji duK yamutu bani jin Karfi bani da Kuzari , ga stressing Kaina da na rukayi da tunani yasa Kaina ya dauKi ciwo sosai .
Komawa nayi daga gefen daki na zauna na dafe Kaina da hannu daya nayi tagumi da hannu daya.na cigaba da tunanin da nakeyi. Ban anKara ba sai dai saukar mari naji akumatuna ta gefe daya. Zabura nayi na mike tsaye na danne side din da inna Kande ta mareni ina kuka marar sound " shine dan lalaci irin naKi zaKi zauna baKi gama mani aiki ba koh ?" Wuce ki cigaba da ayyukan da kikeyi yanzunnan!" inna kande tacemani afusace .
Ta shiga Dakinta tafito tareda kokarin saka hijabi ajikinta " natafi gidan barira in kinga dama kigama aikinnan da wuri idan kuma kinga dama ki tsaya sakarci anan zaki yabama aya zakinta" ta fice ta bar gidan .
Kuka nacigaba dayi na dauki tsintsiya nafara shara nagama nayi wanke wanke sannan na gyara dakuna na dauko bucket din dibar ruwa da niyyar infita dibar ruwa . mantawa nayi da ban jawo gidan ba saboda saurin da nakeyi kada inna kande tadawo ta iskeni bangama abunda zanyi ba. gurin juyawa inkoma rufe gidanne yasa nayi tuntube nafadi naji ciwo ababban yatsana na kafa . zafi naji sosai amman sai na daure na mike na karasa isa kofar gidan na jawo gidan narufe na kuma dauki bucket din da yafadi ya gangara gefe nacigaba da tafiya . kafata naruka ja ahankali har saida na isa gurin dibar ruwan agajiye.
Isata kenan nasha kwana na iske banyi sa'a ba saboda uban layin da na iske ban taba samun irinshi ba sai ranar gashi sai rigima kaurayen unguwarmu suketa yi agurin . gashi ruwan gidanmu yakusa karewa saura kadan bare ma inbari sai gobe sannan indawo in diba ruwan .
araina nace "koda akwai ruwa agida nakoma ban diba ruwa ba ai yau sunana sorry" karasawa nayi nasamu nagano karshen layin nima nadasa nawa na cigaba da bin layin .
Shiru shiru layin kamar bayada niyyar karewa gashi ni ce ta karshe , ga gida da nabaro babu kowa aciki , ga inna kande bansan ranar komawarta ba dan in tatafi gidan inna barira dawowarta sai sanda aka ganta sannan . wani lokacin ta dade wani lokacin kuma ta dawo da wuri .
Addu'a nayitayi araina Allah yasa yau kada inna kande tadawo dawuri . layi kuma haka muka cigaba da binshi mukaci tsayuwarmu amman kamar ma kara mutane akeyi agurin babu cigaba ko kadan . haka nasha tsayuwata har saida wani yazo ya cemana "wlh daman kun tafi dan Nura janwuya ya zuciya ya balle kan famfon dan haka kowa ya watse "
bansan sanda nafara salati ba dan nasan yau inna kande abunda zata yimani sai yafi na kullum muni . watsewa mutane suka cigaba dayi nikuma banda kuka babu abunda nakeyi araina nace "ni shikenan yau rayuwata takare dan famfon kwara daya da yarage muna dibar ruwa dashi anzo anballe mana shi gashi babu wani gurin dibar ruwa da yake kusa ballantana inje chan in diba ta ina zani fara maganin matsalarnan toh !? Yaushe nakoma gida har naje kasuwa nasawo kayan hadin fanke na koma gida na kwaba fanken nasoya shi har naje talla na dawo ? Ni duk ba ma wannan ne yafi damuna ba , inkoma babu ruwa acikin bucket dinnan duk irin tsayuwar bin layin da nasha . ga kuma warning din da inna kande tayimani akan kada ta dawo ta iskeni bangama abunda nakeyi ba .
kukana na cigaba dayi har na isa gidan.kofar shiga gidan na ruka turawa ahankali tareda yin sallama , banga kowa ba kuma babu wanda ya amsa mani sallamar da nayi .
yar ajiyar zuciya nayi naji dadi da naga alamar inna kande bata dawo ba . tunanin ta inda zani fara samo solution na farayi .wata zuciyar tace "infara zuwa kasuwa, wata zuciyar kuma tace "Aah indai fara tunanin ta inda zani fara samo ruwan tukunna" .
Araina nace "toh koma miye zanfara yi lokaci ya ruga da yakure yanzu dolena inna kande zatazo ta sameni ban ida yin abunda zanyi ba "hakan ne yasa nayi deciding infara zuwa kasuwa insawo kayan hadin fanken insoya shi sannan inkoma kasuwar da tallar fanken, idan Allah ya taimakeni na saida shi dawuri lokacin da nadawo gidan sai insan yanda zaniyi insamo ruwan .
fita nayi daga gidan da niyyar inje kasuwa insawo kayan yin fanken "Amatullah ina zakije ne ?" Muryar inna kande ce naji tana tambayata . gabana yafadi sosai atsorace nabata amsa da cewa "bansamo ruwan ba famfon aka balle shine yanzu zanije kasuwa insawo kayan yin fanke" da saurin ta takaraso inda nake tawani fizgoni tajani mukayi cikin gida " ganin gari da kyashi zaki koya koh ? toh ba agidannan ba" inna kande tacemani afusace .
amsa nabata da cewa "wlh inna dagaske nakeyi famfon ne aka balle kizo mutafi tare in gwada maki kigani wlh ba karya nakeyi ba"mari ta kwasheni dashi ta cigaba da dukana "ni zaki yima karya ? Munafukar yarinya kawai maKira bazanije din ba "
fashewa nayi da kuka inna kande takara da cewa " wuce kitafi ki saido mani fankena kada ki kara yimani wata asarar kuma kidawo ki deboman ruwa aduk inda zakije ki nemoshi , idan kinga dama ma kije bangon duniya ki samo shi munafuka kawai" kuka na cigaba dayi nafita ina tafe ina goge hawayen dake bin fuskata raina abace .
Nagama tallar fanken nasamu na saidoshi duka nakama hanyar komawa gida , na isa gidan nashiga nayi sallama na iske inna kande zaune tsakar gida akan tabarma "bani kudin cinikin" tafada kamar yanda tasabayi kullum .
fiddo kudin nayi nabata ta amsa ta kirga nakuma shiga kitchen na ajiye bucket din fanken na dauki bucket din dibar ruwa nafita daga gidan ina tafe inata tunanin ta inda zani samo ruwa.